Author : Mrs Sadauki Category : Hausa Read
ga idonsa na kaina.Mutane na soma fita amma ya dakatar da mu ni da Mujahida,haka aka fita aka bar mu .
Gilashin idonsa ya cire yana mai kafe mu da ido,tuni Mujahida ta soma yin hawaye cikin tsare gida ya ce “mene ne take raɗa miki a kunne?”
“Komi!” ta faɗa tana shafar hawaye .
“Mene ne kike faɗa mata?” ni ma ya tambaye ni.Na ce “ban ce mata komai ba” kawai sai ya miƙe tsaye ya ɗauko bulalarsa yana mai cewa “zaɓi uku zan baku,na farko ku sanar da ni cikin lalama,na biyu zan dake ku in jikinku yayi tsami sai ku sanar da ni,na ukun kuma zan kira iyayenku na basu takardunku na ce kun fi ƙarfinmu mun sallame ku”
Kallon juna muka yi ni da Mujahida,ina ganin ta buɗe baki za ta yi magana na yi saurin girgiza mata kai ina cewa “don Allah Mujahida ki rufa mini asiri kar ki ce komai” ban rufe bakina ba kuwa ya shiga zuba mana bulalarsa,in yayi mini biyu sai ita ma ya yi mata can ya tsaya ya ce “za ku sanar mini ko kuwa?”
Mujahida wacce dukan da yake yi mata ya fi ƙarfi saboda ya san ita ce kawai za ta yi magana don taurin kan Khadeeja shi ne shaida ba za ta saduda ba ko kashe ta zai yi.Cikin tsanani fitar hayyaci ta shaidawa Sheikh Rayyadeen abin da na faɗa mata ɗin,idonsa ne suka yi ja sosai jijiyoyin kansa suka fito raɗo-raɗo rai ɓace ya cewa Mujahida “ke ki tafi” da gudunta kuwa ta fice.Ina ganin haka na zube gwiwaina ƙasa na soma yin kuka kamar raina zai fita,sam ban ji zan iya haɗa ido da shi ba haka kuma ba zan taɓa yafewa Mujahida ba.
Kujera ya jawo ya zauna yana mai cewa “ina jinki,ki maimaita abin da ƙawarki ta faɗa yanzu da bakinki ko kuma in kira mahaifinki ki sanar da mu abin da kike nufi”.....
Saura page guda free page ya ida,zaɓi group ɗin da za ki yi karatu ƴar uwa normal group only 300, VIP kuma 500 ne via
2670215530
ZULFAU YAHAYA
ECOBANK
DM +22795045822
[18/12 12:58] MRS SADAUKI: *MAFARKI*👁️🦋🦋🦋
🦋🦋🦋
🦋🦋
Mallakar : 🦋
Chamsiya Laouali Rabo
```MRS SADAUKI 💫✍️```
10
Idona na shatatar da hawaye na ɗan ɗago kaina dakyar ina duban Sheikh Rayyadeen wanda ya yi kicin-kicin da rai kamar mai shirin fasa kuka.
“Don Allah ka rufa mini asiri ka yi haƙuri wallahi ba zan sake ba” na furta cikin muryar kuka.
“Kenan kin faɗa ɗin dai ko? Faɗa mini rashin ingantacciyar tarbiyya ne? Ko kuwa tsaurin ido ne na yaran yanzu? Ni sa'anki ne? Ko ina wasa da ke?”
Duk tambayoyin da ya jero mini babu ɗaya da na amsa,kuka kawai nake yi ina roƙon Allah a zuci kar ya taɓa bai wa Sheikh ikon kiran Daddyna.
“Tun da aure kike so zan sanar da shi Bin Abdullahi ɗin ya nemo miki miji” ya furta yana mai miƙe wa ya fita ya bar ni cikin ɗumbin tashin hankali.Dakyar na samu jarumtar tashi,zuciyata a cunkushe na je na shiga mota dakyar nake driving ikon Allah ne kawai ya kai ni gida.Ina fita na shige ciki,Daddy da Momy duk suna falo amma ban gaishe su ba.Kan bed na zube ina mai fashewa da sabon kuka,a haka Momy ta shigo ta same ni.
“Auta lafiya meke damunki?” ita ce tambayar da ta yi mini tana mai zaunawa bakin gado.Rungume ta na yi gammm kafin na ce “wata ƙawarmu ce ta rasu”
“Ayya! Allah ya jiƙanta ,ke kuma addu'a ya kamata ki yi mata mamaci bai son ana yi masa kuka” Momy ta faɗa tana shafar fuskata,kai na jinjina mata kafin na miƙe na shiga toilet.Iya hijabi kawai na cire na je na tsaya ƙarƙashin shower na sakarwa da kaina ruwa,na lumshe ido ina jin zuciyata duk babu daɗi.
Kalaman Sheikh Rayyadeen tamkar cida haka suka dinga kutso kwanyata suna firgita ni.Na toshe kunnuwana kafin na zube ƙasa dirshen ina yi wa kaina tambayoyin da babu mai bani amsarsu “shin mene ne laifina don kawai ina sonsa? Ni kaɗai ce nake da irin gurɓataccen tunanin na kasancewa da wanda nake so ko kuwa duka masoya haka suke ji?” ganin wannan ba za ta fishe ni ba na miƙe na cire kayan jikina,tsarkake jikina na yi sannan kuma na haɗa ruwan ɗumi na shiga na kwanta kamar daga sama haka na soma jin yanayin nan yana fizgata na son lulawa duniyar da ban san taƙaimaimai ina ne ba amma na bata suna kawai MAFARKI domin a cikinsa ne kawai nake tsintar kaina.
Yau kuma cikin wata ƴar ƙaramar buka ce nake mai ɗauke da wasu tarkace irinsu;ƙaho,ƙaton kan bijimin sa,fatun namomin daji daban-daban,kwari da baka na ƙashi,wasu abubuwan ma ban san sunansu ba.
A kwance nake kan baƙar fatar akuya,an yi wani circle da kyandir duk sun zagaye ni.Kusan kaina Nina ce a tsaye sai manyan idonta take juyawa,can kusan ƙafafuna kuwa Ummah ce Kakata riƙe da wata ƙwarya.
“Lokaci yayi” cewar ita Nina ɗin.Sai kawai Ummah ta soma zuba mini ruwan da ke cikin ƙwaryar tana bin duk illahirin jikina tana zubawa duk ɗigo ɗaya in sun taɓa fatata wani irin shock ne nake ji kamar lantarki ya kama ni.Ana zuwa daidai kaina ji na yi kamar raina zai fita ,ana gama wankan kuma sai aka kunna wani turare wanda bai da hayaƙi sai dai ƙamshinsa wasu kalamai Ummah ke furtawa waɗanda ban san mene ne ma'anarsu ba.
“Barka da shigowa wannan duniya!” Nina ta furta tana mai kwantowa jikina,kamar yadda ruwa ke shiga ƙarƙashin ƙasa haka Nina ta ɓata a cikin ɓargona.Na ja wani dogon numfashi wanda ya yi daidai da wanzuwata a wani wurin,ƙofar wani gida ce ina tsaye daga gefe ina kallon abincin ruhina Sheikh Rayyadeen tare da wata budurwa .Na ƙarasa kusa da su ina mai ɗauke budurwa da mari tare da yi mata kashedi “ Sheikh Rayyadeen nawa ne ni ɗaya,ba kuma zan yi sharing nasa da wata ba”
“Ni kuma ba ni sonki,kuma ba zan taɓa aurenki ba” Sheikh ya furta mini yana jifata da kallon tsana,hawaye suka soma bin kumatuna daidai nan na farka .Wani abin mamaki kuma da kuka na tashi kamar wata yarinyar goye,na yi saurin tashi na fito daga cikin ruwan na yi alwala kafin na ɗaura towel na fita.
Kayan bacci na saka,na yi sallar magarib da isha'i sannan na sauka.Falon babu kowa sai Ummah a zaune ta saka tv a gaba tana kallon India Film ,na ɗan yi murmushi ina mai cewa “ƙawali kallo ne ake yi?”
Ta dube ni kafin ta ce “sai yaushe za ki sanar da shi kina sonsa?”
Mai shirin kuka an jefe shi da kashin awaki,kawai sai na faɗa jikinta ina hawaye.“Akwai wacce take so tun tuni”
“Shi ya faɗa miki hakan ?”
“A'a a gabana ta sanar da shi”
“Je ki ci abinci to” ta furta tare da miƙewa tsaye tana yi mini wani irin kallo,da sauri na kamo hannunta ina mai cewa “na yi miki alƙawari gobe zan sanar da shi” sai ta yi wani murmushi tana shafar kaina,sai dai fa ba normal shafa ba ce a'a ina jin wani ɓoyayyen sirri na ratsa ni wanda ya mantar da ni duk wata damuwata.
Da hannunta ta bani abinci mai magani,a ɗakinta kuma na kwana a wannan daren.Wanda a cikinsa abubuwa da dama sun faru,Ummah ta koya mini abubuwa da dama duk da cewa cikin MAFARKI ne amma gaskiyar magana ita ce komai reality ne.
Washegari da wani irin ciwon kai na tashi,sai dai ban san dalili ba don duk mafarkan da na yi na manta su.
Bayan na yi sallar asubah kitchen na shiga na taya ƴar aiki girka abin da za a yi breakfast kafin kuma na haura sama na yi wanka tare da shirin makaranta,karon farko a rayuwata da na ɗauki turare mai ƙamshi na fesa a jikina shi ma ɗin ina son bar wa Sheikh Rayyadeen aiki ne ina son ya riƙe ƙamshin turarena ta yadda ko ina zai ji shi sai ya tuna da inda ya fara jinsa kamar dai yadda ni ma ya zautar da ni da nasa turaren.
Ko da na fito sai Ummah kawai a falon tana tsaye tana kallon saman ɗakina da alamun ni take jira.Ina zuwa ta jawo ni tare da dangwala mini wani abu a tsakiyar goshi sai kuma baƙin kwalli da ya kasance ban ɗauke shi abin ado ba ban saba shafa shi fa.Wannan yasa sai da aka sha daga sannan na bari ta shafa mini shi,na turo baki gaba ina cewa “haba dai ƙawali kamar dai abin tsafi”
“Soyayyarki tsabtatacciya ce ƙawali babu wani tsafi da zai shigo ciki, wannan fa kwallin Momynki ne na karɓo .Kuma tsaya ki gani yadda zai yi matuƙar tasiri kin san ido na ɗaya daga cikin abin da ake amfani da su don isar da saƙon so” Ummah ta faɗa .
Na ce “kenan ba da baki zan furta masa ba?”
Ummah ta ɓata rai tana mai cewa “au da kin zata ki furta masa nake nufi?”
Ban ce komai ba na wuce,yau dai direba ya sauke ni .Na kai dubana a parking special,babu motarsa duk sai na ji babu daɗi.Da na shiga aji Mujahida na gani,ta taso kamar kullum za ta rungume ni amma na ture ta tare da yin gaba na bar ta tsaye.
Zaune na yi tare da fiddo littafi na soma dubawa amma a zahiri ba karatun nake yi ba.
“Ki yi haƙuri don Allah wallahi banda wani zaɓi ne shi yasa na sanar da shi” Mujahida ta faɗa tana mai yin zaune kusa da ni .Ban ɗago ba haka kuma ban ce mata komai ba sai ita ce ta ci gaba da cewa,“wallahi tun jiya da na tafi gida na kasa sukuni na so ma kira ki sai kuma aka yi katari banda kuɗi a layina ga kuma Ya Hamza bai kira ni ba ballantana na sanar da shi”
Miƙewa na yi a hankali na fita na bar mata ajin,can wajen wasu shuke-shuke na nufa na zauna ina kallon yadda ruwa ke faltsa suna zuba kan ciyayi.
★SHEIKH RAYYADEEN
A ɓangarensa kuwa sosai ya ji zafin yadda ƙanƙanuwar yarinya irin Khadeeja har za ta iya yin gurɓataccen tunani a kansa.Zuciyarsa har azalza take yi yana jin kamar ya kama da wuta don baƙin ciki,yana isa gida yayi parking tare da bai wa masu kula da gidansa key ya ce a wanke motar.
Yana shiga falo da kukan Rashida ya soma cin karo, wannan yasa ya nufi ɗakinta da sauri.A takure ya same ta wuri guda tana ƙanƙame jikinta ga Ammy a tsaye riƙe da kofin ruwa.
“Malamin da Abbanku ya ce zai yi mata karatu yanzun nan ya fita,shi ya bada ruwan nan a bata ta sha” Ammy ta faɗa kamar za ta yi kuka.
Sheikh ya karɓi kofin,ya je a gabanta ya tsaya kanta ya kamo yayi Bismillah ya soma bata ruwan idonta ta zuba masa waɗanda da a ce ya lura da kyau da zai gane sak na Grand-Maa ne don ba su bar komai daga siffarsu ba.
Abin da Sheikh Rayyadeen ɗin kawai ya iya tsinta cikinsu shi ne zallar sonsa,ya yi saurin kawar da kai kafin ya janye kofin daga bakinta don tuni ta shanye.A nan ta ɓingiri ta shiga yin baccin wahala.
Sai a lokacin suka gaisa da Ammy kafin su fito,ta ce “ɗazu Mamarku ta zo nan har sun fara kawo kaya”
Ya ce “babu damuwa zan shiga daga ciki”
Ammy ta yi saurin tsayar da shi tana mai cewa “amma ya na ga kamar ranka a ɓace?”
“Babu komai Ammy kawai gajiya ce” ya bata amsa kafin ya wuce sama.Kayan jikinsa ya rage ya shiga toilet don yin wanka saboda magarib ta gabato.Bayan ya gama wankan gaban mirror ɗin da ke cikin toilet ya ja ya tsaya yana ƙarewa faffaɗan ƙirjinsa kallo,yayin da kuma rashin kunyar Khadeeja ke keta tunaninsa.Da ya ji ransa na shirin ƙara ɓaci sai kawai ya fita,ya shirya cikin jallabiya ya fesa turare tare kuma da ɗaukar dadduma ya fita don tuni an soma kiran sallah .Ba shi ya dawo ba sai bayan isha'i,yau kwata-kwata bai da ra'ayin cin abinci abu mai ɗan sanyi yake so hakan yasa iya zoɓo kawai ya sha ya wuce ɗakinsa,ita ma Ammy ba ta wani takura masa ba sai kallon tausayi da ta bi ɗan nata da shi.
Kan bed ya hau tare da kunna system ya soma yin bincike kan madu'in da zai yi wa'azi a wannan juma'ar.Duk yadda yake son ajiye hankali wuri guda abu ya cuttura kalaman Khadeeja ne kawai ke yi masa yawo,can kuma saƙon text ya shigo sai ya ga sunan Maryama.Sallama ce ta yi masa tare da gaishe shi,a duniya ya tsani mace marar aji shi yasa kaf ƴan matan da ke kawo masa tallar kansu yake jin ba zai iya soyayya da su ba.
Ya ja tsuki a fili kafin ya danna kiran Sheikh Laminu,ringung biyu ya ɗaga yana mai yi masa sallama.Bayan ya amsa ne yake cewa “aboki kenan sai da ka bai wa yarinyar can lambata?”
Sheikh Laminu ya tuntsire da dariya ya ce “Maryama ce yarinya? Fatan dai ba shirme ta yi maka ba? Ɗazu na shaida mata yadda muka yi da kai shi ne na tura mata hotonka da kuma lambarka ”
Sheikh Rayyadeen ya yi shiru kafin kuma ya ce “okay!” sai ya kashe kiran,bai yi mata reply ba sai aikinsa da ya ci gaba da yi har kusan ƙarfe biyun dare kafin ya rufe system ɗin ya je yayi alwala yayi nafiloli.A nan kan dadduma yayi bacci mai cike da mafarkin Khadeeja,abin da ta faɗa ɗin dai ne ya faru wato yana rungume da ita ya saka ta a ƙirjinsa suna kwance kan bed sai faman manne masa take yi tana ƙara dagula masa lissafi wanda hakan ta kai shi da raba su da suturar jikinsu har suka raya daren da soyayyar baki da kuma ta gangar jiki.
Da ya farka ji yayi kamar ya kama da wuta,ga lokacin sallah tuni yayi don wasu masallatai har sun fara ga kuma yadda wanka ya hau kansa.Duk da sosai ya ji daɗin mafarkin amma kuma bai hana takaici kama shi ba yana daɗa jin tsanar fitinaniyar yarinyar wacce ta addabi rayuwarsa.
Cikin woshin mashin ya saka kayansa da dadduma kafin ya tsabtataccen jikinsa,ko da ya tafi masjid iya raka'a ɗaya ya samu sai bayan an salamce ya miƙe ya kawo cikon sannan ya zauna yayi azkhar.Bai dawo gida ba sai da rana ta fito sosai,jikinsa duk a sanyaye don rabon da ya rasa sallar asubah tun yana ganiyar ƙurciyarsa.
Sai da ya shiga kitchen ya gaishe da Ammy sannan ya je ya dubo Rashida yau tana zaune kan dadduma da alamu kamar hankalinta ya ɗan dawo jikinta.
Sallamar da yayi ta amsa kafin ta ɗago ta dube shi cike da rauni,shi kuwa Sheikh sosai ya ji daɗin ganinta haka.
“Ya jikin naki?” ya tambaye ta.
Ta ce “da sauƙi Ya Sheikh ” kasancewar haka take kiransa saboda tun suna yara ta bar masa girman.
Ya ɗan murmusa ya ce “Allah ya ƙara miki lafiya ƙanwata”
Ita ma murmushin ta yi kafin ta ce “amin!” addu'o'in da ya saba yi mata ya yi kafin ya juya,har ya kai bakin ƙofa ya ji muryarta tana cewa “ina ɗalibarka wacce na gani ranar nan?”
Da wani irin sauri ya juyo ya dube ta,kafin ya ce “wace ɗaliba? Ai suna da yawa”
Ta girgiza kai ta ce “ka san wacce nake nufi Ya Sheikh ” ta ida furicin tana mai yin kwanciya,kafin ma ya kai ga yin magana tuni Rashida ta yi bacci.
Da wannan abin al'ajabin Sheikh ya nufi ɗakinsa,sai da ya sake yin wanka sannan ya shirya cikin fararen kaya yau kuma baƙar alkyaba ya saka da jan hirami ya feshe jikinsa da turare sannan ya sauko.
Ammy ta tarbe shi tana mai cewa “ga abincinka nan na kawo ma tsakiyar falo ”
“Azumi nake yi Ammy ” ya bata amsa.
“Yau fa Laraba ce” ta faɗa da ɗan mamaki.
Ya ce “eh na sani Ammy,na tafi sai na dawo”
“Amma Deeni...” yayi saurin katse ta da cewa “Ammy na makara ƙarfe takwas saura kuma sabbin ɗalibai ne da ni ”
“To a dawo lafiya”
“Amin”
Haka ya fice ya shiga motarsa,yana gudu yana ta nazarin maganar Rashida sai mamaki yake yi kan cewa da ta yi wai ya san wace ɗaliba ce yake nufi.Yana shigowa harabar makarantar ya ga yadda ruwa suka fara ɓullo shuke-shuken suna shigowa har inda babu su.Sai da ya fara yin parking ɗin motar kafin ya fito ya nufi can.
★
Ruwa na ɗaya daga cikin abin da ke bani sha'awa,yadda suke faltsar ba ƙaramin burge ni hakan ke yi ba.Wannan yasa da mai gadi ya kashe pampon sai na ji haushi,yana gusawa na je na sake kunnawa tare da tsayuwa ina kallo daga ƙarshe ma jakata na ajiye na je ina saka hannuwana a ruwan ina wasa.
Ba zan iya ƙa'ide lokacin da na ɗauka a wurin ba,na shagala sosai a wasar kafin na soma ganin wata narkekiyar tsutsa tana fitowa na miƙe da sauri ina mai yin wata irin razananiyar ƙara na yi tako ɗaya ƙafata ta zame na yi tuntuɓe tare da yin gaba,sai dai ban faɗi a ko ina ba sai kan ƙirjin Sheikh Rayyadeen wanda ban san me ya zo yi kuma a nan ba .Tsabar ruɗewar da na yi shi ya mantar da ni tsoronsa da nake yi,ƙanƙame shi na yi gam igiyar numfashina na soma cirewa,“maci..ma .cijiii!” na furta,ina jin lokacin da yake bubuga fuskata cikin ɗimuwa yana cewa “kar ki rufe idonki! Kar ki some mini” idon nawa na soma ƙoƙarin buɗewa ina ɗan juya su,sai dai firgicin da ya kame mini zuciya shi ya hana ni yin yadda yake so ɗin.Ba zan ce na suma ba,haka kuma ba zan ce ɗari bisa ɗari ina cikin hayyacina ba sai dai ina ɗan tsintar maganar mutanen da