MAFARKI Love and Horror Story By Mrs Sadauki.txt

Author :  Mrs Sadauki Category :  Hausa Read

Chapter   11 / 18

30K to 33K   out of 53.5K words

tuni hankalinsu ya kawo gare mu.
Ina jin lokacin da yake cewa “ku zo ku kama ta kuka wani tsaya kallona” sai kuma na ji an ciciɓe ni ana tafiya da ni yayin da kuma amon muryar Sheikh ke ratsa kunnena yana yin masifa.Daga nan ne na ji ɗif,ban san kuma wane lokaci aka sake ɗauka ba kafin na ja ajiyar zuciya na buɗe idona Sheikh Rayyadeen na gani riƙe da kaina yana yi mini karatu.

“Ta buɗe idonta” muryar Mujahida ce wannan karon,sai ya saki kan nawa tare da tashi ya wani juya mana baya.Na tashi a hankali ina kallon ƙawata wacce idonta suka yi ja da alamun ta sha kuka,hannuna ta kama ta miƙar da ni sannan muka nufi ƙofa na ɗan juya domin satar kallonsa daidai shi ma ya juyo idonmu suka sarƙe cikin na juna.Daidai nan free page ya ida duk mai son ci gaba zai iya biyan 300 kuɗin normal group,ko kuma 500 na VIP group via

2670215530
ZULFAU YAHAYA
ECOBANK
DM +22795045822

*NB:* Yanzu nake rubuta shi banda complete ɗinsa,in kina da niyyar shiga group ki tura kuɗinki kai tsaye ki bani receip Ni kuma zan saka ki group.Daga lokacin da book ya kammala zai koma 1k.

18 Disamba 2025.
[18/12 13:06] MRS SADAUKI: *INUWAR ALJAN*👻



```LoVe aNd HoRrOr story```👽


By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI💫✍️}



*SADAUKARWA:* Ga Rachida Mamar ƴan biyu, alherin Allah ya luluɓe ki . Ubangijin rahama ya kula da lamurranki👏🏻

*FCWA*☀️

________________________


01



Sakacin iyaye na ɗaya daga cikin abin da ke jefa rayuwar yara yin mu'amala da aljanu tun suna ƙananu ba tare da an ankara cewa wannan illa ne ba.
Sunana David,ɗan farko gun wasu shagalalun iyaye waɗanda suka mayar da sa'insa abin ado,cin amanar juna ruwan sha,wasa da tarbiyyar ƴaƴansu tabi'arsu.Shekaruna ashirin da biyar kacal a duniya amma in aka ganni za a iya bani shekaru talatin saboda yadda ƙwanjina ya buɗe silar aikin wahala.Tun ina ɗan yaro mahaifiyata ta rataya mini nauyin kula da ƙannaina,tun daga yi musu tsarki,wanka da kuma basu abinci a baki madadin ita ta yi.Komai tsawon dare in ƙanena yayi bahaya ni ne ke zuwa na wanke masa na kuma kai banɗaki na zubar,babu wata addu'ar neman kariya ko wani furici da zan furta domin gusar da wani abin cutar wa a irin haka ne na haɗu da wata baƙar siffa wacce duk da ƙanƙantar shekaruna bai hana na fahimci wannan ba bil'adama ba ce.


A tsaye nake tsakiyar banɗaki hannuna riƙe da fo ,yayin da kuma siffar ke tsugunne kan inda mutum ke hawa don yin buƙatarsa.A lokacin wani irin tsoro ya ziyarce ni,sai dai tamkar itaciya haka na kasa motsi sai ma ido da na ƙanƙance ina ƙarewa siffar kallo.Mace ce a zubin halitta don ga dogon gashinta nan ya zubo har yana jan ƙasa,fuskarta baƙa ƙirin ce mai ɗauke da wasu ƴan ƙananun ƙahonni daidai gefe da gefen hanci,bakinta a buɗe yake wanda hakan zai iya baka damar ganin dogayen haƙoranta biyu da suka zarce sauran.Duk a cikin duhun daren idanuwana suka bani ikon ganin wannan ikon Allahn,a hankali na ga ta taso ta zo gare ni ba tare da ta ce komai ba ta karɓi fo ɗin hannuna sai ta ɗora babban yatsanta a tsakiyar goshina wani irin abu na ji mai mugun zafi ya ratsa ni wanda yasa na fita hayyacina.Ko da na farka Ummah na gani gefena tana jiƙa wani zane a ruwa tana ɗora mini yayin da kuma idonta suka yi ja alamun ta yi kuka.Muna haɗa ido da ita ta ce “Davido?” a cikin muryarta na tsinto tsantsar tausayina,a bakinta kuma na ji cewa an same ni a yashe ga ƙasa daidai ƙofar banɗaki .

Mahaifina ya matso yana cewa “har yanzu jikin nasa da zafi?”

“Eh kamar gawarshi har wani tiriri ke tashi,dubi hatta ruwan da nake tsoma zanen sun ɗauki gumi” Ummah ta faɗa tana matsar ƙwalla.

Abba ya ce “ki goya Joy mu tafi mu kai shi gidan mai magani” ba ta ce komai ba haka ta ɗauki ƙanena Joy wanda bai rufe murfin shekara biyu ba,ni kuma Abba ne ya saɓe ni zuwa gidan mai magani.

Tun da muka shigo farfajiyar gidan idona suka soma yi mini gane-gane.Abin da ido bai kamata ya gani ba ni ras nake ganinsa,duk mutanen da suka zo babu lafiya kallo ɗaya na yi wa kowanne daga ciki na hango matsalarsa.A bisa bangunan gidan mai magani kuwa kamar yadda ƙadangaru ke yawo haka ko ta ina aljanu ne ƙanana da manyansu.Lokacin da muka shiga cikin ƴar bukarsa kuwa muna haɗa ido da shi na ga ya ɗan tsorata,amma sai ya ɓoye tsoron tare da bada umarnin a kwantar da ni kan tabarmar da ake shimfiɗe majinyata.A ido tabarma ce,amma a baɗini bijinmi wani dodo ne,bai tambayi iyayena abin da ya faru ba amma sai ni ya tambaya shi ɗin ma ba ta baki ba a'a ta ido.

“Wane ne kai? Me kake so a gare ni har ka bari aka kawo ka wurina alhalin ka fi ƙarfina?” su ne tambayoyin da idonsa suka watso mini amma ni sam ban basa amsa ba,kuma ban san dalilina na yin haka ba.Ƙila shi kuma ya fahimci har zuwa lokacin ƙarfin ikon da ke jikina ban fara yin aiki da shi ba ne ko kuwa tasirinsa bai bi jikina ba ne oho,sai ya ɗauko wata ƙatuwar laya ya ɗaura ta a damtsena tare da cewa “zuwa saukowar zazzaɓin rana duk wannan zafin jikin nasa zai sauka zai kuma samu lafiya” Abba ya basa kuɗi amma ya ƙi karɓa a haka muka dawo gida.Kamar yadda ya faɗa ɗin kuwa haka ta faru,ina warware wa kawai sai na fara walwala tare da mantawa da wannan siffar da na gani .Yayin da kuma Abba da Ummah suka dasa rashin mutumcinsu daga inda suka tsaya,dama iya na ɗaya rana ne ba su yi masifar da suka saba ba da yi wa juna gori wasu kalaman sam ba su dace ba.



A lokacin da na shiga zangon shekara goma sha biyar a duniya na soma yin aikin ƙarfi don ciyar da ƙannaina biyu Joy da kuma Joyel wacce ta kasance autarmu.Tamkar mahaifi haka suka ɗauke ni,da zarar na shigo haka suke zuwa da gudu su tarbe ni da murna iya wannan annushuwar da nake gani a tattare da su shi ke wanzar da nawa farin cikin har izuwa yanzu da nake ganiyar shekara ashirin da biyar.



“Ba ka da aikin yi kullum sai shan giya da bin mata a hakan wai kai miji ne”

“In ba miji ba ne ni ai ba zan baki yara har uku ba”

“Uwar me kake yi wa yaran ? ”

“In ban yi musu komai ke da ke uwarsu ai ina yi miki wata tsiyar da har ta sa kika kasa barina kika manne mini”

“Zancen banza yo kar ka sake yi,ka zata kai kaɗai ne namiji a duniya?”

“Kenan dama abin da nake zargi gaskiya ne kina cin amanata?”

Wannan ita ce sa'insar da iyayenmu suka tashi da ita a safiyar yau duk sun cika mana gida da surutunsu da babu daɗin ji.Cike da ɓacin rai na tashi daga kwancen da nake ,tun ina haƙurin saurarensu har na kasa jura na tunkari ɗakinsu.Ban ɗaga labule ba,a bakin ƙofa na ce “don Allah ko za ku iya yi mana shiru ko mun samu mu yi bacci cikin salama?”

Daga can cikin ɗaki Ummah ta ce “kan ubanka! Haifarmu ka yi da za ka bamu umarni?”

Shi kuwa Abba wata irin dariya ya yi kafin ya ce “ai shi ne daidai ke tun da ke ma ɗin ba mutumci ne da ke ba ga shi nan kin haifi ɗan daba ”

“Ko ma dai mene ne babu ruwanka da ɗana ”

“Ni ma ai nawa ne ina ce ni ne ubansa ko?”

“Wa ya sani abu cikin duhu!” Ummah na faɗar haka na gusa daga gurin.Ƙofar gida na fita na zauna kan dakali ina jin zuciyata duk babu daɗi.


Wani irin yammm! Yammm! Na soma jin ƙafata na yi mini ko da na duba sai na ga tururuwa ce duk ta yaɓe mini ƙafa kamar ta samu wani suga.Girgiza ƙafar na yi amma ko ɗaya ba ta faɗi ba kamar ma an sa super glue ne a manne su.Da sauri na kai hannu don kakaɓe su sai dai wani abun mamaki bayan na shafa ƙafata sai na ga wayam babu komai kuma ba su zuba a ƙasa ba.Wani irin matsanancin ciwon kai ne ya ziyarce ni,dole na miƙe na koma cikin gida na cika bokiti da ruwa na kai banɗaki .Ina tsaka da yin wanka na soma jin wani irin yanayi wanda tun da nake zan iya cewa sau ɗaya tak na taɓa samun kaina a cikinsa shi ɗin ma a mafarki a lokacin da na shiga zangon balaga.


Idona a rufe suke na goga sabulu ban wanke ba,yayin da kuma nake jin tamkar ana shafar duk illahirin jikina ana yi mini abin da ban taɓa jin makamancinsa ba.A wannan lokaci ba zan iya tantance ina cikin hayyacina ne ba ko kuwa ya gushe,abu ɗaya zan tuna shi ne na samu kaina a matsayin namiji har na samu nutsuwa,sai dai da wa? Ban sani ba.Ina dawowa cikin tunanina na ida yin wanka,na fito na je ɗakina na shirya .Ciwon kan da ya sauko mini tuni na neme shi na rasa,na fito kenan zan fita neman kuɗi sai ga su Joy sun fito su ma cikin shirin zuwa makaranta.

Da turanci suka gaishe ni na amsa musu ni ma da turancin,Joy ya ci gaba da yin magana don yana ɗaya daga cikin abin da yake yi mini wani sa'in yayi mini magana da turanci kasancewar tawa makarantar ba ta yi nisa ba na fita.Amma wani abin mamaki sai na samu kaina da iya turancin, Joy ya ce “amma Yaya ya aka yi ka iya turanci haka?” shiru na yi ina kallonsa,ni ma ban sani ba amma sai na share na miƙa musu kuɗin da za su ci abinci na fice.


Direct inda muke haɗuwa ni da abokaina na tafi,duk sun hallara kuwa da alamu ni suke jira.Hannu na basu duk muka gaisa kafin na samu wuri na zauna a daidai tsakiyarsu wanda kuma kusan kullum muddin za mu haɗu ni a tsakiya nake zama ,in suna son tsokanata suna cewa ni ne shugabansu.


“Yau dai in mun tafi aiki sai dare na dawo saboda ina son kuɗi sosai zan fara tara kuɗin aurena ” Isa ya faɗa yana wani jan gemu.

Abdul ya karɓe da “ai kuwa kamar ka shiga zuciyata ni ma haka na yi tunani ya kamata a ce mun fara tara kuɗin aure tun yanzu kafin ƙarshen shekara ta zo tun da layi ya kawo kanmu”

Isa ya ce “a'a yanzu fa layinsu David ne masu shekara ashirin da biyar”

“To ai ba wani girme mana ya yi ba kawai ƴan watanni ne”

Da na ga za su ɓata mini lokaci na miƙe na tsaye na ce “ko za mu iya tafiya?” duk suka miƙe suna dariya kafin mu tafi can wurin aikinmu na dako.A nan ɗin ma wani abin mamaki ya faru da ni,a yayin da abokaina ke ta aiki tuƙuru don samun kuɗi masu yawa ni kuma kamar wani shashasha haka na samu wani lungu na ɓingire ina bacci wanda ban san dalili ba.Sai yamma lis na farka,duk wata kasala ce nake ji ta rufe ni amma a haka na samu ruwa na wanke fuskata.

“Ina ka tafi tun ɗazu?” Isa ne ya yi mini tambayar ,yayin da kuma Abdul ke tsaye yana kallona.Dakyar na buɗe baki na ce “ina can kwance ina bacci tun safe”

“Amma kuma babu inda ba mu duba ba kuma har can ɗin mun je ba mu ganka ba” cewar Abdul yana mai ci gaba da tsure ni da ido .Shiru na yi don ban san taƙamaimai abin da zan ce ba,Isa ya ja ajiyar zuciya ya ce “tashi mu ƙarasa aikin to” haka na miƙe muka yi aikin a tare da aka zo raba kuɗi nasu sun ninka nawa biyar amma da yake abokan ƙwarai gare ni sai suka ƙara mini cikin nasu kafin mu koma.

Ina shiga gida da Ummah na fara cin karo,lissafin bashin da ta ciyo mini ta soma yi mini daga ƙarshe ta tara hannunta alamun na bata kuɗin.Hannu na saka aljihu na ciro dukkan kuɗin na miƙa mata,har zan tafi amma wani abu ya ja hankalina.Zanen kunamar da ke hannun Ummah na ga yana motsi har da wani buɗe baki kunamar take yi,cak na tsaya ina mai ci gaba da kallon zanen yayin da ita kuma Ummah ke ƙirga kuɗin.

“Lafiya me aka yi kake kallona?” ta tambaya,ba tare da na bata amsa ba na wuce ɗakina.Tsaye na yi bakin ƙofa na riƙe ƙugu tare da yi wa kaina tambaya “wai shin meke faruwa da ni ne? Ko na haukace ne? ” tamkar bugawar guduma haka na ji kunnuwana sun bada wani sauti duummm! Sai kuma na ji tamkar ana kiran sunana a wani wurin da ni kaina ban san ina ne ba.Kamar zararre haka na fito,a lokacin tuni gari ya ƙara yin duhu .Tafiya kawai nake yi ba tare da na san inda zan je ba,har yanzu kuma ina jin sautin nan na kamar ana kiran sunana.A haka na yi nisa sosai a tafiya har na iso cikin wani wuri mai ciyayi da kuma dogayen bishiyoyi,haka nake ratsa wa ta cikinsu ba tare da wani tunani ba a haka har na iso gaban wani kabari.Haske na ga yana ɓulɓulowa ta cikinsa,ina zube gwiwaina ƙasa muka samu contact da ƙasar wurin sai yanayin tafiyar kaɗawar iska ya canza,ƙamshi wurin ya ɗauki yanayin damshi kamar irin an yi ruwa an ɗauke.A kan kabarin wasu irin ƙananun baƙaƙen duwatsu ne a zube kamar shara,sai kuma wani farin kyandir daga tsakiya wanda ya fara ci da wuta da kansa,wani irin abu nake ji kamar ana fizgo ruhina tamkar dai akwai wani ɓoyayyen ruhi da ke jawo ni izuwa gare shi.Ba tare da tunanin komai ba na soma ture ƙasar kabarin ina buɗe shi,sama da minti talatin na ɗauka kafin yi nasarar buɗe shi duka.Wani ƙyalle ne na ci karo da shi a shimfiɗe a samansa wani ƙaton littafi ne akai,an yi masa cover da wata fatar dabba tamkar mai motsin rai,a ƙasa an yi wani rubutu wanda ba da Yaren da na taɓa ji ko gani ba ne,amma sai na ji rubutun da kansa yana yi mini magana.

Ina sa hannu na ɗauki littafin sai wani irin shock ya ziyarci yatsun hannuna suka fitar da wani hasken wuta irin kamar waya ta ƙone.Bishiyoyin da ke zagaye da ni ne suka soma yin wata irin rawa har kana jin suna kai wa juna karo,yayin da kuma wani huci wanda kana ji ba na bil'adama ba ne ya soma karo da juna yana fitar da wani iska da ya saka furanni faɗowa suna mutuwa murus.Page ɗin farko na buɗe,nan take na soma jin ana yi mini wankin ido na soma gane-gane ina ganin abubuwan da suka faru lokacin baya a cikin littafin tamkar an kunna tv.Abubuwa ne waɗanda hankali ba zai ɗauka ba,mata da maza suna bayar da jininsu domin ƙaddamar da yarjejeniyar a tsakaninsu da Aljanai ,lamarin da muke ta tunanin tatsuniya ce ashe gaske ne an yi su a ƙarnin baya .Littafin na riƙe a hannuna yayin da kuma kukan ƙananun yaran da aka sayar da ruhikansu ko kuma aka bayar da jininsu matsayin hadaya na ta kawowa dodon kunnena farmaki,gefe guda kuma dubban ahali ne tsundum cikin rayuwar ƙunci saboda tun kakanni da iyaye sun yi harƙalla da Aljanu a yanzu kuma suna biyan bashin ƙarfin ikon da aka basu.

Duk page ɗin da zan buɗa tana ɗauke da wani baƙin sirri da ya gabata.Na ga ahali da dama waɗanda suka yi ƙaurin suna a zube gaban baƙaƙen ruhikan da ido bai isa ya gani ba amma sun yi harƙalla da su don samun dauɗar duniya ko iko.Wata page ɗin kuma magana take yi kan ƙungiyoyin asiri waɗanda aka ƙulla ta hanyar jini da kuma sassan jikin ɗan Adam ,yayin da kuma wata ke magana kan mutanen da aka jefa wa ƙunci a zukata ta hanyar tsafi wasu kuma an haukata su ,yayin da wasu aka ɓatar da su daga duniyar bil'adama zuwa ta ruhaniya saboda sun gwada tonawa azzalumai asiri.


Numfashina ne na ji yana son ɗaukewa,littafin kamar yana son koyar da ni,ya canza tunanina,ko kuma ya gwada imanina.Ji na yi ruhina yana kimsa mini wasu kalamai,yana cika mini ƙwaƙwalwata da ilimin da aka yi hani,a kuma wannan lokacin ne na ji wani irin tsoro mai tsanani ya ya daskarar da ni,sai kuma idona suka ci karo da wani rubutun da aka yi da manyan harufa.

“DUK WANDA YA TAƁA WANNAN LITTAFI SHI NE SHAIDAR INUWARMU.WANDA YA KARANTA SHI KUMA YA ZAMA *INUWAR ALJAN*” kalmar ƙarshe ta inuwar aljan wacce rubutunta yake da jan jini na ƙara maimaita a zuci,sai kuma na fahimci cewa wannan littafi ba wai iya kundi ne mai ɗauke da sirri ba,a'a shi kansa yana rayuwa ne yana tattare da motsin rai.Yana ankare da ni tun tuni,ko kuma dai yana amayar da wani sirrina da nake ɗauke da shi tun tuni.Ji nake ana kallona,ana ankare da ni ana kuma gwada ni da kuma tsare ni da ido waɗanda ba a iya gani.A nan take kuma na fahimci wani abu ,na canza har abada kuma ba zan dawo yadda nake ba tun farko .......
[18/12 13:06] MRS SADAUKI: *INUWAR ALJAN*👻



```LoVe aNd HoRrOr story```👽


By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI💫✍️}



*SADAUKARWA:* Ga Rachida Mamar ƴan biyu, alherin Allah ya luluɓe ki . Ubangijin rahama ya kula da lamurranki👏🏻

*FCWA*☀️

________________________


02


Banda wani zaɓi wanda ya wuce na taho gida da wannan littafin sirrin wanda nake jinsa tamkar wani jigo na rayuwata.Wuri mai kyau na yi masa a cikin akwatin kayana na ajiye shi,abincin dare sam ban ma yi tunanin ci ba don dama duk wunin yau ba zan ce ga abin da na ci ba.
A wannan daren sam ban yi baccin kirki ba,da zarar na samu na ɗan tsunduma cikin bacci sai na soma ganin baƙaƙen inuwoyi masu jajayen idanuwa suna ambaton sunana suna kuma nuna mini

11 / 18