MAFARKI Love and Horror Story By Mrs Sadauki.txt

Author :  Mrs Sadauki Category :  Hausa Read

Chapter   1 / 18

1 to 3K   out of 53.5K words

[11/12 11:59] MRS SADAUKI: *MAFARKI*🦋🦋🦋
🦋🦋🦋
🦋🦋
Mallakar : 🦋
Chamsiya Laouali Rabo
```MRS SADAUKI 💫✍️```
SADAUKARWA: Ga mata ma'abotan saka hijabi.🤗

01

Yau ma kamar kullum tun safe na yi wanka na shirya cikin uniform ɗin makaranta,na fesa turare marar ƙamshi kafin na ɗauki jakata mai ɗauke da Alkur'ani da sauran littafai da ake koya mana.Cike da nutsuwa na sauko ƙasa,da Momy idona ya yi tozali matar kirki wacce daular da muke ciki ba ta saka ta zama raguwa ko mai ƙiwar aiki ba kullum a tsaye take domin farin cikin ahalinta.

Duk wata sangartata ce na ji ta motsa,na tattare zumbulelen hijabina wanda tsabar girmansa har jan ƙasa yake yi.Da ɗan guduna kamar zan faɗi na je na rungume ta ina mai yi mata sallama madadin na ce ina kwana,saboda haka Daddynmu ya koyar da mu yin sallama kafin kowacce gaisuwa.

“Wa'aleyki salam autar Momy” ta amsa mini.

Na turo baki don na tsani a ce mini auta ina mugun ƙaunar yara wannan yasa kullum fatana Momy ta haihu.Na ce “ni dai ba auta ba Momy,kin ga Mamarsu Mujahida ma ta haihu”

Ta yi ɗan murmushi mai sauti kafin ta ja hancina ta ce “wuce dai ki je direba na jiranki,ki aje hankalinki ki yi karatu banda surutu”

Na ce “to Momy ki haɗa mini lemun zoɓo da kanki ,in an kusa shan ruwa kuma a yi mini salade na fruits”

“In sha Allah auta, Allah ya tsare ki ya maido mini ke lafiya”

“Amin Momy ” na amsa ina mai ɗaura niƙaf a fuskata kafin na fita harabar gidanmu wacce take ɗauke da shuke-shuke gwanin sha'awa.Da sallama na ƙarasa wurinsa ina mai buɗe baya na zauna,shi kuma ya shiga ya yi wa motar key.
Muna hawa babban titi na ciro wayata na saka ta silence ,sai kuma na shiga gallery tare da danna kundin da nake ajiye hotunansa.Kamar wacce ta zauce haka nake kallon sajensa wanda ya haɗe da dogon gemunsa mai cikar gargasa baƙa ƙirin sai ɗaiɗaiku daga tsakiya da suka fitar da fari.Idona ya ciko da ruwan hawaye ina jin kuma wani murmushi na sauko mini wanda ba komai ya haifar da shi ba sai zuciyata da ta raya mini ‘ saura ƙiris ki cimma burinki’

Tsayawar da motar ta yi shi ya fargar da ni mun kawo,a hankali na buɗe murfin motar na fita wanda hakan yayi daidai da tahowar motarsa.Haka na yi tsaye ina bin motar da ido har ta tsaya inda malamai ke ajiye motocinsu,ya ɗan ɗauki lokaci kafin ya fito.Kamar kullum yau ma sanye yake cikin fararen kaya sai ya ɗora alkyabar nan da malaman Saudiya ke sakawa,ita kuma baƙa ce haka ma hiramin kansa baƙi ne yayin da gilashinsa kuma ya kasance fari.Da sauri na ɗauke dubana daga gare shi na tunkari ajinmu zuciyata na dokawa,ina yin sallama ƴan matan ajin waɗanda suka zo duk suka juyo yayin da Mujahida ta wani zo da sauri ta rungume ni tare da yi mini raɗa a kunne wacce ta ƙara tsananta bugun zuciyata.


Ta janye daga jikina tana dariya,na riƙo hannunta ina mai cewa “wai da gaske? ”

“Wallahi kuwa ni ma yanzu da na je can ofishin shugaban makaranta na ji ana zancen” ta bani amsa.

Na ce “amma kuma ba a yi sanarwa ba”

Ta ce “ƙila sun canza tsari”

Daga haka na je na zauna ,kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki haka na yi sukuku duk hirar da Mujahida ke yi mini ta yadda bikin gidansu zai kasance haka-haka nake jin ta a haka har ajin ya cika.Ƙarfe takwas na bugawa kuma malaminmu ya shigo da sallama,bayan mun amsa sai ya zauna yana fuskantarmu kafin ya fara da cewa “yau za a fara zana jarabawa, binciken karatun Alkur'ani shi ne farko waɗanda ba su da gyara da yawa iya su kaɗai ne za su tafi aji na gaba wanda ya kasance ajin ƙarshe”

Malam na gama wannan jawabin Mujahida ta kalle ni tana murmushi ta ce “yanzu kin yarda?”

Na ce “ƙawata tsoro nake ji”

Ta ja tsaki ƙasa-ƙasa kafin ta ce “na me kuma? Bayan duk lokacin da kika ɗauka kina burin ganin wannan lokacin? Ko dai kin daina sonsa?”

Na dube ta da sauri ina mai cewa “na daina? Kuma kika ganni a raye”

Ta ɗan bangaje ni tana dariya,kafin kuma duk mu nutsu saboda buga teburi da malam ya yi alamun a nutsu.Bai wani ɓata lokaci ba kuwa ya soma binciken karatun,kasancewar da tsarin ABCD aka bi wannan yasa har aka fita shan iska ba a kawo sunana ba.

Muna fitowa Mujahida ta ce “ni kam Khadeeja na tambaye ki,yanzu in mun gama jarabawa muka shiga ajin ƙarshe wace kalma ce ta farko da za ki furtawa Sheikh Rayyadeen?”

Na yi ɗan murmushi kafin na ce “to ai kin bari ki ga in mun ci exam ɗin ko?”

Ta ce “na ma san za mu ci ai”

“To Allah yasa”
“Amin! Ina jinki me za ki ce masa?”

“Zan faɗa masa ina sonsa fiye da rayuw...” sauran maganar ce ta maƙale mini a maƙoshi sakamakon ido huɗu da muka yi da Sheikh Rayyadeen duk da yana ɗan nesa da ni amma kallon da ya yi mini kamar mai nuni ne da ya ji abin da na furta,wani abin mamaki kuma sai na kasa ɗauke idona daga cikin nasa ɗin yayin da shi kuma ya fara tunkaro inda muke.Yana dab da isowa na ji Mujahida na cewa “kamar fa wurinmu zai zo” furicinta ya ida hautsana cikina kawai na yi baya da mugun sauri na koma cikin aji.

“Khadeeja” na ji Malam Ibrahim ya furta,na juyo da sauri ina mai cewa “ka yi haƙuri malam ”

“Bai komai kin ga dama ina ta son yi miki magana,har yanzu ba ki gama tunanin ba ?”

Cike da kunyar abin da zan faɗa masa na ɗan kawar da kai gefe na ce “shi so abu ne da ke da alaƙa da zuciya...” shiru na yi saboda lura da inuwar mutum a bakin ƙofa.

“Sheikh !”malam Ibrahim ya faɗa da ƙarfi muryarsa na fitar da amon tsoro.Kamar wacce aka yi wa allurar hauka haka na ruga a guje domin na fita,ina dab na kai gare shi na ji wani abu lummm ya disashe ganina.Kan ƙirjinsa na tsinci kaina wanda hakan ya yi daidai da tsayawar bugun zuciyata,ban sani ba suma ne na yi ko kuwa mene ne oho abin da na sani shi ne kawai bayan na dawo hayyacina na samu kaina a can wani wuri da aka ware domin malamai su huta.


Zaune na yi ina kallon ɗakin ina jin kaina na ɗan sara mini,na yi tunanin ni ɗaya ce a wurin sai da Mujahida ta shigo ne da sallama na ji an amsa mata daga can bayana.Da wani matsanancin sauri na juya idona kuwa ya sauka cikin nasa,yanzu babu gilashi a fuskarsa wanda hakan ya ƙara tona asirin kyawun manyan fararen idonsa.Wannan karon kasa jurewa na yi kawai sai na yi juyo kaina tare da sunne shi, Mujahida ta ƙarasa ta miƙa masa gorar ruwa.

Murya cike da nutsuwa ya ce “kuna iya tafiya”

Sai ta zo ta kama hannuna ta miƙar da ni tsaye,sai da muka kai bakin ƙofar fita sannan na juyo na saci kallonsa wannan karon idonsa a lumshe suke ya ɗaga gorar ruwan yana sha har suna ɗiga a gemunsa wanda hakan ya nuna a matuƙar buƙace yake da su.


Muna fitowa Mujahida ke cewa “yau na ga ikon Allah kin ga yadda ki ka sandare a jikin Sheikh Rayyadeen? Kamar mai cutar sanƙarau,wajen mu huɗu muka ɗauke ki zuwa ajin malamai bawan Allah shi kuwa Sheikh sai hankalinsa ya tashi shi ne ya tsaya kanki yana ta yi miki karatu har sai da numfashinki ya dawo normal ”


Tun da ta fara magana nake kallonta amma ban ce komai ba a haka muka ƙarasa can ajinmu.Yadda duk suka zubo mini idonsu ya saka na ji duk na tsargu,hatta shi kansa malam Ibrahim kallon nawa yake yi.Zaune na yi kawai,ina sauraren yadda yake bincikar karatun sauran ɗalibai tuni ma an wuce sunana.Kwance na yi jikin table na lumshe idona nan take hoton yadda na faɗa jikin Sheikh ya shigo tunanina,yadda ya wani riƙo ni da mugun ƙarfi da hannuwansa masu taushi duk ina tune daga nan ban tuna komai ba.Ina a haka har lokacin tashi yayi muka fito,sai a lokacin kuma na tuna babu niƙaf a fuskata.

“Mujahida ina niƙaf ɗina?” na tambaye ta ina mai kamo hannunta.Ta ce “oho ni ma ban sani ba,ko ƙila tana can ajin malamai”

Ban ƙara ce mata komai ba haka muka nufi wurin da ake cin abinci,gefe kawai na zauna har ta gama ci muka fito zuwa masjid na mata wanda yake babba ne akwai kuma banɗakuna.Sai da muka yi alwala kafin mu shiga mu zauna,saboda na ture tunaninsa daga cikin kwanyata na ɗauko hirar bikin gidansu nan fa muka ta zantawa muna dariya.Lokacin sallah na gabatowa masjid ɗin ya soma cika,kafin kuma mu miƙe mu fara daidaita sahu.Yau ma Sheikh Rayyadeen ne ya bamu sallah,har aka gama idona na lumshe don ji na yi ƙira'arsa ta yau ta fi ta kullum daɗi.Bayan mun gama kwantawa na yi domin na rumtsa kafin lokacin shiga aji yayi.

Ban san iya lokacin da na ɗauka ina hutawa ba amma ko da na tashi na hangi Mujahida ita ma tana baccin.Fita na yi na shiga banɗaki bayan na yi addu'a,ko ina tsaf yake babu datti don har wanka ma wasu na yi amma ni dai ban taɓa yi ba in ba yau da nake jin zafi na rufe ni ba.

Wankan na yi na ɗaura alwala na mayar da kayana kafin na fito,fitowar tawa ta yi daidai da fitowar Mujahida ita ma cikin kiɗima take cewa “ƙarfe uku ta buga fa har da minti wajen biyar bari na yi alwala kawai”

Na ce “da yake da na tashi ban duba lokaci ba”ciki na shiga na fiddo mai na shafa da turare sannan na ɗauko jakakunanmu na fito na tsaya.Tana fitowa na miƙa mata tata kafin mu wuce aji, Allah yayi sa'a ma Malam bai shiga ba.Ko da ya shigo kuma sai aka raba mana takardu muka zana jarabawa wacce ta ƙunshi abubuwa da dama,ba mu yi awa ɗaya ba kuma duk aka lashe amshe saboda lokacin sallah da ya yi ina ta jiran jin muryar abincin ruhi amma sai na ji ta wani malami daban.Bayan mun dawo aka ƙara bamu muka ƙarasa duk wanda ya ida sai ya fita wannan yasa da na gama na fito na ciro wayata na soma lalubo wayar direba amma a kashe.


Ji na yi kamar na mutu tsabar takaici,haka na yi ta tafiya har na fita daga cikin makarantar ga shi fuskata a buɗe mutane sai kallona suke yi ga abin hawa ya yi wuyar samu.Abinka da ƴar Daddy kawai sai na ji hawaye sun cika mini ido,ina nan tsaye na ga motar gidanmu.A gabana ya tsaya tare fitowa ya buɗe mini murfi yana bani haƙuri kan ya manta ne bai taho da wuri ba.Ji na yi takaici ya ƙara rufe ni kukan da nake ta riƙo ya kubce mini a hankali na fara magana ba cikin hayaniya ba,“ta yaya mutum zai manta da haƙin da ya rataya a wuyansa? Dama ana manta aikin wajibi ne?”

Ya haɗe hannuwansa biyu yana bani haƙuri,ban ƙara cewa komai ba na shiga na zauna ina shafar hawaye.Ina ɗaga kai na hangi Sheikh Rayyadeen a tsaye kuma da dukkan alamu ya ga komai don idonsa na kan motarmu ne,zuciyata ce na ji tana bugawa a haka dai ya ja mu zuwa gida.

Ina shiga yadda na ga an cika dianing da kayan lambu da na motsa baki na ji a raina Daddy zai dawo sai dai falon tsit yake.Ina shirin nufar ɗakina na ji tambaya daga sama “ina niƙaf ɗinki?” muryar Daddy ce ,cak na tsaya ina kallonsa yana cikin shiga ta manyan kaya har da hulla ya ɗora.Ban basa amsar tambayar ba sai nufarsa na yi na je na rungume shi ina kukan farin cikin ganinsa.

Ya tallabo fuskata yana goge mini hawayen kafin ya ce “Ummita ba na hana ki fita babu niƙafi ba? ”

Na kwaɓe baki na ce “ai da zan fita na tafi da ita faɗuwa ta yi ban sani ba”

“Ta ya ta faɗi har ba ki sani ba?” shiru na yi ban basa amsa ba,sai kuma can na canza akalar zancen “Daddy shi ne ba ka sanar da ni za ka dawo ba”

“Na cewa Momynki ta sanar da ke,kenan ba ta faɗa miki ba?”

Na turo baki gaba na ce “Daddy ai ka san Momy na kishina so take ta fara ganinka kafin ni shi yasa ta ƙi faɗa mini”

Yayi murmushi mai ɗan sauti kafin ya ce “ƙila tana tsoron ki ƙi zuwa makaranta ne shi yasa”

“Da dukkan alamu gulmata ake yi ƴa da uba” Momy ta faɗa tana mai fitowa daga ɗakinta ta saka wani rantsatsen less,dariya kawai na yi na wuce can ɗakina da ke hawa na farko.

Uniform ɗin na cire na shiga wanka,a gaggauce na shirya cikin doguwar riga ta atamfa.Ko da na fito tuni Daddy na zaune yana addu'a saboda gabatowar lokacin shan ruwa,ni ma kujera na ja na zauna na fara nawa addu'o'in idona na lumshe nake roƙon Allah ya mallaka mini Sheikh Rayyadeen matsayin miji.

★SHEIKH RAYYADEEN


Matashin malami ne wanda har yanzu yake cikin ganiyar samartaka,duk da shekarunsa sun ɗan ja amma fatar jikinsa ba ta nuna hakan ba.Shekarunsa arba'in da ɗaya a duniya yana dab da cika da biyu,fari ne sol yana da ƴar ƙiba amma ba sosai ba.Shi ɗin ya fito daga ƙabilu biyu,mahaifinsa kanuri ne ɗan asalin garin Diffa da ke nan ƙasar Nijar yayin da Mahaifiyarsa ita kuma ta kasance Balarabar Nijar ce suna rayuwa a babban birnin Yamai.

Wannan yasa kyawunsa ya fito da wani fasali na daban,wanda hatta shi da kansa ya san shi kyakkyawa ne don yana ɗaya daga cikin abin da yasa mata ke tururuwa suna kawo masa tayin soyayya amma bai karɓa a bisa wani dalili nasa da ya ɓoyewa kansa.

Malamta kusan gadon gidansu ne don kusan kowa yana da ilimin addini,sai dai banbancinsu da shi kawai ita ce aƙida duk da tun farko karatun allo ya yi amma daga ƙarshe da ya canza akalarsa zuwa karatun habsi wannan kuma ya samo asali ne saboda keta ƙasashen Larabawa da ya yi ya ƙara samun gogewa ta fanni daban-daban.


Shi ne da kansa ya buɗe makarantar NOOR-RULLAH sannan kuma ya zuba malamai daban-daban ya kuma bai wa wani matsayin jagoranci yayin da shi kuma ya zo a matsayin malami.In banda mahaifiyarsa babu wata halitta da ta san sirrinsa,komai zai yi yana ɓoyewa bai son bayyanawa.

Yana ɗaya daga cikin tabi'unsa shi ne baiwa sirri da amana muhimmanci,yana son turare saboda mutum ne mai musulmar tsabta.Ya tsani yawan surutu,bai cika son shishigi ba wannan yasa kusan bai da abokai barkatai sai dai in na karatu wannan kenan;

Bayan ya gama haɗa komai ya mayar da komai kan fasali sai ya ɗauki key ɗin motarsa ya fito.Kusan makarantar ta yi tsit saboda lokacin tashi tuni ya kusa,a hankali yake driving lokaci zuwa lokaci fuskarta na faɗo masa a rai da kuma irin yadda ta yi shure-shure da yana yi mata karatu,yadda take kuka tana ƙanƙame shi gaban ɗaliban da yasa suka kai ta can.Ya ɗan ja tsuki yana jin wani irin takaicin yarinyar da ya ji suna kira da Khadeeja,kamar mahaukaci haka shi kaɗai ya soma yin magana “ni da ba haka Ammyna take ba,ban ma san wane ne ya zaɓa mata suna mafi daraja ba” ya ƙara jan wani tsaki yana mai karyar hancin motarsa tare da yin Horne,babu jimawa aka buɗe ƙaton get ɗin ya shiga a hankali ya je ya parker motar ya fito.


Tun kafin ya shiga falon yake jin masifar Grand-Maa ,yana yin sallama ta ja baki ta yi shiru tana mai cewa “to ga ustazu nan” Ammy wacce ke tsaye kanta a sukunye ta ja numfashin samun ƴanci tare da ɗagowa ta dubi Sheikh da ya yi tsaye ransa na ɗan susa, Ammy ta yi masa alama da kar ya ce komai haka ya daure ya gaishe da Grand-Maa cikin sakin fuska ta ce “ustazu sannu da zuwa ya na ga ranka duk a dagule ko yau ɗin ma ka samu wasiƙar soyayya daga shashun ƴan mata?”

Ya ɗan murmusa ya ce “Grand-Maa ke kullum ba ki rasa abin dariya,ke da kin san ban ko sakin fuska ta ya za a kawo mini wasiƙa?”

Tsakiyar idonsa ta kalla tare da yin shiru,tun yana jiran ta ce wani abu har ya juya ya kamo hannun Ammy ya ja ta can sashensu.Suna shiga ta ce “duk abin da ka ga Grand-Maa na yi tsufa ne sheikh Rayyadeen,kar ka taɓa damuwa”

Ya ce “haba Ammy ta ya ba zan damu ba alhalin tana yi miki abubuwan da suke sosa mini rai” Ammy ta ɓata fuska ta ce “tun da ta haifa mini miji ina da wata ne? Yadda kake mugun jina a zuciyarka haka shi ma Abih ɗinka ke son mahaifiyarsa,ko za ka ji daɗi in matarka ta yi ba daidai ba in na yi mata faɗa sai ɗanka ya zo shigar mata?”

Ya marairaice fuska yana mai cewa “haba dai Ammy ta ya ma zan auro matar da za ta raina ki?”

Ta yi ƴar dariya tana mai cewa “to ai misali ne na buga maka,kuma ma ma fi akasarin ustazan yanzu matansu duk shegiyar tsiwa ce da su da sangarta ka ga kuwa ni ba zan juri na ga ba a kula mini da kai yadda ya kamata ba”

Bai san dalili ba haka kawai fuskar Khadeeja ta faɗo masa a rai,ya wani tamke fuska yana cewa “ni ma na tsane ta Ammy,ba ki ga yadda ta ɓare baki tana kuka ba kawai daga direba ya jinkirta zuwa ya ɗauke ta”

“Wace ce?” Ammy

1 / 18