Kudirar Allah Book Complete

Author :  Nazeefa Sabo Nashe Category :  Read Hausa Novels

Chapter   3 / 22

6K to 9K   out of 64.9K words

in ta bi shi da kallo murmushin kan fuskarta na sake yalwata ta ce  Ka dawo kenan Mujaheed? Shi d in ma murmushin da kai tsaye za a kira na k arfin hali ya saki yana d aga mata kai kafin ya rusuna ya gaisheta. Ta amsa masa cike da kulawa saboda yarda take jin Jaheed d in kamar ita ta durk usa ta haifesa bata banbance soyayyar sa da ta nata y ay an data tsuguna ta haifesu abu d aya ta sani Ba ita ta yi nak udarsa da shayar da shi amma duk wata hidima da Uwa take wa d anta ita ta yiwa Jaheed, shayarwa ce dai a hakan a haukar Uwarsa ita ta shayar da shi, abin mamaki yarda take ba shi kulawa ba zaka ce k wak walwarta da motsi ba duk da akwai wani keb antaccen sirri da ita ka dai ce ta sani.

Jaheed ya dubi Najwa yana fa din  Najee samo min ruwa. Da sauri ta mik e don a rayuwarta tana girmama lamarin Jaheed da kuma duk wata hidima data danganceshi, yarda take son sa bata jin tana son nata jinin haka. Ruwan mai sanyi ta d auko a fridge d in da yake dinning area d in Umma. Ta kawo masa a k aramin tray. Bai bi ta kan cup d in da take mik a masa ba ya b alle murfin ruwan ya fara kwankwa da. Sai da ya shanye tas kamar ruwan ne zai tafi da bak in cikin da ya masa dafifi a zuciyarsa sannan ya ajiye robar yana sakin huci a hankali. Umma murmushi ta saki ganin yarda yake wayancewa wajen son kawar da b acin ran da ya kasa b oyuwa a fuskarsa ba duk da k ok arin danne shi da yake. Ta fi kowa sanin Jaheed da halayensa kaf idan yana cikin farin ciki ta sani kamar yarda idan yana cikin b acin rai duk k ok arin sa da son danne b acin ra??????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????????nsa hakan baya b oyuwa gareta a k wayar idanunsa take banbance halin da yake ciki, don haka cikin raunin murya ta dubeshi tana furta  Sun ce ka turo ko? Da sauri Jaheed ya d ago yana kallonta cikin mamakin jin abinda ta ce, ya yi mamaki k warai da gaske da har ta gano abinda yake ciki, kamar ya ce mata ya aka yi kika gane sai dai ya ja bakinsa ya tsuke yana duban T.V ha de da  d aga kai a hankali muryarsa ta kasa b oye b acin ran da yake ciki saboda yarda ta raunana ya ce  Sun ce Umma. Sakin ajiyar zuciya ta yi tana furta  Kada ka damu wannan karan za a dace In sha Allah, abin buk ata ka dage da addu a. Shiru ya yi yana jin sauk in nauyin da k irjinsa ya yi, kalamin Ummansa ya sauk ak a masa fargabar sa da b acin ransa. Umma ta dubi Najwa ta ce  Je ki zubo masa abinci daga ganin wannan idon kana jin yunwa. Murmushi ya saki a hankali yana jin dad in kulawar da Umma take ba shi har yanzu ganinsa take kamar yaro, ko don bai yi aure bane oho, ko kuma tausayawa irin rayuwar da ya taso a ciki take shine bai sani ba.  Ka ci abinci ka je ka samu Nene ka gaya mata. Ya
D aya kai kawai yana mamakin duk sanda irin wannan zata faru sai Umman ta umarceshi da ya gayawa mahaifiyarsa ta kan ce  Ko kallonka ta yi bata maka addu a ba zai da da da maka balle idan ka furta addu ar itama zata maimaita Allah kuma Zai amsa In sha Allah. Jaheed murmushi kawai ya saki yana amsar Abincin da Najwa ta zubo masa a plate ganin favorite food d insa ne Alkubus da miyar taushe yasa ya saki murmushi gefe guda kuma kunun aya ne. Zamewa ya yi ya zauna a kan carpet don yafi ganewa ya ci abinci k afar sa a tank washe kuma yafi cin abinci da hannu idan ba a bak on waje ba shi yasa sau tari yafi ganewa cin abinci a falon Umma inda zai bararraje ya tsoma hannunsa ya ci son ransa. Ya wanke hannun A wash hand basin da yake dinning area d in sannan ya dawo ya fara cin abincin yana fa din  Madalla da Umman mu mai da din tuwo. Murmushi Umma ta yi ta ce  Ka hango Alkhbus ba dole Ai ka fara
santi, dama sai kacewa Khairin ta dage ta iya Alkubus mayensa zata aura. Murmushi ya saki a zuciyarsa yana fatan Allah ya amsa addu ar Umma yau ya gan shi ga shi ga Khairi a gida d aya matsayin ma aurata da yafi kowa murna a duniya don ya tabbata a ranar ba na biyunsa wajen farin ciki, bai san kuma irin godiyar da zai wa Allah ba gani yake ko kwana ya yi yana sallah godiyar ta yi ka dan. Sai da ya cinye abincin tas ya kuma taune tantak washin sannan ya yi Hamdala yana duban Najwa da take kallonsa k asa k asa, haka kawai Jaheed yake burgeta duk wani abu da ya yi burgeta yake yi, sau tari tana hasasho Mijin da zata aura ya zama mai halaye kamanni da komai irin na Jaheed, tun kan ta san ba d an uwanta bane da suke ciki d aya balle yanzu data fara girma sai take auna Jaheed d in a matsayin Mijin aurenta tun bayan data san ba maharraminta bane. Jaheed ya dubeta yana furta  Zo ki kwashe kwanukan nan, kullum
Baki da aiki sai kallo ya kamata Umma ta fara saka ki aiki Wallahi kada ki tashi baki iya komai ba. D an mitsitsin bakinta ta turo kafin cikin shagwab a ta ce  Kai Ya Jaheed Wallahi ina aiki yau fa ni na yi alkubus d in nan. Wani irin waro ido ya yi yana kallonta ba Najwa ba hatta Umma sai da ya sata dariya yana furta  Lie Lie ya mik e kafin ya kai mata rank washi a kai ya ce  Mai k arya dai d an wuta. Ta dubi Umma tana furta  Umma gaya masa don Allah ba ni na yi ba? Umma tana murmushi ta ce  Gobe ya tsaya ki yi a gabansa sai ya tabbatar. Girgiza kai ya yi yana fa din  Ah to kin dace tunda kin gado hannun Umma. Ya fad a yana tura k ofar da zata kai shi Inda parlorn Nenensa yake. Najwa zata bi shi Umma ta saka baki ta kirata sau tari ita take hanata binsa musamman a irin wannan lokacin da yake matuk ar buk atar d umin mahaifiyarsa ko dai bata magantu ba idan ya gaya mata damuwarsa Zai ji sauk i cikin k irjinsa, don haka ta hanata bin sa Najwan ta dawo tana turo bakinta gaba na jin haushin rashin binsa duk da sonta da hakan don tana son kullum ta dinga ganin Nenen musamman idan suna tare da Jaheed sai ta dinga jin wani irin farin ciki data kan rasa dalili.



A zaune ya tarar da ita tsaf da ita cikin shigar doguwar rigar atamfa jikinta sanye da hijab kamar kullum. Ba abinda zai da ka gane tana hauka sai idanunta idan ta zazzaro maka su sai kuma yanayin yarda take mayar maka da maganar da duk ka furta sai ta maimaita maka kamar mai karatu. Tana ganinsa ta d ago a fisge tana kallonsa fuskarta na d an sakin murmushi ka dan mai bayyana matsayin ta na mahaukaciya. Jaheed murmushi ya saki ya zauna a gefenta kamar yarda ya saba yana kama hannuwanta ya matsa su ka dan ya ce  Yau Nene ba kya kallo? Sake maimaita masa abinda ya ce ta yi. Jaheed ya saki ajiyar zuciya yana fatan ranar da Ummansa zata samu waraka ko Zata fa di inda asalinta da danginta suke ko da wannan ya tsira zai gode wa Allah idan ma bai samu dangin mahaifin nasa ba, fiye da yanzu da bai san kowa nasa ba yake watagangaririya a rayuwa. Idanu ya sauke cikin na Nenen data kafa masa nata idon kamar mai son gano wani abu a cikin idon nasa. Shiru zuwa wani lokaci suna kallon kallo kafin Jaheed ya sauke nasa idon yana furta  Ki yi min addu a Nene sun ce na turo. Ta sake maimaita abinda ya ce Jaheed ya d ago yana kallonta yana mamakin yanayin damuwa da ya gani tattare da ita kamar yarda ta saba a duk sanda zai zo mata da makamanciyar magana irin wannan mamakin hakan yake sosai tunda ya san bata da hankalin da Zata dinga feeling farin ciki ko bak in ciki a cikin ranta, bai san me yake janyo mata wannan yanayin ba mai bayyana zallar damuwar da take ciki. Idan ba idanunsa ne ya gaya masa ba har tarin k walla ya gano kwance cikin k wayar idanunta. Bai ji komai a ransa ba tunda ya san Nenen ba abinda ta sani irin maimaita magana na ta salon haukan kenan da tun tashinsa a haka ya santa.  Allah ya baka abinda kake so Jaheed Allah yasa su baka aurenta Jaheed. Hakan kuwa da yake so ta furta hakan ta maimaita masa ya saki murmushi har lotsawar hab arsa tana sake k aruwa, itama murmushin ta saki tata lotsawar hab ar na sake bayyyana wanda wannan ne kawai abinda suke kamanceceniya da shi banda haka ba ta inda Jaheed yake kama da ita komansu mabanbanci ne. Kwanciya ya yi a cinyarta yana sakin ajiyar zuciya a hankali kafin ya d au hannun Nenen ya saka a kansa a duk sanda yake cikin damuwa wannan d in yana dag cikin abinda yake kawar masa da Rabin damuwarsa. Nenen ta shiga yamutsa masa Sumar kansa tsawon lokaci kafin ya d ago yana mayar da k wallar idanunsa da suke zuba ba shiri, a gaban Nene kawai yake iya sakar k wallarsa ta zuba bai damu ba banda haka ba wanda zai ce ya san k wallarsa tun bayan girmansa sai Nenne da yake iya bayyana rauninsa kai tsaye a wajenta. Bai juyo ya kalleta ba da itama zai ga tata k wallar da take zuba ba k akkautawa saka kansa kawai ya yi ya fice daga d akin. Sai da ya tsaya a corridor ya kawar da duk wata fuska ta damuwa sannan ya saka glass d in idanunsa bak i wuluk don bata son Umma taga idanun da suka canja sannan ya fice da sauri ya ji da di sosai da bai samu Umman da Najee a babban parlourn ba.



Yana fita Nene ta kifa kanta tana wani irin kuka mai tsuma zuciya, kukan tausayin Jaheed yake da yarda da sanin ta ta b oye masa waye shi? Sannan ta d auki haukan k arya ta d orawa kanta duk don gudun kada a tambayeta asalinta da na Jaheed d in. Tana tausayin d anta kamar yarda sau tari zuciyarta take son ta bayyana masa asalinsa sai dai tsoron bala in da sanin asalin nasa zai haifar yana togaceta daga aikata hakan, zamanta a matsayin mahaukaciya da rashin sanin asalin Jaheed shi ya fiye musu alheri daga ita har Jaheed d in fiye da bayyanar gaskiyar lamarin, tabbas abinda ta b oye shine alheri garesu gaba d aya daga ita har duk wani masoyin ta. Da sauri ta mik e tana dannawa k ofar d akin mukulli kafin ta juyo ta fa da toilet da azama ta d auro alwala. Tana fitowa sallaya ta shimfi da ta fuskanci alk ibla cikin nutsuwa ta tada sallah. Rako i da yawa ta yi kafin cikin sujjadar k arshe ta fashe da kuka tana furta  Ya Allah ka zama gatanmu ni da Jaheed a rayuwa, Allah ka bashi mata ta gari ka gajarta masa wahalar rayuwar neman aure.



To fa! Wai me Nenne take b oyewa ne? Menene asalin Jaheed da rashin bayyana hakan yafi alheri garesu fiye da bayyana hakan? Daga ji dai kun san tafiyar mai zafi ce akwai rikita rikita ta gasken gaske yanzu aka fara. Shin kin biya kuwa 500 kacal dai kada ta gagareki hajiya a yi wannan tafiyar ba ke. Kai tsaya ki biya ta asusun banki kamar haka 2118666253 UBA

Sai ki tura shaidar biya ta wannan numberr 08033748387.


Vip 1k (Za a tura musu kai tsaye har gida.)


Nagode sosai


JIKAR NASHE CE
'


K UDIRAR ALLAH.


3.


NAZEEFAH SABO NASHE.

08033748387.




___________


Doguwar addu a Nene ta ja sosai kafin ta d ago kanta a hankali idanunta na zubar da k walla, ta mik e zuwa gefen gadon. Zuciyarta take jin tana harba mata da sauri tuno abinda ya wakana a rayuwarta wanda girman k addarar zata iya cewa ya wuce duk tunanin mai tunani.


Zugum ta yi a gefen gadon hannayenta dafe da k uncinta, tana nazarin yarda rayuwa take gudu kamar yau ta zo gidan da jaririnta Jaheed a hannu ga shi har ya girma ana maganar aurensa ba tare da Ubansa ya san da cikinsa ba balle ya san da shi. To ta ina zai san da shi bayan ita kanta ba zata ce ga fuskar Uban ba, bata tab a saninsa ba balle ta san sanda ya kusanceta abu guda ta sani cikin nasa ne kamar yarda ta ji a bakin wasu mutane da ba zata ce su waye ba. Ta lumshe ido zuciyarta na cigaba da dukan tara-tara ko sunan Mutumin ta tuna sai ta ji tashin hankalinta ya hauhawa balle kai tsaye ta danganta shi da Uban Jaheed. Motsin da ta ji yana kusanto d akinta ne ya sata saurin mayar da fuskar haukanta ta yarda ba zaka tab a zaton ita d in mai hankali ba ce. Najwa ce ta shigo da kwanon abincinta
Na dare flask mai kyau d an madaidaici sai dogon jug da aka zubo mata kunun aya a ciki. Murmushi take sakar mata da alama shak uwa a tsakaninsu ta zauna daf da ita tana furta  Allah yasa dai Nene ta yi sallah? Maimaita maganar Najwan ta yi ha de da waftar kwanon hannunta kai tsaye ta fara cin abincin cikin alamu na rashin nutsuwa. Najwa tana kallonta ta wafce kwanon
Kafin cikin kwanciyar murya ta ce  Baki fa da ba? Itama ta maimaita Najwa ta ce Bismillahirrahmanirraheem. Itama ta maimaita sannan Najwan ta mik a mata kwanon abincin bayan ta saka ta wanke hannunta a y ar robar da ta shigo da ita.
Sosai ta ci abincin kafin ta sha kunun ayar. Najwa ta kunna mata kallo suka zauna suna kallon sau tari a irin wannan lokacin Najwa ce take zame mata abokiyar hira yarinyar ta d auko nagarta da kyawun halayen iyayenta. Bata raina na gaba da ita sam sab anin su Najma. Suna zaune suna kallon Najwa na tsefe mata kanta.


5?l?5?l?~~Kamar yarda Haidar ya yi alk awari bayan an idar da Sallahr magriba da kansa ya ja Jaheed zuwa wajen Baffa don gaya masa ance Jaheed d in ya turo. Shiru Baffa ya yi bayan jin mai ya kawo su, tashin hankalin da yake zuciyarsa bai b uya a kan fuskarsa ba duk da k ok arin aikata hakan da ya yi. Har wata zufa ce take zubo masa. Shiru ya bak unci wajen kowa da nazarin da yake a ransa. B angaren Jaheed tausayin kansa ne ya kama shi ganin kamar ba zai nasara ba a yarda alamun Baffan Suka nuna. Tsawon mintuna kafin Baffa ya d ago yana sakin ajiyar zuciya ya ce  Za a je In sha Allah, Ina fatan wannan karan ya zamo na k arshe da zamu je neman aure idan ba su baka ba In sha Allah a cikin zuri ata zan baka Mata. Gaban Jaheed ya wani irin bugawa tsoro ya d an shige shi ba don komai ba sai don ya san tunda Baffa ya ce haka ba kowa yake nufi a cikin zuri artasa ba sai Najma ko Nasma su ne y an mata Najwa bata isa aure ba idan kuwa haka ne akwai babbar matsala shin Baffa bai san tsanar da yaran suka masa bane, ba kuma sa ganinsa da gashi sai dai zai ji kunya k warai da gaske ba zai iya Ingice kyautar Baffan nasa ba. Mutumin da shine jigon rayuwarsa, nakamashin dukkan wasu nasarori da ya cimma a rayuwa.  Zamu je gobe In sha Allah bayan sallahr magriba sai ka bani numberr mahaifin yarinyar na sanar masa. D aga kai kawai Jaheed ya yi yana fatan wannan karan ya dace da auren Khairi kafin Baffan ya gingimo masa auren Najma ko Nasma da suke masa kallon wulak antaccen Bawa mara galihu. Jiki a sanyaye suka mik e suka bar wajen Baffan, shima nasa jikin a sanyaye ya bi bayan su da kallo tausayin Jaheed d in yana sake mamayar zuciyarsa, tabbas da yana da iko da ya mayar da Jaheed jininsa d ansa na halak malak ba d an rik o ba.

Sallama Jaheed ya yi da Haidar ya fa da nasu b angaren inda d akunan samarin gidan suke. Gwiwarsa a salub e take kamar yarda gangar jikinsa ta zama salaf ba k warin ko sisi. Yana karya kwanar lungun da zai sada shi da B angarensu suka kusa gabza karo da ita tana ta sauri zata isa wajen saurayinta. Wani irin banzan tsaki ta ja masa kafin ta zabga masa harara cikin mayalwatan idanun ta ta kuma tsartar da miyau tana furta  Nonsense. Cak
Jaheed ya tsaya yana jin kamar ya zabga mata mari sai dai fuskar Baffa yake ganowa kawai a cikin tata fuskar don haka ya kasa samun nutsuwar marin nata ya cije leb ensa kawai ya wuce yana jin sanda ta sake furucin  D AN MAHAUKACIYA KAWAI. Da d an k arfi ta yi maganar don haka maganar

3 / 22