MAFARKI Love and Horror Story By Mrs Sadauki.txt

Author :  Mrs Sadauki Category :  Hausa Read

Chapter   7 / 18

18K to 21K   out of 53.5K words

lokacin da bacci ya ɗauke ni ba ya kai ni duniyata ta MAFARKI.


Yau kuma cikin wata asibiti ce na tsinci ruhina,ina tafe ina dube-dube kamar wacce ta ɓata kafin kuma na soma shiga ɗaki bayan ɗaki har na isa wani mai lamba uku.A can ƙarshen gado na hango ta tana kuka,gashin kanta duk ya cunkushe haka ma kayan jikinta duk sun yage,yayin da fatarta ke fitar da jini saboda yagar kanta da take yi da manyan akaifunta.

Ina yin tsaye bakin ƙofar ta tsaya cak da kukan da take yi tana kallona,a zahiri mahaukaciya ce amma a baɗini da hankalinta rasss.
“Me yasa ki ke zaune a asibitin mahaukata alhalin da hankalinki?” ita ce tambayar da na jefo mata.

Jikinta ta ƙanƙame tana mai cewa “alhaki ne! ” tako biyu na yi kawai amma na ganni a gabanta,hannunta na kama na jimƙe sosai sai ta soma magana kamar an kunna rediyo.

“Ƴar talakawa ce ni,na auri talaka na rayu da shi na tsawon shekaru har na haifa masa ƴan mata biyu.Amma rayuwarmu na nan a talauce,ƙarfin babu ta sa na soma yin aikatau don ciyar da yarana saboda mijina ya koma cima zaune.Yawan aikin da nake yi yasa cikina ɓarewa ina tsaka da gugar tiles,nan na zube jini na bin ƙafafuna ina murƙususu.Na ɗan fita hayyacina na wani lokaci kafin na dawo normal,nan na yi tozali da abu ma fi girman ɗaga hankali.Uwar mai gidan da nake yi wa aiki ce na yi tozali da ita ta kwashe ɓarin da na yi ta saka shi a kwalba tana siɗar yatsunta da suka yi kace-kace da jini.Ƙwala-ƙwalan idonta kuma suna juyawa babu sirki kamar na ƴar tsanar roba,wagegen bakinta ta buɗe mini tana wani irin murmushin ajali kafin ta ce “ni da mai ciki ba mu iya zama wuri guda,yawuna tsinkewa suke yi ” wani tashin hankalin ne ya sake rufe ni,don kuwa na fahimci ita ɗin mayya ce na yunƙura da niyyar maƙure mata wuya shi ne ta cire igiyar da ke saita tunanina ta haɗiye a bakinta,kin ji dalilin zuwana a nan ɗin ” ta ƙarashe faɗa tana mai janye hannunta yayin da kuma idonta suke canza kala zuwa kore kamar dai na Rashida.

Ina gama jin labarinta na fito daga cikin ɗakin,cikin wani lungu mai tsananin duhu wata mata ta bayyana a gare ni tana mai yi mini wani jawabi mai kamar bushara.“Duk wasu matsalolin da muke faɗa miki a MAFARKI don su nusar da ke ne gidan da kike son kutsa kanki ciki.Hadiza(cewa da Ummah mahaifiyar Daddy) ta yi wa duniyarmu hidima wannan yasa muka yi alƙawarin kare bayanta, wannan ɗin haƙinmu ne.Ungo wannan ruwan ki zuba su a cikin baƙar tukunyar da kika ɓoye a ƙarƙashin gado” ta ƙarashe tare da miƙo mini wata ƴar mitsitsiyar kwalba na karɓa tare da jimƙe ta gam cikin tafin hannuna.Daidai nan na farka,wata irin ƙirshiwa ce nake ji ina shirin dirowa daga kan gado na ji wani abu cikin hannuna ko da na duba sai na yi tozali da kwalba.Nan take kuma mafarkin da na yi ya dawo mini cikin kai,sauka na yi na jawo tukunyar na buɗe ta tare da zuba ruwan ciki wani abin mamaki shi ne yadda ɗigon ruwan da ba su wuce biyar ba amma suka kusan cika tukunyar .A sannu a hankali na ga ƙwan na ƙara girma yana yin motsi,kafin kuma ya soma tsagewa .Ido kawai na zuba ina kallo har ida buɗewa duka,wata ƴar jaririyar halitta ta fito mai kamar mutum kamar kuma aljana,tana da manyan ido da kunnuwa faka-faka sai ɗan ƙaramin hanci.Wani tsalle ta yi tare da yin suka kan jikina,na buɗe murya cincin ƙarfina na ƙwala razananiyar ƙara da mugun sauri ta sauka daga gare ni ta yi suka ta haye gadona tana mai zubo mini idonta da suke wasar canza launi....


Normal group 300, VIP 500 via 2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank DM +22795045822
[15/12 09:13] MRS SADAUKI: *MAFARKI*👁️🦋🦋🦋
🦋🦋🦋
🦋🦋
Mallakar : 🦋
Chamsiya Laouali Rabo
```MRS SADAUKI 💫✍️```

07

Ban taɓa shiga tashin hankali ba irin na yanzu,kuka nake yi na rashin mafita.Ga shi dai ni ce da kaina na binciko wannan baƙin sirri amma kuma sam ban ji zan iya zama tare da aljana ba a ɗaki guda,ita kuwa shegiyar halittar sai ci gaba take da kallona tana juya ido kafin ta ce “ sunana Nina halittar prophecy,na rayu a wasu ƙarnikan baya,yanzu kuma kin sake haifata kin raya ni ”


Jikin ƙofar toilet na ƙara matsawa na riƙe ta gam,jin kuma wata lukutar masifa wai ni na haife ta.Wani tsallen ta sake ta diro ƙasa kafin ta ci gaba da cewa “kar ki ji tsorona,aikina shi ne nusar da ke hanyar da za ki bi don cimma burinki na samu Sheikh Rayyadeen ”

Ambaton sunansa da ta yi shi ya ɓarar mini da dukkan tsoronta da nake ji,kan gwiwaina na zube ina mai cewa “da gaske za ki taimaka mini na samu Sheikh Rayyadeen?”


Ta jinjina kai kafin ta ce “bani hannunki na dama” a tsorace na miƙa mata su,caraf ta saka yatsana manuniya a baki ta dantse da haƙoranta wani abu ya shige ni mai kamar lantarki ya soma caza ni kafin wani lokaci na tsinci kaina kwance a kan capet Daddy da Momy da kuma Ummah kewaye da ni.Ɗaya bayan ɗaya na kalle su kafin na ja numfashi na ce “meke faruwa da ni kamar ni kamar ba ni ba?”


“Alhamdullah tun da kin farka,je ki haɗa mata wani abu ta samu ta ci” cewar Daddy yana mai kallon Momy,amma Ummah ta yi karaf ta ce “a'a bari na haɗa mata” sai ta fita.

Tashi na yi zaune ina mai ɗan lumshe ido haɗi da sauraren yadda jijiyar gefen wuyana ke wani bala'in harbawa.Babu jimawa Ummah ta kawo mini abinci,amma kallo guda na yi masa na san da ta saka magani amma haka na ci kafin in shiga toilet na yi wanka da ruwan ɗumi.Ko da na fito babu kowa ɗakin,kimtsawa na yi na saka sabuwar pad tare da uniform ɗin makaranta.Ina saukowa ƙasa duk sai suka yi murnar ganina,sai a lokacin na gaishe su Daddy ya ce “mu je na sauke ki makarantar a motata ” cike da jin daɗi na yi masa godiya kafin mu fita,yau a gaba na zauna kusan Daddyna sai da ya fara tuƙi a babban titi sannan ya miƙo mini wayata wacce ban san yaushe ya ɗauke ta ba kuma ni kaina da na tashi ban ma neme ta ba. Ina karɓarta sai na ga an ɗora mini hoton Sheikh Rayyadeen kan fuskar wayar,hakan ya tabbatar mini yanzu Daddy ya san mene ne burina wata irin kunya ce ta kama ni,sai kawai na sunne kai ina shafar screen ɗin da ke ɗauke da haske yana nuno mini abincin ruhina.


“Tun yaushe kuka fara soyayya Ummita?” Daddy ya jefo mini tambayar.

A kunyace na ce “Daddy ba soyayya muke yi ba,hasali ma bai san ina sonsa ba”

“Don me? Ai sai ki sanar da shi” da sauri na ɗago kai na dube shi jin abin da yake cewa,ya jinjina mini kai kafin ya ce “manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama da kansa ya yi mana nuni da hakan,ya ce duk wanda muka ji muna so mu faɗa masa”


Na rufe fuska na ce “ni dai Daddy kunya nake ji” yayi ƴar dariya kafin ya ce “duk da cewa ba zubar da aji ba ne mace ta furtawa namiji kalmar so,amma kuma na ji daɗin haka daga gare ki .Na san ba ke ce ta farko da kike sonsa ba,ƙila ma har wasu sun taɓa furta masa to ke ina so ki zama daban da sauran.Duk namiji in dai malami ne shi to yana ƙaunar ɗalibarsa ko ɗalibi mai ƙwazo,to ke yi ƙoƙarin kasancewa haka”


A shagwaɓe na ce “Daddy tun tuni fa nake ta ƙoƙarin hakan,amma a cikin ajinmu fa har da mahadatan Alkur'ani akwai”

“Ke ma ki haddace Ummita ”

“In sha Allah Daddy” na furta daidai nan kuma muka kawo makarantar,har ciki ya shigar da ni na yi masa sallama na fita.Daddy na tafiya na kai dubana inda ake parking amma ban ga motarsa ba,jiki a sanyaye na nufi sabon ajinmu sai na tarar da wani sabon tsari wai layin da za mu zauna daban.A gaba na zauna,babu jimawa Mujahida ta zo ita ma bayan mun gaisa take cewa “yau kuma mafarkin me kika yi?” shiru na yi kafin na tuna matar da na gani a gadon asibiti,bayan na gama labarta mata ta ce “ko mu je can asibitin mahaukata ɗin mu gani?”

Na ce “har mu tashi daga makarantar safe,amma kin san muddin na ganta har azahiri to wallahi zan sa a raina ba wai kawai MAFARKI ba ne akwai wani ɓoyayyen lamari da ke faruwa da ni”

Shiru duk muka yi sakamakon shigowar malam Hafiz wanda ya kasance shugaban makarantar.

“Ku fitar da littattafai ko kuma alƙur'ani ku yi karatu yanzu Sheikh ya kira ya ce zai zo a makare a shaida muku ku fara yin karatu kamar yadda ya tsara muku” yana gama faɗar haka kuwa aka fara yin karatun sai dai yau ɗin ma Sadiya ce ke son lallai sai ta koyar da ni amma na ƙi.


★SHEIKH RAYYADEEN

Tun bayan da ya fito daga gidansu Khadeeja ya nufi wata makaranta da yake bada karatun dare zuciyarsa fal takaici da haushin Deeja.Ya hau ya zauna kan cewa raina shi ne ta yi shi yasa har take basa umarni,umarnin ma na ya saɓawa Ubangijinsa yayi ƙarya.Sosai ma yayi mamakin cewa ƴar malam Ben Abdullahi ce,don su haka suke kiransa .Ya ja tsaki ya fi shuren masaki,yana jin inda ma da ta ce yayi ƙaryar kwashe ta yayi da mari.Yana isa makarantar kafin ya shiga ciki sai da yayi sallar isha'i sannan ya wuce ya koya musu bayan nan ya dawo gida.Yau ba tare da shi aka ci abincin dare ba wannan yasa bai san abin da ke faruwa ba sai da ya shiga babban falon sashensu ya tarar Ammy na zaune tana kuka idonta sun kaɗa sun yi ja sosai.

Tun kafin ya ji dalilin kukan nata hankalinsa yayi matuƙar tashi,da sauri ya ƙarasa yana mai yi mata sallama tare da tambayar “Ammy lafiya me kuma ya faru?”

Kamar wata ƙaramar yarinya haka ta jimƙe hannunsa gam tana mai ci gaba da yin hawayen da yake ɗaga masa hankali.
Jijiyoyin kansa ne duk suka fito,ya ce “na sani yau ma Grand-Maa ce ta taɓa ki babu komai ni na san abin da zan yi, Please Ammy ki bar kuka”

Ya faɗi haka tare da goge mata hawaye,ita kuma ta jinjina masa kai.Dakyar ya samu kanta ta shaida masa abin da ya faru,“Maa ta baiwa mahaifinka zaɓi ko dai ya sake ni ko kuma ita ta bar masa gidansa sai ya je ya canza uwa,shi ne shi kuma sam babu uzuri ko tambayar dalili ya hau ni da masifa har da cewa asiri na yi masa” ran Sheikh ne ya ƙara ɓaci sosai.Sai dai bai sanar da ita matakin da ya ɗauka ba,ɗakinsa ya shiga ya ɗauko mata maganin ciwon kai da na bacci ya bata ta sha babu jimawa kuwa bacci ya ɗauke ta.


Babban falo ya fita ya je buga ƙofar ɗakin Saude mai aiki,bayan ta fito ya shaida mata yana son a yi masa aiki ne.Haka ya ja ta can zuwa sashen Ammy ta soma jera kayanta a trolly yayin da shi kuma ya kira amininsa Sheikh Laminu yana son a kawo masa babbar mota wacce za ta kwasar masa kaya,duk da shi ɗin bai ƙasar amma motocinsa ne haka yasa aka aiko mota biyu har da ma masu kwasar kaya.Sai ga shi abu kamar a mafarki ana kwashe kayan Ammy,hankalin Mama ne ya tashi duk da ta san abin da ya faru amma ba ta yi tsammanin gaske Abban yara zai iya sakin abokiyar zaman nata ba.Tambayar duniya ta yi wa Sheikh ya ƙi yi mata magana,ga Ammy sai bacci take yi sai bayan an kwashe abubuwan amfaninta kawai, ya tashe ta shi ma ba wai ta wartsake ba ne garas haka ya taimaka ya riƙe ta suka fita ya saka ta a motarsa,Rashida haka ya kai ta mota ita dama kayanta suna can gidan mijinta.A nasa ɓangaren ma kaf kayansa ya kwashe,motarsa ce a gaba yayin da na kayansu ke bin bayansa har suka isa babbar palace ɗinsa wacce ya gina domin matarsa da kuma ahalin gidansu sai dai kuma a dare ɗaya an rushe masa plan ɗin surprise ɗin da yake son yi musu.

Duk wani abu da za a buƙata a cikin rayuwar ɗanAdam duk ya saka su.Lokacin da suka iso gidan ƙarfe ɗaya saura,amma tsabar yadda zuciyarsa ke tafasa haka cikin wannan daren ya narka musu kuɗi suka shiga jera masa abubuwansa da kayan jikinsa,na Ammy kuwa Saude ce ta fara shimfiɗa zanen gado suka kwantar da ita kafin ta soma aikin amma yadda bacci ya fi ƙarfinta haka ta haƙura ba ta yi shi ba.


A ɓangaren Sheikh kasa baccin yayi,baƙin ciki ne iri-iri ke taso masa dakyar ya iya tashi ya nufi danƙareren benen saman da yasa aka gina masa duk don domin shi da matarsa ,amma ga shi an dawo babu ita a ciki.Haka ya soma ƙarewa ɗakin kallo tun daga kujeru har labulaye da capet sun machin,ba kuma sai an faɗa maka ba miliyoyin kuɗi ne aka kashe ba.A hankali ya taka ya shiga ƙaton bedroom ɗin wanda shi ma tsabar girmansa yasa sai da aka zuba masa kujeru sai dai wannan ɗin ɗaya ce mai katafaren girma kai kace ma wani gadon ne,a gabanta an ɗora capet mai taushi da ƙaramin banci na gilas .Shi kuwa gadon wasu labulaye ne farare tasss sun kai goma aka yi masa wata kwalliya da su ta yadda in mutum na ciki ba za ka sani ba.


Wanka ya yi sannan ya shimfiɗa dadduma ya shiga jero nafiloli sam bai rumtsa ba ko kaɗan har aka kira sallah ya fita yayi,sai bayan ya dawo ne ya soma jin baccin kafin ya kwanta sai ya turawa shugaban makaranta saƙo.Sosai ya samu bacci mai daɗi ya ɗauke shi,ƴan magana na cewa abin da ka kwanta da shi a rai to shi kake mafarki hakan ce ta faru da Sheikh Rayyadeen ya yi mafarkin yayi aure sun tare a wannan gidan har da ma haihuwar yara biyu.Ko da ya farka kusan ƙarfe takwas na safe,wanka ya fara yi ya saka jallabiya ya sauko ƙasa amma da mamakinsa Ammy ya tarar a falon ita da mai aiki Saude.

A hankali ya ƙarasa yayi musu sallama tare da gaishe su,yana zaunawa ita Sauden sai ta tashi yayin da shi kuma ya sunne kai yana mai cewa “yi haƙuri Ammy na san ranki ya ɓace da kika tashi kika ganki a wannan gidan”

“Ko kaɗan raina bai ɓace ba Deeni,in akwai abin da ban ji daɗinsa ba shi ne ta yadda silata ka rushe plan ɗinka na sai ranar da za a kawo matar aurenka za ka shaidawa ahali su ma nan ɗin gidansu ne”

Yayi wani ɗan murmushi wanda a cikinsa za ka iya hango damuwa ya ce “Ammy lokacin ina da burin auren Safara'u ne,na yi tunanin ita za ta ƙetarewa baƙar ƙaddarata sai dai ashe ita ce ma za ta rufe babin kwaɗayin yin aure a rayuwata”


Ammy ta yi ɗan shiru kamar mai nazari kafin ta ce “ina yi maka kwaɗayin yin aure Sheikh Rayyadeen ɗina,kar ka taɓa yanke zuwan tsammani daga Ubangijin rahama”'

Ya ce “na sani Ammy,ba wai na fidda rai ba ne a'a banda burin son ƴar kowa gudun kar na shafa mata kashin kaji ”

“To ka auri Khadeeja”

Ya wani dube ta da sauri kafin ya ce “Ammy ban sonta ”

Ta ce “su ma ai sauran waɗanda ka yi burin aure babu wacce ka taɓa so Deeni”

“Yunwa nake ji Ammyna,duk jiya ban ci komai ba” ya faɗa tare da jingina jikin kujera yana jin zuciyarsa na dokawa,tsoronsa guda ɗaya ne tak kar Ammy ta ɗaukin dogon buri ta ɗora kan sai ya auri Khadeeja.Bai so hakan ya kasance abu na farko da zai bijire wa umarninta,don shi kaɗai ya san matakin tsanar da yake yi wa Khadeejar.Sam zuciyarsa ba ta yarda cewa wannan za ta iya ma mata tagari ga mijinta ba ballantana uwar kirki ga ƴaƴanta,to ita kanta yarinya ce tana buƙatar a yi mata tarbiyya da kuma horon girmama manya,in son samu ne a bulalaye ta domin ta cire rashin kunya da tsaurin ido.Ya ja tsaki a fili tuna yadda jiya ta wani tsure shi da ido ko kunyarsa ba ta ji ba,tsabar iskanci kuma ko gaishe shi ba ta yi ba sai ma dai ƙawarta ce mai hankali ta yi haka.

Ammy wacce ta zuba masa ido jin lokaci guda ya canza musu akalar zance,tana shirin tashi kuma ta ji yayi tsaki ita kuwa murmushi ta yi don tana ji a ranta tunanin Khadeejatu ne yake yi.


Kitchen ta shiga ta haɗo masa abin da suka ɗan girka ta kawo masa,da mamaki ya ce “Ammy ina kuka samu gas ?”

“Na mai gadi ne Saude ta karɓo ,shi kuma na aika ya sayo mini komai” ta basa amsa .

Ya ce “in sha Allah zuwa an jima duk za a kawo komai na dangin abinci har da butalin gas ɗin”

Ammy ta ce “Allah yi maka albarka ya kare ka,ta tsare ma dukiyarka ya kuma ƙara buɗi na alkhairi ”

Ya amsa da “amin Ammyna na gode sosai”

Bayan ya gama yin breakfast ɗin ya koma ciki,sai da ya sake yin wani wanka yayi brush ya fesa turaren baki sannan ya fito.Cike da nutsuwa ya shafa mai ya gyara saje da guminsa da kuma sumar kansa wacce take kwance luf irin ta larabawa.Yau ma fararen kaya ya saka,sai ya ɗora alkyabar maza mai ruwan ƙasa ya saka

7 / 18