Kudirar Allah Book Complete

Author :  Nazeefa Sabo Nashe Category :  Read Hausa Novels

Chapter   15 / 22

42K to 45K   out of 64.9K words

irin na wannan lokacin ba. Jikinta a sanyaye ta ce  Ki yi hak uri Umma don Allah. Umman ta d aga mata kai tana furta  Hak uri na d aya ki cire wannan makauniyar soyayyar daga ranki, mazan yanzu sun aureki suna tsananin son ki ma ya aka cika balle ke ce kika nuna mai tar son sa a fili, ki zama mai aji na gaya miki. Najee ta d aga kai, tana sake jaddada kalmar hak urinta. Ta kuma k udirta a ranta daga ranar zata dage da addu a Allah ya bata ikon rage son Jaheed a zuciyarta.




________


Kashegari an idar da Sallahr Juma a su Najma da Nasma na zaune a falon Mahmeey ta babbar loud speaker da ke cikin gidan suka dinga jin sanarwar d aurin aure basu damu ba. Saboda girman masallacin duk sati yawanci ana d aura aure a masallacin don haka ba su mayar da hankali wajen saurarar su wa za a d aurawa aure ba. Sai da Najma ta ji ance an d aura auren Muhammad Mujaheed da amaryarsa Ummul Khaieey. Zan iya cewa wata irin wuta Najma ta dinga gani a idanunta kunnuwanta suka d auke na wuncin gadi. Ta mik e da sauri idanu waje tana kallon Nasma ta ce  Ba dai Jaheed aka d aurawa aure ba? Cikin
Mamaki Nasma ta ce  Idan ma shine ina ruwanki Najma? Da kike neman sakawa kan ki damuwa? Ta girgiza kanta tana furta  Ba zaki gane ba Nasma, taimaka min ki je cikin gida ki jiyo min gaskiyar zance. Nasma tsaki ta ja tana mik ewa ta shige d akin Mahmeey tana furta  Da alama wani abu ya shiga kan ki, bari na sanar da Mahmeey. Mahmeey ta d ago tana kallon Nasma bayan jin abinda ta ce ta yi tsaki kafin ta mik e ta fita parlourn. A zaune suka tarar da Najma duk ta hargitse gashin kanta. Mahmeey tsaki ta zabga mata ta ce  Kina hauka ne Najma? Wani irin abu ne wannan? Jaheed d in da aka d aurawa aure shine kika sakawa kanki damuwa? Son sa kika fara yi? To idan ma son sa kika fara yi ki zare maza maza don ba zan tab a bari ki koma gidan matsiyacin can ba, balle ma y ar uwarki Ubanki ya basa sai ki d auke hankalinki daga kansa. Wani irin bugu zuciyarta ta buga da k arfin gaske a fili ta furta  Najee kuma? Sai ta hau yamutsa gashin kanta. Mahmeey baki ta bu de tana kallonta da mamakinta kamar wacce Jaheed ya yiwa asiri me take shirin gani haka? Ta zauna tana dafata a hankali ta ce  Najma juyo ki gaya min menene a ranki game da wancan banzan d an mahaukaciyar? Najma ta runtse idonta da k arfin gaske tana furta  Son sa nake Mahmeey son sa zai illata min zuciya tun bayan rabuwar mu kullum da matsanancin tunaninsa da kewarsa nake kwana, wallahi ina son sa.. kafin ta rufe bakinta Mahmeey ta zabga mata wasu irin maruka masu zafin gaske tana huci ta furta  Ashe kuwa lokacin mutuwarki ya zo, don ko zaki mutu ba zaki komawa auren wancan banzan yaron ba d an mahaukaciya mara asali da tushe& &  Najma ta runtse idonta a fili ta furta  Wallahi Ina son sa Mahmeey I love him so much& ..



JIKAR NASHE
'

Saura 3pages shafukan bati su k are hanzarta biyan naki, don jin wace waina za a toya a masarautar gabas idan Najee ta je shin zata samo silar cikin Jaheed da Hassan d in sa? Ko kuma tata k addarar zata gamu da ita? Duka yana cikin wancan tafiyar biya 500 kacal a asusun banki kamar haka. 2118666253 UBA. Sai ki tura shaidar biya 08033748387.


Special people 1k kacal. Sai na ji ku.


KUDIRAR ALLAH

18.


NAZEEFAH SABO NASHE.


08033748387.



________________


Wani irin kallo Mahmeey ta zuba mata, mai cike da nuna zallar takaici kafin ta zabga tsaki ta ce  Tunda kina son sa Ai sai ki bi sa, shashashar yarinya kawai. Daga haka ta wuce ta bar ta anan zaune hannunta cikin tulin sumar kanta tana ja a hankali kamar wata mahaukaciya sabon kamu. Da gaske ita kanta gani take kamar sihiri aka mata, ta yaya mutumin da ta tsana a rayuwa zai koma mata masoyin da take jin ba zata iya rayuwa ba idan ba shi? Hawaye ne suka cigaba da mata sintiri a fuska. Cikin rashin nutsuwar jiki da ta ruhi ta mik e a hankali zuwa cikin d akinta. Windown d akin ta yaye tana hango tarin Mutanen da Jaheed ya kasa b oyuwa a cikinsu. Gaba d aya ya fi so kyau da cikar zati. Yanzu shikkenan ta rasa shi? Murmushinsa kawai take hangowa ta windown da alama yana cikin tsananin farin cikin da ya kasa b oyuwa. Haushi da tsananin kishin sa ne suka shiga kama mata zuciya ta kife kanta a saman windown tana sakin ajiyar zuciya a hankali take furta  Why? Me yasa zuciyata? Me yasa ? Baki min adalci ba. Ta share hawayen ha de da jan wayarta kai tsaye ta shiga Instagram searching sunansa ta yi abinda bata tab a kwatanta yi ba. Mamaki ya kamata ganin yarda yake da tarin followers fin million d aya. Ashe Jaheed celebrity ne bata sani ba? Ta shiga comments d insa inda ya yi posting wani pic d insa da ya yi masifar kyau ba zata manta ba pic d in da sallah ya yi shi don ta tuna sanda ya saka shaddar, gani ta yi y an mata suna ta furta wow! Wow! A comment majority sun kasa hak uri har da masu cewa check your dm sir. Da sauri ta wurgar da wayar ta kifa kanta a pillow ta saki kuka mai ratsa zuciya.

******

Jaheed kuwa zan iya cewa farin ciki da yake ciki a ranar ji yake ba na biyunsa, don haka cikin fara a da yalwar murmushi yake amsa gaisuwar abokansa. Haka aka gama hotuna abokan su ka watse bayan Faruk ya sanar musu gobe akwai kai amarya Suna buk atar su zo su musu kara. Sai sannan suka samu damar shiga cikin gida shi da Faruk. Najwa da take tsaye a parlourn ta k i d ago da kanta balle ta kalleshi don wani irin haushinsa take ji da kishi mai zafin gaske. Nene kanta ba wani fara a take ba don ta ita da ba a fara d aura wannan auren ba. Umma ce kawai ta tareshi da fara a tana fa din  Ma sha Allah Jaheed ango. Ya d an sunne kai yana murmushi, ta gefen ido ya ke hangen Najee da ta k i juyowa ta kalleshi. Bai mata magana ba, Umma ta masa fatan alheri kafin ta kalli Nene ta ce  Saura ke Nene ban ji kin ce komai ba?  Allah ya yi albarka shine kawai abidna zan ce. Umma ta saki murmushi tana fa din  A haka ma mu ne da godiya.  Najee Jaheed ya fa da a hankali ta d ago da k yar tana kallonsa kafin ta ha diye abinda take ji a ranta da k yar ta furta  Congratulations Ya. Jaheed. Ya lumshe idonsa yana furta  Thanks Najee, Allah ya nuna mana namu. Ta d auke kanta ba tare da ta amsa ba, sai Nene ce ta masa da saurinta tana fa din  Ameen, ranar kuwa da na yi rawa da juyi. Dariya sosai Umma da Jaheed har ma da Faruk suka yi. Haka suka zauna ana ta hira har Baffa ma ya shigo aka cigaba da hirar da shi. Yana sake jaddadawa Jaheed hakkokin da suka rataya a kansa a matsayin sa na Miji, idan kuma ya zalunci matarsa ya sani tabbas sai Allah ya saka mata. Jaheed ya amsa kansa a k asa idan bai manta ba irin waccan nasihar da Baffa ya masa ce wancan satin da za a kai masa Najma sai ga shi still yana maimaita masa tabbas Baffa ya ci ya amsa sunan Nagartaccen Mutum dattijon k warai.




******


Bayan sati guda& ..


Jaheed da amaryar sa suka d aga Qatar bayan sun yiwa y an uwa sallama cike da kewar juna suka bar ahalinsu zuwa wata k asar. Najma hankalinta ya tashi sosai da sosai ta rasa nutsuwarta sosai take son Jaheed a yanzu da ta tabbatar ya mata nasiha.


Lokacin ana saura sati guda azimi. Baffa ya fara shirin tafiya Umara da yake duk shekara yawanci a can yake aziminsa, kowace shekara kuma akwai matar da yake tafiya da ita. Wannan zuwan sai ya fa da kan Mahmeey. Don haka a daren da zai yi tafiya ya tara duka ahalinsa kamar yarda ya saba. Ya musu nasiha da su ji tsoron Allah musamman idan baya nan, su tuna duk abidna za su yi Allah na kallonsu. Kowa ya amsa a lokacin wata dabara ta fa dowa Umma a zuciya da sauri ta kalli Baffan yana shirin raba musu ku di kamar yarda ya saba, ta ce  Baffa ina neman alfarma don Allah. Ya juyo yana maida hankalinsa gareta  Ina jin ki. Ta gyara zamanta tana furta  Dama cewa zan yi tunda ana hutun makaranta don Allah Najma zata Bauchi wajen Hajiya Inna hutu ita da Nene zan aika saboda su d ebe mata kewa ka san jikin tsufa. Ya juya yana nazarinta baya jin shakkar tura Najma wajen Hajiya Inna don ya san Macece mai nagarta da sanin ya kamata, Yayar Umman ce amma kallon Uwa yake mata don ita ta rik e Umman har ta ba shi aurenta. Har ta fitar da rai zai yarda sai kuma ta ji ya ce  Kwana nawa za su yi? Kin san ban fiye son y a mace da barin gida ba, don Ma dai Hajja Inna ce da kai tsaye zan ce a a Cikin fara a Umma ta ce  Ko ana gobe Sallah sai su dawo. Ya girgiza kai yana furta  Kada su wuce haka, idan sun shirya sai Habu Driver ya kai su. Umma ta shiga godiya cikin farin ciki.


Kashegari kuwa da sassafe Baffa da Mahmeey suka wuce Makka, Bayan Baffan yasa su Najma da Nasma sun ha de kayansu kaf sun koma b angaren Umma don kula da tarbiyyarsu.

Sai da ta gama komai sannan ta shiga d akin Nenen. A saman sallaya ta sameta na azkar bayan ta idar da Sallahr walaha. Ta zauna a gefen gadon tana fa din Allah ya amsa mana dai Nene. Ameen Nene ta ce tana nazarin fuskar Umman da alama akwai abinda yake tafe da ita.  Yaushe za mu tafi Bauchin da na ji kina gayawa Baffa? Umma tana murmushi ta ce  Ba bauchi za ku ba Nene, GARIN GABAS za ku ke da Najee&  wani irin waro ido Nene ta yi tana kallonta murya na rawa ta ce  GARIN GABAS kuma?
Umma ta d aga kai cike da gasgata wa ta ce  Yanzu nake son mu fara wannan yak in na gano silar samuwar cikin Jaheed da d an uwansa, Najee ba zata iya ita ka dai ba, ni kuma shekaru Uku ina tunanin sun yi nisa don haka zaku tafi tare ki taimaka mata bayan kun yi Basajan Kamanninku. Nene hankalinta tashe take kallon Umma Sam bata gano wasa a icon Umman ba, da gaske abinda yake zuciyarta kenan. Ta saki ajiyar zuciya a hankali muryarta a raunane ta ce  Ina jin tsoron Umman Yara, wallahi ina tsoron shiga masarautar nan. Umma ta dubeta duk da tana jin tausayin yanayin da ta ganta bai hanata murtiske tsoron nata ba ta ce  Wannan shine lokacin da ya dace ku je Nene, zamanki anan d in ba tare da kin san me can yake ciki ba ina ga sam ba mafita ba ce, ki je can ku yi fito na fito da koma waye ya yi silar shigar Ki cikin matsalar nan. Najwa tana da wayo kuma tana da kaifin basira da hankali fiye da ta wani babban don haka na tabbata zata taimaka miki, zan nuna muku abubuwan da zaku yi Basaja da su a jikin ku da fatarku ta yarda duk bala in mutum ba zai gane ku ba In sha Allah har sai mun cimma mafita. Nene ta saki ajiyar zuciya tana d aga kanta a hankali duk da tana jin tsoron har a lokacin sai maganar Umma ta k arfafa mata gwiwa, ita da kanta ta san zamanta a nan d in bai da wata ma ana zuwa can d in ta fuskanci k alubalen shine abinda ya kamaceta, don haka ta amince da shawarar Umma d ari bisa d ari ta kuma samu k warin gwiwa a tattare da ita.  Yaushe za mu tafi? Ta ce tana kallon Umma. Umma ta saki ajiyar zuciya tana jin murnar nasarar da ta samu a kan Nene ta amincewarta ta ce  Jibi In sha Allah, sai dai ina so ki kiyaye kin san dai ban gayawa Baffa inda za ku ba, ita kanta Hajja yanzu sai na kirata na rok eta kada ta sanar da Baffa inda kuka je, Nene bana son a samu matsala don ke da kan ki kin san Baffa mutum ne mai kafaffen ra ayi don haka ki kiyaye. Nene ta d aga kai tana furta  In sha Allah. Umma ta mik e ta fice daga d akin.

A d akinta ta zaunar da Najee ta gaya mata dukkan shirinsu. Haka kawai sai Najee ta ji gabanta na matsanancin bugu. Da sauri ta kalli Umma ta ce  Umma da ni kuma za a? Umma ta d aga kai tana nazarin y ar tata da ta bayyana dukkan tsoronta ga lamarin. Don son ta k arfafeta sai ta ce  Da ke za a je Najwa ina ji a jikina zaki iya don kina da kaifin basira da hangen nesa, In sha Allah kuma ba abinda zai faru. Najwa ta d an lumshe idonta tana amsawa a hankali. Tana kallon Umman ta fice daga d akinta ta barta cikin yanayi na bugun zuciya da ma rauninta gaba d aya da ba zata iya cewa ga sababinsu ba.



Shirye shirye suka kankama Umma ta musu duk wani tanadi da za su buk ata a can. Kafin ta samo wani abu da za su shafa a jikinsu kalar jikinsu ta dawo bak a na lokaci ka dan idan kuma suka wanke shikkenan. Hak oran roba aka sakawa Najwa da zai b oye duk wani kamanninta sai ta zama irin mutanen nan masu Gatso yanayin shigarsu ya yi kama da na mutanen nan da ake kira bararoji. Sun dai nuna alamun suna cikin wahala matuk a ainun. Da Asussuba suka yi wannan shirin Umma ta kira Faruk ta sanar da shi komai. Ta kuma umarceshi ya kai su har cikin garin Gabas d in ya tabbata sun shiga cikin masarautar kafin barowarsa garin. Duk da Faruk ya ji tsoro shima a farko amma da Umma ta bayyana masa dalilinta sai ya ji tsoron ya kau, ya samu k warin gwiwa suka tafi ya saka location na sunan garin a wayarsa abinka da Zamani nan da nan waya ta nuna masa hanyar da zata sada shi da Babban garin Gabas d in. Umma ta musu fatan alheri ta juya gida don bata amince Driver ya kai su ba, zuciyatta ta fi aminta da Faruk ta san idan Faruk ne bata yarda za a yi Baffa ya san inda suka je sab anin Driver da zai iya gayawa wani k arshe har sirrin da ba sa so ya bayyana a zo a sani ta shiga uku wajen Baffa.




_________MASARAUTAR GABAS& &



Tunda suka iso cikin garin gaban Nene da na Najwa bai daina fa duwa ba. Shi kansa Faruk haka kawai ya ji nasa gaban yana fa duwa. Ya dai yi addu a ya bar abin a ransa. Yana kallon Nene ta mudubi ya ce  Yanzu ya za ayi ku samu shiga gidan Sarautar nan, don daga gani akwai matakan tsaro a gidan. Nene ta bi gidan da kallo gaba d aya fasalin da ta san shi ya canja, banda ma an rubuta Masarautar Gabas bai zama lallai ta amince shi ba ne. Saboda yarda ginin ya zama na Zamani mai matuk ar kyau da burge mai kallonsa. Ta saki ajiyar zuciya tana furta  Shine abin tambaya Faruk, ni kai na ban san ta yarda za mu shiga gidan sarautar nan ba, asalima Wallahi tsoro nake ji& 






JIKAR NASHE
'
KUDIRAR ALLAH..


19.


NAZEEFAH SABO NASHE

08033748387.


Faruk ya saki ajiyar zuciya a hankali Kafin ya furta Ina zuwa. Ya fita daga motar cikin takun nutsuwarsa ya isa bakin babbar k ofar mai tambarin sarauta. Babban gate ne mai girman gaske kalar ruwan gold. Tun daga nesa zaka hango tsaruwarsa da girmansa kamar Anan aka dasa shi. Daga ganinsa mutanen da suke bakin gate d in suka taso suna masa wani duba. Faruk ya samo nutsuwar dole ya sakawa fuskarsa duk da k ok arin zuciyarsa na son tona masa asiri. Hannu ya mik a wa wanda ya fara zuwa wajensa d in. Bak in mutum ne dogo sosai mai siffar samudawa. Sai da ya  dan yi Jim kafin ya mik awa Faruk hannu yana furta  Bawan Allah me ke tafe da kai? In dai Sarki kake son gani gwara ma ka juya yau bai sanar mana zai ga kowa ba, don shirye shirye na din Yarima wanda zai gaji sarki bayan mutuwar sa ake saboda haka bai da damar ganin kowa. Faruk ya saki ajiyar zuciya yana furta  Kamar ka san abinda ya kawo ni kenan, yanzu idan zan ga Sarkin ta

15 / 22