Kudirar Allah Book Complete

Author :  Nazeefa Sabo Nashe Category :  Read Hausa Novels

Chapter   6 / 22

15K to 18K   out of 64.9K words

iya cewa ba tab a ganin irinsa ba ko da a cikin fina finai. Tana kwance ta ji kamar shigowar mutane suna magana k asa k asa da alamar farin ciki a cikin muryar tasu duk da ta kasa banbance muryar tasu tunda sun bu da ta sun kuma kaurarata inda duk masifar ka ba zaka iya shaida mamallakin muryar ba ko da kuwa ka masa farin sani balle a ce baka san shi ba. Aka haske ta da fitila mai tsananin haske kafin cikin bu dewar murya mai sanye da bak ak en kayan sink if ya fara magana,  Burin mu ya cika mun gama namu aikin, abinda za mu jira yanzu shine bayyanar cikin a jikinta idan aka dace sai mu jira haihuwarta kafin mu k wace jaririn ita kuma mu salwantar da rayuwarta. D aya daga ciki ya ce  Wannan shine abinda ya dace da ita, an kuma umarcemu kada mu sake ta gudu kada mu barta a haske ma balle ta samu damar guduwa da zarar ta haihu kuma sunanta gawa don gudun tonuwar asirin mu.

Wannan shine abinda ya tayar mata da hankali tunda duk maganganun nasu sun yi su ne a cukurku de ba kuma su bata wata k ofa da zata gane dalilinsu na aikata hakan ba. Abu d aya ta sani an tirsasa ta samun cikin ne aka kuma tsareta aka killace a wannan bak in d akin tun bayyanar cikin aka kuma saka manyan fadawa marasa Imani su tsareta su killaceta ba kuma za a saketa ba har sai bayan ta haife abinda ke cikinta sannan a kuma k wace d an ita kuma a koreta bayan an haukatar da ita ko kuma a kasheta kamar yarda ta ji masu bak ak en kayan suna fa da Hauka zata iya warkewa su Kuma basa son ta samu sauk i ta tona musu asiri gwara kawai idan ta cika musu burinsu su kasheta, ta san za su iya tunda bata da wani gata iyayenta bayi ne da aka siyesu suke bauta shekara da shekaru bata san asalin su ba idan ma akwai zuwa yanzu ta san sun k are tunda yak i aka yi ya ci garin hakan yasa Iyayenta suka zama ganimar yak i mamallakinsu kuma ya zo ya siyar da su a wannan masarauta mai cike da d imbin tarihi.


Duk wannan maganganun ta ji su ne a daren da aka gark ameta a d akin. Bayan kwana biyu matar mai bak in kaya ta kawo ziyara d akin bata santa ba don bata bari taga fuskarta ba har ila yau ta kasa tantance muryarta don muryar tana fita a kaurare ne saboda bata san a san wacece ita, duka tana ji ta bada umarni. Abu d aya ta sani koma wacece tana son cikin ne tana kuma muradinsa ba don ta cutar da shi ba sai don cika wani burinta a kansa, ta fuskanci haka ne ta hanyar abinci mai kyau da gina jiki da ake bata wanda ake son duk masu ciki sun ci, a duk kuma bayan satittika akwai likitan da ake sawa yazo ya duba lafiyarta da abinda yake cikin. D akin ne dai a duk daren duniya ake kashe fitilun cikinsa daga waje switch d in fitilun yake don haka idan suka gark ameta bata da ikon sake ganin gaske sai kuma washegari ta inda suke da tabbacin ko Karen hauka ne ya cijeta ba zata fita da rana ba tunda ta san da zarar ta aikata hakan kai tsaye zata amsa sunan GAWA a cikin k urataccen lokaci. Mutane na biyu kuwa da suke zuwa su ma ta lura suna buk atar cikin sai dai ko misk ala zarratin babu tausayi da imani a tare da su abinda ta lura kowa da abinda yake so game da ita ba kuma su san suna tarayya wajen son cikin su dukkansu ba kamar yarda alamu suka nuna Mutanen farko ba su san mutane na biyu sun san da ita ba kowa bulayi yake cikin duhu da kuma k wak war son cikin.


A lissafin su a yanzu cikin nata ya isa haihuwa don haka aka sake tsaurara matakan tsaro a bakin d akin, ba wanda ya san da ita a ciki saboda girman masarautar can a gefen masarautar aka killaceta. Ganin hasken da ya gauraye d akin yasa ta san safiya ta yi idan kuma ba safiya ba ce ta yi tabbas masu kawo mata ziyara ne, gabanta ya fa di duk da basu kasance masu cutarwa a gareta ba amma maganar kisan ta girgiza hankalinta shi yasa a duk sanda ta gansu take tsintar kanta cikin wani yanayi mai bayyana tsagwaron tashin hankalin da zuciyarta take ciki. Aka turo jibgegiyar k ofa mai tsawon gaske wacce aka d aure ta tamau da jibegegiyar sark a don ta itace ma da sun bar kayarsu a bu de don ta san ko Karen hauka ne ya cijeta bata isa ta tsallake umarninsu ba idan ba so take su yi gunduwa gunduwa da namanta ba, don kowa ya san Tarihin masarautar Sarkin Gabas bai fiye Zafafawa rayuwa kamar yarda wad anda suke kewaye da shi suka zama
Mugaye na gasken gaske, suka kuma mayar da ran bayi ba a bakin komai ba su kashe wanda suke so a lokacin da suka ga dama da son ran Sarkin ko ba son ransa don shi dai kawai zaune yake a kan kujerar mulki amma don ya ci gadonta kuma a k aidar garin duk wanda ya ci gadon kujera daga Ubansa babban d a shi ake bawa mulki, hakan yasa ake wata irin rayuwa a masarautar kowa ya zama mugun kansa. Shi yake mulki amma a b angaren gudanarwa mulki ya zama d an kallo don shakulatun b angaro suke da mulkinnasa su ci zarafi da keta Haddin duk wanda suke so.


Aka turo k ofar da k arfi, hakan yasa da sauri ta yi k asa da kanta don basu bata damar kallonsu ba, ko kuma don ta saba a haka dama suke a gidan sarautar wasu mutane ne su marasa galihu da basu isa su yi iko ko da da yatsansu ba sai abinda aka zartar a kansu.


Takun suka shiga yi mai cike da firgitarwa da razanarwa k amshin turarensu mai k arfin gaske da ko ba a fa dawa mutum ya san mai tsada ne ya cigaba da samun muhalli a cikin d akin a duk sanda suka shigo sai d akin ya yi kwanaki yana zuba wannan mayataccen k amshin.

Zama suka yi a saman kujera su biyu ne dai kamar yarda suka saba zuwa, sai wata likita da take sunk ife cikin nata bak in kayan baka ganin komai a jikinta har fuskarta. Cikin tausasawar kalami dkamar ba wad anda suke son cutar da ita ba suka bata umarnin kwanciya a kan gado don likitan ta mata awo, saboda a cikin d akin har Scanner machine na duba yaro akwai. Likitan ta fara aikinta su kuma suka kafawa scanner d in ido ta inda tas suke hango jaririn a cikin mahaifiyarsa yana ta wutsilniya da alama mai lafiya ne kuma namijin da suke fata, gefe guda kuma wani dunk ulallen abu suke gani a cikin nata da suka kasa gane menene. D aya daga cikin mutanen suka ce  Abin da aka fata ya samu, burin Uwargijiya zai cika ga yaro Masha Allah kyakykyawa da shi. Na kusa da shi ya kalli likitan yana furta  Zuwa wani lokaci za a yi tiyatar a cire yaron ita kuma daga nan ka san yarda zaki mana da ita Uwargijiya dai ta gaya miki bata son ko yatsanta a bari so take ana zaro Babyn a aika da ita barzahu ta yarda ba wani balli da zai tashi daga baya. Doctor ta saki murmushi tana fa din  Ai haka za a aikata kamar yarda ta ce don har na tanadi Allurar da zan mata da zarar na gama mata theatre d in, dole ne cika burin Uwargijiya. Suka shek e da dariya ba tare sun damu da ita ba duk da sun san tana ji sanin cewa baiwa ce ba abinda za ta iya yi yasa suka saki jiki suke fa dar komai a gabanta.

Aka umarceta ta mik e ta zauna sannan aka turo wani kwando gabanta mai cike da abin sha masu k ara jini da kuzari. Tashin hankalin da take ciki bai hanata ci ba don ta san bata isa ta ce ba zata cin ba, ko da kuwa idan ta ci za tayi amansa bata da wannan damar. Ta ci sosai aka kuma bata tatacciyar madarar shanu mai d umi ta sha kafin su fice su barta a d akin cikin gigitaccen tashin hankali. A tsorace take a tsorace da kalaminsu da kai tsaye yake nuna kasheta za suyi bayan sun cire abinda suke buk ata. Wani hawaye masu zafin gaske suka zubo mata tausayin kanta take yi na rashin madafa cikin kuka take furta  Ya Allah ka zama gata na kafin jibi. Tunda a jibin aka ce za a cire cikin ita kuma su kasheta& ..





JIkar Nashe
'



(Free pages sun kusa k arewa, Kin biya kuwa? Idan baki biya ba daure ki biya ta wannan account d in y ar uwa. Tsagwaron labarin na gaba wannan duk tsakure ne. 2118666253 UBA. Sai ki tura shaidar biya ta number kamar haka: 08033748387.



KUDIRAR ALLAH.

Page 7.


NAZEEFAH SABO NASHE.

08033748387.

(Ina barar addu arku an min mutuwa kada kwana biyu ku ji ni shiru. Nagode ku cigaba dai da biya In sha Allah nan da kwana biyu za mu d ora.)




Ina godiya Aysher Adam (Ayshacool K anwar maza)
And

Na ima Sulaiman Sarauta (Nimcyluv)


Bisa k ok ari da suke wajen ganin littafin KUDIRAR ALLAH ya samu karb uwa nagode sosai really appreciated. >?p?




       

Tunda kashegari ta yi hankalinta ya sake tashi, tsoro da firgici ya sake shigarta ta sani sarai kwana d aya ya rage mata a duniyar gaba d aya idan har suka cire cikin za su aiwatar da kisan kamar yarda suka fa da.


Shiru take zaune a cikin duhun, zuciyarta ma ta kasa aikinta yarda ya kamata, balle har k wak walwa ta karb i sak on itama ta yi aikin da take so. Hawaye ne kwance a idanunta hannunta ta d ora saman cikin tana jin yarda yake watsalniya da harbawa da k arfin gaske kamar mai shirin fitowa duniyar a lokacin. Wani irin ciwo ta fara ji na tashin hankali tun tana d aukar lamarin wasa har ta tabbatar al amarin ya wuce yarda take zato. Gumi ne ko ta ina yake zuba a jikinta. Cikin tashin hankali ta durk ushe a k asan carpet tana karanta addu ar duk da tazo bakinta.

Ko ba a gaya mata ba, ta san nak uda take ganin yarda wani ruwa yake bin k afafunta ta sani da zarar ta haihu a yau ba sai gobe ba za su kasheta tunda abin da suke buk ata ya samu.

Motsin da ta ji na bu de k ofar shi ya sake razanata ta dunk ule waje d aya ciwon nak udar ma ta neme shi ta rasa don tsoron ya danne shi. K amshin turaren da ta ji wanda ya banbanta da wanda ta saba ji ne ya sake d aga mata hankali da tunanin wanene kuma? Taku ake cikin isa da tak ama ta ji ana nufota gadan gadan bayan an haska hasken torch light ya hasko inda take. Duhu bai bata damar ganin kowanene ba sai dai koma waye ya banbanta da wa dancan mutanen da suke zuwa. Murya a kaurare ta ji an bada Umarnin kunna fitila ta hanyar cewa  Kunna haske. Kafin k iftawar ido kuwa sai ga hasken ya gwauraye d akin. Mai tahowar bai fasa iso wa inda take ba, har ya iso ya zauna a gefen gado duk da bata banbance mace ce ko namiji saboda yarda kayan da suke jikinsa suka b oye duk wata sura da za a tantance jinsin Namiji ne ko Mace. Ji ta yi cikin raunin muryar da ta kasa tantance tausayi ne yasa ta fita a sirrance ko kuma asalin muryar ce ta so fallasa kanta saboda firgicin ganin halin da take ciki.  Hasbunallah labor take a ka fa da a ru de kafin kace me ta ga an mik a hannu wanda yake tsaye daga gefe ya mik o brief case cikin zafin nama aka ce  Fita ka tsaya a waje ka tabbatar kuma ba wanda hankalinsa zai yi yo nan d in, dama ce muka samu sai mu gode wa Allah. Aka fa da cikin murya mai kauri da bayar da umarni kai tsaye. Da sauri mutumin da aka wa Umarnin ya fita zaro kayan aiki aka fara a gaggauce mai kayan basajan ya ko ta fara taimaka mata. Ta sha wuya sosai kafin cikin k arfin ikon Allah ta haifo d a namiji. Hamdala ta ji an yi, aka kuma d aga jaririn ana kallonsa murya cike da rauni ta ce  Alhamdulillah Muhammad Murad ya iso duniya. Aka fa da ana sakin ajiyar zuciya had e da sanya Babyn a k irji aka ba shi kyakykyawan runguma. Ba tare da kyankyamin jinin da ke jikinsa ba. Ciwon ya lafa mata sosai tana kallon yaronta a hannun mutumin da bata san waye ba? Ko ganinsa bata da ikon yi. Tsaf aka goge shi da turaruka na alfarma kafin a mik o mata shi cikin kaurin murya aka ce  Ki masa kallon k arshe ki kuma k addara a zuciyarki ko cikinsa baki tab a d auka ba balle ki haifeshi kin gama aikin ki, ni ba zan d au ranki ba kamar yarda wad ancan sakarkarun suke son d auka burina samun yaron don haka zan miki sallama a yanzu zan kuma nuna miki hanyar da kai tsaye zata rabautar da ke daga mummuman kisan da za su miki, ki nesanta kan ki da masarautar gabas da duk abinda zai danganta ki da masarautar idan kina son zaman lafiyar ki kenan idan ba haka ba masu farautar ranki zasu iya yi miki kisan wulak anci. Ki yi sallama da gidan jininki kisa masa albarka don ko bakomai ke kika haifeshi duk da ba zaki amsa sunan Uwarsa ba har abada! Karb ar yaron ta yi hannunta na rawa ta sumbaci goshinsa kafin ta furta  Allah ya yi maka albarka Muraad! Wasu hawaye na zuba daga kwarmin idonta tana kallo aka karb e d an sannan aka umarceta ta shiga band aki ta tsaftace kanta. Kaya masu kyau aka bata ta saka sannan aka bata wasu zinare masu tarin yawa. Daga haka ta ji an yi fito sai shigowar Basamuden mutumin ta gani.  Ka fita da ita can bayan gari kafin wayewar garin asuba idan kuma har aka Kamaku kada ka sake sunana ya fito a bakinka. D aga kai ya yi yana kallonta ya nuna mata hanya. Nene na kuka ta bi bayansa bata da yarda zata yi amma zuciyarta ta yi rauni ganin zata bar gidan jininta dama iyayenta bari na har abada.


Tunda suka fara tafiya ta fara jin ciwo na sake turnik e ta sai dai ta daure ta kasa furtawa drivern ciwon da take ji. Tafiyar awa guda ya yi kafin ya ajiyeta a wani k aramin k auye yana furta  Daga nan ki k ara gaba, don nan d in ma yana cikin yankin masarautar gabas idan kuma kin k i ba ruwana. Ya mik a mata ku di masu yawa a enveloped ya fisgi motarsa da k arfin gaske.

Nene ta durk ushe a wajen bayan wata Bishiya tana hawaye saboda azabar ciwon da yake cin ta mararta kamar zata rabe biyu saboda tsananin azabar ciwo. Murk ususu kawai take kamar wata haihuwar zata sake yi. Tsawon lokaci tana wannan halin kafin Allah ya kawo wasu mata guda uku sun dawo daga d ebo itace. Da sauri suka rufa a kanta suna mamakin kasancewarta a wajen don dai bata yi kama da y an yankinsu ba tafi kama da k abilar fulani su kuma barebari ne. Kamata suka yi suna tambayarta abinda ya sameta? Ko kafin ta basu amsa sai ji suka yi ta yi wani nishi sai ga yaro ya sumb ulo da sauri suka cafe shi. Mamaki ya kama Nene ganin wata haihuwar ta sake yi. Tsoron kada asirinta ya tonu yasa nan take ta aro haukan dole ta k ak aba wa kanta. Tana kallo matan suka ruga wata bukka sai gasu sun sake fitowa aka yankewa yaro ci iya kafin su kamata su kai ya cikin gida. Duk da bata so bin su ba sai dai ba yarda zata yi dole ta bi su tana zaro ido don gudun kada su tambayeta daga inda take. Wanka suka bata ta yi da ruwa mai zafi kafin su tambayeta kayan jariri a sannan suka gane mahaukaciya ce. Cikin tausayi suke bin ta da kallo aka samo kaya a cikin kayan yaran da suke gidan aka zunduma masa aka na deshi cikin zani. Itama suka bata kaya ta canja na jikinta. Tambayar duniya da suka mata ta k i ba su amsa sai zare ido take har suka hak ura suka k yaleta so take kawai su bata jaririnta ta rungume shi a jikinta ta ji sanyin rad ad in da ke zuciyarta. Da kansu suka fahimci tana son ganin jaririn suka mik a mata shi ita kuma nan take ta ba shi Nono tana sakin ajiyar zuciya da Hamdala ga Allah da ya mata wata kyautar d an bayan rasa wancan da ta yi.


Cikin dare zuciyarta ta kasa nutsuwa da zama a wannan k auyen kasancewar ya mata kusa da garin Gabas hakan yasa ta d au jaririnta ta Goya ta sulale ta fice daga cikin gidan ba tare da sanin masu gidan ba.


Har duhun asuba ya washe tana gararamba daga wannan sak o

6 / 22