Kudirar Allah Book Complete

Author :  Nazeefa Sabo Nashe Category :  Read Hausa Novels

Chapter   5 / 22

12K to 15K   out of 64.9K words

Zuciyar Jaheed da hauhawar jininsa don haka ya masa allurai masu k arfi da zasu samar masa da nutsuwa ya kuma buk aci a bar shi ya samu hutun In sha Allah everything will be alright. Ya fa da yana kallon Baffan. Ganin barci mai nauyi ya d aukeshi yasa suka fice daga d akin. Jikinsu a sanyaye da fatan samuwar lafiyar Jaheed d in.




Ranar Juma a ne duk hakan ta faru a ranar kuma bayan an sakko daga babban masallachi Baffan ya buk aci mutane su tsaya zasu taya shi d aura auren d ansa. Aka kuwa tsaya cikin dandazon jama ar Baffan ya mik awa waliyyin amaryar Jaheed sadakinsa ha de da bada Umarnin a d aura auren& & .




To fa!

Ko wa Baffa ya aurawa Jaheed a cikin y ay ansa Najma? Nasma? Ko yarinya Najwa?


Ina jiran amsar ku&


JIKAR NASHE
'

Don biyan littafin nan kai tsaye danna numberr account d in nan

2118666253 UBA don free pages ya kusa k arewa. Tafiyar dai mai nisan zango ce kamar yarda rikici da soyayyar da take cikin littafin sun girmama.
Ina tsoron kada a yi babu ke hanzarta biya ki danno min shaidar biya ta wannan numberr 08033748387.



JIKAR NASHE TAKU CE!


KUDIRAR ALLAH..


Page 5.


NAZEEFAH SABO NASHE.

08033748387.



Tuni mai sanarwa ya fara kwararato a loud speaker yana sanar da AN DAURA AUREN AISHA ILU MAI FATA WATO NAJMA DA MUHAMMAD MUJAHEED MAI FATA. Ras gaban Haidar da yake waje ya fa di yana tunanin anya kuwa Baffa ya san me ya aikata? Ya san k iyayyar da ke tsakanin Najma da Jaheed kuwa kiyayyar da take jin kamar ta soke shi da wuk a ta huta da ganinsa, da Baffa ya nemi shawararsa da kai tsaye zai gaya masa ya ba shi Najwa sai ya raineta a gidansa. Ya ciji yatsa tausayin Jaheed yana kama shi irin tozarci da rashin mutuncin da Najma zata masa a duk sanda ta ji labarin an aura masa ita. Ya saki ajiyar zuciya kawai yana fatan Allah yasa hakan ya zama alheri garesu baki d aya.


Cikin gidan basu san me yake faruwa ba, kamar yarda labari bai isar musu ba. Jaheed na cikin d akinsa a kwance duk da jikin da sauk i sai dai har yanzu zuciyarsa ba da di ji yake banda k arfin Imanin da yake togaceshi daga aikata kisa da ba abinda zai hana shi kashe kansa ya huta da wannan takaicin duniyar da yake ciki. A kai a kai yake ganin missed call d in Khairi sai dai ya kasa d agawa a duk sanda kuma zai ga missed call d inta sai ya ji hankalinsa ya ninka na baya tashi. Hawaye yake zubar wa sosai kamar yarda ra da din zuciyarsa yake sake rub anya. Ba zai iya irga adadin kiran ba kamar yarda itama Khairin bata gaji da kiran nasa ba da tura masa text messages mai bayyana tashin hankalin da take ciki ba. Bai bu de message d in ba saboda ya san duk abinda message d in ya k unsa ba zai wuce bayyana rashin nutsuwa da tashin hankalin da zuciyarta take ciki ba, kamar yarda tasa ma take ciki.

Gidan tsit sakamakon masallachin juma a r da jama ar gidan da hadiman gidan suka tafi. Don haka zuciyarsa ta sake samun damar zurfafa da tunanin. Da k yar ya mik e ya shiga wanka don ya san a irin wannan lokacin Baffan baya amsar uzirin kowa na k in zaman cikin parlournsa. Don haka ya daure ya fita daga part d in samarin zuwa na Baffa sanye cikin doguwar rigar jallabiya fara sol data sake fito da fuskarsa data zama fayau alamun rashin lafiya kwance cikin kyakykyawar idaniyarsa.



A kuma lokacin Baffa da shi da ahalinsa su Haidar da k annensa da ma hadiman gidan suka dawo gidan. Fuskarsu d auke da murmushi mai bayyana asalin murnar da zuk ata suke ciki, idan ka d auke Haidar da tasa zuciyar take cike da raunin tausayawa Mujaheed na auren da aka aura masa ba tare da shirinsa ba, da ace Najma wata mutuniyar kirki ce da sai ya ce abokinsa ya yi dace k warai da kyakykyawar mace ta nunawa da kerewa sa a. Sai dai Najman Kyawun d an miciji gareta.


A babban falon gidan Baffa ya zube inda anan duka ahalin gidan aka saba taruwa duk ranar juma a a ci abinci a kuma yi wasa da dariya kasancewar Baffan mutum ne mai barkwanci a wasu lokutan idan yana jin nisha di. Aka ta shigo da coolers na abinci masu kyau da inganci wad anda daga ganinsu ka san an lashe mak udan ku di wajen siyensu.
Bata Abincin Baffa yake ba don haka hankalinsa gaba  d aya bai kai kan abincin ba balle ya ga yarda Umma ta tsarashi Alkubus ne da Masa sai aka musu peppe soup na kaza dagargajajjiya sai zob o da ya sha kayan k amshi da fura mai sanyi a gefe da ta sha zuma. Burin Baffa ya tara su ya sanar da su abin alherin da yake ganin shi ya k ulla. Don haka da k yar ya hak urcewa zuciyarsa aka gama cin abincin aka kwashe kwanukan tas kafin a yi addu a aka shafa sannan Baffan ya yi gyaran murya ya yi sallamar data saka kowa da yake wajen ya tattaro hankalinsa da nutsuwarsa kan Baffan. Kowa ya ga yanayin fuskarsa ya san wani abu ne mai mahimmanci zai fa da don haka suma suka sanya nutsuwa a zuk atansu da kan???? 
  
 !"#$%&'()*+,-./0123456789:;<=>?@ABCDEFGHIJKLMNOPQRSTUVWXYZ[\]^_`abcdefghijklmnopqrstuvwxyz{|}~? fuskokinsu. Baffa ya kalli Najee ya ce  Maza ki kira min Nenne don abin ya shafe ta. Gaban Jaheed ya fa di jin abinda Baffan ya ce ya fara addu ar Allah yasa ba wani lamari mai girma bane yasa Baffan ya buk aci ganin Nennen a irin wannan lokacin don ba kasafai Nennen ta fiye son shiga taron mutane ba.


Nenne a zaune saman sallayar take hannunta d auke da carbi tana ja. Sanin cewa ba wanda zai shigo a irin wannan lokacin yasa tana cikin nutsuwarta. Najee ta tura k ofar tana sakin sallama, sallamar ta tsaya mata a mak oshi ganin Nennen zaune cikin nutsuwa akan Sajjada tana rik e da carbi. Nennen ma a firgice ta kalli Najee ta rasa kuma yarda zata yi ta riki de ta koma mahaukaciyarta a fuskar zahiri. Najee ta shigo cikin d akin tana sake mutstsike idanun ta don tabbatar da zahirin abinda ta gani. Da sauri Nenne ta aro tunanin dole ta sanyawa zuciyarta da wani irin sauri ta fara jan Carbin tana nuna alamun hauka a tattare da ita. Najee ta dubeta kafin ta saki ajiyar zuciya ganin da alama Nenen bata san abinda take ba ba mamaki yanayin haukan yau da sallah yazo mata. Ta mik a mata hannu tana furta  Mu je Baffa na son ganinki. Nene ta maimaita kafin ta mik e ta bi bayan Najeen tana sake waro idonta kamar mahaukaciyar gaske suka nufi Babban parlourn Baffan da yake harabar gidan sai dai yana da k ofa ta cikin sashensa da yake cikin gidan.


Baffa cikin nutsuwa ya nunawa Najwa kusa da Umma ya ce  Zaunar da ita. Sannan ya gyara zama ya na furta  Dalili ne mai girman gaske yasa na taraku anan. Albishir d in da zan muku ina kuma mai farin cikin furta muku a yau burin da na da de da shi cikin zuciyata ya cika, zo nan Najma. Najma da gabanta ya wani irin fa duwa ba tare da ta san dalili ba ta mik e jikinta na rawa ta isa gaban mahaifinta da ya ke kallonta kamar yau ya fara ganinta. Hannu yasa ya jata kusa da shi azuciyarsa yana fatan Allah yasa ta amince da k addarar auren da ta k ullu tsakaninta da Jaheed kada ta bujire masa. Dafa kanta ya yi yana fa din  D ago Najma ki gaya min wanene ni? Tambayar ce ta mata banbarakwai don haka ta rasa amsar da zata ba shi illa ha diye wani kakkauran yawu da ta yi, ta san koma wane lamari abin mai girma ne kuma ba mamaki ita ya shafa.  Ki yi magana ma. Muryarta na rawa ta furta  Kai Babana ne?  Kin amince da hakan? Ta d aga kanta wannan karan cikin rauni. Ya saki ajiyar zuciya yana furta  Ina da iko da ke ko bani da shi? Kai tsaye ta furta  Kana da shi Baffa.  Alhamdulillah ya fa da yana sakin kanta ha de da zura hannu a aljihunsa ya zaro ku di bandir biyu yana mik a mata, hannunta na rawa ta saka ta amshi ku din hannu bibbiyu tana tunanin ku din menene sai ta ji amsar daga bakin Baffa cikin kakkaurar murya yana furta  Alhamdulillah yau na cika umarnin Ubangiji na aurar da ke ga Mijin da ya dace wannan shine sadakinki, ki shirya wani watan In sha Allah zaki tare a gidansa zaki yi azimi na zab a miki Jaheed a matsayin Mijin aurenki& &  d if ji da ganin wasu da dama daga cikin jama ar parlourn ya d auke na wuncin gadi. Jaheed ne farko sai Najma data kasa tantance abinda Baffan ya ce don tuni ta manta a duniyar da take da alama suman zaune ta yi. Sai Najwa da ta ji jikinta ya fara rawa jin a yau Wai Jaheed da take mafarki a matsayin Mijin aure shi ya auri Najma ba ita ba. Mahmeey kuwa tashin hankalinta ya fi k arfin kwatance kamar yarda na Nene ya kasa b oyuwa jin wai mara kunyar yarinyar data mugun tsanarta take kuma mata rashin kunya son ranta a gidan itace a matsayin Matar Jaheed sam ba irin matar da take masa Fata ba kenan. Umma kanta wannan ha din bai mata ba da kuma Baffan ya yi shawara da ita da ta gaya masa Najee ce ta dace da Jaheed ba Najma ba. Mahmeey ta mik e cikin tashin hankali tana kallon Baffa cikin gatsali ta ce  Amma dai Isma il a mafarki ka d aura auren nan ko? Don in dai ni na haifi Najma to sunan auren nan haramtacce a yanzu ba nan gaba ba wallahi sai ya sakar min y a& & & ..




A yi hak uri ina busy biki ya sa kwana biyu ban yi typing ba yanzu ma daure wa na yi na muku& .



JIKAR NASHE
'

KUDIRAR ALLAH.


Page 6.


NAZEEFAH SABO NASHE.



Baffa shiru ya yi duk da yarda yake jin zuciyarsa na matuk ar zafafa da jin rad ad in furucin Mahmeey idan har ya ce zai yi wata maganar ba zata zamo mai kyau ba, don haka ya rufe idonsa kawai yana sauraran kausasan kalaman da suke sake tafasa masa zuciya. Bata fasa fa dar duk kalmar da tazo bakinta ba, game da Nene da Jaheed.  Ka rasa wanda zaka aurawa y ata sai b aragurbi wanda baa san asali da tushensa d an mahaukaciyar da ka tsinto a hanya, d an da tabbas ba shi da suna da ya wuce shege to wallahil azeem sai ya sakar min y ata koda hakan na nufin komai ma. Baffa sai a lokacin ya d ago yana kallonta idanunsa suna bayyana wutar masifar da zuciyarsa take ciki.  Kika sake wani abin ya samu auren nan ki k addara a bakin naki auren& . Daga haka ya mik e ya kewayeta ya wuce don idan har ya cigaba da zama zata k arasa kunyata shi a gaban jama ar da suke ganin kima da mutuncinsa. Duk da dai a yanzun ma ba abinda ya yi saura. Tana ganin ya wuce ta juyo a fusace tana kallon Jaheed  Na fa da maka ka sakar min y a tun kafin ka yi aikin da ka sani don Wallahi ba ta yarda zan yarda na amince na ha da jini da d an mahaukaciya ba. Runtse idanunsa Jaheed ya yi yana saurarar dafin kalamanta da suke kamar za su huda masa zuciya saboda tsananin zafinsu. Ganin lamarin Mahmeeyn k ara ta azzara yasa Umma mik ewa cikin b acin rai ta ja hannun Nene da take zaune kamar mutum mutumi tsananin tafasar da zuciyarta take ciki kuwa Allah ne ka dai ya sani a wannan lokacin ji take kamar ta fasa musu sirrin da take aikin kudundunewa shekaru da shekaru. Umma tana jin sanda ta saki ajiyar zuciya mai nauyin gaske sai dai bata cikin yanayin da zata gane mai ya janyowa Nenen ajiyar zuciyar. Jaheed ma ganin sun fita ya mik e yana jin kamar ya kifa don jirin da yake d ibarsa. Lura da haka yasa Haidar saurin mik ewa ya rungumeshi ta gefe don kada ya fa di. Mahmeey ta bi su da wani mugun kallo kafin ta isa wajen Najma da take zaune kamar mutum mutumi da alama mutuwar zaune ta yi ko nace suman zaune. Don Mahmeey tana tab a ta ta yi baya ta fa di Mahmeey ta saka salati da kuka lokaci guda tana furta Shikkenan Isma il Ka kashe min y a burinka ya cika dama duk gidan nan y ay a na ka sakawa ido. Bai ma san me take ba don yana can cikin d akinsa zuciyarsa da ransa a jagule ji yake kamar ya fito ya zabga mata saki uku. Ruwa ta d ebo ta watsa mata sosai a fuska sai a lokacin ta kawo wani gwauran Numfashi tana kallon Mahmeey ta ce  Allah yasa mafarki nake Mahmeey ba gaske ba, idan gaske ne wallahi zan iya kashe kai na&  Mahmeey ta yi saurin rufe mata baki kafin ta ja hannunta tana furta  Mu je Najwa ki k addara mafarkin ki ke don wannan auren sunansa wasa Wallahi ko zan yi yawo tsirara ba zan bar auren nan ba sai na lallata shi. Kuka Najma ta fashe da shi sosai sanin cewa ba mafarkin take ba wato ta tabbata dai an d aura mata aure da mutumin da tafi tsana tab akwai tashin hankali kenan.


****
Umma kuwa Suna fita direct sashenta ta wuce hannunta rik e da Nene da take ta kakkarwa Umman tana jin yarda jikinta yake b ari bata kawo komai a ranta ba sai tunanin ko hayaniyar da aka yi ne ya tsorata ta.

Ta shige da ita d akinta zaunar da ita ta yi gefen gado kafin ta rufa mata bargo tana furta  Ki yi barci Nenne In sha Allah bakomai. Da zata lura Nenne wannan karan bata amsa mata maganar ba ba ta maimaita kamar yarda ta saba ba lumshe idanunta kawai ta yi don da gaske tana buk atar hutun itama ba kuma ta buk atar a hanata nutsuwa zuciyarta take buk ata da aiwatar da shegen tunanin da ya zame mata jiki ta Yaya cikin d an Sarkin gabas ya shiga jikinta ba tare da ita ko Sarkin sun tab a ganin juna a zahiri ba? Me ya faru ne? Ta fara tunano sanda lamarin ya faru kamar Majigi haka ya fara yawo a kwakwalwarta& & ..





************

Shekaru 29 da suka wuce& ..

__________________________



Wani d aki ne mai matuk ar duhu da rashin wadatacciyar iska, a cikin d akin Nene ce a zaune da k aton cikin haihuwa ko yau ko gobe, tsawon watanninta takwas a cikin d akin tun bayan bayyanar cikin jikinta da kai tsaye zata kira shi CIKIN KADDARA KO CIKIN KUDIRAR ALLAH. Tuni ta saba da zaman d akin don ta tabbatarwa kanta zamanta cikin d akin shine kwanciyar hankalinta fiye da bayyanar ta cikin mutane. Bata san dalili ba a duk sanda ta kalli cikin sai wani tsoro da firgici sun shiga zuciyarta, tsoro take ji irin tsoron da yake jijjiga k wakwalwa gani take a duk sanda ta haihu a masarautar sunan kanta fillalle don ga duk wanda ya ji labarin jinin sarki ta haifa D an Sarki na fari ne a jikinta wanda ita da kanta tana tsoron bayyana hakan ga mutane duk da ta san Cikinta halastaccen ciki ne da ko shi kansa Sarkin bai san da shi ba, ta yaya ma zai san da shi alhali bai san da ita kanta Uwar cikin a doron k asa ba, bai tab a ganinta ido da ido ba a zahiri bata sani ba ko a cikin mafarki, kamar yarda ita ma lamarin yake gareta kamar almara ko kai tsaye ta kira shi Mafarkin. Da wani baki zata gayawa Sarkin d ansa Halastaccen d a ne ba shege ba kamar yarda ta san mutane da dama za su yi hasashe. Ta yaya ma zai yarda da halaccinsa tunda ba wanda ya d aura mata aure da shi? Me ya kaita? Tabbas ta san idan ta bayyana kanta ,tabbas shi zai zama tsanin tafiyar ta lahira. Duk da ita kanta dole ce ta saka ta aikata hakan da kuma barazanar d aukar ranta.

Ta runste ido tana sakin wata zafaffiyar ajiyar zuciya ita gata k addara ta kaita ga samun cikin d an Sarkin bisa tursasawar Mutum guda da kai tsaye za a iya kiransa mai son zuciyarsa ko kuma mai son zuciyarta, don takamaimai ta rasa a wani jinsi zata saka mahaluk in da ya jefata cikin wannan sark ak iyar da babu mai fitar da ita sai Allah, Mace ce ko Namiji waye kuma a cikin masarautar? Abinda har kullum take wa kanta tambaya kenan tun bayan samuwar cikin nata, ba tare da sanin shi Kansa mai martaban ba, ta yaya ma cikin ya shiga shine abinda ta kasa sani ta hanyar ha da shimfid a ma ana kusanta tsakanin Miji da Mata ko kuma ta wani lamarin can daban da Allah ne ka dai ya barwa kansa sani, bata sani ba ba kuma ta san hanyar da zata bi ta sani d in ba.
Abu d aya ta sani a daren da komai ma ya farun ta tsinci kanta a wani killataccen d aki mai kyawun gaske wanda zata

5 / 22