MAFARKI Love and Horror Story By Mrs Sadauki.txt

Author :  Mrs Sadauki Category :  Hausa Read

Chapter   13 / 18

36K to 39K   out of 53.5K words

ya ciro wani abu daga aljihunsa ya shayar da Joy,nan take sai ya soma aman wani baƙin abu ana cikin haka sai kuwa wasu baƙaƙen inuwoyi suka fara bayyana a cikin gidan gawar.....
[18/12 13:06] MRS SADAUKI: *INUWAR ALJAN*👻



```LoVe aNd HoRrOr story```👽


By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI💫✍️}



*SADAUKARWA:* Ga Rachida Mamar ƴan biyu, alherin Allah ya luluɓe ki . Ubangijin rahama ya kula da lamurranki👏🏻

*FCWA*☀️

________________________

03

Yadda baƙaƙen inuwoyin suka zagaye wurin shi ya haifar da dissashewar ƙwan lantarkin mutuwaren.A daidai wannan lokacin ne matashin mai wankan gawa wanda har zuwa yanzu ban san sunansa ba ya soma yin magana.

“Kar ku yi kuskuren taɓa patient ɗina,kun yi naku aikin kun kashe shi yanzu kuma ku bari na yi nawa aikin” ya faɗa cikin muryar gargaɗi.Sai kuma na ga duk sun nutsu sun bar motsi,wani abu ya ƙara cirowa daga aljihu ya shafa a goshin Joy nan take gurbin idonsa wanda babu komai a ciki ya soma ɓulɓulowa da jini can sai ga dukkan idanuwansa biyu sun dawo.Kamar yadda mutum mai rai ke kallo haka Joy ya dube ni da idonsa kafin ya yi baya ya kwanta ya lumshe ido,gefen wuyansa wanda yake a ɓurme nan ma sai da ya zuba maganin da ban san na mine ne ba shi ma ya dawo daidai .

Inuwoyin da suka kawo mana caffa? Tuni sun ɓace kamar walƙiya.Na ja ajiyar zuciya na dubi matashin na ce “kana da baiwa ! Haifarka aka yi da ita ?”

“Sunana Nelson ɗa ga Sarkin yaƙin Daular Uganda ” ya bani amsar da ba ita na tambaye shi ba yana mai ci gaba da gyara gawar Joy har ya kammala.

Ƙofa aka buɗe,mai gadi ne da wani suka shigo suka kawo akwatin gawa sai muka haɗu mu duka huɗun muka saka gawar a ciki. Tare da fito da ita aka saka a mota,Ummah na duba sai na ga tana kallon Nelson na ɗan matsa kusa da ita na ce “ko kin san shi ne?”

“Mutane na can gida suna jiranmu mu je” shi ne abin da ta faɗa tare da yin gaba,na juya na kalli Nelson wanda shi ma na ga yana kallon Ummah wani iri.Na ce “na gode ” ya jinjina kai.Sai na wuce na shiga mota,kusa da ita na zauna kafin na ce “a ina kika samu kuɗi?”

Ko kallona ba ta yi ba,a haka muka ƙarasa gida.Tun da muka shigo layinmu na soma jin ƙarar sautin ganguna ana kiɗe-kiɗe,muna isa aka zo aka sauke gawa aka ajiye ta a wurin da aka yi mata tanadi aka ci gaba da yin kiɗa da rawa da waƙe-waƙe.

Hannuwana na harɗe ina kallon akwatin da ke ɗauke da Joy,duk wasu tsoffin moments ɗinmu ne suka ta kawowa ƙwaƙwalwata ziyara ina tuna yadda yake mugun sona da girmama ni.Wasu hawaye masu ɗumi ne suka zubo mini,daga bayana na ji muryar Isa yana cewa “David ashe rasuwa ƙanenmu ya yi? To Allah ya jiƙansa ya yi masa gafara,yanzun nan muka dawo daga wurin interview tun jiya da muka tafi”
Na ida juyowa ina kallonsu,tsabar yadda hankalina ya ɗan gushe sam ban san mene ne shi Abdul ke faɗa ba kawai dai na ga bakinsa na yin motsi.


Ji nake yi kamar na shaƙe musu wuya na kashe su kamar yadda suka yi wa ɗan uwana,amma wani sashe na zuciyata na bani wata irin shawara mai muhimmanci wacce nake ganin ita ce daidai da rayuwarsu.Rungume su na yi a tare na soma kuka biyu,ɗaya na rashin ƙanena ɗayan kuma takaicin rungumar da na yi wa abokana kuma manyan maƙiyana.Rarrashina suka fara,ina jin yadda suke sauke ajiyar zuciya mai nuni da sun samu salamar ruhi,ƙila suna tsoron kar a ce na fahimci suna da hannu a mutuwar Joy.

Keɓaɓen wuri muka zauna har zuwa lokacin da manyan pastoci suka ƙaraso duk kowa ya miƙe.Addu'o'i suka fara yi kafin a buɗe akwatin gawa aka cewa Abba da Ummah su zo su yi masa kallon ƙarshe,sai dai wani abin mamaki Isa da Abdul ƙoƙarin kutsawa suke yi ban san mene ne nufinsu ba amma dai ina da tabbacin ba mai kyau ne ba wannan yasa na kasa na tsare na ƙi bari su gusa daga kusa da ni.

Abdul ya shiga matso ƙwallar munafurci yana mai cewa “bari na matsa na ga ƙanenmu shikenan mun rabu da shi yaro mai kirki” hannunsa na yi saurin riƙewa na ce “kar ka tafi” sam ban yi tunanin furicina zai yi babban tasiri ba,kamar wani dutse haka Abdul ya kasa motsi da Isa ya so matsawa kuwa iya kallo na yi masa shi ma ya kasa wani kataɓus har aka rufe akwatin gawar aka ɗauke shi domin kai shi makwancinsa.Muna tafe ana waƙa har aka isa maƙabarta aka binne shi sannan muka dawo gida ,abinci aka rarraba da abun sha daga nan mutane suka ɓage da yin hirarrakin duniya.


Su Isa kuwa kasa zama suka yi haka suka yi mini sallama suka tafi,ni ma wuraren ƙarfe shidda haka na silale na tafi can mutuware na kuwa ci sa'a na ga Nelson.A zaune na tarar da shi yana shayi,muna haɗa ido ya sakar mini irin murmushin nan na dama na san za ka dawo.Gefensa na samu na zauna kan banci kafin na ce “barka da warhaka”


Ba tare da ya amsa ganuwar da na yi masa ba ya ce “ka yi nasarar hana su jefa ƙwayar cutar tsafi a cikin akwatin gawar ƙanenka amma hakan ba shi ke nufin yaƙi ya ƙare ba,akwai sauran rina a kaba”

Na dube shi da kyau na ce “me zai faru kuma?” sai da ya miƙo mini kofin shayi sannan ya ce “za su sake yunƙurin cikar burinsu ta hanyar farmakar kabarinsa tabbas za su je”

Hankali tashe na ce “mene ne mafita?” sai da Nelson ya yi mini wani kallon tsakiyar ido kafin ya ce “ka tambayi littafin sirrinka ”

Ƙyaf-ƙyaf na yi da ido ina mamakin ta ya aka yi ya san ina da littafin sirri,amma sai kuma na ƙi yarda na nuna na san abin da ma yake nufi don ƙila shi ma aiko shi ne aka yi.Na ce “wane littafi kuma?”

Wata dariya ya yi kafin ya ce “kar ka nuna kamar ba ka san abin da nake magana akai ba,za ka iya yi wa kowa ƙarya amma banda ni don haka ka bar ɓoye-ɓoye littafin sirrin Ruhaniya yana hannunka”

“Kai ta ya aka yi ka sani?” na tambaye shi.

“Saboda mahaifina ne mawallafin littafin ” ya bani amsa kai tsaye,na ce “kenan ba Aljanu ne suka rubuta shi ba?”

“Akwai wani banbanci ne tsakanin matsafi da Aljanu?”shi ma ya tambaye ni.

“Wane ne matsafi?” na sake yi masa sabuwar tambaya,ya bani amsa da “ni da kai”

“Ni ba matsafi ba ne”

“Da ace zancenka gaskiya ne to da littafin sirri bai zaɓe ka ba matsayin wanda zai karanta shi ya kuma maido tarihin ƙarnin baya” Nelson ya faɗa yana kallon kofin shayin da ya bani wanda har zuwa yanzu ban sha ba,saurin shanye wa na yi na miƙa masa kofin ina shirin yin magana na ji wani irin rau da idona kamar an watsa mini yaji.Bibbiyu nake ganin Nelson wanda ya soma karanto wasu ɗalasiman tsafi yana mai jimƙe hannuna,kamar wata leda haka ƙafafuwanmu suka bar ƙasa muka yi sama muna shawagi cikin sararin samaniya.Tun ina kallon duniya cikin hayyacina har na neme shi na rasa,ko da na dawo normal a wani ruɓaɓen ɗaki na tsinci kaina a kwance kan gadon kara irin na ƙarnin farko.Da sauri na tashi zaune ina dafe kaina da ke mugun sara mini,daidai nan aka buɗo ƙofa wani tsoho ne ya shigo hannunsa riƙe da sandar tsafi sai wani sheƙin baƙar azaba take.


“Ka tashi? Barka da zuwa fadar Jacki! Ungo wannan na san ba za ka rasa jin yunwa ba” tsohon ya faɗa yana mai miƙo mini wata guntuwar gurasa da ya ciro daga aljihunsa.

“Wane ne kai? Me nake yi a nan?” na tambaye shi a harzuƙe ina mai miƙewa tsaye,kafin ya bani amsa Nelson ya shigo a hasale na yi cikinsa zan kai masa naushi amma abin mamaki tsohon nan na nuna sandarsa kawai na yi baya cikin iska na dawo na faɗa kan gado.


Cikin bayar da umarni ya ce “ka nutsu da kyau don za ka fi fahimtar dalilin zuwanka nan” nutsuwar na yi don ban ga hanyar ɓulle mini ba muddin na kawo gardama.

Ya saki ɗan murmushi kafin ya ci gaba da cewa “wannan ɗana ne,na san ya baka labarin cewa ni ne Sarkin yaƙin wannan Daular ta Uganda.Ni ne babban abokin mahaifinka,duk wata shawara da za a zartar a masarauta ni ne nan ne basa ita a ƙarshe dai ina son ka ɗauki ɗana Nelson matsayin mai baka shawara”

Wata dariya na yi kafin na ce “ni kuma meke haɗina da Uganda da kuma sarauta?”

Bai ce komai ba sai sandarsa da ya nuna a kusurwar ɗakin nan take wani haske ya fito mai kamar madubi kafin kuma wata madaidaiciyar ƙofa ta bayyana.Na waro ido ina mai miƙewa tsaye,a hankali na taka na isa can na yi tsaye.Wata masarauta ce idona yayi tozali da ita,kamar dai a mafarkina kusan duk al'ummar yankin suna da nakasa ɗaiɗaiku masu lafiya.Ina cikin baza ido kuwa kallona ya sauka kan yarinyar nan,tabbas ita ce na gani ko shakka babu yarinyar da ta bani ƴaƴan itaciyar.Tana tsaye tana kallon wani gun idonta na zubar da ruwan hawaye,inda ta tsure da ido na duba sai na hangi wani babban mutum cikin naɗin sarauta da na ƙare masa kallo da kyau sai na ga sak irin fuskata ce da shi,banbancinmu shi ne tasa ta fi manyanta.


“Wannan shi ne Sarki Alfanso, adalin Sarki kuma gwarzon yaƙi,shugaba ɗaya tamkar dubu,wanda bai jin tsoro ko shakkar faɗar gaskiya ko da zai rasa ransa.Shi ne mahaifinka!” tsohon ya faɗa yana dadaɓa kafaɗata,kasa cewa komai na yi tsabar shock.Duk tsiyata bai yiyuwa na ƙaryata cewa ni ɗin jinin wancan mutumin ne,sai dai ta ya aka yi hakan ta faru? Ban sani ba.



“Nan ina ne muke?” na tambaya.
“Kana cikin masarautarku ne wato Uganda ” tsoho Jacki ya bani amsa.

“Ita waccan kukan mene ne take yi?” na tambaye shi tare da nuna yarinyar.

Ya bani amsa kai tsaye da cewa “ita ɗin ta fito Albino girl,rayuwarsu nada matuƙar haɗari a duniya saboda a kullum matsafa cikin nemansu suke yi.A irin hare-haren da ake kawo mana ne aka tafi da mahaifiyarta shi ne mafarin kukanta ”

Na maida dubana da kyau a gare ta na ce “to amma me yasa take kallon Sarki?”

“Saboda ya ce babu wata hanya da za a san a wacce masarauta ce aka kai mahaifiyarta”

“Kenan Masarautu ne ke kawo farmakin?” bai bani amsa ba sai sandarsa ya dangane da ƙasa,magijin da ke bani damar ganin yarinyar mafarkina ya ɓace.Tsoho Jacki ya dube ni ya ce “mabuɗin littafinka shi ne ka rubuta cikkaken sunanka a jikin takardar littafin sirri” sai kuma ya juya ya dubi Nelson ya ce “ku koma can inda kuka fito” ya jinjina kai kafin ya zo ya kama hannu ko kafin na furta wata kalma sai tsintar kanmu na yi a kan bancin da ke bakin mutuware.


“Ya kamata ka koma gida don yau muna da aikin dare” Nelson ya faɗa .

“Ta ya aka yi duk ka yi wannan? Ina nufin muka bar wannan ƙasar zuwa Uganda?” na tambaye shi.

“Babu wuya ai kai ma za ka iya yi,fiye da wannan ma”ya bani amsa,ban ƙara cewa komai ba na miƙe tsaye,ta ido na yi masa sallama kafin na fito bakin ƙofar asibitin.


Ina nan tsaye motoci na ta bi suna wucewa kamar wanda bai san ciwon kansa ba haka na ƙi gusawa har dare ya shigo ,iska haɗi da ruwan sama suka fara sauka sai a lokacin na motsa don neman abin da zai kai ni gida sai dai kamar an yi ruwan an ɗauke haka taxi ta bar wucewa. Ina tsaka da tafiyar ƙasa na hangi wata baƙar mota tana gudu a tsiyace,idona tamkar na mage haka suke fitar da haske suke zuƙo mini abin da ke cikin duhu.A irin haka ne na hangi Joyel a bayan mota tana ta shure-shure,tana zaune tsakiyar Isa da Abdul .Kamar wanda aka yi wa allurar ƙarfin doki haka na soma yin gudu ina bin motar har muka fita daga cikin gari .Titi motar ta saki ta ratsa jan yashi ni kuma ina bayansu,a haka har suka yi parking daidai ƙofar wani gida . Cak na yi tsaye ina kallon yadda suka ɗauke ta suka shiga da ita cikin wani gida wanda kaf wurin shi ɗaya ne,suna shiga aka rufe ƙofar sai dai ina isa bakin ƙofar wani abin mamaki na ratsa ta cikinta na wuce.Sai kuma na yi tsaye muna ƴar kallon-kallon tsakanin wasu baƙin fuska da kuma su Isa waɗanda tsabar shock yasa suka saki Joyel ba su shirya ba.Da wani matsananci gudu ta zo ta rungume ni tana kuka,ɗaya daga ciki ya ce “wane ne kuma wannan?”

Ni na basa amsa da kaina da kuma amon muryar da ba tawa ba,“mutuwarka ce!” rufe bakina ke da wuya ya faɗi warwas kansa na fita daga gangar jikinsa wanda sanadiyar haka Joyel ta suma a jikina.....
[18/12 13:06] MRS SADAUKI: *INUWAR ALJAN*👻



```LoVe aNd HoRrOr story```👽


By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI💫✍️}



*SADAUKARWA:* Ga Rachida Mamar ƴan biyu, alherin Allah ya luluɓe ki . Ubangijin rahama ya kula da lamurranki👏🏻

*FCWA*☀️

________________________

04


Cikin rigar rashin mutumcin da na aro na yaɓawa kaina na ce “ku sanar da ni abin da Joyel ke yi a wannan gidan tare da ku”

Cikin rikicewar tunani Abdul ya fara yi mini bayani daki-daki,“ka yi haƙuri David wallahi su pasto ne suka saka mu wannan aikin,su ne suka yi mana alƙawarin bamu aikin gwamnati da kuma arziki mai ɗumbin yawa muddin za mu kashe Joy bayan mun aiwatar da abin da suka ce sai kuma suka bamu maganin da za mu zuba a cikin akwatin gawar amma ka hana faruwar haka shi ne kuma suka buƙaci mu kawo Joyel ”

Zuciyata na tafasa na ce “ita kuma me za ku yi mata?”

“Budurcinta kawai za mu cire” ya bani amsa .

Na maimaita kalmar kawai a zuci kafin na ƙure Abdul da rikitatun idona,ba tare da na furta komai ko wani motsi ba jikin Abdul ya soma yin rawa harshensa na zazzalowa kafin kuma ya yanke ya faɗi kamar yadda ake datsa nama to haka wata ƙara ta ziyarci wurin harshen Abdul na guntsirewa ƙasa ya faɗi.


Isa ya saki wani mahaukacin ciwo kafin ya soma suratai na alamun hauka ya aure shi.Wani irin daɗi ne na ji a raina ganin ya haukace,ɗayan kuma na nakasa shi.Kan kafaɗata na saɓi Joyel na tashi sama cikin iska ,kamar leda haka nake shawagi a sama har na isa ƙofar gidanmu .
Ina tura ƙofa na ci karo da Ummah a tsaye tsakar gida tana yin tsafi ido rufe,jikinta babu kaya daga ita sai ɗaurin ƙirji na wani jan zane.A gabanta kuwa wata ƴar madaidaiciyar tukunyar ƙasa ce cike da ruwa,muna haɗa ido da ita ta yi saurin lumshe nata waɗanda suke a juye sak irin na tumakai.Ban ce mata komai ba na shiga ɗakinta na shimfiɗe Joyel ,ina nan tsaye na ji motsi bayana.

“Daga ina kuke? Me ya samu Joyel ɗin?” na ji muryar Ummah,share tambayoyin nata na yi na ce “ki zo ki taimaka mata ta farfaɗo” sai kuma na fice muna yi wa juna wani irin kallo.Ɗakina na shiga,kayan jikina da suka jiƙe na cire na rataye su jikin ƙarfen da nake aje sakale kaya.

Ba tare da na juya ba na yi wani furici nan take ƙofar ɗakin ta sakawa kanta sakata,na ja wani dogon numfashi kafin na buɗe akwati na ciro littafin sirri na ajiye kan teburi.Pages suka fara ƙarrr na buɗe kansu har suka tsaya a daidai farar page ɗin da babu komai a cikinta.Nan ne na ji wata murya cikin ƙwaƙwalwata na yi mini magana “jinin jikinka shi ne tawadar rubutu” ban ɓata lokaci ba kuwa na samu allurar da nake yin ɗinki na tsaki yatsana,jini ya soma ɓulɓulowa wani kare na ɗauka na rubuta sunan David Jakob amma sai ban ga komai ba.Iskan bakina na hura daidai saitin sunan Abba nan take ya goge na maye gurbinsa da na Alfanso nan take rubutu ya soma bayyana jikin takardar kamar ana ƙyanƙyasarsa.


Ina fara karanta farkon abin da ke rubuce kamar magic sai ga shi abin da na karanto ɗin ya soma bayyana a gare ni kamar na kunna magiji ko tv sai na soma ganin video ɗin shuɗaɗen zamanin da ya wuce na can wasu ƙarni da kuma na shekaru baya.

Wata Masarauta ce mai girma da tsari wacce ta dace da zaratan dakarun yaƙi.Wani sarki ne mai jini a jiki ya fito,kallo ɗaya za ka yi masa za ka fahimci shi da imani da tausayi sun yi hannun riga.Wata magana ce ya yi mai kama da raini da kuma cin fuska,“duk wani mai nakasa na ƙasar nan,daga yau ina mai bada umarni da ya koma can keɓaɓen wurin da na sa aka gina .Ban son ganin nakasshe ko ɗaya na yawo a doron masarautata, wannan shi ne adalcin da ƴata tilo ta yanke wanda ya saɓawa nawa wanda na faɗa a jiya na cewa za a kashe duk wani mai nakasa in kuma nan gaba aka haifo yaro da ita za mu sadaukar da shi matsayin hadaya ga ababen bautarmu masu inganta gobenmu ” Sarkin ya faɗa yana kallon wata matashiyar budurwa wacce ba kowa ce ba illa Ummana.Wani irin kafirin murmushi ta yi tana mai bai wa sojojin yaƙin damar aiwatar da abin da mahaifinta ya ce.

Daga can cikin duban al'ummar wani matashin gurgu ya matso a gaba cikin ɗaga murya ya ce “ya sarkinmu mai adalci a sake duba wannan hukunci,ta ya za a ce a mayar da mu bayan gari kamar dai wasu dabbobi? Shin nakasasshe shi ya halicci kansa?” yana gama rufe baki sai masu nakasa suka fara yin shewa haɗi da taɓa masa, wannan ba ƙaramin abu ba ne.Lamari ne mai nuni da cewa shi ɗin jarumi ne tun da har ya iya yin magana a gaban Sarkin da ba ka isa ka ɗaga kai ka kalle

13 / 18