Kudirar Allah Book Complete

Author :  Nazeefa Sabo Nashe Category :  Read Hausa Novels

Chapter   19 / 22

54K to 57K   out of 64.9K words

ya zama wani irin gini mai kyawun gaske. Ta dinga bin wajen da kallo tana tunano zamanin baya Lokacin k uruciyarta kafin k addara mai girma ta yi facali da wancan farin cikin da take ciki. Hanyar sassan bayi take bi da ido zuciyarsa na bugu da k arfi tsoro take ji sosai bata son a ce ta rasa iyayenta kamar yarda zuciyarta take hasasho mata. Fulani Saddik a ta juyo idanunta cikin na Nene tana sake nazarin fuskarta duk zarginta yana son tabbata daga ganin yanayin idanuwan Nenen ta san abinda duk take tunani zai iya zama gaskiya. Bata mata magana ba illa wucewa da ta yi tana nawa hadimanta umarnin su kai su Nenen wani keb antaccen d aki inda take ajiye manyan bak in da bata son su yi nisa da ita. A sashenta d akin yake cikin babban parlourn ta. Hadimanta suka bita da kallo suna mamakin abinda ta ce don ko su suna iya k irga sau nawa k afafunsu suka shiga cikin d akin balle a kai wa dannan yamutsatstsun mutanen da ko kyan kama ba su da ita. Sai dai basu da hurumi ba kuma su isa su tambayi Fulanin dalilinta ba don haka suka ja baki suka shiru tare da bin umarnin Fulanin kai tsaye, bayan sun wurgi su Nenen da wani kallon banza na raini. Nene ta saki murmushi kawai don ta san hassada ce irin ta d an Adam da ba ya iya b oyewa.


Babban d aki ne mai girman gaske mai d auke da wani faffa dan gado da ya sha filillika irin dai shimfi da gidan sarauta. Sai zabga wani irin k amshi yake na turaren wuta da na Humrar d aki. K asansa malale yake da carpet mai taushin gaske.  Nan ne d akin sai a kiyaye banda k auyanci, ni Wallahi ban san me ya sa Fulani tayi shawarar kawo ku nan ba.  Me yasa ba zaki je ki tambayi Fulanin dalili ba? Najwa ta fa da fuskarta a ha de cikin jin haushi da tsanar halayyar wasu mutanen masu wulak anta mutum tun basu san irin girman da Allah ya masa ba, ji fa a rashin sani bata san Nene b ace Uwar Murad amma ji abinda take gaya mata.  Kada ki min rashin kunya yarinya ji da munin da Allah ya baki da Uban hak oranki. Ta fa da tana hararar Najwan. Najwa ta bu de baki zata yi magana Nene ta dakatar da ita.  Barta Najwa akwai ranar mayar da magana ba yanzu ba. Sai da ta harari Nenen sannan suka yi tsaki suka fita bak in cikinsu guda basa son Fulanin ta kawo wanda zai maye gurbinsu tunda sun saba yi mata almundahana da hainci akan duk wasu abubuwanta. Suna fita Najwa ta ce  Amma Nene me yasa kika dakatar da ni baki bar ni na ci Ubansu ba. Nene ta saki murmushi tana furta ba yanzu ba Najee akwai lokaci. Suka mayar da kansu kan sake kallon d akin duk da arziki ba bak on su bane amma d akin nan ya tafi da duk hankalinsu. Najee ta  Dane gadon har da tsalle tana murmushi ta ce  Na d ane gadon Uwar Sarkin Gabas, Nene Allah ya nuna mana ranar da zasu san ke ce Mahaifiyar Sarkin Gabas daga kan wad annan barorin zan fara rashin mutunci, Nene har shi fa Murad d in ba zan k yaleshi ba sai na rama kallon hadarin kajin da yake min. Nene murmushi kawai ta saki kafin ta furta  Ai dole Najeen Nene ni kaina sai na tayaki rama wa don ina kallon idanunsa da hararar da yake zabga miki, don yaga an canja miki kamanni Bai san Najee na ko larabawa albarka ba wajen kyau sai dai a nuna mata hasken fata don ko gashi ba su fiki ba, tun yanzu ma kenan ina ga nan gaba mak erin y an mata ya k ere min ke za a ga cikakkiyar mace mai cikakkiyar sura ta nunawa a jarida. Najee murmushi ta saki tana sunkuyar da kai. Kafin ta ce  Da gaske Nene ni kyakykyawa ce? Amma ana cewa su Yaya Nasma sun fi ni kyau. Nene ta girgiza kai  Ko ka dan sun dai fi ki hasken fata amma zallar kyau da dirin jiki Ai Najee na ba baya bace"  farin ciki ya lullub e Najwa kafin ta mik e ta shiga toilet don yin wanka sai kuma gata ta fito a guje Nene ta kalleta tace  Lafiya? A hankali don kada kowa ya ji ta ce  Nene idan na yi wankan abinda zan shafa kamar fa mun bar shi a asibiti. Nene ta saka hannu a aljihunta ta zaro robar mai d auke da bak in abin ta mik a mata  Ban manta ba Najee, ta ya zan manta da abinda shine rufin asirin mu.
Suka saka dariya gaba d aya.
Najee ta ce  Wallahi Nene d azu na tsorata na fa zata Sun ji abinda muke fa da. Nene ta saki murmushi kawai ba tare da ta ce komai ba. Najee ta sake cewa  Yanzu da sun je abinda muka ce me za mu ce da su?  Ba abinda za ku ce sai dai Zan yi murna sosai idan har ya tabbata hasashen da nake haka yake. Suka tsinkayi muryarta daga sama tana shigowa cikin k asaitacciyar shigar da take bayyana kasancewarta Fulanin Sarki ta yi kyau sosai kamar ba yanzu suka rabu da ita ba har ta sake fesa wani wankan sai zabga k amshi take. Fuskarta d auke da murmushi ta shigo cikin taku d aid aya. Ita ka dai ce ba hadiman nata, hannunta janye da wata babbar trolley. Sak suka yi suna kallonta fusakrsu d auke da tsoro da razani har ma da firgita gaba d aya. Murmushin bai bar saman fuskarta ba ta samu waje daf da Nene a bakin gadon ta zauna.  Tun asibiti na ji duk abinda kuke fa da. Ta sake tsunduma su cikin mamaki  Mafarki na ya tabbatar na bayyanuwar Mahaifiyar Murad burin da na da de ina son cika shi a rayuwata sai ga shi yazo min a lokacin da ban tsammata ba, wata zuciyar na ce min k arya kuke amma wata zuciyar na k arfafa ni akan tabbas ke d in ke ce Mahaifiyar Murad da ta d au cikinsa ta kuma haife shi. Ta fa da tana nuna Nene da ta yi mutuwar zaune don yanzu lamarin ya zarce suman zaune gaba d aya bata fahimtar komai, razanar da zuciyarta take ciki ta zarce dukkan tunanin mai karatu, bata san a wata fuska Fulani zata dubeta ba, shin zata taimaketa ne ko kuwa itama da nata burin? Idan har taimakonta zata yi me yasa tun a lokacin bata sanar da Murad abinda kunnuwanta suka jiye mata ba? Me yasa ta zab i ta b oye masa? Alhali abin murna ne da farin ciki yau a ce yaga mahaifiyarsa?

 Na san zaki yi mamakin dalilin da yasa na b oyewa Murad kasantuwarki mahaifiyarsa, Ina da nawa Burin da kuma shara din da sai kin min alk awarin zaki cika shi sannan zan taimaka miki cika naki burin, kafin nan ina so ku yi wanka ku ci abinci ku huta sosai zan zo mu yi magana, idan kin fahimci ki d ora kan ki akan turbar zaman lafiya, rashin fahimta ta kuwa yana nufin abubuwa da dama&  Daga haka ta mik e har a lokacin dai idanunta akan Nene tana sakar mata murmushin da Nenen ta kasa fassara shi, bata san a matsayin da zata ajiye k ayataccen murmushin nata ba, Me fulani take nufi? Shine tambayar da ta cika zuciyarta har ta hanata katab us tana kallo Fulanin ta fice daga d akin bayan ta d aga mata hannu tana furta  Na baku Awanni hu du zan dawo, kafin nan ina son na jaddada miki bana son k arya a duk zancen da zaki gaya min, sannan kuma bana son mutum mai sab a alk awari idan na sameki da d aya daga cikin wa dannan akwai hukunci mai tsananin gaske ciki kuwa har da b atar da ke daga sararin duniyar nan& & .. Daga haka ta fice da sauri bayan ta ja musu k ofar da k arfin gaske. Bugun k ofar ya yi daidai da bugun zuciyar Nene da k arfin gaske. Ta dafe wajen tana jan Hasbunallah a hankali, Ba abinda ta fahimta a zancen fulanin da ya zarce itama akwai nata b oyayyen k udirin& Ta kalli Najee da take tsaye itama kamar statue ta kafawa Nenen ido cike da nata tsoron da fargabar.  Zama bai gan mu ba Najee na lura itama da tata manufar ya zama dole mu bar gidan nan a yau d in nan kafin komai ma ya faru. Najee ta ware ido ita da kanta ta amince da abinda Nenen ta ce don haka ta fasa shiga wankan da ta yi niyya suka fara tunanin ta hanyar da zasu bi su tsere daga gidan nan ba tare da Fulani ta gan su ba.  Ki lek a Parlour idan kin ga wa dannan marasa mutuncin bayin ki kira min su. Najee ta d aga kai tana lek a parlourn cikin sa a kuwa sai ta gansu. Murya k asa k asa ta ce su je in ji Nene don Allah. Da dai kamar ba za su je ba, sai suka tuna mahimmancin su a wajen Fulani don haka suka bi bayanta. A tsaye suka ga Nenen tana ganinsu ta saki ajiyar zuciya.  Yauwa don Allah taimako zaku mana, ku nuna mana hanyar da zata fitar da mu mu kan mu bama son zaman gidan nan. Kallon kallo Suka shiga yi wa juna kafin su saki murmushi su girgiza kai  Fulani ta ce ko Parlour kada a bar ku ku fita har sai idan ita ta bada izini. Nene da Najee suka zaro ido& ..




Mhmmmmmmn! Baki biya ba ko har yanzu? Book one ya kusa zuwa k arshe ki biya d ari biyar kacal don samun kashi na biyu. Tura ta asusu kamar haka 2118666253 UBA sai ki tura shaidar biya ta number kamar haka 08033748387. Gundarin zak in labarin cike da zazzafar k iyayya da soyayya suna gaba. >?p?




JIKAR NASHE
'

KUDIRAR ALLAH

24.


08033748387.
NAZEEFAH SABO NASHE.


______________


Fargabar Nene ta sake k aruwa jin abinda Hadiman Suka furta, da alama kuma ko mai za su ce musu ba zasu bar su su fita ba, umarnin mahaifiyarsu za su bi. Don haka ma bata rok esu ba ta ja hannun Najwa kawai suka zauna suna kallo Hadiman Suka fita suna dariya k asa k asa, da alama sun hango mugunta Fulanin ta shirya musu. Najwa ta kalli Nene tana sakin ajiyar zuciya ta furta  Mun ga ta kan mu Nene wai me matar nan take shirya mana ne?  Alheri In sha Allah. Nene ta furta duk da zuciyarta tana taraddadi akan amsar da ta bawa Najeen. Tsawon sa oi suna zaune a haka suka daure suka yi wanka suka kuma samu kaya a kayan da Fulanin ta kawo musu cike da akwati duka dogayen riguna ne free sizes don haka duk suka musu daidai. Fuskarsu suka sake shafa mata shuni. Abinci ka dan suka tsakura saboda fargabar da zuciyarsu take ciki. Suna zaune shiru cikin taraddadi Fulani ta sake danno kai cikin d akin, k amshin dadda adan turarenta ne ya sa suka san itace. A hankali ta sauke idanunta cikin nasu, wannan karan ba wannan yalwataccen murmushin, fuskarta a ha de take sosai kamar bata tab a dariya ba. Ta bi kwanukan da kallo kafin ta furta  Dafatan kun ci abinci? Don maganar da za mu yi tana buk atar nutsuwa. Da sauri Nene ta d aga kai. Ta dubi Najee da idanunta duk suka duba ru dewa dariya ta so saki sai dai ta yi k ok ari k warai da gaske wajen ganin ta danne dariyar.  Wannan y ar ki ce? Ta fa da tana duban Fulani  Bana son amsar k arya a duk tambayar da zan yi. Da sauri Nene ta girgiza kai  Ba y ata ba ce, amma bata banbanci da y ar tawa.  Amsa guda cal na fi buk ata. Fulani ta fa da tana d aga yatsunta guda  Bana buk atar kwan gaba kwan baya. Nene ta saki ajiyar zuciya kafin murya a k asa ta ce  Ba y ata ba ce.  Na sani Fulani ta fa da tana sake tamke fuskarta kafin ta saki wani guntun murmushi da ya tsaya iya kan leb enta kawai.  Sunanta Na gaskiya Najwa y ar ga Alhaji Mai fata. Wannan karan gaba d aya sai da cikinsu ya hautsina da k arfin gaske suka dubi Fulanin da kyau da tunanin ko ba ita bace wani Aljannun ne ya yi Basaja da kamanninta.  Kuna mamakin yarda aka yi na sani ne? Shiru ba amsa illa ha diyar yawu da suka yi da saurin gaske.  Na san komai, tun bayan da na ji abinda kuka fa da a asibiti na yi duk wani bincike na sirri a kan ku, aka kuma gaya min ko ku su waye, da gaske ke ce Mahaifiyar Murad da d an uwansa Mujaheed da kika sake haifa bayan barinki gidan nan, abu guda da ban sani ba akan ki aka kuma k i sanar da ni shine ta yarda aka yi y ay an Sarki suka wanzu a cikin ki? Ina so na sani shin Murad da  dan uwansa y an halak ne kamar yarda aka rubuta a takardar da aka tsinci Murad d in da ita idan d an halak ne ya ya aka yi ya zama halastaccen alhali ba a d aura muku aure da Sarki ba, baya ga haka ta yaya kika tara da Sarki har kika samu cikinsu da mu Matan Sarkin muka kasa samu? shine abinda nake son na sani, Bana son k arya kin san yana daga cikin shara di na. Nene ta sunkuyar da kanta tsoron Fulani ya gama mama ye dukka zuciyarta wace irin mace ce ita? Ko dai tana aiki da Jinnu?  Yi min magana bamu da lokacin b atawa. Fulani ta fa da idanunta na kallon can wani gefe.  Wallahi ban san ta yarda aka yi cikinsu ya shiga jikina ba abu guda na sani wata rana& & .


Nan Nene ta shiga bata labarin abinda ta sani. Kafin ta gama Fulanin ta ware ido tana kallonta cikin al ajabi, wannan wani irin abu ne? Ta yaya za a fahimci wanene wanda ya shirya dukka wannan kitimurmurar? Bata nuna komai akan fuskarta ba ta bar tashin hankalin a cikin zuciyarta ta dawo da kallonta kan Nene tana furta.  Ni na raini Murad tun daga jarirantaka har yanzu, ni na san halinsa ciki da bai ina son sa fiye da son da nakewa duk wata halitta abayan k asa ciki kuwa har da Ubansa, ina son ki min alfarma kada ki sanar da kowa wannan zancen zan kuma tayaki bincike a hankali har zuwa sanda zamu cimma burinmu, zaki iya tantance k amshin turaren da kika ce shi ka dai ne abinda zaki shaida daga wa dancan mutanen? Nene ta d aga kai ko a yanzu na ji turaren nan ba abinda zai saka na kasa gane shi saboda sanin da na masa.  Alhamdulillah Fulani ta fa da cikin kwanciyar hankali  In sha Allah asirin duk wanda ya ha da wannan kitimurmurar ya kusa tonuwa. Ki kwantar da hankalinki ba Zan cuceki ba wallahi zan daraja ki a matsayin wacce ta haifa min sanyin idaniya a duniya zan baki dukka kulawa amma idan kin bani ha din kai. Nene ta d aga kai cike da gamsuwa Fulani ta dubi Najwa tana dariya  Ladidi ko Najwa? Najee itama dariyar ta yi tana furta  Duk wanda kika kira Ranki ya da de. Murmushi ta yi tana dafata ta furta  Ki zauna a Ladidinki bana son kuma ki goge wannan bak in painting da yake fuskarki Don Allah har zuwa sanda zan cimma buri na. Najee ta d aga kai tana sakin murmushi a hankali. Fulani ta mik e tana duba agogonta  Bari na bar ku ku huta zuciyarku ta samu nutsuwwa don na san d azu na tsorata ku. Ta fa da tana dariya suma dariyar suka yi suna tunanin yanayin da suka kasance a d azun don tsabar firgita da razana ba inda baya rawa a jikinsu.




________***

Su Umma da Najma kuwa suna zuwa wajen likitan bayan duk wasu gwaje gwaje likita ya tabbatar da shigar ciki sati hu du cif. A tsorace Umma ta dinga kallon Najma tana furta  Ciki kuma? Sai ta ha diye maganarta ta mik e tana yi wa Doctorn godiya kafin ta ja Hannun Najma suka fice daga asibitin.  Jaheed ya kusanceki ne? Umma ta fa da a motar bayan ta tayar da niyyar fara driving. Kunya ce ta rufafwa Najma ta sunkuyar da kanta kawai tana wasa da yatsun hannunta. Umma kallo guda ta mata ta tabbatar da amsar tambayar ta sai ta saki ajiyar zuciya tana fa din  Alhamdulillah! Hakan yanzu zai nuna miki girman k addarar Ubangiji ga Bawa, na san k addarar cikin nan ce ta kai Jaheed ga kusantarki ga shi nan kina d auke da jikan mahaukaciya a cikin ki, Ya zaki yi da wancan k iyayyar da kike masa, tunda Allah ya nuna miki ikonsa. Shi yasa ba a son bawa ya zurfafa k iyayyarsa ga abu don wata rana mak iyi kan zama masoyi. Shiru Najma

19 / 22