Kudirar Allah Book Complete

Author :  Nazeefa Sabo Nashe Category :  Read Hausa Novels

Chapter   13 / 22

36K to 39K   out of 64.9K words

ok arin kawar da waccan fuskar firgicin zuwa fuskar kamala da zata bayyana ainahin gaskiyar da zuciyarta ke ciki. Kallo ya mata irin dogon kallon nan da yake ratsa cikin ido mai sanya mutum ko yana da gaskiya ya daburce.  Ke Nene wacece ke? Zuwa yanzu na tabbatar da kina cikin hankalinki. Bakinta ne ya fara rawa kafin ta dafe kanta da take jin yana sara mata tana tsoron zuwan wannan ranar ga shi tazo mata a lokacin da bata shirya ba, me zata cewa mutumin da ya mata halacci a rayuwa? Sam bai kamata ta sake k irk irar k arya ta gaya masa a wannan lokacin ba da tasirin idanunsa ka dai zai iya jijjiga zuk ata. Umma ce ta dafa ta cike da k arfin hali ta ce  Baffa kamar bata gama dawowa daidai ba, ka bari idan ta samu nutsuwar zuciyarta na san da kanta zata maka bayani. Baffa ya yi shiru maganar Umma na masa yawo a kai ya yarda da kaso tamanin cikin zancenta sai dai wata zuciyar na k aryata duk abinda ta ce. Sai kawai ya saki ajiyar zuciya ba tare da ya furta komai ba ya fice daga sashen gaba d aya yana ji a ransa ko ba yau ba zai yi bincike da kansa. Umma ta saki ajiyar zuciya tana bin bayansa da kallo kafin ta nunawa Najee k ofar d akin Nene ta mata alamar su wuce don ita kanta yanzu hutun take buk ata hutun zuciya da na kwanya gaba d aya. Najee ta ja hannun Nenen da sauri suka shige sashenta.


****


Najma kuwa jikinta a sanyaye ta shiga d akin Mahmeey da take kwance tana barci hankalinta kwance. Najma ta ja k afafunta da suke Mata ciwo ta zauna da k yar a gefen gadon tana kiran Sunan Mahmeey a hankali. Mahmeey ta bu de idonta da kyar jin an kira sunanta daga sama. Da sauri ta tashi idanunta a bu de tana kallon Najma cikin mamaki  Ke kuma daga ina haka da sassafe? Najma ta sauke idanunta a hankali tana ji k una da rad ad in zuciyarta na sake hauhawa da gaske lamarin ya mata ciwo ga keta mutunci ga sakin aure da ma bai karb e budurcinta bane da sauk i amma yanzu duk wanda zata aura a matsayin bazawara zai aureta. Ta runtse ido tana sake jin haushin kanta da Jaheed duk lokaci guda.  Ki min magan Malama kin tasa ni gaba kina kuka. Mahmeey ta fa da cikin b acin rai. Najma ta saki ajiyar zuciya ta ce  Ya sakeni Mahmeey bayan ya cuceni ya k wace budurcina. What! Mahmeey ta fa da tana ware ido  Wani banzan zance nake ji daga bakin ki? Yanzu zuwa kika yi ya yaudareki ya k wace budurcin sannan don rashin mutunci ya sako min ke. Najma kuka ta saka mai k arfin gaske tana fa dawa jikin Mahmeeyn. Kukanta ya sake harzik a zuciyar Mahmeey ta dinga jin itama kamar ta saka kukan saboda tsananin bak in cikin da zuciyarta take ciki. Tsanar Jaheed ta sake k arfi a zuciyarta. Mik ewa ta yi da azama tana zura hijabinta wajen Baffa zata je ta gaya masa rashin mutuncin da d an gaban goshinsa ya aikata, bata san tuni Baffa ya san zancen ba.


Tana murza k ofar bedroom d in ta sameta a bu de don haka kai tsaye ta danna kanta cikin d akin, ba sabon abu bane wajen Baffa tuni ya banbance halayyar matansa ya san halin kowacce don haka ko da ya ji an danno d akin bai bu de idonsa ba don ya san Mahmeey ce. Tsaye ta yi a gaban gadon tana k arewa fuskarsa mai bayyana kasala da tashin hankali kallo.  Sai ka tashi ai, ka ji tozarcin da d an gaban goshin naka ya maka, bayan ya kusanci y ar ka sannan da safe ya aikota da saki. Wani irin murmushi na gefen baki Baffa ya saki idanunsa a lumshe ba tare da ya bu de su ba ya fara magana  Ni na saka ya saketa. Da sauri Mahmeey ta waro ido jin abinda Baffan ya ce  Kai fa kace ka saka ya saketa? To saboda me?  Saboda sakin shi ya dace da mara tarbiyyar y ar ki wacce zata iya saka wuk a a wuyan mutum da niyyar hallaka shi, kin ci sa a ma da baki tai Cesar a police station ba. Gaban Mahmeey ya fa di bata san sanda ta zauna a gefen gadon ba tana dafe k irji ta ce  Kisa fa ka ce? Me zai saka ta kashe shi? Sai dai idan hawan k awara ya mata ta ji zafi zata hallaka shi, amma ni ban yi mata hu dubar ta kashe shi ba.  Kin bata acid Ai ta watsa masa idan ba ki ce ta kashe shi ba kin ce ta nakastashi Wallahi Zainabu ki bi duniya a hankali. K irjinta ne ya shiga bugu ta mik e jikinta a kasalance ta fice daga bedroom d in tana jinjina k arfin hali irin na Najma idan ta kashe shi bata san itama kasheta za a yi ba? Hakanan ta koma b angarenta ta tasa Najma a gaba da masifa, har sai da Najman ta fa da jikinta cikin tashin hankali ta furta  To na tsane shi ne Mahmeey shi yasa.  Hakan ne ya baki Lasisin kashe shi saboda wauta, kin san idan da ya mutu kema mutuwa za ki yi ko? Rungume Mahmeeyn ta yi kawai don dole ta ja bakinta ta yi shiru jin jikin Najman ya d au zafi sosai.



______


Najee jikinta a sanyaye ta fito daga kitchen ta koma bedroom d in Umma. Haka kawai yau take jin wata irin fa duwar gaba. Umma da take zaune d auke da waya a hannunta tana neman wayar Faruk ta ji ko ya koma wajen Jaheed ta d ago tana kallonta. Jikinta a sanyaye ta zauna gefen Umman ta zauna a bakin resting chair da take kujerar Umma ta d ora hannunta akan goshinta tana furta  Me ya samu autata na ganki haka? Murmushi Najee ta yi tana lumshe idonta ta ce  My heart beats faster Umma. Shiru Umma ta yi sai yanzu maganar da Baffa ya yi ta fa do mata na aurawa Jaheed Najee da sauri ta d an janye Najee daga jikinta tana furta  Tashi Auta mu yi magana. Bugun zuciyar Najee ya sake k arfafa jin abinda Umma ta ce, a idanunta kuma ta hango ba wasa a duk abinda zai fito daga bakin ta.  Baffanki ya bada aurenki da zarar kin gama makaranta don haka ba ke ba kula kowane Namiji. Najee ji ta yi zuciyarta ta daina aiki na wuncin gadi, zufa ta fara karyo mata da k yar ta ce  Umma wa aka bawa aure na?  Jaheed Umman ta fa da idanunta na zagaye fuskar Najee ta hango wani tsantsar farin ciki da ya kasa b oyuwa a idanunta sai kuma ta ga ta runtse ido tana warasu a cikin na Umman ta ce  Me zai saka Yaya Jaheed ya aure ni bayan yana aurar Yayata.  Allah ne ya halatta masa aurenki in dai basa tare da Yayar taki, abin buk ata ki yi addu a Allah yasa hakan shine alheri a rayuwarki. Mamaki ne ya kashe Umma ganin Najee ba tayi wani bak in ciki ba sai ma tarin walwala da jin da di da ta gani tattare da ita, kamar dama jiran irin wannan ranar take. Umma murmushi kawai ta saki don ko da Najee bata fito ta fayyace sirrin zuciyarta ba a yanzu ta san da soyayyar Jaheed a zuciyarta a hankali ta furta  Allah yasa ku zamewa junanku Alheri. Najee idanunta a lumshe kawai ta amsa a zuciyarta da ameen tana sakin ajiyar zuciya wanda Umman ta ji shi har cikin ranta.


Daga haka Umma zameta ta yi a jikinta ta nufi b angaren Nene da take zaune cikin tunani da firgicin zuciya bata san wani kallo Baffa zai yiwa abin ba, shin zai mata uziri ko kuma zai k ullaceta akan b oye masa da ta yi. Turo k ofar ya sake razanata a firgice ta d ago da kanta da idanunta da Suka jigata take kallon Idanun Umma.

A k asan leb enta ta amsa sallamar wanda hakan yasa Umma bata ji ba. Ta zauna a gefen gadon tana kallon Nenen ta fara fa din  Kada ki ce zaki nunawa Baffa gaskiyar lamari a yanzu, b oye masa shine abu mafi alheri a wajena da ke baki d aya. A yanzu ki nuna masa kin dawo cikin hayyacinki amma ba zaki iya tuna rayuwarki ta baya ba, duk rintsi ki nuna masa kin manta komai, idan ba haka ba komai ma zai iya faruwa, musamman a yanzu da yake cikin bak in cikin abinda Najma ta yiwa Jaheed& . Da sauri Nenne cikin fa duwar gaba ta d ago tana duban Umma. Umman ta d aga kai  Allah ya kiyaye amma da yanzu wani labarin ake ba wannan ba, ta yi attempting soka masa wuk a shine dalilin fitar mu cikin dare afujajan amma dai da sauk i kuma Baffa a take ya d au hukunci ya raba auren don idan aka bar su nan gaba ba a san ne zata yi ba& . Da Umma ta san a wani yanayi Nene take da bata cigaba da bayani ba, idanunta ne a waje ta dafe k irjinta da yake mata matsanancin bugu, tana kallon Umman. Umma ta dafata tana furta  Bakomai fa ya samu lafiya cikin hukuncin Ubangiji bari na kira miki shi ki ji muryarsa bai san kuma kin dawo hankalinki ba ban san ya za a yi ba yanzu. Nene ta ha diye yawu da k yar tana furta tunda dai ya samu lafiya bar shi ba sai kin kira shi ba Umman Jaheed ina son in ga wani farin ciki zai yi idan ya fuskanci a yanzu ina cikin hankali na. Umma ta d aga kai tana furta  Shikkenan.


   

Bayan kwana biyu Jaheed ya ji jikinsa da sauk i duk wata azaba da yake ji ta kau daga zuciya da k irjinsa. A yanzu abu guda ke damunsa masifaffiyar sha awar da ya jangalowa kansa, bai sani ba ko don farin shiga a lamarin abinda bai tab a aikatawa bane. Da zarar ya rufe ido ba abinda yake gani sai surar Najma shi dai ya san ba sonta yake ba sai dai ya ta allak a abin da sha awa. Yau ma da sassafe ya yi wanka yana zaune ya dinga ganin kiran Khaireey a wayarsa a hankali ya kai hannu kan wayar ya d aga muryar Khaireey a d ashe sai dai ta nuna zallar farin cikin da take ciki ta ce  Jaheed ka zo Babana ya amince da auren mu, ka zo za ku yi magana da shi& & .





JIKAR NASHE
'

KUDIRAR ALLAH

16.

NAZEEFAH SABO NASHE.

08033748387.

Talla! Talla!! Talla!!!


https://chat.whatsapp.com/BARBh2begGc0KdlLEZDzhk

Ku zo ku yi sayayya tare da Yar Gidan Imam cikin aminci da kwanciyar hankali komai akwai harda kayan gyaran jiki hamshakan mata na supliments kala kala wanda ba su da illa, akwai kuma gagarumin haWin mu na Arabian sabaya powder wanda babu kamarsa wannan ba irin sabayar da ki ka saba gani bace, kayan kicin dogayen riguna kuwa ba'a magana ke dai ki yi sauri ki shigo domin kwasar roman wadannan kayan.




*************
Wani irin duuuum Jaheed ya ji a kunnensa ya kuma kasa gasgata abinda Khairyn ta ce da shi har sai da ta sake maimaitawa.  Kana ji na? Nace Abba ya amince mu auri juna Yayyansa sun shiga cikin lamarin. Sakin ajiyar zuciya ya yi ba tare da ya amsa mata ba saboda maganar zai iya cewa ta masa dirar mikiya ta ina zai fara sanar da Khairi abinda Baffa ya ce zai ha da shi aure da y arsa? Ta ina kuma a yanzu zai fara sanar da Baffa maganar auren Khairyn? Me Baffan zai d auka akan hakan? Baya son y arsa shi yasa ya kafe zai auri Khairi. Tabbas yana cikin TSAKA MAI WUYA LITTAFIN JANAFTY. Rashin amsar da zai bawa Khairi yasa ya zame wayar daga kunnensa bayan ya furta  Okay cikin sanyin muryar da Khairi bata gasgata ta Jaheed ba ce,a irin soyayyar da suke wa Juna ta zata Jaheed da zarar ya ji amincewar Abbanta zai k walla ihu da murna na tsananin farin ciki madadin haka Jaheed katse kiran ya yi yama kashe wayar gaba d aya yana sakin ajiyar zuciya. Zuciyarsa hutu take buk ata da dogon tunanin yarda zai rabu da kowa lafiya ba tare da ya sab a musu ba.

Tsawon mintuna yana kwnace ya kasa aiwatar da komai kowace shawara ya yi sai yaga bata dace a wannan gab ar ba. Don haka ba shiri ya kira wayar Faruk don shine abokinsa abokin shawararsa kuma wanda baya iya b oyewa damuwarsa a yanzu d in ma yana ganin duk shawarar da Faruk ya bashi da ita zai yi aiki tunda dai tasa zuciyar ta kasa aikin da ya kamata.


Ringing biyu ta yi Faruk ya d aga wayar kamar dama jiran kiran yake. Jaheed ya saki ajiyar zuciya ya ce  Kana ji na Faruk? Faruk ya amsa da  Yes ina jin ka. Jaheed rasa ta inda zai fara ya yi saboda shi kansa Faruk d in bai san fassarar da zai yiwa lamarin ba. Don haka kawai sai ya ce  Idan ba abinda kake don Allah ina son ganinka. Faruk ya amsa da  Ba abinda nake, on my way to your house dama right now. Daga haka ya kashe wayar.


Mintuna biyar ne suka kawo shi gidan Jaheed d in. A zaune ya same shi ya zuba hannayensa biyu a k ucninsa cikin dogon tunanin da yasa ko bu de k ofarsa bai ji ba balle shigowarsa, har sai da ya dafa kafa darsa sannan ya d ago da sauri yana sakin ajiyar zuciya. Faruk ya saki tsaki yana furta  Ban san sau nawa zan gaya maka dogon tunani illa ne ga lafiyar zuciyar ka ba. Jaheed murmushi ya sakar masa yana furta  Tunani dole ne Faruk ga wanda tunanin ya kama, ni sai na dinga ganin kamar ni ka dai duniya yake juyin waina da ni, kamar na fi kowa matsala a rayuwa. Faruk ya zauna cike da tausayin Jaheed yana furta  Kai kake ganin haka, wani yana can gefe yana sha awar taka rayuwar dafatan cewa dama shine kai. Yanzu kuma me ya faru? Wayarsa Jaheed ya d aga yana dialling numberr Khaireey. Bugu biyu ta d aga muryarta na nuna kamar fushi take da shi. Ya saka wayar a hands free yana fa din  D azu Khaireey kaina na ciwo ban ji abinda kike cewa ba, kin san na samu minor accident me kika ce? Sakin ajiyar zuciya ta yi sai yanzu zuciyarta ta yi sanyi daga zafin data d auka d azu muryarta cike da k warin gwiwa ta ce  Abba na ya ce ka turo jibi a d aura mana aure, ya yarda bayan Yayyensa da na Umma sun nuna masa rashin kyautatawar abinda aka yi da kuma tuna masa idan shine wannan k addarar ta fa da a kansa ya zai yi, a yanzu jikinsa ya yi sanyi ya kuma yi nadamar wancan hukuncin da ya yanke, da kansa ma ya ce zai zo wajen Baffa neman afuwa. Jaheed ya juya yana kallon Faruk da shima kallonsa yake yana kuma sauraran duk abinda Khaireey take fa da a cikin wayar. Jaheed ya zame wayar a kunnensa bayan ya ce da Khaireeyn  Za mu yi waya later In sha Allah, na yi bak o. Khaireey bata kawo komai a ranta ba ta ce  Okay Habibi sai na ji ka. Da shi da Faruk d in a tare suka saki ajiyar zuciya, Faruk ya ce  Wannan fa shine ana wata ga wata, ni ba ta maganar ka da Najee nake ji ba, maganar Baffa da yarda zai zo ya amince ka auri Khairey yake yarda ya d au fushi da mahaifin yarinyar nan, amma dai tunda ya ce zai je ya same shi da kansa sai ka bari mu ga yarda zata kaya, kai dai kada ka tofa taka, Allah ya zab a maka abinda ya fi alheri, ni ko d aya bana ganin laifin Khairy don yarinyar ta cancanci a jinjina mata yarda ta tsaya tsayin da ka wajen nuna maka soyayya duk da maganganu marasa da di da ta ji a kanka. Idan har ka sameta tabbas zan maka murna. Jaheed girgiza kai ya yi don ya yarda da duk abinda Faruk ya fa da, abu guda ne ba zai iya ba watsa wa Baffa k asa a ido, ko da kuwa son Khairy zai illata masa zuciya zai rungumi k addara matuk ar Baffan bai amince ba, abu na biyu zai amince ko bayan auren Khairy ya ha da da Najee ko don martaba da girman Baffan duk da a ido kallon k anwa yake wa Najee bai tab a kawar da matsayin hakan a zuciyarsa ba, bai kuma tab a yi mata wani kallo da ya wuce wannan kallon ba na Yaya da k anwa ba. A haka suka tsayar da shawarar da niyyar sai abinda Baffan ya ce su ba za su yanke shawara da kan su ba, ba kuma za su je su tari Baffan da maganar ba har sai idan shine ya tare su da maganar.




A yammacin ranar ya yi wanka tunda ya d an ji dama dama a jikinsa. Farar t.shirt

13 / 22