Author : Mrs Sadauki Category : Hausa Read
ta yi wa Ammy bayanin dalilin ciwonta amma Sheikh ya dakatar da ita yana mai cewa “Ammy tana buƙatar hutu don haka a bata magani ta sha”
Ammy ta jinjina kai ta ja ta zuwa can sashenta ,garin tafarnuwa na habbatu sauda da zuma ta haɗa ta bata ta sha babu jimawa kuwa ta soma yin bacci wanda ba a ɗauki lokaci ba ta tsinci kanta wani wurin sai dai kuma ta shaida ɗakin da take ba kowane ne ba sai na Grand-Maa.
Babu jimawa fuskarta ta bayyana a gare ta tana mai cewa “wato kin zo ki sanarwa da Ammynki abin da ke damunki? Wato asirina za ki tona? To ki sani wannan baccin shi ne za ki yi ta yi har ƙarshen rayuwarki don ba zan bari ki farka ba” Grand-Maa ta faɗa tana mai buɗe bakin Rashida ta zuba mata wani rubuta da aka rubuta kalmomin tsafi,tana gama zuba mata shi kuwa Rashida ta soma fizge-fizge wanda hakan ya jawo hankalin Ammy ita kuma ta kira Sheikh.Babu jimawa suka kwashe ta zuwa asibiti ba tare da sun san cewa ba a uƙuba suka jefa ta ba.......
[13/12 09:05] MRS SADAUKI: *MAFARKI*👁️🦋🦋🦋
🦋🦋🦋
🦋🦋
Mallakar : 🦋
Chamsiya Laouali Rabo
```MRS SADAUKI 💫✍️```
05
An kwantar da Rashida kan gadon asibiti da tunanin za ta samu lafiya sai dai abin da Ammy ba ta sani asibitin cike take da miyagu don kusan maguna/ƙuliyoyin da ke yawo mutane ne a cikin siffar mage.Sheikh bai wani jima ba wannan yasa lokacin da wata mage ta shigo sam babu wani mai jarumtar da zai hana ta,ita Ammy ta yi tunanin normal mage ce har da cilla mata guntun burodi amma maimakon ta ci a'a sai suka da ta yi ta haye gadon da Rashida ke kwance tana mai yagarta a fuska har sai sawun akaifunta suka fito raɗau tare da jini.
“Innalillahi wa'inna ileyhi raji'un !” Ammy ta faɗa tare da zuwa ta cabko magen,sai dai madadin ta ji tsoka a'a wani irin abu ta ji kamar lagwami kafin ta ƙyafta ido sai ga mage ta koma tsumma.Ammy ta yi wurgi da shi tare da komawa gefe tana zarar ido haɗi da yin duk addu'ar da ta zo bakinta.Babu jimawa wata nurse ta shigo,babbar mace ce don za ta kai sa'an Ammyn.Kicin-kicin da fuska ta shigo tare da miƙawa Ammy takarda ta ce “wannan maganin muke so ki je ki nemo”
Da ɗan mamaki ta dube ta sannan ta ce “kafin yarona ya tafi ai ya bada kuɗi masu yawa ya ce ko buƙatar wani abu ya tashi ku cire ciki”
“To ban yi niyyar cira a ciki ba,ungo ki sayo ko kuma ku fita ku bamu asibitinmu ” ta faɗa tana wani ƙanƙance ido tana yi wa Ammy wani irin kallo wanda ba baƙo ba ne a wurinta,kusan kullum Grand-Maa na yi mata shi,kuma sosai take tsoronsa.
Ba tare da ta ce komai ba ta jawo waya ta kira Sheikh ,sai dai har ta yanke bai ɗaga ba.Sam Ammy ji ta yi ba ta iya fita ta bar ƴarta ita ɗaya,kawai sai ta tura gadon da kanta har ta fito waje.Mai tsaron get ne ya je ya taro mata mai taxi,haka shi ya taimaka mata ta saka Rashidar.Ammy na shirin shiga taxi ya dakatar da ita tare yi mata magana can ƙasan maƙoshi “ciwonta ba na asibiti ba ne Hajiya,in son samu ne ki mayar da ita gida don ina mai baki tabbaci kusan duk asibitocin yanzu irin wannan ce duk miyagu sun fi yawa.Da zarar kuma kun shiga akwai wani dafi a cikin ruhinta da zai jawo hankalin sauran miyagun zuwa gare ta”
Ammy na jin haka ta yi masa godiya har da basa kuɗi kafin ta shiga,har sun ɗauki titin wata asibiti amma ta ce ya kai ta can gida,ta kwatanta masa unguwar.Tun kafin su isa ta kira Mama a waya ta shaida mata, wannan yasa taxi na tsayawa ta zo ita da Aliya suka kama mata suka shigar da Rashida ciki.Baiwar Allah numfashi ma dakyar take yinsa,kallo ɗaya Mama ta yi mata ta fahimci damuwar hakan yasa cikin dauriyar zuciya ta ce “Khadi ina neman alfarma ki kai Rashida ɗakina na yi jinyarta”
Zaman amana suke yi da kwanciyar hankali wannan yasa Ammy ko tunani ba ta yi ba ta amince suka kai ta can.Mama ba ta ɓata lokaci ba ta soma yi wa Rashidar hayaƙin turaren Mayu,duk ɗakin ya turniƙe da hayaƙi.A hankali ta soma yin tari alamun ta sake dawowa duniya a karo na biyu,ta buɗe idonta wasu hawaye na yi mata zuba.Maƙoshinta take jin an riƙe shi gam an yi masa mugun ƙulli wanda ba ta ɓatawa kanta lokaci wurin gwada yin magana ba tuni ta fahimci abin da ke faruwa da ita,babban tashin hankalinta kuma bai wuce sanin ashe Grand-Maa ce wannan tsohuwar da ta taɓa bayyana a gabansu ga shi kuma ba ta da bakin da za ta iya yin bayani.
Ɗakin ne ya dawo normal duk hayaƙin ya ɓace,sai a lokacin Mama ta ga idon Rashidar a buɗe sosai ta ji daɗi duk da dama ta san da wuya mutum ya shaƙi turaren nan bai farfaɗo ba.
“Ya jikin naki?” ta tambaye ta ,da kai ta amsa mata kafin ta ja fatun idonta ta rufe tana tunanin duk wannan tashin hankalin ya faru ne silar binciken wayar miji.
A can ɓangaren Sheikh Rayyadeen kuwa tun bayan da ya dawo daga asibiti ya shige ɗakinsa,wani irin tuƙiƙin baƙin ciki ne ke rufe shi yadda ƙanƙanuwar yarinya ta raina shi ta nuna masa taurin kai.Ji ya yi ya matsu gobe ta yi don ya je makaranta,yana son yi mata hukunci mai tsauri domin ta shiga hayyacinta.
Zama ya yi ya ɗauko system ɗinsa yayi bincike,yana nan zaune Ammy ta shigo ta sanar da shi halin da ake ciki kafin ta ƙara da cewa “Sheikh ina ga lokaci ya yi da zan koma ƙauyen nan da na taɓa faɗa maka zan je na karɓowa Rashida magani wurin tsohuwar nan”
Ya ɗan ja numfashi kafin ya ce “amma Ammy kin tabbata ba shirka ba ce ?”
“Magani ne kawai fa take bayarwa,ba ta yin dibo kai ne da kanka za ka faɗa mata matsalolinka sai ta baka maganin da ya dace.Shekarun da suka shuɗe ita ce ta bani magani na sha har na samu cikinka ya tsaya ban yi ɓari ba”
“Yaushe za mu tafi?” yayi tambayar don ya san tun da ta ce za ta je to in ba zuwan suka yi ba to ba zai samu kanta ba.
“Yanzu!” ta basa amsa tare da miƙewa ta fita wanda tuni ya fahimci me take nufi, wannan yasa ya miƙe ya kimtsa.Ba su wani ɗauki lokaci ba suka fito ,direba ne ya ja su sannan babu wanda ya san sun fita.Tafiya ce ta awanni wajen biyar, Sheikh na baya zaune kusa da Ammynsa wacce ba sai an faɗa maka hankalinta ba kwance yake ba.
Sallah kawai ke tsayar da su,abinci ma iya direban ne kawai ya ci har suka isa ƙauyen wanda iya idonka kawai sun isa su yi maka fassararsa.Kirarin da suke yi wa ƙauyen BABU RABON MUGU A CIKI,ko ta ina ka duba wasu alamomi ne masu nuni da kariya a haka Ammy ta dinga nuna masa hanya har suka isa ƙofar gidan tsohuwar sai dai aka samu akasi a rufe yake.
Duk fitowa suka yi, Sheikh ya ce “ga shi gidan a ƙargame ba ki da lambarta?”
“A'a bani da,ga wani yaro can tambayo mana shi ka ji ƙila tana nan kusa ”
Da hannu Sheikh ya kira yaron, Ammy ta ce“ ina tsohuwa mai wannan gidan don Allah?”
“Ta tafi birni yau ɗin nan” ya bata amsa.
“Amma ko ka san yaushe za ta dawo?” kai ya girgiza,ba su da wani zaɓi a dole suka koma cikin mota.Cike da takaicin rashin ganin tsohuwar suka juyo mota,ba su kawo gida ba sai cikin dare suna shiga suka ƙara tarar da wani tashin hankalin Rashida ta farka sai dai ba ta cikin hankalinta har yawu ke yi mata zuba.Haka Ammy ta sa kuka tana yi,yayin da Mama ke cewa “wallahi ban san abin da ya faru ba ni dai na bar ta a ɗaki ta buɗe idonta daga in shiga kitchen in fito ne na same ta tana ƙyalƙyata dariya”
Sheikh dai bai ce komai ba sai kofi ya samu ya zuba ruwa ya yi mata addu'a,wurin fa shan ruwan ne aka yi daga don sai da aka dadanne ta aka ɗura mata su.Baiwar Allah sai ta soma jan ajiyar zuciya tana kallon Sheikh Rayyadeen,a cikin ƙwayar idonta yake hango wani duba wanda ba nata ba sai dai sam bai ba hakan muhimmanci ba.
Sashen Ammy aka mayar da Rashida,da lokaci yayi haka aka haɗu wurin cin abinci a nan ne Abba ya samu labarin abin da ke faruwa.Faɗa ya soma yi musu me yasa ba a kira shi a waya an sanar da shi ba, Grand-Maa ta yi caraf ta ce “saboda ba kai ka haifi Rashidar ba,inda ƴarka ce akwai ƴar isk...” yadda Sheikh ya buga table da mugun ƙarfi har kwanukan sama sai da suka motsa,shi ya katse hanzarin Grand-Maa ta kasa ƙarasa abin da take da niyyar faɗa.Idonsa sun kaɗa sun yi ja,duk safiyar yau in banda baƙin ciki babu abin da yake cin karo da shi,duk zafin ran sai ya soma zube shi kan Grand-Maa wacce ta yi tsuru-tsuru kamar an rutsa kwarto.
Muryarsa har wani sarƙewa take yi wurin cewa “ ba zan taɓa ɗaukar cin mutumcin mahaifiyata ba a gurin ko ma wane ne,a kullum ina yawan nusar da kai Abih ka dinga faɗawa Grand-Maa darajar aurenka ce da ke kan Ammy yasa take yi mata abubuwa har nake yin shiru,amma ba ta gani.Ta yaya ne za ka bari tana zagin Ammyna a gabanka amma ba ka cewa komai?”
Ran Abba ne shi ma ya ɓace ya ce “Rayyadeen ni kake yi wa faɗa? Ai da haɗe mu ka yi ka yi mana duka sai mu san kana son mahaifiyarka,wato uwarka ta fi tawa uwar kenan? Kai me yasa ba za ka yi wa mahaifiyarka magana ba? Ka faɗa mata ta tsarkake bakinta kafin ta yi magana”
Sheikh har ya buɗe baki amma Ammy ta dakatar da shi ta hanyar kiran sunansa,“Deeni yi shiru” ba don ya so ba ya ja bakinsa yana mai tsure Grand-Maa da ido don tun da ya fito daga ƙauyen can yake jin tsanarta tun bisa hanya ba tare da ya san dalili ba.
Tsam ya tashi zai tafi amma Abba ya dakatar da shi yana mai ce masa “ka nemo malamin ruƙiya ya dinga zuwa nan gida yana yi mata karatu”
Grand-Maa ta ce “da dai asibiti aka kai ta Mahmuda saboda alamomin hauka duk sun tabbata”
Mama ta karɓe da “babu wani hauka iskokai ne ga kanta” Grand-Maa ta fiddo idonta na mugunta wanda iya Mama ce kawai ke iya ganinsu,ita kuma sam hakan bai bata tsoro ba sai ma gefen wuyanta da ta soma shafawa inda take ajiyar nata makamin muguntar.Dole dangin naƙi yasa Grand-Maa ta tsuke shegen bakinta,shi kuwa Sheikh sashensu ya wuce sai da ya fara shiga wurin Rashida ya tofa mata“ As'alullahul azima rabal arshil azimi an yashfiyaki ” ƙafa bakwai kamar yadda Manzon tsirai ya umarce mu da mu yi in mun je duba marar lafiya.
Daga nan ɗakinsa ya wuce,wanka yayi ya canza kaya ya ɗauko Alkur'ani kenan zai fara yin karatu Ammy ta yi sallama.Ya amsa,sai ta shigo hannunta ɗauke da tray, Sheikh ya wani langaɓe kai kamar ƙaramin yaro yayin da Ammy ta soma haɗa masa abincin da bai ci ba a can.Haka ta zauna sai bayan ya gama ci sannan ta fita,shi kuma karatun yayi bayan ya gama ya yi dogayen addu'o'i yana roƙon Allah lafiya da kuma kyautar aure da sauransu.
Lokacin da ya kwanta ƙarfe biyu saura ,hakan yasa bai wani jima ba bacci ya ɗauke shi.
Washegari bayan ya dawo daga masjid ma sai da ya je ya duba Rashida ya yi mata addu'o'i sannan ya je ya fara shirin zuwa makaranta.
Tun da safe ya shaidawa shugaban zai zo yau , wannan ya sa aka ƙara tsabtace makarantar fiye da kullum.
Tsit kake jin ɗalibai babu haniya saboda kawai an ga motarsa,shi Sheikh ya banbanta da sauran malamai duk girman ɗalibi in yayi laifi tsaf zai zane shi.Ya sha dukan ƴan mata sai su turo samarinsu wasu su yi masa kashedi wasu kuma da niyyar ramawa suka zo.Amma kuma hakan bai sa ya canza ba,kusan kuma hakan ne yasa duk ake tsoronsa don bulalarsa ma in ka kalle ta sai gabanka ya faɗi.
Yana shiga ajin wani ƙamshi ya bugi hancinsa,bayan sun amsa sallamar da yayi musu sai ya samu wuri ya zauna kafin ya ɗago a hankali ya maido dubansa gare su.
Kowacce ta saka uniform,nan babu matsala sai ya soma kiran sunan ɗalibai bayan ya gama ne ya ce “sabbin zuwa su koma wannan layin” ai kuwa duk tashi suka yi ɗin,ɗaya bayan ɗaya haka yake kiran sunansu yana binciken karatunsu da ya zo kan Khadeeja sai ya lura ita sam ba ta ma yi karatun Alkur'ani ba amma aka ƙetara ta zuwa aji na gaba,ransa ne ya ɓace duk da ya lura ta yi kaf ɗaliban maki a karatun litattafai.
“Nana Khadeeja Abdullahi” ya kira sunan nata tare da ɗaga kai,Mujahida ce ta basa amsa da “ba ta zo ba malam ba ta da lafiya”
“Ita ta faɗa miki ko kuwa ƙarya kika yi don ki kare ta?” ya tambaya yana haɗe rai, Mujahida ta sunne kai tare da yin shiru sai ya ji ita ma tana basa haushi.Ya ce “tashi tsaye” ai kuwa jikinta na yin rawa ta miƙe,shi kuwa babu tausayi haka yayi mata bulala uku saboda ƙaryar da ta yi sai ga Mujahida da guntuwar ƙwalla.
Bayan ya gama bincikar karatun nasu,sai ya fara tambayar manyan ajin abubuwan da suka faru nan ne fa Sadiya uwar kauɗi ta shaida masa abin da ya faru jiya sai maƙe murya take yi tana yin ƙalƙala duk don ta burge Sheikh Rayyadeen.Sai dai bai ce komai ba ya soma yin karatu har lokacin shan iska yayi, Mujahida yau sam ba ta da walwala haka ta yi ta jaraba kiran Khadeeja amma ba a ɗauka ga kuma lambar Hamza ita ba ma ta shiga.
Bayan sun dawo aji ne ya tura sabbin ɗalibai gun waɗanda ya yarda da iliminsu domin su sauƙaƙa musu karatun wanda kuma hakan sabon tsari ne ya ɓullo,don ya rantse dole Khadeeja wurin Sadiya zai tura ta duk ranar da ta zo.
★KHADEEJA
Sam kasa rumtsawa na yi ita kuwa Ummah sai faman shafa mini maganin aboniki take yi kafin can mu haɗa ido da ita.Da dafe ƙirji tana mai cewa “mu ga idonki” sai ta gwale mini su kamar wata doctor haka ta sa fitila ta duba,wani kwalli ta ɗauko ta rambaɗa mini mai mugun yaji tana mai cewa “dama na san Allah ba zai ɗauki raina ba har sai ya nuna mini wanda zai gaje ni ” sai ta soma shafa mini wani maganin a goshi,sannu a hankali na soma jin bacci na surata har na tsinci kaina a duniyar MAFARKI.Yau ma kamar wancan lokacin a gidansu Sheikh na tsinci ruhina,duk abin da ya faru ga Rashida bayan tafiyata haka aka yi mini wahayinsa.Hatta zuwan Sheikh Rayyadeen ƙauye duk an nuna mini da kuma abin da zai faru a futur,wato ya bugi ƙawata Mujahida daga nan kuma sai aka cilla ni wani wurin.Da na ƙarewa wurin kallo sai na gano farfajiyar gidansu Sheikh ce, waige-waige na fara yi har idona ya sauka ka wani tsohon toilet duk ya gurɓace daga can cikin ƙasar.Da wani sauri na ƙarasa na isa wurin na zube tare da soma yin tono,na yi rame mai zurfi kafin na cimma wata baƙar tukunya mai murfi haka na ciro ta.Na buɗe ta,hoton Sheikh ne a ciki yana ɗan matashi bai fi shekara ashirin da bakwai ba,a hoton an zagaye wasu gaɓoɓinsa,na farko idonsa,na biyu kunnuwansa,na uku bakinsa,na ƙarshe kuma al'aurarsa sam ban san me hakan ke nufi ba kawai dai na samu kaina da ɗauko tukunyar na bi ta ƙofa na fita.Tafiyar ƙasa na yi har na iso gidanmu,cikin furanni na ɓoye tukunyar yayin da hotonsa kuma na riƙe shi a hannuna na zo na shiga ɗakina na kwanta ina bacci,kuma duk hakan ya faru ne a MAFARKI.
Washegari da sarawar kai na tashi,idona har wani zafi suke yi mini.Na tashi dakyar na zauna kan katifar,tuni gari yayi haske babu Ummah sai ƙullin kayanta.Na zira ƙafata kenan don zuwa banɗaki na ji na taka wani abu mai sulɓi kamar leda,amma ban wani duba ba na je na shiga toilet sai kuma na samu baƙon watana ya zo.Wanka na yi da ruwan ɗumi na fito,cak na tsaya ina kallon yadda iska ke tunkuɗo wani kwali har ya iso gabana,na duƙa na ɗauka ina birkito shi sai na ga hoton Sheikh a nan take kuma mafarkin da na yi ya faɗo mini a rai sak irin hoton banbancinsa da na cikin MAFARKI shi ne wannan bai da zagayen nan da aka kewaye gaɓoɓinsa.
Mamaki kamar zai kashe ni haka na zumbula hijabina na fita zuwa ɗakina,falon tsit yake babu kowa sai masifar Ummah da nake jiyowa ita da ƴar aiki.Sama na haura ,na ɗauki pad da pant na saka sannan na zira doguwar riga ta kanti na fesa turare na shafa mai.Kan bed na haye tare da riƙe hoton Sheikh ina kallo sai yanzu ma idea wanko hotunansa ta zo mini,tsam na manna shi a ƙirji kafin na lumshe ido zuciyata na ɗan dokawa a haka bacci ɓarawo ya kwashe ni sai wuraren ƙarfe sha ɗaya na rana na farka shi ma Ummah ce ta zo kaina tana balbale ni.
Na turo baki