Kudirar Allah Book Complete

Author :  Nazeefa Sabo Nashe Category :  Read Hausa Novels

Chapter   14 / 22

39K to 42K   out of 64.9K words

ya saka da wando black da yake akwai sanyi a garin sai ya kawo bak ar rigar sanyi mai d an girma ya saka a jikinsa inda ya rufe kansa da hular rigar. K amshin turaren Rasasi kawai yake zabgawa. Ya fito sanye da black slippers a k afarsa, fuskarsa ta bayyana yanayin da zuciyarsa take ciki na rashin sukuni da farin ciki, duk da k ok arin sa na kawar da hakan. A motarsa k irar Benz fara tas ya fita. Gidan su yake son zuwa su gaisa tunda kwanansa uku bai je gidan ba.


In dai zaka gan shi a lokacin sai ya burgeka don kai tsaye zaka hango kamanceceniyarsu da shahararren d an film d in India Sharuk khan sai dai haske da Sharukh d in ya fi shi.


Tunda ya hango Baffa zaune a harabar gidan kan babbar daddumar da ake shimfi da masa duk Bayan sallahr Isha i, sai ya ji gabansa ya fa di. Kwarjinin Baffan ya sake girmama a idaniyarsa. Bai san sanda ya cusa hannunsa cikin tarin sumar kansa ba. Ya k arasa saman daddumar Baffan jikinsa a sanyaye ya durk ushe a gabansa. Ido Baffan ya zuba masa yana amsa gaisuwar sa, kamar dama Jaheed d in ya san shi yake jira.

Amsa gaisuwar sa ya yi yana sake nazarin fuskarsa sosai, kallon da ya sake girgiza hanjin Jaheed sai ya dinga fassara kallon Baffan a mazaunin Butulu mara kirki balle adalci.  Ya jikin naka? Ya samu muryar Baffan a sama yana tambayarsa. Cikin rawar baki Jaheed ya amsa da  Alhamdulillah!  Ma sha Allah. Baffan ya furta yana cigaba da danna casbahan hannunsa.  Surikin ka ya zo jiya. Wani irin dum kan Jaheed ya yi jin abinda Baffan ya ce, hakan na nufi da Baffan ya ji haushi kenan ko me? Bai dawo daga tunani da fargabar da ya shiga ba ya ji Baffan ya cigaba da fa din  Na bashi ku din sadakinka na aurar y arsa bayan na gama yarda da nadamar da ya yi, ina fatan ta zame maka mata ta gari In sha Allah. Magana ta biyu maganar Najwa tunda na Riga na maka alk awarin aurenta ba zan janye ba In sha Allah, idan ta gama makaranta zan aura maka ita idan kana sonta. Da sauri Jaheed ya d ago ba tare da ya shirya fa dar abinda ya zo bakinsa ba ya ce  Ba abinda zai hana ni auren Najee Baffa in dai ina raye, nagode da karamcinka gareni, idan kuma har wannan auren bai maka ba, kana da iko a kai na zan iya janye magan???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~?ar auren In dai baka so.  Bana hana aure Mujaheed, kuma na yaba da hankalin yarinyar don haka har a zuciyata na amince maka aurenta, gobe idan an sakko daga masallaci za a d aura maka aure da ita, ka san tsari na bana son bidi a saboda haka na sanar da mahaifin ta Walima kawai za a yi ta tare a gidanka. Jaheed shiru ya yi kansa a k asa bai zata abubuwa za su zo masa da sauk i haka ba. Ya saki ajiyar zuciya kafin ya d ago ya ce  Sai dai Baffa ka min hak uri na Riga na nemi Visa a k asar QATAR zan je k arin karatu In sha Allah, ko za a bari sai na dawo sai ta tare. Baffa ya d au tsawon lokaci yana kallon Jaheed d in har Jaheed d in ya d an tsargu bai sare da lamarin ba sai da ya ce  Yanzu Mujaheed har zaka iya yanke shawarar abinda ya dace da kai ba tare da sani na ba? Ko duk laifin Najma ne ya shafe ni? Da sauri Jaheed ya hau girgiza kai  Wallahi Allah Baffa bakomai a raina, dama na da de ina nema sai yanzu suka bani amma idan baka so zan bar shi Wallahi. Baffa sai sannan hankalinsa ya kwanta  Ba zan ce kada ka je neman ilimi ba, kamar yarda ba zan amince ka tsallaka wata k asar ba matar aure ba, idan kaga na amince ka bar k asar nan sai dai idan ka tafi tare da matar ka don haka ka shirya sama mata visa ku ranka ya ku tafi gaba d aya. Wani irin sanyi ne ya shiga zuciyar Mujaheed yana jin girma da kimar Baffa na sake girmama a zuciyarsa, Da gaske Baffa d abi u da halayensa kwatankwacin irin halayyar sahabbai ne. Burinsa kenan tafiya da Khaireey sai ga shi komai ya zo masa da sauk i. Godiya ya yiwa Baffan sosai dafatan gama da duniya lafiya kafin Baffa ya dakatar da shi da fa din  Ameen, ta shi maza ka je wajen iyaye ka mata, Allah ya yi maka albarka. Jaheed ya amsa da ameen, ya mik e don shiga cikin gidan.




A balcony ya hangota zaune a saman kujerar da ke wajen. Suka ha da ido ya yi sauri kawar da kansa. Ita kuma da sauri ta bi shi da kallo zuciyarta na cigaba da wani irin k akkarfan bugu. K amshin turaren sa da ya kasa barin hancinta ta cigaba da shak a tana jin zuciyatta na sake k unci da tunano mata Jaheed a daren farkonsa gidan aurenta. Ta lumshe idanunta tana jin saukar hawayen da bata san dalilin su ba, haka kawai yake tsintar kanta a wannan yanayin tun bayan da aka tabbatar mata Jaheed ya saketa.



Da sallama ya shiga b angaren Umma. Najee ce ka dai a parlourn tana aikin bulbula turaren wuta. Saura k iris abin turaren wutan ya sub uce a hannunta Sabo da jin muryarsa da ta yi ta doki dodon kunnenta. Muryarta na rawa ta ce  Ya. Jaheed sannu da zuwa. Cikin idanunta ya kalla yana nazarin yarda ta kasa sakewa da shi da alama ta samu labarin abinda Baffa yake shirin k ulla wa tsakaninsu. Ta k i yarda sam su ha da ido don wata irin kunyarsa take ji. Lumshe ido ya yi yana furta  Amaryar Jaheed ya da kunya tun yanzu? Ai kafin kace me? Ya nemeta ya rasa don da mugun gudu ta b ace daga wajen b at. Jaheed ya saki murmushi yana sosa kansa a zuciyarsa yake tunanin duk sanda ya auri Najee zai yi fama da yarintarta, musamman kasancewarta Auta da bata san komai ba sai shagwab a. Autar ma wacce ta tashi a tsakiyar maza.

Fitowar Umma ce ta saka shi dawo da hankalinsa kanta. Ya gaisheta irin gaisuwar da suka saba yi. Ta masa ya jiki sannan ta masa fatan alheri akan auren da aka ce zai yi gobe, duk da ba wanda ya sani Baffan ita ka dai kawai ya sanarwa, ita kuma ko Najee bata gayawa ba ta bar abin a ranta, kamar yarda Baffan ya ce so yake ya bawa kowa mamaki. Jaheed ya amsa yana d an jin kunyarta, bata bi ta tasa ba don ta san me ya saka shi jin kunyar Sabo da zai yiwa y arta kishiya, ita kuwa ina ita ina shiga hurumin Ubangiji fatan alheri kawai zata bi su da shi. Don haka ta ce  Tashi ka shiga wajen Nene, tunda ta san ka ji ciwon nan hankalinta yake kanka na san kawaici kawai take. Jaheed ya amsa yana mamakin Umma da tace wai kawaici Nene take ko ina taga hankalin da zata san wani abu kawaici? Tunda bai san ta dawo cikin hankalinta ba.



A zaune ya sameta cikin kamalalliyar shigarta. Hannunta d auke da alk ur ani Mai girma. Jaheed ya shiga cikin d akin yana mamakin ganin Nenensa da Alkur ani, kamar wata mai cikakken hankali. Idonta ta d ago ta zuba masa tana kallon yarda ya zube a gabanta.  Nene Ina wuni? Ya fa da kamar yarda ya saba. So yake ya ji ta maimaita masa abinda ya ce kamar yarda ta saba sai ya ji ta ce  Lafiya lau Mujaheed d an Albarka ya jikin naka?





JIKAR NASHE CE
'

K UDIRAR ALLAH

17.


NAZEEFAH SABO NASHE.

08033748387.

(Allah ya baki lafiya Na ima Sulaiman sarauta. (Nimcyluv).



Wani irin d agowa Jaheed ya yi kamar a firgice ya zubawa Nene da Itama take kallonsa ido. Da gaske kallon da Yake mata na tsananin mamakin jin amsawar da ta masa ne. Bai tsammaci hakan ba a irin wannan lokacin, Nene murmushi ta sakar masa tana kallon tsakiyar idanunsa ganin yarda mamakinsa ya kasa b uya da alama ko yana tunanin mafarkin da ya saba ne. Don haka ta kai hannunta na kama na hannunsa da ya dunk ule waje d aya, idanunsa a lumshe yana fatan ko mafarkin yake kada ya farka nan kusa. Nenensa a cikin hankalinta tana amsa masa maganarsa cikin nutsuwa ba irin harigidon da ta saba ba. Yau shi kuwa wace irin godiya zai yi wa rabbul izzati. Bai dawo daga mamakin ba ya ji muryarta mai taushi ta amsa masa tambayoyin da bai bayyana su ba.  Ni ce dai Nenen ka Jaheed, ba mafarki kake ba Allah ya dawo min da hankalina. Ta fa da tana jan istigfari a zuciyarta. Jaheed ya saki ajiyar zuciya mai k arfin gaske yana furta  Alhamdulillah! Cikin muryar da ta bayyana rauninsa gurin Rabbil Izzati, don tuni hawaye suka gauraye idanunsa sauka suke da zafinsu cikin sark ewar harshe ya ce  Nene sanar da ni, wacece ke? Daga wani gari ki ke? Idan kuma nan ne garin ku wanene mahaifina? Ya Ubangiji Allah yasa kada zargin mutane na cewa ni shege ne ya tabbata. Ya fa da yana duban Nenen da ta lula cikin duniyar tunani. Banda tana tsoron makomarta da ta Jaheed d in gaba d aya da a yau zata sanar da shi shi wanene? Sai dai tsoro da fargaba ba zai barta ba, bata son abinda zai nesanta da Jaheed ba kuma ta son ya je inda za a wulak anta shi tunda bata da wata shaida da zata bayyana mahaifinsa kai tsaye a garin Gabas, dole ne sai ya yi bincike kafin ta gano ainahin wanda ya jefata a cikin wannan sark ak iyar mai wuyar warwara.

K irjin Jaheed ya cigaba da wani irin bugu da k arfin gaske, ya ayyana shikkenan ta faru ta k are ba sai Nene ta bu de baki ta yi magana ba ya san shi d in shege ne mara asali wanda ba a san ubansa ba, ba mamaki ma hakan ne sanadiyyar d auke war hankali da tunanin Nene. Hucin numfashi Nene ta furzar kafin a hankali ta furta  Ba zan iya tuna komai nawa ba Jaheed! Harta sunana da sunan garin dana fito ba zan iya tuna su ba sai dai mu yi ta addu a har zuwa lokacin da zan tuna komai d in& . Murnar Jaheed ta koma ciki ya zuba mata ido cike da tausaya mata, wace irin k addara ce wannan mai girman gaske yake bibiyar Nene da shima kansa, yana rok on Ubangiji Allah yasa su amsa jarrabawar nan daidai. Hannu yasa ya d auke k wallar data tarar masa, kafin ya mayar da hannu ya share k wallar da take idanun Nenen yana sakar mata murmushin da kai tsaye za a kira na dole ko na yak e. Nene ta sakar masa murmushin itama, don k ok arin kawar mata da damuwa sai ya soko zancen aurensa.  Gobe za a d aura min aure da Khaireey Nene. Take annurin da Nene take tare da shi ya d auke tsaf daga fuskarta. Cikin b acin rai ta ce  Aure kuma? Ina maganar Najwa da Baffa ya baka? A idanunta ya hango tsananin son aurensa da Najee ya sani dole dama zata yi farin ciki da zamowar Najee surikarta, amma bai san wannan dalilin zai saka ta k i Khaireey ba. Murmushi ya sakar mata yana furta  Nene a yanzu Najeenki ta yi k arama da aure, so ki ajiye min ita sai na da 2 to 3 yrs kamar yarda Baffa ya ce, ni kuma na miki alk awarin rik e miki Najee da soyayya mai girma a zuciyata. Sai sannan ta saki murmushi ta na furta  Mujaheed bana son ka yi wa Baffanku butulci duk duniya baka da wanda ya fi shi, ina son ka jajircewa zuciyarka wajen ganin ka kyautata masa duk runtsi kada ka bijirewa auren Najwa ka min wannan alk awarin? Jaheed ba tare da jin komai a zuciyarsa ba ya damk e hannunta yana d aga mata kai  Na miki Nene duk runtsi duk wahala ba zan k i auren Najee ba. Ta saki ajiyar zuciya tana furta  Allah maka albarka, amma tabbas da Baffa ya yi shawara da ni, da ba a fara waccan maganar ba har sai an d aura aurenka da Najwa idan ya so nan gaba ta tare Amma dai itace Uwargida. Dariya sosai Jaheed ya yi ya ce  Kai Nene banda son kai. Itama dariyar ta yi tana furta  Son kai ko gaskiya duk duniya ba wanda nakewa son da nakewa Najwa a cikin raina nake jin yarinyar kamar ni na haifeta. Jaheed ya jinjina kai ba tun yanzu ya fuskanci hakan ba, tun Nenen na cikin hauka ko tana ciwo Najee kawai taka bata abinci ta karb a. Ya ce  Burinki zai cika In sha Allah, Najee zata haifa miki jikoki masu yawa. Ta bu de ido tana kallonsa kafin ta furta  Mujaheed baka da kunya dama? Dariya ya yi sosai kafin ya mik e ya fice da sauri yana jin wani farin ciki da nutsuwa a zuciyarsa ba don komai ba sai don dawowar Nene cikin hankalinta.


A parlour ya samu Umma tana zaune idanunta akan T.V tana kallon tashar da ta fi so wato Sunna t.v. Ta gefe ta kalleshi ganin yarda yake zabga fara a ta tabbatar ya gano Nenensa ta samu lafiya.  Akwai labari a bakinka Mujaheed. Ta fa da tana d auke idanunta daga saman T.Vn. Murmushi ya saki ya na zama a gefenta ya ce  Akwai Umma, ashe Nene ta dawo cikin hayyacinta. Ta d aga kai tana murmushi  Ta dawo Mujaheed, ina sane na k i sanar maka na fi so ka gani da idonka, Alhamdulilah Abu d aya ya rage ta tuno rayuwarta ta baya wannan kuma sai a hankali In sha Allah. Mujaheed ya d aga kai yana cewa  Allah yasa Umma, bari na wuce sai da safe. Yana shirin mik ewa ta ce  Ya maganar lefe Mujaheed? Ya d an sosa kansa ya ce  Za a yi Umma, a min list a kuma fa da min ku din da za su isa sai na bayar. Umma ta d aga kai tana kallonsa  Ashe kuwa Baffa baya raye? Da sauri ya waro idonsa don rashin gane inda zancen Umma ya nufa. Ta d aga kai cike da tabbatarwa  Ka san dai shi yake muku lefe ko? Tambayar da na maka maganar sizes d in yarinya nake maka ba na ku di ba Alhaji Mujaheed. Dariya Mujaheed ya yi sosai yana furta  Tuba nake Umman mu zan tambayeta In sha Allah, ko kuma na bawa Najee numberr wayarta sai ta tambayeta.
Umma ta watsa masa wani kallo ta ce  Saboda me zaka saka kishiya ta tambayi kishiya sizes don ha din fa da? Jaheed ya waro ido shi har ga Allah ya ma manta bai gayawa Khaireey maganar Najee ba, kamar yarda itama Najeen bai sanar da ita gobe za a d aura masa aure ba. Umma dariya ta masa sosai ganin yarda tsoronsa ya bayyana ta ce  Kada ka zama matsoracin namiji mana ko an gaya maka zama da mace fiye da d aya na rago ne, ka sanar da ita maganar Najwan ne? Ita kuma Najwa ka sanar da ita maganar auren da zaka d aura gobe? Tun yanzu ya kamata ka fara daidaita tunaninsu&  K arar abinda ya fa di a hannun Najee ne ya saka su juyawa da sauri. Suka zuba mata ido da glass cup d in da ta d ebo kunun aya zata sha a ciki. Idanunta a waje take kallonsu bata damu da b arnar da ta yi ba, k ok arin ma taka glasses d in take da sauri Umma
Cikin tsawa ta dakatar da ita.  Kina hauka ne Najee? Ba ki ga abinda ke gabanki bane sai kin taka kin ji ciwo? Da sauri ta ja baya sai dai tuni kwalba ta nutse a k afarta, bata damu ba ta ce  Aure zai yi gobe Umma? Umma ta zuba mata harara da ta saka ta yin shiru da sauran zancen da yake bakinta.
 Wuce ka tafi Mujaheed dare ya yi. Ta yi saurin fa da ba don komai ba sai don bata son Mujaheed d in ya hango lagon Najeen. Yana fita ta mik e a zafafe ta isa gaban Najeen ji kake tasss ta wanketa da mari.  Aure zai yi ko zaki hana shi ne uwarsa? Shin wai ma nawa kike da har kika san maganar aure? Na sake jin zancen aurenki Da Jaheed a bakin ki sai na yi k asa k asa da ke, ni ba banzar uwa ba ce da zan d auki rashin kunyar yaran Zamani. Wuce ki bani waje, ki cika min ciki ki ga idan ban hanaki aurensa ba, dama ina lura da ke tunda aka yi maganar nan kike wani rawar kai, sai kin zubar da ajinki tun kafin ya so ki ke kin nuna maitarki a fili, na sake gani zaki ga abinda zan miki, bayan gaisuwa ban amince wata magana ta sake shiga tsakaninku ba. Shiru Najee ta yi hawaye na sauka a idanunta bata tab a ganin b acin ran Umma

14 / 22