Kudirar Allah Book Complete

Author :  Nazeefa Sabo Nashe Category :  Read Hausa Novels

Chapter   18 / 22

51K to 54K   out of 64.9K words

1 ya kusa k arewa idan kina son Book 2 ki biya 500 kacal ta wannan asusun 2118666253 UBA. Kai tsaye sai ki tura shaidar biya ta wannan numberr 08033748387. Kada a yi babu ke yanzu aka fara badak alar da dukkan da din littafin na gaba. Baa fara komai ba akwai rantsatstsiyar soyayya mai gigita kwanya bayan zafaffiyar k iyayya. Ki siya ki karanta ina tabbatar miki ba zaki yi nadama ba.


KUDIRAR ALLAH

22.

08033748387.

NAZEEFAH SABO NASHE
'


________________



Sunan da ta ambata na Murad sai ya tsaya mata a mak oshi sakamakon dakushewar da muryarta ta yi, sai kuma a lokacin ta ankara da wautar da ta so tafkawa. Da sauri ta runtse idonta bugun zuciyarta na sake hauhawa kamar yarda na Murad yake yi ba tare da ya san na menene ba. Bai ji sautin sunan ba don haka bai san ta kira shi ba ba ma shiba duk wanda yake d akin bai jin ba illa Najwa da ta gane abinda Nenen ta furta idanu ta fito da su waje tana fatan Allah yasa Murad d in bai fahimci abinda Nenen take nufi da bata san me za su ce su wanke kan su ba. Addu arta ta karb u ganin yarda fuskar Murad d in ta nuna bai san abinda Nenen ta ce ba. Ta saki ajiyar zuciya mai k arfin gaske wanda ya ja hankalin jama ar wajen kanta. Da sauri ta gyara zamanta tana k ok arin daidaita hak oran roban da suke bakinta wanda ta kasa sabawa da su har yanzu dalilin girman da suka yi wa bakinta ga gatson dole da suka sakata ga bak in da aka shafa mata mai kamar shuni don haka ta yi muni ba na wasa ba dole Murad ya tsani kallonta. Idanu ya zuba mata jin ajiyar zuciyar da ta yi mai nauyin gaske harara ya zuba mata ka dan kafin ya mayar da kallonsa kan Nene yana karantar yanayinta ya d an furzar da hucin numfashi yana furta  Dafatan dai ba matsala? Nene ta lumshe idonta tana jin d igar hawaye akan k uncinta kasa amsa masa ta yi da bakinta don ta san idan ta ce eeh ma k arya take don haka ta d aga kai. Ya d an yi luuu da idanunsa alamun gajiya na sake bayyana a cikin idanun nasa ya d aga mata hannu yana furta  Allah ya bada lafiya. Sannan ya fara tafiya da baya da baya still idanunsa cikin na Nene da ta kasa janye idanun akan sa. Murmushi kawai ya sakar mata ya juya da sauri don ficewa daga d akin bayan ya sake furta Witch! Ganin kallon da ta bi shi da shi, Allah sarki Najwa bai san ita ba kallon komai take masa sai na mamakin yarda yake kama da Jaheed.
Karo Suka kusa yi da Mammansa Fulani Saddika data shigo d akin ita da fadawanta da ma aikatan jinyar da suka rakota. Ko ba a fa da ba dama ta san yana asibitin tun shigowarta jin yarda k amshinsa ya kara de asibitin, mamaki ya kamata ganin Murad da kansa yau ya zo dubiya asibitin ta bi shi da kallo.  Kai kuma fa? Me ka zo yi ko ciwon kan ne ya matsa maka? Duk da ta san da wuya yazo asibitin ganin likita saboda yana da special Doctor d insa da yake gani a Nigeria in dai ciwon bai yi zafi ba, idan kuwa ya yi zafi ya gwammace ya tsallaka k asar masu jajayen kunnuwa a duba shi tunda dama a can ya fi kauri. Lumshe idanunsa ya yi kafin ya girgiza kai a hankali yarda ita ka dai zata ji ya ce  Na zo ne kawai na duba patient d in ki. Mamma ta ware ido tana furta  Are you sure? Ya d aga kai yana murmushi kafin ya fice da sassarfa yana d aga mata hannu. Mamma ta bi bayansa da kallo tana mamakin abinda ya ce Lallai patient d inta ta ci a kirata mai sa a tunda har Murad ya tako ya zo dubata. Ta jinjina lamarin kafin ta saki ajiyar zuciya itama ta shiga d akin don duba patient d in. Idanunta a lumshe ta tarar da ita duk ba barci take ba sai son bawa zuciya nutsuwa daga zuzzurfan tunanin da yake damalmala kwanyarta. Sallamar da ta ji ne yasa ta ta bu de idanunta tana kallon Fulani Saddik a gabanta ya fa di don ko a maye take kamannin Fulanin ba zai b ace mata ba, Mace Adala kenan mai nagartattun halaye da ake kira ta fisu kaf ta fi matan sarki. Da ace bata b atar da nata kamannin ba ta hanyar Basaja da tsaf Fulanin zata shaida ta don sun yi zaman mutunci da ita kusan itace nagartacciyar baiwarta wacce ta amince ta san duk wani sirrinta. Sai dai a yanzu kam ba zata shaida ta ba ba don nata kamannin sun canja ba sai don canjin da aka musu na dole don gudun kada a ganesu. Fulani ta zuba mata ido kafin murya da sanyi ta ce  Sannu da jiki baiwar Allah, dafatan dai kina samun sauk i. Nene ta d aga kai tana k ak alo nata murmushin da kai tsaye za a kira na dole.  Yi magana mana baiwar Allah ba dai matsala ko? Murya a sanyaye ta furta  Alhamdulillah na samu sauk i. Fulani ta saki murmushi tana furta  Ma sha Allah, haka ake so. Sai magana ta gaba a ina za a samu danginku a sanar musu don naga kamar k aramar y ar taki ba zata iya jinyarki ba, tunda an ce jininki ya hau kina buk atar hutu sosai. Najwa gabanta ne ya fa di su ka ha da ido da Nene da itama take kallonta da sauri ta d an girgizawa Nene kai. Murya a sanyaye Nene ta ce  Garin mu da nisa Hajiya, Kuma ko Anje can d in ba mu da kowa bamu da wanda zai iya jinyata ki bar ni da yarinyata zata iya komai. Fulani ta juya tana kallon Najwa kafin ta jijjiga kai ta ce  Ya sunanki? Da sauri Najee ta furta  Sunana Ladidi. Fulani ta  d aga kai tana furta  Ladidi Ai ba sunan gaskiya bane, sunanki na gaskiya nake son ji. Najwa ta ja ajiyar numfashi kafin ta ce  Hadiza nake. Fulani ta d aga kai tana furta  Ai kuwa sunanki yafi k arfin furtawa ga duk wani mazaunin Fadar nan sai dai mu dinga kiranki Ladidin. Sabida sunan mai Babban d aki ne Mahaifiyar Sarkin Gabas. Najwa ta saki murmushi kawai wanda gatsonta ya sake bayyana. A zuciyar Fulani ta jaddada munin Najwa ga bak i kamar mutanen South Africa.  Shikkenan ko mu zamu tafi, zan saka a dinga kawo muku abinci idan an kawo muku abincin sai ku dinga fa da musu idan kuna son wani abu kafin a sallameku mu ga abinda Allah zai yi. Nene ta d aga kai tana furta  Mun gode Allah ya k ara girma da d aukaka ya tsare gabanki da bayanki.  Ameen Fulani ta fa da a hankali ta juya tana kallon Najwa ta ce  Ladidi Zan aiko da kaya don Allah ki cire na jikinki ki yi wanka ko kya yi kyan gani. Najwa ta d aga kai tana sakin murmushin da ko ka dan bai mata kyau ba, sai ma muni da ya k ara mata. Sai da suka fita sannan ta kalli Nene Suka saki dariya a tare. Najwa ta ce  Wai Nenne muni na yi ne sosai? Nene dariya ta yi sosai ta ce  Ai Najwa don baki ga yarda kika koma ba ki je ki ga mudubi a toilet. Da sauri Najwa ta mik e ta shiga toilet d in. Ware ido ta yi kafin ta saki dariya ganin yarda fuskarta ta yi dole duk wanda ya kalleta ya ji bata burge shi ba ashe shi yasa Murad ya ce mata Witch. Ta ha diye yawu da k yar saboda haushin Sunan da ya kirata da shi sai yanzu ta tuna ma anar Witch Mayya! Haushin Murad ta ji sosai a ranta kafin ta fito daga toilet d in tana sakin dariya tace  Cab Nene haka na koma Blacky! Nene ta saki murmushi tana furta  Kamar ba Kyakykyawar Najee d in Jaheed ba. Kunya ce ta kama Najee tana hasasota matsayin matar Jaheed sai kuma nan da nan kishi da jin haushin matarsa ya rufeta, ko sai yaushe za a kirata da Matar Jaheed? Ta tambayi kanta, sam bata san maganar ta fito fili ba Nene ta saki dariya tana furta  In sha Allah shekara I war haka kin amsa wannan sunan haka za a yi auren ko baki gama makaranta ba. Da sauri Najwa ta rufe fuskarta fahimtar da ta yi Nene ta ji zancen da take da zuciyarta. Nene ta saki murmushi kawai tana jin a ranta kamar itama ta janyo wannan lokacin tana burin ha da jini da Baffa da Umma salihar mace mai nagartuwar halayya.





_____________


Cikin toilet d in take tsaye tana aman da ya k i tsaya mata, ya zame mata jiki duk safiya sai ta yi shi kamar masifa ga shi kore sharr. Jiri ne yake d iban ta da k yar ta fara k ok arin dafa bango don fitowa daga bathroom d in. Sai ga Umman Najee nan ta shigo da d an hanzari idanunta akan Najma da ta wani d ashe ta yi fari tas ga rama ta yi ba ta wasa ba. Bata mata magana ba ta kamata suka fita zuwa d aki, a bakin gadon ta zaunar da ita tana furta  Yau kam duk kafiyarki sai mun je asibiti, wannan ciwon ya isheni ina dalili? Kin ga yarda kika dawo kuwa kamar mai yaron ciki? Daga ita har Umma sai da zuciyarsu ta buga da k arfin gaske suka zubawa juna ido kowa da tunanin da yake cin ransa. Umma nata fargabar kada dai magana Najma ta d auko musu, don ita bata san Jaheed ya kusanceta ba, ita kuwa Najma addu a take dafatan Allah yasa cikin Jaheed ne a jikin ta ko wannan ya yi dalilin da zai saka ya dawo ya saurareta. Ido Umma ta zuba mata duk da ba likita bace ita amma yawan shekarun da ta yi tana rainon ciki da haifeshi ya ci ace ta fuskanci ciki. Ta sake ajiyar zuciya kafin ta mik e ta zaro hijab tana mik a mata  Tashi mu tafi tun yanzu. Najma ba yarda ta iya ta mik e jikinta ba k wari ta bi bayan Umman suka fita falo Umman na rik e da hannunta zuciyarta na bugun jin tsoron tabbatuwar tunaninta.




____


Fulani Raheena kuwa tun bayan komawarta gida zuciyarta ta kasa nutsuwa da maganganun Baffan Gwandu da suke hasasho mata fallasuwar nata sirrin data tone ta zuba shi a cikin k asa sai dai a yau tana tunanin akwai wanda ya kusa tono shi. Ya aka yi matsalar da take ciki ta yi kamanceceniya da ta Baffan Gwandu? Su waye wa dannan mutanen da suke wasa da hankalinsu a da ta zata nata hankalin ita ka dai ake watangaririya da shi ashe har da na jama a da yawa a cikin a masarautar nan? Ya zama dole ta gano su waye idan ma Jinnu ne su dole su ba???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?yyana don wannan karan komai zai faru sai dai ya faru akan tonuwar b aragurbin k wan da zai addabi jama ar da ke ciki da wajen masarautar Gabas. Bata da hannu a cikin samuwar cikin Murad tata matsalar ta daban ce ta kuma zarce matsalar da Sarki yake ciki ta samuwar cikin Murad da rashin sanin wacece mahaifiyarsa duka wannan mai sauk i ce akan tata. Ta zauna a gefen gado dab as bayan ta lalubo sirrintaccen layin wayarta ta saka a wata k aramar waya ta daban. Bugu biyu numberr ya shiga kamar yarda ta tsammata waccan kaurararriyar muryarce ta yi magana bayan sakin dariyar da ta kusa saka Fulani yin fitsari a wando.  Tunanin ki ya baki daidai mowar sarki, b aragurbin k wanki ya kusa fashewa idan kuma ya fashe zai addabi masarautar gabas, hanya d aya ce ki gaggauta saka Murad ya auri y arki kamar yarda muka gaya miki itace zata mana ajalinsa shi kuma Mukhtar ki bar mu da shi ya kusa barin duniya ma gaba d aya.  Me yasa zaku ce sai ya auri k anwata alhali kun san sarai a matsayin y kuma ina son na san ko ku su waye? Me yasa kuka saka ni a cikin wancan gagarumar matsalar?  Saboda kin cancanci shiga matsalar sakamakon zalamarki da kika nuna na son haihuwar Magajin sarki wannan shine hujja mun baki abinda kike so kema ya zama dole ki mana abinda muke so daga gobe muke so ki fara aiwatar da k udirinki na ha da Murad aure da k anwarki sanin ko mu su waye Kuma ba zai amfaneki da komai ba, idan lokacin sani ya yi da kan ki zaki sani. Daga haka suka kashe wayar. Fulani ta bi wayar da kallo kafin ta saki ajiyar zuciya hawayen nadama na sauka a idanunta da alama dai ta kusa tashi a tutar babu idan kuwa haka ne ya zama dole ta saka Murad ya auri K anwarta in dai hakan shi zai saka ta samu cikar burinta.




       -


Nene ta mik e tana kallon Najwa har zata ambaci sunanta sai kuma ta yi murmushi ta furta  Ladidi burin mu ya cika na shigowa masarautar Gabas abu guda ya rage mana samun hanyar da zamu shiga ainahin cikin masarautar don samo wancan rufaffen sirrin, ina jin tsoro Najwa bana son a sheganta min y ay a banda haka da tuni na bayyana kai na a matsayin Mahaifiyar Muraad& & .
Turo k ofar da aka yi da k arfi ne yasa Nene yin shiru da zancen tana d aga idonta tana kallon mai tahowar k amshin turaren sa yana dukar hancinsu idanunsa ya zube a kan Nene fuskarsa na nuna alamun duk ya gama jin abinda suka ce, hantar cikin Najwa ta juya har kana iya juyo k ararta ita kuwa Nene suman zaune ta yi tana k ok arin saita numfashinta da ya kusa d aukewa& & .. ya cigaba da shiga cikin d akin cikin takun isa Fulani Saddik a na bayansa& & ..



Ku min afuwa ciwon kai ne ya tasa ni gaba kwana biyu amma dai da sauk i sosai Alhamdulillah


KUDIRAR ALLAH.



23.


08033748387.




NAZEEFAH SABO NASHE.
'


_________________


Alhamdulillah na ji sauk i ina godiya Anty Hadiza Sodangi abisa kulawarki gareni, na yi addu a kuma an dace, Rabbi ya saka miki da mafificiyar Aljanna ya raya miki zuri a akan tafarkin shiriya.


______________


Nene wani irin ha diyar yawu take wanda bata shiryawa zuwansa a wannan lokacin ba, zufa ta gama jik a ta ta ko ina duk da sanyin a.c d in da take cikin d akin. Kallo d aya zaka musu ka tabbatar da rashin gaskiya a tare da su musamman Najwa da ta kasa kallonsu. Fulani Saddik a wani murmushi ta saki bayan ta kalli Murad ta tabbatar shi bai ji abinda ta ji ba saboda airpods d in da ke kunnensa yana amsa waya. Ta juya tana kallon Nene kallo mai bayyana tuhuma sai dai ta danne abin a ranta ta ce  Ya jikin naki? Nene da ta kusa sakin fitsari a wando ta d aga mata kai cikin raunin murya ta ce  Alhamdulillah Fulanin ta ce  Ma sha Allah Ai daga gani jiki ya yi kyau shi yasa ma likitocin suka sanar min sun baki sallama, to sakamakon maganar da na ji kuna yi jiya na rashin wajen zama sai na yanke shawarar tafiya da ku can wajena kafin a samu mahallin saka ku. Murad ya bu de ido yana kallonta  Wajenki Mamma? Ta d aga kai cike da gamsarwa ta ce  Ba su da inda ya kamata su zauna fiye da wajen nawa, zan saka a cigita gida idan komai ya lafa sai su koma can a yanzu dai kam can ne ya kama ce su. Shiru ya yi banda yana tausayin Uwar ba yarda za a yi ya yarda Mamma ta d auki wannan mummunar yarinyar ta kai gidanta, amma haka kawai yake da feeling na tausayi akan Babarta don haka sai ya share ya d an tab e baki ha de da ware hannu yana furta  As you wished Mamma Allah ya bada lada. Daga haka ya juya ya bar d akin dama sam bai san me yasa ya biyo Mamman ma. Suka bi bayansa da kallo har Mamman kafin ta juyo da kanta tana kallon Nene irin kallon k urilla mai cike da son tabbatar da zarginta, sai dai a ilimi irin nata ta yi k ok ari k warai da gaske ta b oye mamakin jin maganar ta nuna musu gaba d aya ma bata ji abinda suka ce ba.  Ku taso mu tafi amma bana buk atar komai kawai ku taho zallar ku ka dai nake buk ata. Nene ta saki ajiyar zuciya tana mik ewa jikinta cike da kasala zuciyarta na sake sanar da ita tabbas Fulani ta ji maganar nan kawai sharewa ta yi ta nuna bata ji, sai itama ta daure kawai ta ha diye nata k udirin. Suka bi Fulanin inda hadimanta suke bakin k ofa suna jiranta.



A sashen Fulanin motoci biyun Suka yi Parkin Fulani ta fita kafin ta umarcesu su ma su fito. Jikinsu na rawa suka fito Nene tana bin wajen da kallo, wajen dai fulanin ne dai da ta sani sai dai an yi renovating d insa

18 / 22