Author : Mrs Sadauki Category : Hausa Read
da ta ɓoye mini a cikin labarinta sannan a wajenta ne kawai za mu samu tarihin gidansu Sheikh ” haka muka ta yin hira har muka isa asibitin.
Kamar yadda tsarin yake sai ka je ka nemi izini sannan ka je wurin mutum,sai da muka je can muka nemi izini sunanta aka tambaye ni.
Na ce “gaskiya na manta sunanta sai dai wancan lokacin da muka zo ni da Kakata a ɗaki mai lamba uku ne take”
Shiru ya yi yana kallona na wani lokaci kafin ya miƙa mini wata ƴar guntuwar takarda na karɓa sannan muka fito.Kamar a MAFARKI haka na dinga bin hanyoyin har muka kawo ɗakin,ina yin tsaye ƙofar ta bada ƙiiii tare da buɗe kanta ban san ta ya aka yi ba ƙafata ce ta dama ta yi mini nauyi wannan yasa a dole na shiga da ƙafar hagu,wanda ya yi daidai da tashinta tana yin ihu.Da sauri na ƙarasa na kamo hannunta,shiru ta yi tana kallona da idonta da suke son canza siffa suna ɗaukar na tsohuwa kafin na kai ga furta wani abu fuskar Grand-Maa ta bayyana madadin ta mahaukaciyar,da wata irin murya ta maƙetata take cewa “wane ruhi ne ya zo wanda idona suka kasa ganinsa?”
Shiru na yi ina nazari kafin na kai yatsana cikin idon nata na tsokane,muryar Grand-Maa na ji tana ihu kafin kuma fuskar baiwar Allah ta dawo normal.Ƙanƙame ni ta yi tana mai cewa “ki tafi da ni don Allah kar ki bar ni a nan”
Wani likita ne ya shigo yana cewa “lokacin yi mata magani ya yi ku fita” sai ya matsa ya yi mata allurar bacci....
Normal group 300 ne, VIP 500 via
2670215530
ZULFAU YAHAYA
ECOBANK
DM +22795045822
[17/12 09:25] MRS SADAUKI: *MAFARKI*👁️🦋🦋🦋
🦋🦋🦋
🦋🦋
Mallakar : 🦋
Chamsiya Laouali Rabo
```MRS SADAUKI 💫✍️```
09
Haka muka fito ba don mun so ba,makaranta muka koma don a can muke wuni kullum har sai an yi karatun maraice kafin mu koma gida.
Mujahida ce ta nufi toilet,sai dai ba ta jima da shiga ba na ji ta fasa ihu.Da saurina na isa wurin ko ƙofa ba ta rufe ba tana tsaye kamar gunki.
“Me aka yi?” na tambaye ta,da idonta masu zubar da hawaye ta yi mini alama.Ina dubawa na ga wani ƙadangare ne babba a kwance yana maida numfashi shi ma alamun duk a gajiye yake.
A kallon farko da na yi masa na fahimci ba wannan ba ce ainahin siffarsa,ina son jin daga gare shi amma ganin Mujahida cikin wannan halin yasa na ce masa “ka fita daga toilet ka koma kan bishiyoyi tun da akwai su dayawa a cikin makarantar nan amma a nan za ka iya tsorata mutane ” ina gama rufe bakina ya soma jan ciki tare da nufo ƙofa Mujahida ta yi tsalle ta ɗale kan jikina wanda ya haifar mana faɗuwa don ba zan iya ɗaukar nauyinta ba.Ko da muka miƙe tuni ƙadangaren ya fice,ga kuma kayanmu sun ɓace da ruwan toilet duk da dai a tsabtace take .
Cikin masifa nake cewa “ja can matsoraciya kin sa duk kayanmu sun ɓace” haka na cire zumbulelen hijabina na wanke shi Allah ya yi sa'a banda riga ta.
Can wajen masjid na nufa don shanyan hijabin nawa amma sai na sake shi ya ƙara kwasar wata dauɗar sakamakon ido huɗu da muka yi da Sheikh Rayyadeen wanda ban san uwar me ta maido shi makarantar ba.
Jikina na rawa na ɗauko hijabin tare da rufe ƙirjina kasancewar rigar da na saka mai ƙananun hannuwa ce.Kai ya kawar tare da yin gaba abinsa,hijabin da ban shanya ba na dawo da abina na ƙara wankewa na saka shi a haka nan.Sosai hankalina yake a tashe,na ji kunya sosai da ya ganni a haka.Mujahida ma ta lura da canjina amma kuma sai na ɓoye mata ban sanar da ita ba.
Har aka yi sallah muka shiga aji hijabina bai bushe ba,duk da sanyin da ya kwasa na damuna haka na zauna da shi.
★SHEIKH RAYYADEEN
Sosai yayi mamakin yadda Sadiya ta yi fatali da kunyarsu ta ƴa mata take wani zuba masa kalaman soyayya har da wani cewa tana iya rasa rayuwarta muddin bai karɓi soyayyarta ba,shi dai kallonta yayi kafin ya ce ta ja ya rufe motarsa.A hanya ma haka ya yi ta tunani har yake jin tsoron kar dai zuciyarsa ta aminta da zancen soyayyar.Yana isa gida da Ammynsa ya ci karo a farfajiya tana yi wa sabbin ƴan aikin da shi ne ya bada umarnin a kawo su bayani.Tana ganinsa ta saki murmushi tare da sallamarsu,yau jinsa yake matsayin Deeni wannan yasa yana zuwa kusa da ita ya kamo kafaɗarta ya soma janta ciki yana mai gaishe ta da tambayarta ya baƙunta.
Sai da suka isa tsakiyar falo ne take cewa “ɗazu Mamarku ta kira ta ce ita ma za ta dawo nan”
Ya ce “babu damuwa Ammy dama ai na tsara dukkan ahalin ne za su tare a nan”
“Allah yi maka albarka”
Ya amsa da “amin” har zai wuce ta ce “ina rigarka ta sama don ba haka ka fita ba,kuma ba ka saba rabuwa da ita ba”
A nan take yadda Khadeeja ta tofa masa yawu ya faɗo masa,ransa ne ya ji ya ɓace amma ya daure ya ce “tana can makaranta Ammy ”
“Ko yau ma kun yi faɗa?”
“Haba dai Ammy sai ka ce wata babbar mace da har zan tsaya yin faɗa da ita,ɗalibata ce fa ƙaramar yarinya ko yau sai da na zane ta” yadda yake magana za ka iya cankar cewa zuciyarsa cike da zafi take.
Ammy ta yi ɗan murmushi kafin ta ce “je ka yi wanka,zan haɗa ma abincinka kafin ka fito”
Haka ya wuce can sama, Ammy ta bi bayansa da kallo ita kaɗai take hango masa irin tarin kulawar da zai samu a wurin macen da yake ganin yarinya ce.
Yana shiga ya rage kayansa sannan ya shiga toilet ya sakarwa kansa,shower ruwan na ratsa gashinsa suna sauka a duk illahirin jikinsa.Tunani yake yi ta yaya ne ma zai fallasa sirrinsa ga ƙanƙanuwar yarinya irin Khadeeja wacce ba ta wuce a yi rainonta ba,don ya lura akwai ƙurciya a tattare da ita in ba haka ba me zai sa ta dinga gudu a cikin makarantar duk jikinta na motsawa in ba don Allah yasa ma tsit wurin yake ba duk ɗalibai na cikin aji.Kansa ya kalla shi kansa ba kasafai yake son duban jikinsa ba to ballantana ya bari wata ta kalle shi.Babban towel ya jawo ya ɗaura a ƙugu sannan ya ɗauki ƙarami ya fita yana tsane jikinsa.Cike da nutsuwa ya shirya cikin jallabiya fara ya fesa turare sannan ya sauka ƙasa.Tuni kuwa Ammy ta kawo komai tsakiyar falo,ya zauna kan capet ya tanƙwashe ƙafafu da kasan ya zuba yayi Bismillah ya soma ci sai ga Ammy ta fito.
Kan kujera ta zauna suna taɓa hira wacce rabinta ita ce ke yi don shi Sheikh Rayyadeen bai cika yin magana ba,don ma wai Ammyn ce shi yasa har yake kama mata amma haka a cikin abokai shi ɗan kallo ne in kuwa ka yawaita jin muryarsa hirar addini ce.
Bayan ya gama aka kira ƴar aiki ta zo ta kwashe,ya miƙe ya haura sama yayi brush sannan ya sake fitowa.Kan kujera ya kwanta yana lumshe ido so yake ya ɗan yi bacci amma Ammy ta tsiro masa da hirar Khadeeja.
“Me ta yi ka dake ta?”
Duk da ya gane amma sai ya nuna bai san wace ce take magana akai ba.Ya ce “Wa fa?”
“Deeja mana” ta basa amsa tana wani yin murmushi mai sauti, Sheikh ya ɗan ware idonsa ya ga yadda fuskar Ammy ta cika da annuri .
“Tana da tsiwa ne yarinyar, ga taurin kai kamar rainon aljanu” ya faɗa yana cije jan leɓensa na ƙasa.
Ammy ta yi dariya ta ce “ni ma lokacin da ina daidai gaɓar shekarunta haka nake,kusan Abuh sai ya dake ni musamman a fagen yawan yin faɗa da rigima”
Sheikh ya ce “Ammy ki bar faɗar haka don goya mata baya,ni dai na san Mummyna ba haka take ba”
Ammy ta kama kunnensa ta ja tana mai cewa “kai ma da kana yaro ai haka kake,kullum cikin yin faɗa kana damun Rashida ”
Ambaton sunanta yasa Sheikh cewa “tana ina ma? Ya aka yi ban gan ta ba?”
“Tana ɗakinta,na bata magani ne sai ya saka ta bacci ”
“Mijinta ya kira?”
“A'a bai kira ba,dama ina jiranka ne har ka dawo na sa ka kira mini shi”
Sheikh Rayyadeen ya ce “a'a don me za mu kira shi? Kawai ki barsa ƙila ya bar sonta ne”
“Kamar ya na bari? A'a ban so aurenta ya samu tangarɗa ka ga in sha Allah tana samun lafiya zan mayar da ita ɗakinta”
Sheikh bai ƙara cewa komai ba,ganin haka Ammy ta dasa daga inda ta tsaya ta ce “ka bai wa Khadeejatun makullin?”
“Na bata Ammy ”
“To tashi ka dubo mini ka gani ko ta ɗauki motar”
Sheikh ya ce “haba dai Ammy sai ka ce dai ita ce ƴarki ba ni ba,motsi kaɗan sai kin kira sunanta ko dai kin bar sona ne ban sani ba?”
“Soyayyar taka ce ta saka nake yawan ambatonta tashi ka tafi Deenina”
Ya turo baki gaba kamar wani ƙaramin yaro, Ammy ta gumtse dariyarta tana mai cewa in ka ganta kuma ka kira ni a waya ka bani ita .
Bai ce komai ba ya je sama ya ɗauko key,shi takaicin ɗaya yadda zai tafi unguwar can har yayi tozali da gidan Abba .Amma haka ya daure ya tafi,bai ga motarta ba kawai sai ya yanke shawarar bari ya je makaranta yana zuwa kuwa ya tarar da motar.A hankali ya fita,sanin babu inda take tsayawa sai cikin masjid na mata yasa ya nufi can.Yana tsaka da tunanin me ma zai ce mata har ya samu su yi wayar da Ammy kwatsam ya ga abin da ya ɗaga masa hankali.Khadeeja ya gani babu hijabi ga shi rigar jikinta ƙarama babu wani tudu da kware da ba ta bayyana ba,tashin hankalin bai tsaya iya nan ba shi ne kama shi da ta yi yana kallonta ido cikin ido suka kalli juna.Da sauri ya kawar da kai tare da juyawa ,idonsa har wani rufewa suke bai gani sosai.Dakyar ya isa bakin motarsa ya shiga ya zauna yana wani haƙi kamar wanda ya yi ƴar tsere.
Jikinsa na rawa ya soma lalube ya yi sa'ar ɗauko gorar ruwa guda,ya buɗe murfin kafin ya kafa ta a baki ya soma sha, numfashinsa na kokowa da magudanar jininsa.
A hankali ya soma jin dama, sai ya jingina jikin kujera yana maida numfashi cikin ikon Allah larurar tasa ta lafa ba kamar wancan lokacin ba da ta saukar masa da zazzaɓi.Motarsa ya ja ya tafi gida,bai samu Ammy a falo ba kawai ya wuce ɗakinsa yana shirin kwanciya Sheikh Laminu ya kira shi don yi masa barka da tarewa cikin sabon gida .
Har sai da kiran ya yanke wani ya shigo sannan ya ɗauka,shiru yayi sai ma abokin nasa ne ya fara gabatar masa da sallama.Sheikh ya amsa a sanyaye wanda tuni shi Sheikh Laminu ya fahimci damuwar saboda shi ɗin amininsa ne ba su ɓoyewa juna sirrinsu.
“Aboki lafiyarka kuwa?”
“Da dai dama,ya kake ya iyali?”
“Lafiyarsu lau sai mitar dai ta kullum da ba ta barin bakinta” ya basa amsa.
Sheikh ya ce “aboki ku je asibiti a yi muku gwaji don a gano matsalar daga wurin wa take”
“Ina jin tsoro ne a ce daga gare ni ne,a zo Mardiya ta guje ni.Ya naka ɓangaren ka samu matar auren ne na ji ka cikin wani hali,na tabbata kuma in ba zancen aurenka aka fara ba to ba za ka shige shi ba”
Sheikh Rayyadeen ya ɗan murmusa yana mai cewa “aboki ban san ranar da za ka rage surutu ba, wannan duk ranar da ka haɗu da mace daidai kai ai an shiga uku sai dai ku haifi rediyo”
Sheikh Laminu ya tuntsire da dariya yana mai cewa “ka san kuwa ina son mace mai surutu,saboda yawancinsu za ka same su da tsiwa”
Sheikh Rayyadeen ya ja tsuki saboda yana furta haka Khadeeja ta faɗo masa a rai.Cike da jin haushi ya ce “kai dama duk inda wani abin shirme yake to can kake,ina wani abin burge wa ga mace mai tsiwa? Na san dai Mardiya ba haka take ba ita mace ce mai hankali ”
“Aboki a kullum ina yi maka addu'ar Allah ya baka mace mai tsiwa don ita ce daidai da kai,ita kaɗai ce za ta ture miskilancinka”
Sheikh ya ɗan gyara kwanciya yana mai cewa “in kuma aka zo fannin shimfiɗa fa?”
Murmushi mai sauti yayi yana mai cewa “shi ne kawai damuwarka shimfiɗar aurenku?”
“To aboki mene ne auren? Duk macen da ba za ta iya ji da nauyina ba mene ne amfanin auro ta? Shi yasa nake son mace mai nutsuwa wacce ta mallaki hankalinta amma ka ga yaran nan sai a hankali banda shirme babu abin da suka iya”
Dariya Sheikh Laminu yayi har da ƙyalƙyatawa kafin ya tsagaita ya ce “in dai irin matar nan kake so ina da wata cousin wallahi dama ta dame ni da na yi mata addu'a Allah ya bata aure shekararta talatin da uku,tana hadda Alkur'ani amma ba ta yi karatun boko mai zurfi ba zan turo ma hotonta in ta yi maka sai mu yi tuwona maina ”
Shiru Sheikh Rayyadeen yayi Allah ya gani yana son aure amma kuma yana jin tsoro kar wani abu ya samu ƴar mutane.Kafin ya kai ga cewa wani abu kuma kiran ya katse,ya ajiye wayar yana mai lumshe ido tare da jan numfashi yana.Hoton Khadeeja ne ya faɗo masa a rai,duniyar Allah duk da bai taɓa yin aure ba amma yana mugun son dukiyar Fulani .Juyi ya sake yi yana jin tsoron sake shiga wani hali,ƙarar shigowar saƙo ne ya ji a wayarsa.Ya jawo ya duba sai ya ga hoton ne Sheikh Laminu ya turo masa,haka ya ƙure hoton da kallo babu laifi Kyakkyawa ce sannan tana da zubin halitta mai kyau don babu hijabi a jikinta kayan atamfa ne ta saka amma sosai suka karɓe ta.
“Ta yi?” ya ga wani saƙon ya shigo.
Ya basa amsa “aboki in dai ka yarda da tarbiyyarta na karɓi tayinka ” sosai Sheikh Laminu ya yi murna nan take ya aiko masa lambarta sai a lokacin ya tambayi sunanta ya ce “Maryama” sai yayi saving kafin ya tashi yayi wanka ya tafi masjid yana dawowa kuma yayi shirin zuwa makaranta.
Yana saukowa ƙasa ya je ya duba Rashida ya tofa mata addu'o'i sannan ya yi wa Ammy sallama.Yana isa makarantar yayi tsinke ajinsa,yana shiga idonsa a kanta ya fara sauka tana kwance a takure sai rawar sanyi take ga kuma fankar aji a kunne.Saurin ɗauke idonsa yayi ya je ya zauna ya soma koya karatunsa,amma lokaci zuwa lokaci yana ɗan satar kallonta da dukkan alamu ma bacci ne take yi.
Lokacin sallar la'asar na yi duk kowa ya soma fita.
Cikin baccin da ya shure ni ban shirya ba na ji muryar Mujahida na cewa “ki tashi lokacin sallah yayi” sai da na ɗan jinkirta kafin na buɗe idona maimakon Mujahida Sheikh Rayyadeen na gani a tsaye.A hankali nake kallonsa,shi kuwa hannunsa na dama yasa ya kamo kaina tare da soma yi mini karatu.
Yadda nake jin ana yin motsi a cikin jijiyoyin kaina shi yasa na fara kiciniyar ƙwatar kaina.Hannuna na ɗora kan nasa da niyyar janye shi amma ya ƙi saki,haka na dinga yin hawaye har sai da ya gaji don kansa sannan ya sake ni.Ina tafiya toilet domin yin alwala na ga jinin period ɗin ya dawo a dole na haƙura da yin sallar na koma cikin aji na kwanta.Ina nan suka fara dawowa daga masjid,ajin na gama cika Sheikh Rayyadeen ya shigo yanzu ma idon muka haɗa na yi saurin ƙanƙame jikina shi kuma ya kawar da kai tare da matsawa ya kashe dukkan fankonin ajin.A sannu a hankali zafi ya fara ziyarta ajin,hakan sosai yayi mini daɗi wanda kuma ina da yaƙinin sauran ɗaliban za su cutu.
Ba a fi minti biyar ba na ɗan gyara zamana ina sauraren darasin da yake yi game da wajabcin sallah ga Musulmi har aka zo babin abin da ke hana sallah daga ƙarshe ya koya mana yadda ake wankan janaba da na haila.Ɗaya daga cikinmu wato sabon shigowa ta ce “malam mene ne banbancin wankan hailar da shi janabar? Mene ne su?”
Duk ƙarancin shekaruna na girme mata,irin yaran nan ne waɗandan iliminsu ne ke sa a kai su ajin manya.Tambayar tata sai ta saka manyan ajin jin kunya,amma shi kuwa Sheikh Rayyadeen tiryan-tiryan ya soma fayyace komai,abubuwan da ke kawo janaba dukkansu sai da ya faɗa ni kaina sai da na sunne kai duk da dai sai ya faɗa da larabci sannan ya fassara.
Abin takaici duk bayanin da yayi daga ƙarshe ita wacce ya yi wa ɗin ba ta fahimci komai ba.
Shi kuwa Sheikh Rayyadeen ganin suna sunne kai yasa shi cewa “tambaya ce ta yi mai muhimmanci,a fagen neman ilimi babu kunya ya kamata duk abin da ba ka sani ba ka yi tambaya a kai”
A hankali na ɗago na dube shi,bawan Allah sai na ga yana goge gumi da tissu alamun zafi yake ji.Mujahida ta yi ƙasa da murya tana mai cewa “dubi saboda ke ya wani kashe fanka sai gumi yake fitarwa mu kuma ya bar mu da jin zafi cikin hijabi”
Kwantawa na yi jikinta ina mai yi mata raɗa,“ina ma a ce cikin ƙirjinsa ne ya rungume ni na ji ɗumin jikinsa ya kike gani?”
Mujahida ta ce “innalillahi!” da ɗan ƙarfi ta faɗa wannan yasa waɗanda suka ji duk suka zubo mana ido.Da sauri na sunne kai ganin kallon da Sheikh ke yi mini sai nake ganin kamar ya ji abin da na ce ɗin ne.
Har lokacin tashi ya yi ban ɗago kai ba,don da zarar na yi yunƙurin haka sai na