Kudirar Allah Book Complete

Author :  Nazeefa Sabo Nashe Category :  Read Hausa Novels

Chapter   2 / 22

3K to 6K   out of 64.9K words

ya gama kallon fuskarta da take d auke da Tsananin farin ciki, da alama sak on da mahaifinta ya bayar ta isar masa shine abinda ya saka ta tarin farin ciki da annashuwa.
Bata sani ba shi sak on yazo masa a hagunce da ta ta fassarar madadin farin ciki kwatankwacin nata, nasa hankalin tashi ya yi ya kuma shiga irin wancan yanayin da yake riskar kansa a duk sanda budurwa zata gaya masa sak on mahaifinta ya ce ya turo. Ya bu de tattausan idanunsa masu tsananin kyau da haiba ya zuba mata su, k walla ce kwance a saman idanun wanda k arfin zuciya da taurin rai yasa ya kasa sakin su su zubo. Namijin gaske ne da yake iya b oye rauni da gazawar zuciyarsa a lokuta da dama, duk da matsalar da yake ciki ya ci
A koka mata koda kuwa kuka ne mai kuwa da kururuwa. K addarace mai girman gaske take watangaririya da rayuwarsa, irin k addarar da kai tsaye mutum zai ce dama Allah bai haliccesaba matuk ar bai jajirce akan doron Imaninsa ba, da sanin cewa Allahn ne dai shine yake jarrabarsa don ya auna nauyin mizanin sa. Ya gani shin bawansa zai iya yarda da k addarar har ma ya rungumeta a yarda ta zo masa. Hawayen da Khairi ta gani cikin idanunsa su suka k arya mata gwiwa har nata farin cikin ya zagwanye ya bi iska. Cikin mabayyanin tashin hankali ta ce  Me ya faru Hubby? Kada dai maganar Abba ce ta b ata maka rai baka shirya aurena bane? Ya girgiza kai yana k ok arin togace tashin hankalinsa ya ce  Na shirya Habibteey, sai dai ke da kan ki tun a farkon fari na sanar da ke wanene ni? Abinda nake tsoro idan Har ke kin amince kina tunanin Abba za su amince idan suka yi bincike a kaina suka gano ni ba kowa bane face d an mahaukaciya da bata san inda kanta yake ba, balle ta gano waye ya mata ciki har ta samar dani? Khairi shiru ta yi zuciyatta itama tana tsallen tashin hankalin. Tuni ta manta da wannan matsalar ta JAHEED sai yanzu da ya farkar da ita, tabbas ita ta san waye mahaifinta mutum ne mai zafin gaske mai kafaffiyar Ak ida wanda ba a tab a tankwara zuciyarsa idan har ya gano wanene JAHEED ko zata mutu ba zai bari ta aure shi ba, ita kuwa a yarda take jin soyayyarsa a zuciyarta zata iya aurensa da amincewar mahaifinta ko babu.
Don haka ta saki ajiyar zuciya tana kallon JAHEED cike da tausayin yanayin k addararsa da ba laifinsa bane asali ma da za a tambayeshi zab i ba zai yarda yazo duniya ta wannan hanyar ba. Murya cike da rauni ta saki ajiyar zuciya hawayen da ta kasa b oyonsu suka fara karakaina a kan k uncinta bata san sanda ta kama hannun JAHEED ba ta ce  Ba mai raba
Mu JAHEED ko suna so ko basa so sai na aureka. Da sonka Allah ya halicceni na tabbata ina jin kai ne maha din rayuwata, ruwa da iska ina tare da kai am always your s. Ta fa da tana saka fuskarta a cikin tafin hannun JAHEED d in tana sakin kuka mai k arfin gaske mai saka tausayi a zuciyar mai sauraro. Shiru JAHEED ya yi yana sauraran kukan nata da yake raunata zuciyarsa yana jin shima kamar ya saki nasa kukan, sai dai dakiya da k arfin zuciyarsa ya hana shi aikata hakan. Madadin hakan wani irin ciwo da bugu zuciyarsa take yi kamar yarda ta saba a lokuta da dama idan haka ta faru da shi. Sau hu du yana neman aure sau hu dun kuma ana hanasa dalilin rashin asali da cikakken tushe yana ji yana gani yake rasa abinda zuciyarsa take so da Muradi. Khairi itace budurwa ta biyar da yaso yana ji kuma a jikinsa wannan shine zai zama ganin da zai mata na k arshe. Shikkenan shi haka rayuwarsa ta zo a juye irin tasa k addarar kenan mai zafi da wuyar sha ani. Kalaman Khairin da take sake kwararo masa mai nuni da tsananin soyayyar da take masa basu k arfafa masa gwiwa ba, don suma wa dancan Matan ba abinda basu ce masa ba k arshe bisa tilas suka rabu bai sake jin d uriyarsu ba.


Ya janye fuskar Khairin daga tafukan hannunsa yana kallon hawayen da take zubar wa yana jin zafin zubar su kamar dalma a zuciayrsa.  Ki yi shiru Khairi ni na san tabbas a wannan karan ma banda sa a, kuma In sha Allah daga kanki ba zan sake soyayya ba zan yi hak uri haka Allah ya k addaro min. Kuka ta saka sosai tana sake k arfafa masa gwiwar ya turo neman aurenta In sha Allah zata yi addu a tana ji kuma a jikinta wannan karan Abbanta zai amince ya ba shi aurenta. Ya yi shiru yana nazarin idanun Khairin soyayyar Khairi mai girma ce a zuciyarsa zai iya cewa bai tab a tsintar kansa a kwatankwacin soyayya irin ta Khairi ba. So yake mata irin son da ake kira Pure love, wanda shi da kansa ba zai ce ga dalilin da yasa yake son Khairi ba. Tun bayan da ya ha du da ita bai sake samun nutsatstsen barci ba kullum itace a cikin barcinsa da tunaninsa. Kamar yarda kullum zuciyarsa take cikin fargaba da rauni akan kada a zo gab ar da zai rasa Khairi, baya jin a wannan karan zai iya jurewa. Ya saki ajiyar zuciya yana jan siraran yatsunta ya sake murza zoben sa da yake hannunta da nata da yake hannunsa wanda suka kira zoben Alk awari. Allah yasa mfarkinsu ya zama gaske yau ya gan su a matsayin ma aurata shi da Khaireey bai san wace irin godiya zai wa Allah ba, tabbas zai iya yin azimi sittin don murnar auren Khaireey.  Shikkenan Habibteey ki je gida, zan je na yi magana da Baffa, za a turo idan Allah yasa an dace shikkenan idan kuma ba a dace ba ina rokonki ki yi hak uri mu rik e k addararmu. Da sauri Khaireey ta girgiza kai  No JAHEED I can t ba zan iya rayuwa ba tare da kai ba JAHEED love. Idan bai yarda ba mu gudu kawai mu yi auren mu. JAHEED ya saki murmushi wanda yake bayyana ciwon da zuciyarsa take masa ya d aga mata kai kawai ba wai don ya amince da tunaninta da ya kira shirme ba sai don son ya
Kwantar mata da hankali. Ya ce  Okay maza ki je gida, ki yi mafarkin JAHEED mafarki mai kyau kin ji Khaireey, ki yi mafarki na ina kissing those sweetable lips. Ya fa da yana k urawa lab banta da suke fusgar hankalinsa ido. Da sauri Khaireey ta runtse idanunta ta fice da Motar da gudu. JAHEED ya saki raunataccen murmushinsa kafin ya lumshe ido hawayen da yake ta killacewa suka samu damar silalo masa. Tabbas soyayyar Khaireey daban ce a zuciyarsa tunda har ya tsiyayar mata da k walla. Da k yar ya samu ya ja motarsa a hankali ya har harabar gidan zuciayrsa na ayyana masa ba mamaki ban kwana ya yi da Khaireeynsa.


_
Yarda yake tuk in cikin rashin nutsuwa shi da kansa bai yi tsammanin zai iya sa gidan da ake rik onsa lafiya saboda yarda zuciyarsa ta rasa sukuni ko ka dan. Mai gadi ya bu de masa gate ya yi parking a wajen da aka tanada don ajiye motoci. Nan d in shine gidansu gidan da tun yana jariri anan ya taso shi da mahaifiyarsa bai san kowa ba sai mai gidan shi ya ba shi duk wata kulawa da shi da Uwar gidansa da yake jin ta tamkar mahaifiyarsa tunda ita ta raineshi har kawo yanzu da ya kai munzalin aure. Ba zai ce baya fuskantar k alubale a zamantakewar gidan ba a a yana samu daga b angaren Matar gidan ta biyu dama y ay anta gaba d aya da suka d au karan tsana suka d ora masa shi da mahaifiyarsa da suke tunanin Akwai dalili mai girma da Baffa yasa yake kula da Mahaukaciyar, duk a zuciyar Baffa bakomai illa son cika umarnin Manzon Allah da kuma tausayi da jin k ai irin na duk wani managarcin d an Adam. Sam Baffa baya banbanta shi da yaransa na cikinsa k aunarsa yake kamar y ay an da ya tsuguna ya haifa, idan banda Anty da take kwaza ba Baffan bane ya haifeshi ba wanda zai gane idan ba fa da maka aka yi ba.


Ya dad e cikin motar saboda yarda gabbansa suke cikin rashin kuzari da raunin zuciya. Kafin ya d auke kwantacciyar k walla da take idanunsa ya saki ajiya zuciya a hankali ya bu de motar ya fito yana zuro k afarsa. Idanunsa suka fa da cikin na Haidar da ya sakar masa murmushi don nufo motar ya yi da ya gaji da jiran Jaheed d in. Haidar tare suka taso shima d an Umma ne ita kuma ta rainesu kamar y an biyu, bata banbanta su ko a wajen kayan sawa har abada ba zai manta karamci Umma a kansa ba. Haidar ya d an daki kafa darsa yana furta  Mutumin daga ina? Jaheed ya saki ajiyar zuciya ya ce  Daga wajen Khaireey. Murmushi Haidar ya yi yana furta  Na Khaireey ba da kanka a sare, amma naga mood d inka is not good me ya faru? Jaheed ya d an dube shi kamar ba zai ce komai ba sai kuma ya tuna yarda suke da Haidar basa iya b oyewa junansu damuwa kamar dai y an biyun zahiri. Ya saki ajiyar zuciya ya ce  Abbanta ya bani umarnin na fito neman aurenta idan da gaske nake yi. Haidar shiru ya yi shima hankalin sa na d an tashi yana tsoron afkuwar rashin nasara kamar yarda wa dancan neman aurarrakin suka dinga lalacewa, an kuma rasa makirin da yake zuwa dangin Y an matan ya kwatsa musu asalin Jaheed. Tun lokacin da shi Haidar ya yi nasa auren Jaheed d in yake ta walagigin neman aure amma an rasa dacewa saboda waccan gundumemiyar matsalar. Jaheed ya dubi Haidar da ya lula duniyar tunani ya ce  Ina ji soyayya ta da Khaireey itama ta zo k arshe kamar yarda wa dancan ma suka wuce
Kamar ba a yi su ba, amma ban tab a jin haushin rasa budurwa ba kamar yarda yanzu zuciyata take cike da rauni da k unci na rasa Khaireey da zan yi a karo na biyar, Ina son Khaireey Haidar. Haidar ya  dago idanunsa da suka ka da suka yi jajir ya zuba akan Jaheed shi d in zuciyarsa ta raunata matuk a ainun saboda tausayin halin da d an uwansa yake ciki. Tabbas da ace Najwa ta girma ta isa aure ba abinda zai hana shi aurawa Jaheed, tunda itace k anwarsa da suke ciki d aya da ita yake iko kaf gidan ita ka dai ce mace a cikin y ay an Umma su biyar, sai dai she is too young shekarunta 14 only. Su kuma wad ancan fitsararrun da suke Uba d aya Nasma Da Najma dama ba a zancensu don sun raina Jaheed d in matuk ar raini sun tsani ko bu de ido su yi su gan shi a gidan. Gudun kada ya sake raunata Zuciyar Jaheed d in sai ya dafa shi. Ya CE  Kada ka karaya mana Bro, In sha Allah Lokaci yazo da kaima zaka angwance ina jin hakan a jikina just pray Nima kuma Zan taya ka. Sannan mu samu Baffa mu sanar masa In sha Allah za a dace, fatan mu kada Allah ya bawa makirin da yake zuwa ya rusa maka maganar aure dama a wannan karan. Jaheed ya d aga kai yana furta  Ameen ba wai don har a zuciyarsa yana saka rai zai samu Khaireey ba sai dai dole zai bi shawarar Haidar don basu tab a k in yiwa juna Biyayya akan shawara ba.

Daidai lokacin rantsatstisyar motar bak a wuluk ta shigo cikin gidan a mugun speed, ga wani ki da mai k arfin gaske an ware a cikin motar. Sauti yake bayarwa sosai. Haidar take ransa ya b aci don ya san ba kowa bace sai Najma itace mai wannan banzar d abi ar yarinya kamar rainon kafirai, ba Kuma laifin kowa bane sai na Uwarta data ke d aure mata k ugu. Jaheed kuwa ji ya yi kamar zata tarwatsa kan sa don a rayuwarsa baya son hayaniya shi mutum ne very cool bai Kuma son shiga shirgin kowa.

Wawan parking ta yi a gefensu, ta fito cikin takun k asaita da nuna isa na isassun mata. Idanunta sanye da bak in shade da ya k ara mata rantsatstsen kyan da take alfahari da shi. Ta cikin glass d in take jifan Jaheed da wani wulak antaccen kallo ta isa ta gefensu zata wuce. Murya a ciki ta ce  Ya Haidar barka da yamma. A ciki ya amsa tana shirin shigewa ya kira sunan ta a tsawace, cak ta tsaya ba tare da ta juyo ba duk da suna shakkar Yaya Haidar  din da fa dansa amma ba zata nuna a gaban mutanen da ta tsana ba.  Ni ka dai kika gani a wajen? Ta juyo a zafafe tana kallon sa kafin ta ce  Kai ka dai ne ya wajaba na gaisa da kai. Mamaki bai bar Haidar ya mata magana ba, tsananin mamakin gadara da tsaurin idon ta. Kunyar Jaheed ce ma ta kama shi, da sam bai nuna ya san me suke ba danna wayar sa kawai yake, duk da maganar yarinyar ta doki dodon kunnensa kuma ta yi masa zafi matuk a sai dai bisa tilas ya shanye don ba yau ya fara karb ar wulak ancinta da rashin mutuncinta ba ya Riga ya saba da ita da y ar uwarta da ma uwarsu gaba d aya basa ganin k ima da mutuncinsa duk da dama shi d in ya sani a wajen mutane ba shi da wata k ima balle daraja irinsu da aka haifa a titi rashin Uba ya kan janyo musu tsana da wulak anci daga wajen jama ar da ba su kai su ba ma balle su taka k afarsu, balle ita wannan da yake ganin karanta ya kai tsaiko, a k ark ashin Ubanta yake, cin sa da shansa tun yana zanin goyo Ubanta ne ya d auke su shi ya samar masa da nagartaccen ilimin da yake tunk aho da shi a yanzu. Don haka ba zai damu ba so samu ne shine zai zama mai gaisheta da nuna ladabi a wajenta abinda suke so kenan, shi kuma ya kasa musu girman kansa da fa din ransa da yake jin sa kamar basarake ya kasa yarda ya amince wa zuciyarsa ya Zauna a taka shi. Ya yarda shi shege ne mara gata mara galihu amma bai amince shi d in mara daraja bane, yana kallon kansa a wani mutum mai daraja ta farko a cikin mutane, don haka ba zai tab a k ask antar da kan sa ba. Haidar ya saki ajiyar zuciya yana kallon Jaheed da ko a fuskarsa bai nuna damuwa da abinda Najma ta masa ba, madadin haka ma wani k ayataccen murmushi ne kwance a kan kyakykyawar fuskarsa mai d auke da zagayyen saje. Cikin sakakkiyar murya ya ce  Yaushe ka ke ganin ya dace na samu Baffa da maganar? Haidar ya saki ajiyar zuciya shima ya nuna bakomai d in kamar yarda Jaheed ya bagarar ya ce  Ko yau da Magriba sai mu same shi mu ji abinda zai ce. Jaheed ya diro daga kan motarsa yana mik a masa hannu ya ce  Allah ya kai mu, ka gaisar min da yara na da madam, ace da d an rigimata wannan week end Zan zo na kai su park. Haidar shima murmushin ya yi ya mik a masa hannu yana jinjina zuciya irin ta Jaheed mai k ok arin nuna komai ba komai ba duk tsananin b acin ran da yake ciki ba dai ka gan shi a kan fuskar sa ba, sau tari har mamakin hakan Haidar yake yi. Ya saki ajiyar zuciya yana fad awa motarsa don ya isa gida da wuri don yaga yamma ta yi.


 Open this link to join my WhatsApp Group: https://
chat.whatsapp.com/.
EZyeAwHEGGhJz1pRBmmale



K UDIRAR ALLAH

2.

NAZEEFAH SABO NASHE
'

08033748387.

Bin motar Haidar ya yi da kallo kafin ya saki sassauk ar ajiyar zuciya yana lumshe idonsa wani irin zafi da turiri yake jin zuciyar sa take yi, duk da k ok arin danne b acin ran da yake yi hakan bai hana bayyanuwar b acin ran akan kyakykyawar fuskarsa ba. Tausayin kansa ya sake mama ye shi kafin ya d au hanyar da zata sada shi da ainahin cikin Gidan direct.

Faffad ar haraba ce mai girman gaske fiye da ta wajen da ake ajiye motoci. Bakomai a harabar sai manyan bishiyu da suka yiwa tsakargidan ado da inuwa mai k ayatuwa a idanun mai kallo. Yanayin damuna da ake ciki ya sake k awata wajen baka sha kar komai sai k amshin tarin bishiyun da suke cikin harabar lemon tsami guava mango da sauran dangoginsu. Ya sake mai da hankalinsa kan k ofar da zata kai shi sashen da Umma take marik iyarsa inda anan aka warewa tasa mahaifiyar nata d akin mai d auke da parlour da toilet aka kuma saka mata duk wani abin more rayuwa duk da zamantowarta mara hankali bai hanata tsaftace d akin ba idan ka shiga zata zaka yi mai cikakken hankali ce mamallakin sashen.

Umma da take zaune a babban parlourn da ya raba sashenta da na Mahaifiyar Jaheed d

2 / 22