Kudirar Allah Book Complete

Author :  Nazeefa Sabo Nashe Category :  Read Hausa Novels

Chapter   17 / 22

48K to 51K   out of 64.9K words

Ku kamata mu kai ta asibitin cikin Fada, a bata duk wata kula da ta dace ni zan raka Murad wajen taron can da zarar an tashi zan taho nan na duba ta Ya Allah ka dubemu ka bata lafiya. Ta fa da tana sauke idanunta kan Najee da ta bi duk ta tsorata da lamarin, ga shi duk motsin da Murad ya yi idanunta na kansa har abin ya fara ba shi haushi. Ya juya a fusace yana kallonta.  Ke d auke idanunki a kai na haba. Da sauri kuwa ta d auke idanun nata a kansa tana mamakin yarda yake masifa banbancin da yake nuna su kenan tsakaninsa da Jaheed shi Salihi ne bai fiya masifa sosai ba, ga yawan fara a shi kuwa wannan bata hango hakan tare da shi ba, tsabar ha de rai girarsa har kusan ha deta take. Tana kallo suka shiga mota aka saka Nenenta a wata Motar daban da sauri ta bi bayansu da d an k ullin kayansu da suke cikin buhu. Wani kallo Murad ya mata ganin ta nufi motar gadan-gadan  Hey you ina zaki? Ya fa da a tsawace sosai cikin muryar da ke bayyana zamowarsa Soja. Ta ja ta tsaya turus gabanta na fad uwa. Mamma ce ta ja tsaki tana harararsa  Ban gane ina zata ba? Mu buge nata Uwa sannan ka dinga tambayar ina zata? So kake mu barta anan don rashin tausayi? Je ki ki shiga can motar kin ji. Da sauri Najee ta shiga motar da aka saka Nenen Muraad ya bi bayanta da harara har da d an guntun tsaki bai san me yasa ba haka kawai sai ya ji yarinyar bata kwanta masa a rai ba, bai sani ba ko don tsananin muninta ne da rashin tsafta Oho? Ya d an tab e baki yana sakin ajiyar zuciya ka dan bai furta komai ba don ya san idan ya furta d in ma Mammah wannan karan zata iya kai masa duka a yarda ya hango tsananin b acin ranta.



Harabar gidan Sarkin Gabas d in ta cika mak il da jama a, abin har ya fara bawa Murad tsoro ganin yarda wajen ya zama ba matsaka tsinke kamar wani taron sallahr idi. Daga cikin motar ya saki ajiyar zuciya yana d an murza goshinsa ka dan saboda wannan abin ne fa sam baya son sarauta ga shi Bahbah ya kafe sai ya na da shi. Mamma da ta lura da yanayinsa ta saki tsaki a fili ta furta  Gwara ma ka sakawa kanka son jama a na dole in gaya maka, don Jama a yanzu ka fara ganinsu tunda ka zo a jinin sarauta nan gaba ma kai ne Sarki da yardar Allah. A fili ya furta  Ba ameen ba Mamma, ni fa bana son maganar sarautar nan wallahi da Bahbah zai bi ta tawa da Abdul ya na da wa abin nan, haka kawai a d orawa mutum abinda zai hana shi nutsuwa a bar ni da jidali, ni kayan sarautar ma ba son saka su nake ba na fi son Normal English wears. Mamma bata sake tanka shi ba, don ba k aramin haushi yake bata ba idan ta ji ya ce baya son sarautar nan ita kuwa burinta kenan ko dai ba a kira ta Uwar sarki ba, za a kirarta marik iyar Sarki tunda dai Murad ba shi da wata Uwar bayan ita. Ta fita daga motar tana furta  Addu a at first place yallab ai. Daga haka ta bi tsakiyar fadawanta zuwa inda aka tana da mata don zama. A kuma lokacin ne masu tafiya da Murad d in suka iso bakin motar suka yi saurin bu de masa ana rufe shi ta gefe da gefe. Murad ji yake kamar ya saka ihu ya runtse idonsa da ke cikin black shades d insa ta yarda duk bala inka ba zaka hango k waya idonsa ba. A haka fuskarsa a ha de ya dinga tafiya ta tsakiyar mutane don wannan shine karo na farko da mutane za su san Sarkin su mai jiran gado. Idanun da suke kansa sun yawaita don haka ya dinga jin matsanancin fa duwar gaba, mutane kuwa kallonsa suke sosai suna yaba kyawu da zatinsa mai bayyana cikar mazantakar d a namiji. Mata da yawa furta Ma sha Allah suke, sun san daga yau ba za su sake samun damar yi masa wannan kallon na k urilla ba. Haka al ada garin take ga duk wanda za a wa na din sarauta mai jiran gado sai ya bi ta cikin jama a sun masa kallon tsaf don duk sanda ya zama sarki ba su da ikon sake ganinsa sai dai a cikin rawani. Sai da ya gama zaga jama ar tas ya gama gaishe da manya sannan ya isa inda aka tanadar masa don ya zauna. Daga inda yake yana hango fuskar Maimartaba da take bayyana tsananin farin cikin da yake ciki. A zuciyarsa ya ce  Don kai ka dai zan amince da wannan sarautar Bahbah, banda haka da nemata za a yi a rasa.

Lokaci guda aka turo amintattun fAdawa biyu suka isa da shi gaban takawa. Inda anan ne za a na da masa rawani a kuma ba shi Sandar Yareema mai jiran gado. A gaban manyan Fada ya gurfana yana kai gaisuwa. Wasu da dama suka amsa cikin farin ciki yayin da fuskokin wasu yak e kawai suke wasu kuma bak in cikinsu ya kasa b oyuwa akan fuskarsu duk da k ok arin da suke na son aikata hakan.


Sarkin na din fada ya mik e ya isa gabansa bayan ya amshi rawani a wajen Maimartaba da ya yi dakonsa da kansa. Ya karb a ya fara nad a masa ana sakin ganguna masu wak a na furta sai ka yi. Ana na din Gaban Murad na wani irin matsanancin bugu zufa na keto masa ko ta ina. Addu ar Malam Jaluzi ya dinga karantawa a kan harshensa kafin ya samu nutsuwa a tattare da shi. Sarki na shirin mik a masa Sanda mai tambarin masarauta a jiki d aya daga cikin mutanen Fadar ya mik e yana kallon Sarki cikin idanunsa ya ce  Ba mu amince da na din wanda ba a san asalinsa ba, idan ana so mu yarda sai ka sanar da mu yarda ka samar da cikinsa da kuma Uwarsa.. Cak Sarki ya yi da sandar a hannunsa yana kallon mutumin da ya yi maganar cikin b acin rai ya furta  Ba ni da wata magana bayan wacce na fa da tuntuni kuma a shari ance babu dalilin da zai saka na kasa na da shi a matsayin Magaji na. Wani ma ya mik e yana cin magani wanda k anin Uba ne ga shi sarki Mukhtar ya ce  Ko da za mu bayyana wa jama a yarda ka samar da cikin sa?




JIKAR NASHE.
'

A yi hak uri da wannan ciwon kai ya saka ni a gaba na gode.


KUDIRAR ALLAH


21.


08033748387.


NAZEEFAH SABO NASHE.


Tuni wajen ya kaure da hayaniya jin abinda tsohon ya ce. Sarkin Gabas kuwa wani kallon cikin ido ya bi Baffan nasa da shi, kafin ya jijjiga kansa a hankali cikin sark ewar murya ta cikin loud speaker ya fa da yarda kowa zai ji.  Ina buk atar sani nima, kamar yarda kowa zai so sanin yarda aka samar da cikin Murad ba mamki daga yanzu mutane su daina zargi na a matsayin mutum banza su amince bani da hannu cikin abinda Allah ya zartar, fa dar taka na nufin k arshen duk wani azzalimi ya zo don na rantse da Allah a yau a yanzu kuma ba sai gobe ba zan fille kan duk wanda aka samu da cin amana da tozarta masarautar Gabas& . Hannun Baffan Gwandu ne ya fara rawa tsoro ya bayyana k arara a fuskarsa duk da k ok arinsa na son yakice haka, ashe bai sani ba kansa yake son k ullewa dumu dumu, burinsa tozarta Sarki shi yasa ya yi wannan maganar amma shi da kansa ba zai ce ga ta yarda aka samar da cikin ba, kwa dayin bawa d ansa Sarautar Waziri na uku shi yasa shi aikata haka, da alk awarin da aka masa na da zarar an samu kujerar ga shi nan yanzu ya jefa kansa cikin zargin Sarki k iri da muzu, don daga ganin Kallon da maimartaba yake masa yana tuhumarsa da abubuwa da dama ba kuma ya k yaleshi ba ne, idan kuwa haka ne ya shiga uku, ya kuma zama dole ya nemi wa dancan mutanen da suka d ora shi akan keken b era duk da bai san su ba bai kuma san su waye ba sakamakon basaja da suka yi a kamanninsu, muryarsu da shigarsu. Ko za a kasheshi a yanzu dai ko yatsansu bai sani ba, bai san kuma kalar jikinsu ba. A yarda suka yi da shi da zarar ya fa di wannan maganar za su mik e su mara masa baya da shi da wanda ya fara maganar sai dai wayam ba su ga kowa ba, abin abin al ajabi da almara sai ka ce wani aikin Jinnu, ko dai ma ba mutane ba ne?

Hayaniyar ta cigaba da wanzuwa a wajen taron kowa burinsa ya san yarda aka samar da cikin Yareema Murad sarki ya ciga da kallon Baffan Gwandu yana furta  Jama a na saurararka kai da wanda ya fara magana. A cikin muryar Maimartaba suka jiyo rashin sassautawa ga duk wanda aka kama da laifin. Baffa k asa ya yi da kansa ta idanun mai martaba ya hango dukkan wata nagarta da martabarsa ta zube a idanun Maimartaba yaron da suka raina aka haifeshi a gabansu. Ya share zufar da ta fara zubo masa a goshi hannunsa har rawa yake don tsoro da razani, Sarki kuma ya kafa ya tsare akan dole sai ya fitar da shi da jama arsa a duhu. Muryarsa na rawa kamar wanda aka shak e ya fara magana  A yi hak uri,wallahi sharrin shai dan ne da ru din duniya, wallahi nima ban san su ba su suka umarceni dana aikata haka idan na fa da za su tashi su mara min baya, ko fuskarsu ban sani ba balle kamanninsu a min afuwa. Waje ya sake kaure da hayaniya masu zagin Baffan Gwandu na yi shi dai ya yi k asa da kansa. Sarki kuwa ido ya kafa musu yana nazarinsu a yanzu shi kansa burinsa sanin wancan kwamacalar ya kuma so a ce sun sani d in. Ya girgiza kai yana kallon fadawansa ya nuna musu su.  Ku killacesu har zuwa sanda za su fa di gaskiya. Haka kuwa aka yi aka tisa k eyarsu zuwa gidan Yarin masarautar. Sarki ya saki ajiyar zuciya kafin ya umarci Sarkin NAD i akan ya cigaba da na dawa Murad rawanin da yake yi. Surutun mutanen ya  dan ragu a wajen kowa yana cigaba da al ajabin lamarin. Gefe guda Fulani Raheena ma a cikin tsananin mamaki take da tsoro game da ru dani da ya haifar mata da wata irin fa duwar gaba, kada dai wad ancan mutanen da itama suke zuwa mata a wata siffa jikinsu sunk uf duk kuma k wak warka baka isa ka gano su waye ba muryarsu ma bata kama da ta wa danda aka sani, kada dai kamar yarda Baffa Gwandu ya ce Aljannu ne su tabbatar Aljannun sune suke tsorata kamar yarda suke tsorata su Baffan. Ta runtse ido a fili ta furta  Ya salam! Tana jin wani matsanancin tsoro yana sake damalmala zuciyatta. Allah Allah take a tashi daga taron ta je ta kira wayar da suka saba magana da mutanen don ta tabbatar da zarginta.


Aka na dawa Murad rawanin da ya zauna tsaf akan sa ya kuma masa kyau sosai ya k ara masa kwarjini da Haiba. Da gaske sarauta ta amshe shi duk da shi yana nesanta kansa da ita da gudun fanfalak i. Ya d an damk e hannunsa kunnuwansa suna cigaba da jiyo masa maganganun mutanen masu yaba kyawun sa da nagartarsa gefe guda kuma ta ajjabi da mamakin yarda aka samar da cikinsa shine yake harzik a kwanyarsa ya dinga sakin ajiyar numfashi a hankali kamar ko wani lokaci da idan tunanin ya masa yawa ya kan haifar masa da ciwon kai mai tsananin gaske yanzun ma hakan ce ta faru ya runtse idonsa yana jan Hasbunallah a hankali. Lura da kamar hayaniyar tana damunsa ne yasa Maimartaba bawa amintattun fadawansa damar matsar da shi zuwa cikin sashensa ko ya samu nutsuwa. Haka kuwa aka yi Murad ya ji da din hakan da suka masa ya mik e da d an hanzari Fadawa Suna fa din gyara kintsi suka yi saurin shigar da shi cikin motarsa da kuma sauri aka ja motar saboda yarda jama a suka fara dafifi a wajen motar da burin d aukar sa a hoto. Murad yana jin sanyin a cn motar ya lumshe idonsa a hankali yana sakin ajiyar zuciya kafin ya cigaba da tunanin da yake. Tafiya mik akkiya aka yi kafin isa Babban sashensa da aka masa gini na Zamani mai kyawun gaske inda Sarkin yake so ya masa aure ya kuma tare a wajen saboda hayaniyar da masarautar ta d auka yasa Sarkin ya ce a kawo shi nan d in, kuma daf yake da Babban clinic d in da yake cikin masarautar.


Ya bi wajen da kallo haka kawai sai ya samu kansa da son zuwa yaga halin da matar da suka buge take ciki, duk da shi mutum ne da bai damu da sabgar mutane ba sai ya ji lamarin Matar ya tsaya masa a rai yana kuma don yaga halin da take ciki. Fadawan ya kalla a hankali yana furta  Let check on her. Suka bi shi da kallo ba tare da sun san me yake nufi ba, tunda ba da su aka bugeta ba balle su san wa yake magana a kai. Idanu suka zuba masa kafin suka ya wuce da d an hanzari cikin irin tafiyar sojoji. Suma bin sa suka yi da sauri tunda ba su san wacece ba. A reception d in asibitin nurses suka dinga kawo masa gaisuwa cike da mamakin wanzuwarsa a asibitin don haka sabon abu ne a wajen su da basu tab a gani ba musamman yau da suka san babbar rana ce a wajensa. Ya tsaya daga jikin Babban counter d in da ke wajen yana kallonsu d aya bayan d aya cikin jin haushin kallon da suke masa ya ce  Where is she? Hope she is alive. Ba tare da gane abinda yake nufi ba suka bi shi da kallo su ba abin su ce masa Who ba? Ba su isa ba ba su da wannan ikon. Cikin takaici ya sake zuba musu manyan idanunsa yana fa din  Can t talk? Rusunar da kai receptionist d in ta yi tana furta  Am sorry Sir, but I didn t understand what you mean. Sai sannan ya san laifinsa ne da bai sanar da su wacce yake nufi ba, ya  dan murza goshinsa yana furta  The old woman da ta samu accident d azu. Sai sannan suka gane abinda yake nufi. Suka d aga kai Suna fa din  Yes she is alive, Allah ya kiyaye ta dai samu rauni a kanta apart from that ba wani abu. Ya saki ajiyar zuciya har zai fita sai kuma ya juya yana furta  Bari na ganta. Ba su yi wata wata ba suka tafi da sauri don nuna masa d akin da aka kwantar da ita. Yana tura d akin idanunsa da na Najwa suka sark e waje d aya, a fili ya ja tsaki yana furta  A witch. Ya d auke kansa da sauri yana kallon Nene da ke kwance idanunta a rufe kamar mai Barci sai dai ba barcin take ba, tsabar tunani ne ya cunkushe mata zuciya na rashin tudun dafawa idan har ta bayyana kanta a matsayin uwarsu Murad ta ya zata sanar da mutane yarda cikin ya shiga alhali ita kanta bata sani ba. Masifaffen k amshin da ta ji ne yasa ta bu de idanunta da sauri sai kuwa idanun suka sark e da na Murad da yake tsaye yana kallonta. Wata irin fa duwar gaba suka shiga duka su biyun suka kuma kasa d auke idanunsu daga kan juna da suke wa junansu kallon k urilla. Murad bai san dalilin kallon ba ita kuwa Nene ta sani, cikin wani irin yanayi take kallonsa k walla na neman zuba daga idanunta, ba na komai ba sai don tsananin farin cikin ganin Murad a gabanta, cikakken mutum managarci mai nutsuwa da duka suka bayyana akan fuskarsa, da gaske Murad ne don ko ka dan babu banbanci a kamanninsu da Jaheed, illa Murad da ya fishi yawan saje da cikar gashin gira da na ido da suke kwance sun wa idanunsa rumfa, ita ka dai ce da take matsayin Uwa zata gane wannan banbancin, wani irin maganad isu ya dinga jan hannunta ji take kamar ta janyo Murad  din ta saka shi a jikinta ta sanar da shi itace Mahaifiyar da ta reneshi a cikinta cikin duhu war d aki, itace mAhaifiyar da ta yi nak udarsa ta haifeshi, sai dai me idan ta sanar da shi hakan wace amsa zata ba shi idan ya tambayeta ta yaya ta samu cikinsa da kuma dalilin da yasa ta tafi ta bar shi? Bata da amsa amma haka nan ta ji zuciyarta ta yi rauni kuka ya kufce mata kukan da tun lokacin da abubuwan suka faru bata samu ta yi shi ba sai yanzu da taga Murad a gabanta cikakken namiji, hannu na rawa leb enta na rawa cikin wata irin murya ta furta  MURAAAAAAD!





JIKAR NASHE
'

Kin siya kuwa ko har yanzu? Book

17 / 22