MAFARKI Love and Horror Story By Mrs Sadauki.txt

Author :  Mrs Sadauki Category :  Hausa Read

Chapter   14 / 18

39K to 42K   out of 53.5K words

shi ba muddin ba shi ya lamunce da hakan ba.

Cike da takaici da baƙin cikin da ya rufe Sarki ya ɗaga hannu,nan take aka sauko da tutar rashin mutumci mai nuni da za a kashe matashin wanda ba kowa ne ba sai wannan mutumin nan da tsoho Jacki ya ce shi ne mahaifina.


Wasu dakaru biyu majiya ƙarfi suka zo suka ja matashi Alfanso suka tafi da shi,shi kuwa cike da ƙwarewa a aikinsa ya saka idonsa cikin na gimbiya Janaki ya jefa mata ƙwayar sonsa da kuma tausayinsa.Wani baƙin kurkuku ne aka tura Alfanso,yayin da kuma ta ɗaya gefen kuma sarki ya cika umarninsa aka soma kwashe nakassu aka kai su keɓaɓen wurin da ya yi musu tanadi.

Ina kawowa nan page ɗin ta ida sai na rufe littafin na mayar da shi ma'ajiyarsa,ina shirin fara tunani na soma jin yanayin kaɗawar iska na canzawa.Ko tantama babu ruhin matar nan wacce zan iya cewa matar da ta mayar da ni mijinta shi ne zai ziyarce ni.Ban yi ƙarya ba don kuwa kamar ƙyaftawar ido haka ta bayyana gabana,a madadin ta zo ta mu'amulance ni kamar yadda ta saba a'a yau tsaye ta yi muna kallon juna.

“Ban san ke wace ce ba,amma abu ɗaya na sani ba za ki taɓa yin nasarar hana zuciyata son albino girl ba” shi ne abin da na samu kaina da furtawa,furicin nawa ba ƙaramin harzuƙata ya yi ba sai na ga ta wani cije haƙora gashin kanta ya watse cikin iska yayin da fuskarta ta yi ja kamar wuta.

Wani irin tsalle ta yi ta faɗo jikina,babu ɓata lokaci ta soma yin abin da ya kawo ta.Sai da komai ya lafa sannan na samu hankalina ya dawo jikina,na ja wani dogon tsaki ina jin takaicin lamarin kafin na buɗe ƙofar ɗakina.Har zuwa yanzu ana ruwan sama,amma haka na fita na cika bokiti na yi wanka.Ina dawowa na tarar an canza mini zanen shimfiɗa,an kuma kunna turaren wuta sai dai ƙamshin ba irin na bil'adama ba ne.Ina jin motsin ruhinta a cikin ɗakin alamun ba ta tafi ba,yi na yi kamar ban fahimci komai ba na shirya cikin kaya marar nauyi na kwanta.Wata murya na ji ana rera waƙa mai bala'in daɗi,sai dai sam hatta waƙar tsohuwar yayi ce ta ƙarnin baya.Amma sosai nake jin daɗinta,ido na soma lumshewa a daidai nan ne na ji motsi a bayana da kuma yanayin nan in an kwanta gefenka sai dai ban iya yin komai ba saboda fin ƙarfin ruhina da aka yi.




A can ɓangaren Ummah kuwa David na barin ɗakin ta matsa kusan Joyel ta dafa kanta ta soma yi mata wasu surkulle tana jin ranta na azalzala saboda abin da bincikenta ya bada.Joyel ta ja wani dogon numfashi tana cewa “Yaya David me yasa ka kashe mutum? Wayyo ! Wayyo!” sai kuma ta buɗe idonta taram kan fuskar Ummah wacce take ta Tinkiya amma idon Joyel ba su isa su ga hakan ba kasancewarta normal mutum.

“Tashi ki sha magani” Ummah ta faɗa .

“Ina David Ummah?” Joyel ta tambaya.

“Yana ɗakinsa” ta bata amsa tana mai tashi ta shige uwar ɗaka.Wani irin motsi ne zuciyarta ke yi mata,ganin David a cikin yanayin ɓacin rai da kuma yadda zubin jarumtarsa ya bayyana yau a fili sai ta tuno da tsohon mikin da zuciyarta ke ɗauke da shi.A fili ta furta “ina sonka Alfanso” karaf a kunnen Abba wanda yake shigowa,cikin kaɗuwar zuciya ya ce “uban wane ne Alfanso?” Ummah ta juyo a firgice sai dai ko kafin ta kai ga yi masa bayani ya rufe ta da duka,tun tana kaucewa har ta soma mayar da martani,ran Abba ya ɓace sosai ya fito waje ya ɗauki wuƙa yana ɓaɓatu “wato ni za ki dinga cin amana kina bin mazan banza sai na kashe ki yau” ita ma Ummah fitowa ta yi waje, Abba ya je zai caka mata wuƙa amma ta juya tsinin wuƙar zuwa ga Abba ta hanyar furta kalmar tsafi.

Ihun Abba shi ya fito da ni daga cikin ɗakina,ban ida fita daga cikin mawuyacin hali ba na kuma shiga wani shock ɗin.Na ga lokacin da bakin Ummah ya motsa na kuma ji sarai abin da ta furta duk da kuwa kamar mai yin raɗa ta yi furicin.Babban tashin hankali a ciki kuma shi ne huda cikin Abba da wuƙar ta yi,nan take kuma jini ya soma yi masa zuba kafin ya faɗi warwas a ƙasa.


Shigowar maƙwabta kuma kamar ƙyaftawar ido ce,ni ma wani furicin na yi wanda ya fito tun daga ƙasan zuciyata sai ga ni kusan Abba hannuna riƙe da wuƙar da ke soke a cikinsa har zuwa yanzu.

Kururuwar Ummah cikin tashin hankali tana ambaton sunana shi ya ida jawo hankulan sauran maƙwabtan da ba su shigo ba.Raina ne nake jin yana ɓaci yayin da kunnuwana ke zuƙo mini munanan kalamai daga bakunan mutanen da suka shigo,babu jimawa kuma jiniyar motar ƴan sanda ta cika wurin.Sai da suka zo suka janye ni ne kawai na cire hannuna daga jikin wuƙar,tsakiyar ido na dubi Ummah ina yi mata wani kallo da ni kaina ban san ma'anarsa yayin da kuma ƴansanda suka maƙala mini ankwa suka fita da ni.

Kamar wani kare haka wasu ɗaiɗaikun mutane suka fara jifata da duwatsu sai dai rasss nake kallon kowanne daga cikinsu .Har muka kai babban ofishin ƴansanda ban ce uffan ba,tun kafin a sauko ni daga cikin mota wani babban jami'i ya fito ya ce a wuce da ni kurkuku tun da dai an kama ni dumu-dumu cikin laifin kisan kai kenan babu buƙatar sai an shari'a.

Ido kawai na rumtse tun da aka canza akalar motar zuwa kurkukun ƴan ta'adda.Motarmu na tsayawa suka fito da ni,sai da aka kai ni wani ɗaki aka canza mini kayan jikina zuwa na ƴan kaso aka kuma saka mini sarƙar ƙafa da ta hannu sannan aka kai ni masaukina.Wurin ko ta ina ƙwayaƙwayin lantarki ne manya-manya sun haska wurin kai ka ce rana ce,idanun mutane ƙur a kaina har aka buɗe ƙaton kejin da aka tunkuɗa ni na faɗi ƙasa warwas nan aka shiga yi mini dariya waɗanda suke masifafu suka shiga tsokanata suna yi mini waƙa.Cike da takaici na miƙe tsaye ina kallon kowanne sai na ga duk sun shiga hankalinsu suna wani ja da baya,daga can gefe na ji wasu masifafun IDON SHARRI(MRS SADAUKI) suna kallona ina waiga wa na ci karo da mamallakinsu,wani matashin saurayi ne da ba zai wuce shekara ashirin da bakwai ba.A kallon farko da na yi masa na ji a raina na samu aboki ,a hankali na cira ƙafata na fara tunkararsa kacar da aka ɗaure mini ƙafafu na fitar da wani irin sauti mai ƙarfi har na isa gare shi.Ina shirin zama ya dakatar da ni,“kar ka take mini yaro” wurin na duba sai dai ban ga komai ba,sai na ga ya kai hannu ya gusar da wani jaririn maciji ,tozali da idona suka yi da macijin shi ya bayyanar mini da wannan tururuwar da na taɓa gani a ƙafata,kamar ƙuda haka suka yaɓe macijin ba su barsa ba har sai da ya mutu.Nan take wanda na yi wa ɗaukar aboki na ga ya ɓingire ya faɗi babu numfashi,yayin da sauran cikin kejin suka fara yin ihun na kashe shi.......
[18/12 13:06] MRS SADAUKI: *INUWAR ALJAN*👻



```LoVe aNd HoRrOr story```👽


By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI💫✍️}



*SADAUKARWA:* Ga Rachida Mamar ƴan biyu, alherin Allah ya luluɓe ki . Ubangijin rahama ya kula da lamurranki👏🏻

*FCWA*☀️

________________________


05

Cikin ikon Allah ni ma nake kallon gawar mutumin da ake ikirarin ni ne na kashe shi alhalin ko yatsansa ban taɓa ba.Tuni kururuwar mutane ta jawo hankali ƴansanda,suka shigo wasu suka fitar da gawar yayin da wasu ke tambayar ba'asi daga ƙarshe dai aka fito da ni aka kai ni wani keɓaɓen wuri wanda iskan shaƙa ma wuya yake yi tsabar matsatsi kuma ni ɗaya ne a ciki.


Kamar wani kumurcin zaki haka nake hargowa ina jin wani abu daga can cikin ɓargon ruhina kamar yana son farkawa wanda hakan ba komai ba ne sai baƙin makamin iko da ke gudana yana rikiɗewa cikin jinina.Adadin fusatata iya adadin yadda inuwar ke daɗa luluɓe raunatacen ruhina mai ɗauke da ƙunci tun na yarinta.Kan kace wani abu na ji abun ya ɗauki mallakar komai nawa,tun daga gangar jikina,ruhina da kuma tunanina.Wani irin ɓacin rai da rashin imani ne nake jin yana tafasa ni yana fitar da tiririn zallar son yin kisa a duk mutumin da ya yi kuskuren shiga gonata.


Ina nan a tsaye cikin sabon al'amarin da ya aure ni aka buɗe ƙofa haɗi da kunna hasken ɗakin.Wani babban jami'i ne ya shigo,kana kallon fuskarsa ka san bai da tausayi ko wasa a cikin aikinsa.


“Ku cire masa wannan kacocin da kuka ɗaure shi da su” shi ne abin da ya faɗa yana mai kallona,ƴansandar da suka rako shi izuwa nan cike da tsoro suka ƙaraso jiki na yi musu rawa suka buɗe makullin da aka rufe kacar kafin su yi baya da sauri su ɓuya a bayan jami'in.


Sai da ya yi mini kallon ƙurilla kafin ya ce “biyo bayana ” sai ya juya ni kuma na take masa baya har zuwa wani ofishi.
Duk ƙamewa suka yi yayin da shi kuma cikin bayar da umarni ya ce “ku rubuta bayanin bogi ku ce an tura shi izuwa babban kurkuku don yanke masa hukuncin kisa,daga ɓangarena zan fitar da nawa jawaban” babu wanda ya yi masa gardama haka suka ƙame tare da yin biyayya ga umarninsa.Sai da aka bani wasu sabbin kaya na saka na cire na gidan yari.


Cike da girmamawa kuma aka yi mana rakiya ni da shi zuwa bakin wata zuƙeƙiyar mota.A baya muka shiga ni da shi aka dinga sharara gudu da mu,har muka isa wani tabkeken wuri ban ce masa kanzil ba ina can cikin kogin tunanin dalilin da yasa Ummah ta kashe Abba da kuma shi nasa dalilin da ya so kashe ta.


Hannuna ya riƙe,wani girrr ya ziyarce ni kamar na taɓa lantarki.Na juya na kai dubana gare shi,ya sakar mini murmushi kafin ya ce “mu fita” ban yi masa muso ba na buɗe ƙofa na fita nan na yi tozali da babbar hotel,ciki muka shiga yana mai yi mini magana “za mu kwana a nan zuwa ƙarfe uku na dare sai mu wuce” kai kawai na jinjina masa kafin mu shiga daga ciki,a reception aka bamu makullin ɗakunan da ya kama mana.Makullin hannuna na shiga juyawa ina jin wani abu na daban na ratsa ni,na ɗaga kai na kalli wanda ya bani key ɗin wato mai kula da hotel ɗin .A tattare da shi na hango zallar tsoro amma ban damu ba na share tare da yin gaba don nemo ɗakin da aka bani.Ina tsayuwa bakin ƙofar na ji wani irin iska na daban ya wuce shuuu,amma a haka na zura makullin ko kafin na juya shi sai na ji ƙofar na buɗe kanta handle na yin motsi kafin ƙiiii ƙofar ta buɗe mini ta bani hanya.Ƙafata ta hagu ita ce ta fara shiga,kamar na shiga wuta haka na ji jikina yayi tsammm wanda hakan yasa don dole na rumtse ido.Kamar walƙiya haka wani haske ya feso mini fuskar wata budurwa,sanye take da doguwar riga kanti kanta babu kallabi hakan ya bai wa doguwar sumar gashin dokin da ta saka bazuwa a kafaɗunta.


Ba za ta wuce shekara ashirin da uku ba,tana da matuƙar kyawu.Yadda take tafiya cike da yanga shi ya ɗauki hankalin mutane da dama da suka zo wani wuri da ban san ina ne ba kawai dai na ganta tsakiyar taro.Kan kujera ta zauna,daga nan ne ta hangi wani mutum yana sanye da suit baƙaƙe tun na mutanen ƙarnin baya,ƙamshin jikinsa kamar na gawar da ta shekare a cikin rana madadin gidan sanyi.Kallonta yake yi cike da zallar maita,yayin da ita kuma ke jin tsikar jikinta na tashi wani irin sanyi na rufe ta maimakon kuma ta gudu a'a sai ma hakan ya tafi da imaninta.Miƙewa yayi daga inda yake ya zo ya miƙa mata hannu tare da yi mata magana ƙasan maƙoshi “taso mu tafi,na jima ina dakon zuwanki na tsawon shekaru masu yawa” ba tare da ta san dalili ba haka miƙe ta bi bayansa suka shiga wata mota har zuwa wannan hotel ɗin da muka zo ni da jami'i da aka basu key ɗin ɗaki kuwa wannan ɗakin nawa shi ne suka shigo.

Da wani irin mugun ƙarfi na ja numfashi tare da yin baya na fito daga ɗakin ina fitar da gumi.Daga bayana na ji muryar jami'in yana cewa “zo mu je ɗakina” na juya na dube shi,ban yi masa muso ba nan ɗin ma na take masa baya.

Muna shiga kamar wanda ya san irin abin da na gani sai cewa ya yi “Nadiya ƙaramar yarinya ce,ƴa ga shugaban ƴansanda wanda yayi ƙaurin suna wurin maƙiya.Duk duniyar nan babu abin da ya fi so irin Nadiya, wannan yasa ya killace ta ya haɗa ta da littatafai don ɗebe mata kewa.A wani dare ƙaddarar Nadiya ta canza ,bayan ta wuni tana karatu haka ta shirya ta tafi bikin shagalin ƙarin shekarar ƙawarta a nan ne ta haɗu da wani mutum wanda yayi daban da mutane.Duk da ta san haka amma ta bi bayansa,kaf ƙawayenta babu wanda ya iya ganin mutumin sun ce ita ɗaya ta fita.Hatta wannan hotel da suka zo masu kula da ita sun ce ita ɗaya ta shigo ta kama ɗaki,kuma da aka duba camara tsaro ta nuna iya ita ɗaya ce . Lokacin da suka shiga ɗaki sai ta kunna ƙwan lantarki,amma lokaci guda ya ɗauke daga nan babu abin da hoton bidiyon ya sake nunawa sai kukanta da kururuwarta haɗi kuma da wani yanayi marar daɗin ji da dukkan alamu tarayya ɓoyayyar siffar ke yi da ita.Sai bayan sati ɗaya sannan aka farga da mutuwarta saboda wari da ɗoyin da hotel ɗin ta ɗauka.An same ta a cikin toilet,jikinta babu sutura fatarta duk ta zagwanye.Fuskarta ta ɗauki wata irin mummunar siffa kamar ta zombie,babban tashin hankalin da aka fuskanta tattare da gawarta shi ne a cikin madubin banɗaki an hangi gangar jikinta na yin motsi wanda ke nuni da ba ta mutu ba tana raye.Can kuma aka ga bakinta ya motsa da aka bi didigin motsi laɓanta sai aka gane cewa ta furta kalmar “ga shi nan zuwa” wasu daga cikin ma'aikata suka gudu yayin da masu ƙarfin hali suka fito da gawar Nadiya aka binne ta.Tun daga wannan rana aka rufe wannan ɗakin ba a sake buɗe shi ba,amma ma'aikatan hotel ɗin sun tabbatar cewa duk dare suna jin sauti na fitowa daga cikin ɗakin wani sa'in kuma amon muryarta ne ke neman agaji ” yana kawowa nan sai yayi shiru.


Na ce “to ni mene ne haɗina da duk wannan ɗin?”

Ya bani amsa da “akwai haɗi sosai ma,yau bayan na kalli video ɗin da aka ɗauka a yayin kai ka can cikin kurkuku sai na ga shigen abin da ya faru ne da Nadiya ,sam babu wata alama ko shaida cewa kai ne ka kashe saurayin nan sai dai na ce wani abu da ke ƙunshe a ruhinka” ya faɗi haka tare da kunna mini video ɗin Nadiyar ta cikin ƴar ƙaramar system ɗinsa sai dai me zan gani? Fuskar Nelson ce shi ne wanda yayi tarayya da ƴar mutane.Sam ban san dalilinsa na yin haka ba,muryar jami'in na ji yana cewa “har zuwa yanzu da nake yi maka magana ba mu samo asalin wanda yayi wannan zaluncin ba,amma kai tabbas na san za ka iya gano wane ne saboda baiwar da kake tattare da ita”

Idona na ɗauke daga kallon video ɗin Nadiyar na mayar da su kan fuskar jami'in,na haɗiye wasu yawu kafin na ce “wace irin baiwa?”

“Je ka kwanta zuwa da safe za mu wuce” ya faɗa yana mai rufe system ɗin tare da nuna mini gado,wani kallo na yi masa mai cike da shakka kafin na je na kwanta ɗin.Ina lumshe ido na ji wani sabon al'amari kuma wanda ban yi zato ba,ruhina ne ke yin magana da esprit ɗina kan na kai ga tantance taƙamaimai abin da ke faruwa tunanina ya ɗan gushe sai tsintar kaina na yi a mutuware.Kamar kullum a zaune na tarar da Nelson kan banci yana shayi,gefensa na samu na zauna amma abin mamaki ya gane da wanzuwata har ma yana iya ganin ruhina.

“Tun ɗazu nake zaman jiran ka ” shi ne abin da Nelson ya furta yayin da kuma ruhina ya ce “ni ma na zo ne mu yi wata magana ”

“Abin da nake son sanar da kai ya fi muhimmanci kan wanda kai za ka faɗa mini” ya furta tare da miƙewa tsaye,sai na ga ya rabu gida biyu waninsa tsaye yayin da kuma waninsa ke zaune a take kuma na fahimci cewa shi ma yayi balaguron ruhi ne...


★UGANDA


Tsugune take gaban wata ƴar ƙaramar rijiya tana leƙon baƙaƙen tafasasshen ruwan da ke ta zafir.Ba ta buɗe bakinta ba,iya idonta ne take juyawa wanda hakan shi ke ƙara hautsana baƙaƙen ruwan masu mugun kauri kamar narkakar dalma.Daga bayanta ta ji muryar Abbanta na kiran sunanta “ EZRA!” ba ta juyo ba sai da ta daidaita saitin idonta ya dawo normal,cikin wani irin rauni ta ga mahaifin nata na kallonta.

Idonta ya kawo ruwa cikin amon muryartar wanda ya kasance da i'ina cikinsa wanda tun asalin haihuwarta da shi ta zo ta ce “Abiiih..kakkkar ka damu na ci alwaaa...shin zan nemo Ummi a duk inda take a faɗin duniyar nan”


Abih ya kawar da kai kafin ya ce “ki tashi ki yi shirin makaranta kar ki makara ƙarfe bakwai ta kusa ”

Cike da takaicin yadda mahaifinta a kullum yake ƙoƙarin ƙaryata abin da ke ƙunshe a zuciyarsa ta miƙe tsaye wanda hakan ya bai wa baƙar doguwar rigarta damar zubewa tana jan ƙasa.Kamar wata macijiya haka take tafiya sululu ba ka ma jin sawun takonta haka kuma kamar wata inuwa sam ido bai ganin lokacin da take cira ƙafarta.

Tana shiga ɗaki ta buɗe wani akwati ta fiddo Bible wanda tsabar tsufansa har wasu takardun sun cire.Biro ta ɗauka da takarda ta rubuta wasu bayanai kafin ta rufe shi ,wani baƙin mayafi ta ɗauka ta yane dogon gashinta wanda

14 / 18