MAFARKI Love and Horror Story By Mrs Sadauki.txt

Author :  Mrs Sadauki Category :  Hausa Read

Chapter   15 / 18

42K to 45K   out of 53.5K words

ya zubo har gadon baya sannan ta fito.


Har ta kai bakin ƙofa ta kuma cin karo da muryar mahaifinta yana cewa “ga wannan baƙin tabarau ki saka domin luluɓe idonki”

Ta juya da mugun sauri tana kallonsa,sai ta ga sam Abih bai so suna haɗa ido yana kauce wa dubanta.Cikin saurin fushin da ya zama ɗabi'arta yasa ta yi amfani da idon nata ta fizgo tabarau ɗin ba tare da ta motsa ko da yatsan ƙafarta ba ne.Tana gama daidaita zaman tabarau ɗin ta fice cikin sauri,tana tafe tana furta wasu ɗalasimai da ita kaɗai ta san ma'anarsu har ta isa makarantarsu .


Tun a bakin ƙofa kunnuwanta suka zuƙo mata gulmarta da ake yi a can ofis ɗin shugaban makarantar,cak ta yi tsaye tana mai kaɗa kunnuwan nata suna yin wani irin motsin rai haɗi da ɗan ƙara girma.

“Ɗalibai da dama suna cutuwa saboda ita ,a ƙaf makarantar nan ita ɗaya ce Albino ta banbanta da students abin da ya fi shi ne kawai a sharanɗa mata saka safar hannu da kuma niƙaf ko kuma dai abin da zai rufe wannan ƙonanniyar fuskartata mai kamar zazzaɓin faɗuwar rana” shi ne abin da muryar wata mata ke faɗa kafin muryar wani mutum ta ɗora da “ya kamata kuma a lura da kyau a zuba mata ido,makin da take samu a kowace jarabawa ya wuce hankali duk ta ƙare tana amfani da baƙin tsafin gidansu ne”.....

Yadda wani jinjirin Jemage yayi mata tsuwa a kunne ne ya janye hankalinta daga sauraren masu hana ruwa gudu.Ta ɗaga kanta sama tana mai kallonsa,babu shiri wani murmushi ya bayyana a fuskarta wanda haka ya bayyanar da haƙoranta masu kalar chocolat.


A zahiri za ka ji kuka ne Jemagen ke yi,amma a baɗini magana ce yake yi mata.Idonta kawai take juyawa suna fitar da wani kalar haske kamar na wutar kyandir,tana a haka ta ji daga bayanta a rungume ta.

“Koojal !” ta furta tana murmushi mai sauti,Jemagen ya ɓace kamar walƙiya yayin da kuma EZRA ta juyo tana facing ƙawarta Koojal wacce ta kasance makauniya ce ba ta gani.

Cike da zumuɗi ta ce “EZRA yau dai za ki cika alƙawarin da ki ka yi mini”

EZRA ta sake yin wani murmushin kafin ta ce “Yesu ya albarkaci rayuwarki Koojal ,da dukkan alamu kin ƙagu ki ga duniyar nan mai cike da ababen tsoro”

Koojal ta ce “Ameine!(Tana nufin Amin kamar yadda in an yi wa musulmi addu'a yake cewa Amin !) Amma dai yau za ki buɗe mini ido ko?”

“Ta buɗe miki ido kamar yaya? ” Malama Sharly ta faɗa wacce fitowarta kenan daga ofis ɗin shugaban makaranta.EZRA ta ƙure ta da ido tana mai juya su suka canza kala,cike da mugunta take haɗe fuska tana yi tana motsa bakinta sai ga Malama Sharly ta zube ƙasa,wanda ya yi daidai da tasowar guguwa iya inda suke ta luluɓe su tana wani laulaye su tana yin sama da su.Ita dai Kajool ba gani take yi ba kawai dai tana jin wani canji ne.EZRA ba ta tsayar da wannan guguwar ba sai da suka isa wani keɓaɓen wuri wanda ita kaɗai ta san ina ne.

Cikin i'ina take kallon Madam Sharly tana cewa “tambaya kike ba? Ta ya zan yi na buɗe wa ƙawata Kajool ido? To idonki zan cire na saka mata”

Kajool wacce ke tsaye kamar itaciya ta waro makafin idonta,yayin da kuma Madam Sharly ta yunƙura za ta gudu don kuwa tuni ta dawo hayyacinta.EZRA ta lumshe idonta ta fara karanta ɗalasima “akasubamatahe! Janukohiii! Jangooo! Jangooo! Jan...jan...jango!” wasu irin ƙananun baƙaƙen macizai suka ɓulɓulowa daga cikin ƙasa suka yi wa Madam Sharly sarƙa ta ko ina.......
[18/12 13:06] MRS SADAUKI: https://chat.whatsapp.com/DINOgJaFqZuCh9dFNLLmp8?mode=ems_copy_t
*INUWAR ALJAN*👻



```LoVe aNd HoRrOr story```👽


By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI💫✍️}



*SADAUKARWA:* Ga Rachida Mamar ƴan biyu, alherin Allah ya luluɓe ki . Ubangijin rahama ya kula da lamurranki👏🏻

*FCWA*☀️

________________________


06


Wani irin murmushi ne EZRA ta yi wanda ba ka ganinsa sai ɗayan biyu,ko dai tana magana da masoyanta irinsu Jemagu,macizai ,kifaye da kuma ƙawarta Koojal, ko kuma in ta yi nasara ne akan wani abu da ta ƙudirta.


Takardar da ta yi rubutu a kai ta fiddo kafin ta dubi Koojal ta ce “kar ki ji tsoro ƙawata,yanzu nan zan yi miki aiki idonki su buɗe” Kooljal ta yi ƙyaf-ƙyaf da idonta waɗanda suke farare tasss babu ɗigon baƙi ko ɗaya kafin ta ce “da gaske kuma na Madam Sharly ne za ki saka mini?” ba ta bata amsa ba,sai aikinta da ta fara tana karanto ɗalasimai kamar haka“marmaid nakhily bahee eyes! Kuncutacu habkur eyes ! Eyes” wata irin ƙara Madam Sharly ta soma yi ,yayin da kuma EZRA ta canza siffa daga mutum zuwa kifanyar ruwa,cikin zafin rai ta matsa kusa da ita tana mai sa hannu ta ciro idon Malama Sharly ɗin sannan ta dawo kusan Koojal ta shafi fuskarta nan take makafin idonta suka faɗo ƙasa kai ka ce dama na roba ne.Cike da ƙwarewa wurin tsafi EZRA ta ciro sanadarin ganin ta saka cikin gurbin idon Koojal sannan ta maida mata nata ɗin da suka zube ita ma Malama Sharly ta mayar mata da nata sai dai fa ba su da amfani.

Tsaye ta yi gaban Koojal ta yi wani furicin a take ita kuma ta buɗe idon ta yi tozali da ƙawarta wacce tun tana makauniya take yawan shafar fuskarta sannan wani sa'in EZRA ɗin da kanta take siffanta mata yadda take wannan yasa ba ta yi mamakin ganin fuskarta fara ƙal ba irin ta Albino.

“EZ..RA! ” ta furta murmushi mai haɗe da kuka yana kubce mata,rungume juna suka yi cike da murna kafin ta shiga yi mata godiya.

“Ina Malama Sharly?” Koojal ta tambaya.

EZRA ta ce“an mayar da ita makaranta” Koojal ta fara dube-dube ta ga manyan duwatsu ne ta ko ina ta ce “nan kuma ina ne?”

“Farfajiyar Mermaid ce,an keɓance wannan wurin ne domin halittun ruwa masu rayuwa a doron duniyar bil'adama” EZRA ta bata amsa.

Koojal ta ce “ko za ki iya zagayawa da ni? ”

“A'a ba dai yau ba sai dai wani lokacin,yanzu za mu koma makaranta ne kafin a farga ba mu nan” ta faɗi haka tana mai kamo hannun ƙawarta,kamar tuntuɓe haka suka tsinci kansu a makaranta cikin kuma ajinsu.Wannan lamari ba ƙaramin burge Koojal ya yi ba,don ita a duniya tana son abin almara sai kuma Allah ya haɗa ta da matsafiya.
Cikin ƙasa-ƙasa da murya ta ce “yanzu da nake gani mutane suna iya ganewa ?”

EZRA ta girgiza mata kai,daidai nan malaminsu ya shigo ajin wanda yana ɗaya daga cikin waɗanda suka yi gulmarta.

Darasi ya fara yana tambayoyi amma babu wanda ya sani sai EZRA,duk da ya ga tana ɗaga hannu amma ƙin saka ta yayi ya juya ya ci gaba da rubutunsa.

Koojal ta dubi littafinta irin wanda makafi ke aiki da shi mai kamar na'ura,shafa shi ta fara yi tana mai kallon rubutun sai ta ji tamkar wata murya na karanto mata abin da ke rubuce ba tare da ta san idanuwanta ke karatun ba.


“Koojal?” malamin ya kira sunanta,cikin sauri ta ce “na'am malam”

“In kin ga matsafi a gabanki mene ne farkon abin da za ki? Shin za ki guduwa ne ko yaya?” ita ce tambayar da malam ya jefo mata.

Koojal ta basa amsa da “zan gaishe shi cike da girmamawa saboda babu abin da ya fi burge ni a duniya kamar tsafi da matsafi”

Duk da ya ji haushin amsar haka ya ƙara jefo mata wata tambayar,“in ya yi ƙoƙarin cutar da ke fa wane mataki za ki ɗauka?”

“Zan karanto addu'o'in kongosa na neman kariya Yesu ya taimake ni ” ta basa amsa.Sai ya saki murmushin jin daɗi ya ce “ta ya ake gane matsafi? Ina tambaya ne ga duk ƴan aji”


Duk kowa shiru ya yi,can ya ci gaba da cewa “Maraton babban malamin Kiristanci ya ce duk wani matsafi ya tsani Bible da kuma Cross wannan ne yasa za ku ga da yawan mabiya addinin ke maƙale da Cross ko kuma ɗan ƙaramin icce mai hoton inda aka maƙala abin bauta Yesu Almasihu wannan babbar kariya ce.Sannan ya ƙara da cewa addu'ar Yesu Almasihu ka cece mu ta yi nauyi a bakin matsafi.Ku maimaita YESU KA CECE MU!” duk ƴan ajin suka furta amma banda EZRA sai kuma ya ci gaba da kawo wasu addu'o'in waɗanda suka saka kanta fara juyawa tana jin tamkar suna ƙona ta ne.

Daga nan inda take zaune ta soma jin jijiyoyin jikinta suna wata irin kumbura suna ƙara girma,ta ware idonta waɗanda hucin azabar halin da take ciki ne ya haddasa suka rine suka zama kamar nunannen tumatur.Kan malam Rohan ta sauke su wanda shi kuma tsabar kaɗuwa da ganin lukutar masifa ya soma yin fitsari a wando ji kake shaaa kamar raƙumi na fitsari.Duk ƴan aji suka sa dariya,babu wanda kuma ya lura da halin da EZRA take ciki in banda shi wanda ya yi sanadiyar shigarta.


Kamar wanda lantarki ya damƙe haka ya kasa yin motsi yana mai ci gaba da kallonta don dole don ita ce da kanta ta hana jijiyoyin jikinsa ci gaba da aiki.Cikin ƙaraji ta yi amfani da wata guragurbin murya mai matuƙar firgitarwa ta ce “wato so kake yi a lalle dole sai ka murƙushe baiwar tsafi da ke gudana a jinina da kuma ire-irena? Ka makaro domin kuwa na da ɗan lokaci tutar tsafi ce za ta dinga kaɗawa a kaf Daular Alfanso”

Malam Rohan wanda yake cikin halin ƙaƙanikayi ya soma motsa baki yana son yin magana amma babu dama,ta hanyar tunaninsa ta bankaɗo abin da ke ƙunshe a ruhinsa.“Duk yadda kike son cikar wannan buri naki har abada ba zai taɓa cika ba ƙasƙantaciyar matsafiya,ba tun yau ba na daɗe da fahimtar cewa laifin ƙazamai nakassu ire-irenki ne suka hassala gimbiya Janaki ta yanke wa iyayenmu hukuncin mayar da su a keɓaɓen wuri ”

Ambaton sunan gimbiya Janaki shi ya ƙara tunzura EZRA ,saboda duk wani mai rai da ke rayuwa a Daular Alfanso ya tsane ta saboda silarta ne suke a bayan gari ba tare da an basu damar cuɗanya da sauran al'ummar yankin Uganda ba .

Daidai saitin zuciyar malam Rohan EZRA ta aika masa da wata kibiyar tsafi ta cake shi nan take ya saki wata irin razananiyar ƙara wacce ta jawo hankulan mutane da dama ciki kuwa har da shugaban makaranta.
Duk students ɗin suka miƙe tsaye cike da tsoro ganin malaminsu yashe a ƙasa yana fitar da wani baƙin hayaƙi kamar tsohon batiri haka fatarsa ke zagwanyewa.Shigowar shugaban makaranta ya yi daidai da dawowar EZRA normal,ita ma sai ta miƙe tsaye kamar sauran ɗaliban tana waro idonta da suke sak irin na mage don ita madadin baƙi wani blue mai ratsin kore ke juya duniyar ganinta.


Kallon tsaf shugaban ya soma yi wa students yayin da sauran malaman da suka samu damar zuwa nan ɗin suka fara ƙoƙarin ceton ɗan uwansu sai dai sun kasa saboda lamari ne na tsafi.


“Kowa ya tafi gida an tashi!” shi ne kawai abin da ya faɗa kowa ya soma fita.EZRA na riƙe da hannun Koojal suka fito,direct kuma can wajen banɗakunan makaranta ta kai ta.

“Me za mu yi a nan?” Koojal ta tambaya,EZRA ta ƙara ƙanƙame ta sosai kafin ta ce “ki jira kaɗan yana zuwa” ko gama rufe bakinta ba ta yi ba kuwa sautin iskan fukafukinsa ya soma kawo musu farmaki.Kamar saukar jirgin sama haka Jemagen ya dira a gabansu,babba ne sosai don ya fi girman Giwa wannan ya tsoratar da Koojal ta ɓuya a bayan EZRA ita kuwa ce mata ta yi “kar ki ji tsoro mana,zo mu hau ya kai mu fadar Mermaid zan nuna miki abubuwan da ban taɓa faɗa miki su ba”

Koojal dai a tsorace ta yarda ta hau bayan Jemagen, EZRA ke gaba ita tana baya a haka ya tashi da su sama.Cikin abin da bai fi minti biyar ba ya kai su wata duniya wacce ba ta bil'adama ba.
Farkon wurin ya soma ne da wani abu mai kamar bakan Gizo,yayin da hotonsa yake kamar madubi.Sauka suka yi suka ratsa ƙofar,nan suka ɓulla a daidai wurin nan da suka zo ɗazu da Malama Sharly.

EZRA ta ce “nan ne tushenmu,ni ɗin jinsi biyu ce .Ba koyon tsafi na yi ba,haifata aka yi da shi sai dai ban taɓa sanin mene ne ba sai da Ummi ta ilmantar da ni.Wannan Jemagen da kika gani shi ne abin hawata,duk inda zan je muddin yana da nisa to da shi nake amfani”


Koojal ta ja ajiyar zuciya ta ce “amma ta ya aka kika san da zamansa?” kafin ta bata amsa wata kifanyar ruwa ta ɓullo ta cikin wani ɗan ƙaramin gurbin ruwa.Ta yi ihu ta ce “ EZRA???” ambaton sunan nata yasa ruwa suka dinga ɓulɓulowa ta ko ina kafin ƙyaftawar ido sai ga su a ƙasan ruwa.Ido Koojal ta buɗe tana kallon halittun ruwa,wasu rabi mutum rabi kifi ko kuma rabi mutum rabi maciji.Tsaye ta yi tana kallon ƙawarta wacce a duniya in aka cire iyayenta babu wacce take so bayan EZRA,yadda ta ga jelar kifi madadin ƙafafu yasa ta waro ido ta matsa da sauri don fargar da ƙawartata sai dai ita ma sai ta ashe ita ma ta zama Siren ɗin.Wani irin kuka ne ya zo mata ba ta shirya ba,wanda ya jawo hankalin EZRA da sauri ta zo ta kama hannunta.Kamar ƙyaftawar ido sai ga su wajen ruwa a saman wata ƙatuwar bishiya....



★ DAVIDO

Ruhina da ruhin Nelson ne suka ɗingiza esprit ɗinmu izuwa maƙabartar da aka binne ƙanena Joy.A tsaye suke suna ta shawarar yadda za su haƙo gawar Joy,na dubi Nelson kafin na ce “mene ne zan yi a yanzu?”

“Ka yi musu magana,ka kuma basu damar ganin ruhinka ” ya bani amsa,sai dai ko kaɗan wannan karon ban tambaye shi ƙarin bayani na game da yadda zan yi hakan ta tabbata.Ƙarasawa na yi na tsaya kai ga kabarin,abu na farko da na yi shi ne bayyana musu hasken ruhina.Sai duk suka ja baya,sai kuma na soma gaggaɓa dariya kafin na soma yi musu magana cikin gargaɗi “tona wannan kabarin shi ne babban kuskuren da za ku aikata a rayuwarku,ina mai baku shawara da ku juya ku koma inda kuka fito”

Ɗaya daga cikinsu wanda yake da ƙarfin hali sai cewa yayi “ba za mu taɓa matsawa daga nan ba sai mun tabbatar da abin da muke zargi,don haka kar ku wani ji tsoro ku tuna cewa littafin sirri ya fi komai muhimmanci a rayuwar kowanne daga cikinmu” ya yi furicin ne tare da duƙawa ya soma ture ƙasar kabarin.Kamar yadda ake ɓalle hannun ƴar tsanar roba haka na yi wa dukkan hannuwansa a lokaci guda suka fita suka yi sama.Cikin iya shege irin nawa na yi amfani da hannuwan na soma ɓalla musu maruka ji kake fauuu,tun suna daurewa har suka soma yin ihu sai dai babu damar guduwa na riƙe ƙafafun.

Koke-kokensu ya jawo hankalin mai gadin maƙabartar,shi kuma babu wani tunani ya kira jami'an tsaro.Ko da suka iso wurin tuni na canza musu kamanni.


“David? David?” na ji muryar Jami'i na tashe ne,dakyar na fizgo ruhina daga waccan duniyar na maido shi gangar jikina.Na ware ido dakyar na sune shi,da sauri na ga ya ɗan ja baya yana haɗiyar yawu.Duk da ban san dalili ba haka na ja fatun idona na rufe,kafin can ƙasan maƙoshi na ce “har gari ya waye ne?”


“Wai don Allah wane ne kai?” na ji ya yi mini wata tambayar rainin hankali sai ka ce ba shi ne ya je ya ɗauko ni ba.

Ni ma cikin rainin wayon na ce “David Jakob,Mama kuma ta ce Davido”

Ya ja dogon tsuki kafin ta bugi gefen cinyata ya ce “banza ba wannan nake nufi ba,a duniyar ruhaniya nake tambaya wane ne kai?”

Zumbur na miƙe tsaye ina mai yi masa wani kallo kafin ni ma na aiko masa da tawa tambayar“ wa ya aiko ka wurina ?” bai ce mini komai ba illa juya mini ƙeya da yayi ya fice.

Ina nan tsaye na ji wata irin ƙara haɗi da buguwar abu kan madubin window.Da sauri na juya sai dai wayam babu kowa,ƙarasawa na yi na buɗe window ɗin ban ida daidaita tsayuwata ba na ji wani irin iska wanda ba zan iya kamanta shi ba ya bugi fuskata.Na lumshe ido ina shaƙarsa ina jin wani irin yanayi kamar ana lilo da ni,ko da na buɗe idona sai na fahimci tuni ƙafafuna sun rabu ga ƙasa wato ina tsaye ne cikin iska.Ban gama fita daga wannan mamaki ba na soma jin ƙasusuwan jikina na fitar da wata irin ƙara kafin kuma a sannu a hankali wani gashin tsuntsuwa ya soma tsiro mini a jiki can kuma ɓoyayyar siffata ta ida fito na rikiɗe na zama Mikiya daidai nan kuma jami'in ya shigo idonsa ƙurrr a kaina......




Ga masu son fara payment,Waɗanda ba su da hali su tura 300 ,masu shi 500, hajiyoyi kuma 1k🌚 via 2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank DM +2279505822
[18/12 13:06] MRS SADAUKI: *INUWAR ALJAN*👻



```LoVe aNd HoRrOr story```👽


By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI💫✍️}



*SADAUKARWA:* Ga Rachida Mamar ƴan biyu, alherin Allah ya luluɓe ki . Ubangijin rahama ya kula da lamurranki👏🏻

*FCWA*☀️

________________________

07

Cikin siffata ta tsuntsu nake kallon jami'i kamar yadda shi ma yake kallona cike da tsoro da firgici.Murya na ɗan rawa ,ya nuna ni da yatsa ya ce “David kai ne ka koma Mikiya?” ban basa amsa ba sai tashi da na yi sama ina kaɗa fukafukaina kafin na bugi gilashin window ya tarwatse haka na fita a guje ina shawagi a sararin samaniya.Cikin abin da bai fi minti biyar biyar na isa gidanmu wanda yake ɗauke da masu zaman jana'izar Abba.Kan wata bishiya da ke cikin gidanmu na sauka ina kallon kowa da ke wurin kafin idona ya sauka kan Ummah wacce ita ma ban sani ba ta ji a jikinta ne da akwai idon sharri a ankare da ita ko me,sai gani na yi ta ɗago kanta sama ta sauke idonta cikin nawa tana wani ƙanƙance su.

“Me ka dawo yi?” ita ce tambayar da ta jefo mini ta ido da dukkan alamu ta gane ni,kai tsaye na bata amsa da “wurinki na zo ,ina son mu yi magana ne”

“Ba ka ganin jama'a

15 / 18