Kudirar Allah Book Complete

Author :  Nazeefa Sabo Nashe Category :  Read Hausa Novels

Chapter   10 / 22

27K to 30K   out of 64.9K words

a k asa cikin tashin hankali Baffa kuwa bai bi ta kan su ba ya fice daga sashen yana jin hakan da ya yi shine daidai idan har ya bar Najma bai aurar da ita ba tabbas Mahmeey zata iya b ata masa tarbiyyarta. Mahmeey shiru ta yi kafin ta jawo wayarta ta fara kiran waya tana magana cikin tashin hankali.  A yi koma me ye akan lamarin nan, bana son a yi tariyar nan Don Allah Malam. Shiru daga d aya gefen kafin Mahmeey ta ce  Na yarda Malam koma me ye a yi masa idan ma haukata shi za a yi a yi, ko kuma a birkita shi ya saketa dole. Ta kashe wayar tana kallon Najma da ta kwanta a jikinta tana kuka.  Ki rufe min baki komai Malam ya ce zai zo da sauk i abu guda muke so ki ba mu ha din kai. Najma ta d aga kanta tana sakin ajiyar zuciya a hankali.




Jaheed kuwa da jan k afa ya shiga sashen Umma. Umma tana ganinsa ta san ba lafiya ba. Ajiyar zuciya ta saki a fili ta furta  Ka yi hak uri Jaheed taka k addarar kenan. Ya saki ajiyar zuciya a hankali kafin ya d aga kai ya kalli Najee da ta yi zuru zuru idan ba kallon tsoro ya mata ba sai yaga kamar har rama ta yi. Ya lumshe idonsa kawai kafin ya ce  Najwa kawo min Lipton tea, amma Honey zaki yi using ba Sugar ba. Najwa da sauri ta mik e don cika umarninsa. Tea d in ya sha mai zafin gaske kafin ya sauke cup d in yana sakin ajiyar zuciya yarda tea d in yake da zafi haka yake jin zafi a zuciyarsa. Tsawon mintuna kafin a hankali idanunsa a lumshe ya ce  Baffa ya ce zata tare gobe. Umma ta d aga kai ta ce  Allah ya nuna mana yasa a ce gara da aka yi. Bai amsa ba don ya san da k yar hakan zata faru. Tsawon 1 hour ba mai iya magana a cikinsu kafin ya mik e cikin rashin sukuni ya yi hanyar sashen mahaifiyarsa. Can yake so ya je ya yi kuka a jikinta ko ya ji sanyi a zuciyarsa. Jin motsi yasa Nene komawa ainahin suffarta ta mahaukaciya duk da rashin sukunin zuciya da ta tashi da shi hakan yasa idanunta suke cike jingim da hawaye. Jaheed ya zauna a gabanta jikinsa a sanyaye ganin kamar bata jin da di ya d ora hannunsa akan goshinta ya ji ba d umi, sai sannan hankalinsa ya kwanta. Hannunsa cikin nata ya ce  Nene gobe zata tare. Idanu kawai ta bi shi da shi, bai damu ba don sau tari tana kasancewa cikin wannan yanayin. Ya d auke idanunsa a kanta. Suka zauna jigum jigum Nenne a
Lokacin zuciyarta ta tafi tunanin irin rayuwar auren da Jaheed zai yi da matar da bata son sa bata k aunarta. Ya da de a zaune kansa a kan cinyarta yana zubar da hawaye addu a yake Allah ya dawo da ita cikin hankalinta ta sanar da shi ko shi waye. Tsawon lokaci yana kwance kafin ya mik e yana d auke hawayen idanunsa ya fice daga d akin. Kuka Nene ta saki sosai tana furta  YA Allah ka kai mu lokacin da zan sanar da Jaheed asalinsa& . Turo k ofar aka yi idanunta ya fa da cikin na Najwa da take kallonta cikin mamakin jin abinda ta fa da don duk abinda ta fa da a cikin kunnuwanta& & &




JIKAR NASHE CE.
'

Kin biya ko kuwa? Book 1 ne free Book 2&3 paid ne akan 500 kacal via 2118666253 UBA

Sai a tura shaidar biya ta wannan numberr 08033748387.


Na gode masu min waya min yi biki lafiya mun gama lafiya sai fatan Allah ya basu zaman lafiya. Na gode sosai


K UDIRAR ALLAH

12.


NAZEEFAH SABO NASHE.


08033748387.



Runtse idanunta ta yi gam sanin cewa Najwa ta gama jin abinda ta fa da d in, ga shi bata da ikon mayar da maganar cikinta da ta mayar. Najwa kuwa cikin mabayyanin mamaki ta k arasa
Wajenta jikinta a kasalance ta zauna daf da ita tana jan hannayenta ta ce  Nene na ji kin yi magana kada ki min pretending da gaske kin san asalin Jaheed duk shekarun nan ki ke walagigi da rayuwarsa sannan kika d orawa kan ki cutar hauka na k arya, me yasa kika aikata haka Nene? Idanunta ta bu de cikin na Najwa da itama ta kafe ta da nata idanun ko k iftawa bata yi. Hawaye ne kawai yake sauka daga idanun Nene ta rasa yarda zata yi ta mayar da su a yanzu dai kam ta san ba zata iya k arya ta Najwa ba don yarinyar tana da kaifin tunani da k wak walwa irin ta manya. Najwa ta sake jan hannunta tana matsawa a hankali ta ce  Ki sanar da ni Nene. Nenen ta saki ajiyar zuciya a karo na farko bayan shekaru da dama ta yi magana da wani cikin hankali ba cikin pretending d in hauka ba.  Ki yi alk awari idan na gaya miki zai zama sirri tsakanin ni da ke ko Jaheed ba zaki fa dawa ba? Najee shiru ta yi tana tunanin d aukan alk awarin tana tunanin girmansa da raunin da zuciyarta take da shi wajen b oyewa Ummanta abu don itace aminiyarta don haka ta tafi tunani. Son jin labarin yasa ta d ago tana kallon Nenen ta ce  Zan d aukar miki alk awarin ba zan gaywa kowa ba sai dai bani da juriyar da zan iya d aukar miki alk awarin ba zan gaywa Umma ba. Nene ta yi shiru don bata son Umman ma ta ji maganar sai dai kuma tana tunanin sanin Umman ba zai zama Aibu ba idan har ba Jaheed za su gaywa ba ita
Kuwa bata son Jaheed ya san maganar har sai ta san sanadin yarda ta samu Mijinta.  Na
Amince ki gayawa Umma.
Ta fa da cikin sanyin murya da taruwar k walla a k asan idonta tsoro take ji sosai idan abu ya fasu a duniya har ya isa inda bata son ya je ta tabbata wad ancan mutanen da suke harin rayuwarta za su iya kasheta. Gefe guda kuma nauyi da kunyar idanun Abba ne yake shirin mama ye tunaninta, da wani ido zata kare kanta da tsawon lokacin da ta d auka tana jinginawa kanta hauka lamarin da girma da kuma
Kunya. Najwa cike da zakwa din son jin labarin ta dafata tana furta  Bari na kira Umma ki bamu labarin nan a gabanta. Kasa hanata ta yi duk da k ok arin hakan da ta yi tana kallo ta fice cike da karsashi. Nene ta lumshe idonta a ranta tana furta shikkenan yau dai ta faru ta k are komai zai bayyana kansa sai fatan Allah yasa su fahimceni su fahimci abinda yasa na aikata hakan.


Daga yanayin fuskarta Umma
Ta gane tana cikin wani tsananin farin ciki da har ya kasa b oyuwa a cikin idanunta. Hannun Umman kawai ta kama tana furta  Umma zo ki ga. Umman tana tambayar ta amma ba amsa jan ta kawai take zuwa sashen Nenen.

A zaune suka samu Nenen, idanunta na zubar da k walla. Najwa ta ce  Nene ga Umman yi magana. Nene ta kasa magana illa ha diyar zuciya kawai da take yi tana danne zuciyarta da take jin b acin rai kamar yanzu komai ma ya faru. Umma kuwa cike da al ajabi take kallon Najwa ta ce  Wai me ya faru kin bar ni a cikin duhu? Najee ta saki ajiyar zuciya tana furta  Umma Nene tana cikin hankalinta yanzu zata miki magana. Umma ta ware ido tana furta  Alhamdulillah bari na kira Baffanku na gaya masa da Mujaheed. Da sauri Najee ta ja hannunta tana girgiza mata kai  Ki zauna Umma bana son ki kira kowa Nene bata son a san tana cikin hankalinta, duk tsawon shekarun nan Ashe ba hauka take ba& . Kallon da Umma ta yiwa Najwa ne ya sata ha diye sauran abinda ta yi niyyar fa da don idanun Umma sun nuna zallar mamaki da
Jin abinda ta ce d in.  Najwa bana son shirmen banza ta yaya zata jinginawa kanta hauka& .
Da gaske ne Umman Jaheed ba mahaukaciya ba ce ni, amma ina son ki min afuwa ki kuma rufa min asiri a yau Zan sanar da ku asalina da abinda ya baro ni daga gida Amma don Allah ya zama sirri bana son ko Jaheed ya sani&  Turus Umma ta zauna a gefen gadon k irjinta yana matsanancin bugu Baffa kawai take tsoron ya san labarin nan don idan har ya sani ba zai yafewa Nenne ba, ya tsani mutum mak aryaci balle ita abin nata ya yi yawa ma sosai ta yarda ta yaudaresu tsawon shekaru ta musu wasa da hankali a zuwan mahaukaciya ce ya dinga kashe ku dinsa a kanta a banza tabbas ba zai sake yarda da lamarinta ba.  Ki yi hak uri ki yafe min dalili mai k arfi ne ya saka ni aikata haka ba son raina ba. Umma ta ja ajiyar zuciya tana ha diyar yawun da bata shirya wucewarsa ba.  Shikkenan ina jin ki, me ya rabo ki da gida kuma wacece ke? sannan Ina son ki gaya min gaskiyar zance bana son k umbiya k umbiya.. Umma ta fa da zuciyatta na sake rauni tana fatan Allah yasa Jaheed ba shege bane ta yi cikinsa ta gudu daga gida ta jinginawa kanta haukan dole.

Nene shiru ta yi zuciyarta rawa take da matsanancin bugu, duk da a ranta tana son furta abinda yake ran nata wanda ya hanata sukuni shekara da shekaru sai dai wata zuciyar tana kwab arta ga barin aikata hakan.  Yi magana mana. Umma ta fa da idanunta akan Nenen da ta ga hannunta yana rawa kamar ma jikinta b ari yake. Don ta kwantar mata da hankali sai ta kama hannayenta  Ki yi magana In sha Allah Zan rufa miki asiri in dai Baffa ne ba kya so ya sani ko wani nasa ba zan bari ya sani ba balle shi, yanzu dai abinda na fi buk ata sanin asalinki da yarda kika samu cikin Jaheed saboda ina jin tsoro a zuciyata ina fatan Jaheed ya zamo tsarkakken d a ba kamar yarda zuciyata take tararrabi ba. Sai sannan Nene ta saki ajiyar zuciya ta d ago raunannun idanunta da suke zubar da k walla ta zubawa Umman kafin ta lumshe su cikin muryarta mai sanyi ta fara ba su labarin rayuwarta& &




___________


Sunana Fatima wacce aka fi kira da Fatu a can garin mu na Gabas. A cikin masarautar aka haifeni a ciki kuma na taso na girma tunda iyayena bayi ne a masarautar. Tun bayan taso wa ta ban tab a ganin sanda Iyayena suka zauna suka huta ba kullum a cikin wahala suke da har ta bayyana a jikkunansu ta hanyar rashin wadatuwar lafiya tattare da su. Sunan Mahaifiyata Inno mahaifina Kuma Babani, mutanene da suka nuna mana asalin soyayya da kulawa musamman ni da na zamo mace a cikin yaransu maza guda biyar.







__________________


~SHEKARU TALATIN DA SUKA WUCE.~


MASARAUTAR GABAS&


Masarauta ce mai tsohon tarihi da girman gaske ha de da k arfin mulki da kuma gamammen arziki. Duk wanda ya san Masarautar gabas ya santa da wadatar arziki game da k ak karfan ikon mulki da ake gudanar da shi bisa son rai da zallar mugunta. Duk da Sarkin sarki ne mai adalci da kuma son kyautatawa al ummar sa, sai aka yi rashin dace da wa danda suke kewaye da shi su kuma mutane ne Mugaye da ba abinda suka sani sai zalunci da son bak antawa talakawa kamar yarda tarihi ya nuna. Mahaifinsu Sarki Abdallah kafin rasuwar sa mutum ne shi mai nagartattun halaye wanda ya sanya mutane suke son sa musamman talakawa da ya zamo Katanga abin jinginarsu, basu tab a kuka da shi ba kamar yarda a zamanin sa aka samu wadatuwar arziki aka rabauta daga talauci don kuwa ya d agawa talakawa k afa sosai ya kuma bu de musu hanyoyin samun ku di a sauk ak e ta yarda kowa yake washshalawa cikin farin ciki da ginuwar arziki.

Y ay ansa Ashirin da takwas sai dai Babban d ansa su biyu kacal mahaifiyarsu da ake kira Fulani ta haifa da shi da y ar uwarsa mace guda Fatume, Shi Kuma sunansa Mukhtar da mahaifinsa yake kira abin zab i. Soyayyar mahaifinsu ga Mukhtar soyayya ce mai girman gaske da baya iya b oyeta a idanunsa kowa ya sani yana son Mukhtar ne saboda rauninsa da tsananin son addininsa da mahaifiyarsa ta d ora shi a kai. Ya yi farin ciki sosai da samun Mukhtar a matsayin Babban d ansa da zai gaji sarautar gabas saboda yarda halaye da d abiunsa suka barranta da na y an uwansa. Su
Mutane ne masu zuciya mara alheri a cikinta sai gungumen
Sharri burinsu kullum cusgunawa talaka da Kuma bak anta musu kamar yarda suke d aukan duk wani talaka wulak antacce kuma k ask antacce. Sosai yake jan Mukhtar a jikinsa tun bayan da ta fara rashin lafiya da yake ji a jikinsa kamar cutar ajali ce ta kama shi ya dinga nuna masa dabarun Mulki da yarda zai dinga samun nasara akan Mak iya koda sun nufoshi da Sharri ba abinda zai same shi da izinin Allah da kuma kariyarsa.

Tun kafin rasuwar Mahaifinsu bak in cikinsu a kan Mukhtar ya bayyana muraran ta yarda suke son ganin bayansa. Sun kuma sha kai masa Farmaki Amma Allah yana kareshi. Kafin mutuwar mahaifinsa Mukhtar ya yi aure da d aya daga cikin y ay an Sarkin Yamma wacce ya yaba da hankalinta. Watanninta bakwai Allah ya yiwa Sarki Abdallah rasuwa. A ranar da kuma ya rasun Mukhtar ya haye kujerarsa ta Mulki inda aka na da shi SARKIN GABAS. Nan y an uwansa suka shiga Hassada da bak in ciki iri iri ta yarda Mukhtar d in ya dinga tsallake sharrinsu da Makircinsu har ma da k ok arin kashe shi da suke son yi duk da komai suna aikata shi ne a b oye a kuma sirrance.


BAYAN SHEKARU DA HAWANSA KAN MULKI.


Bai tab a samun haihuwa ba hakan ya  daga hankalinsa da duk wani mai k aunarsa duk kuma inda ya je za a sanar da shi lafiya yake ko da yake tabbas da gaske lafiya yake tunda Sau kusan biyar matarsa tana haihuwa d an yana rasuwa ko kuma tun cikin bai girma ba sai ta yi b arinsa. Bisa tilas Mukhtar ya Amince da shawarar y an uwansa akan ya k ara aure. Aka aura masa mata Uku lokaci guda suma dai sun d an jima babu haihuwar hakan yasa Mukhtar ya tattara lamarin haihuwa ya jingineshi a gefe, musamman da aka wayi gari k anwarsa ta yi hatsari ta rasu motar ta k one k urmus ko gawarta ba a cire ba, sai d anta da ta bar musu a wajen Mukhtar ta tafi ashe sallamar kenan shikkenan Mukhtar sai ya tattara duk soyayyar sa da kulawarsa ta koma kan Abdallah k arami da ake kira Halifa. Ya saka a zuciyarsa tabbas ba shi da rabon ganin d ansa ne a rayuwa don haka ko Abdallah ka dai Allah ya bar masa ya gode masa.



Wata irin guguwar tashin hankali ta fara faruwa a Masarautar ta yarda akewa y an mata fya de bisa son rai dana zuciya wanda kowa ya shaida ba wanda yake aikata musu hakan sai jinin Sarautar da suke gidan musamman yarda samarin y ay an y an uwan Sarkin suka girma suka balaga to fa a duk sanda suka k yallara ido suka ga budurwa basu da buri irin suga sun keta budurcinta ko da da k arfin tuwo ne.

Sarki Mukhtar bai san da wannan labari ba, ranar da ya ji kuma hankalinsa ba k aramin tashi ya yi ba. Ba shiri ya saka aka tara masa taron Mata da Bayi da y an matan da suke cikin masarautar. Aka cika a filin da yake harabar masarautar zuwa lokacin a k idaye an ketawa y an mata hamsin mutuncinsu wasu sun samu ciki wasu kuma sanadiyyar haka sun rasa ransu, wasu kuma sun samu motsuwar kwanya. Sarki Mukhtar Bn Abdallah, ya dinga sakin ajiyar zuciya ana iya juyo sautin ta ta cikin loud speaker da take hannunsa, kafin ya yi sallama cikin sakakkiyar muryarsa mai bayyana tarin nutsuwarsa da kamalarsa.  Mun yi tur mun yi Allah wadarai da wannan abin da yake faruwa a masarautar Gabas, bisa zalunci da son zuciya an wayi gari ana keta
Mutuncin y an mata, don haka mun zauna da mahukunta masarauta ta yarda zamu saka ido sosai a cikin masarauta duk wanda aka sake samu da laifi irin wannan tabbas hukuncin sa kisa ne, ba zamu yarda da zalunci da keta haddin d iyoyin mu mata ba, abu na gaba Mata mun sabunta musu suturarsu ina nufin y an mata da suke yawo ba mayafi daga cikin bayin mu, a yanzu masarauta Zata raba su kayan da zai rufe jikinsu sink if ba tare da an ga ko da yatsan k afarsu ba madadin wancan kayan da suke sakawa da yake bayyana surar jikinsu yake kuma banbanta su da iyayensu, a yanzu masarauta zata mayar da suturarsu irin ta iyayensu don gujewa ya duwar Fasadi a cikin Masarautar Gabas. Duk Macen da aka sake samu an mata fyad e kai tsaye zamu jingina laifin ne kan Iyayenta akwai kuma mummunan hukunci da zai biyo kanta da iyayenta gaba  daya, don haka ya zama dole gareku Iyaye ku saka ido akan d iyoyin ku mata, ba mu amince da sake ganin Mace bayan sallar Magriba ba ko cikin

10 / 22