Author : Mrs Sadauki Category : Hausa Read
gaba ina cewa “ƙawali ya za ki tashe ni ina hutawa?”
“Tashi maza ki ci abinci babu ruwa da sakarci,kin ga jiya haka kika jigata da kika zauna da yunwa”
Tashi na yi na yi brush na wanke fuskata ko da na fito sai na samu hoton Sheikh Rayyadeen a hannun Ummah tana kallo.A kunyace na karɓe hoton,yayin da ita kuma ta tsuro mini na mujiya kafin ta ce “wane ne?”
“Saurayina mana” na bata amsa ina mai fesa turare.
“A ina kika samu hoton?” ta jefo mini tambayar.
Na ce “ni da saurayina shi ne za ki tambaya ina na same shi? To shi ne ya bani da kansa”
“Ke da shi halan duk makafi ne shi yasa ba ku ga matsalolin da ke tattare da hoton ba?” Ummah ta faɗa cikin ɗaga murya,da sauri na juyo ina kallonta zuciyata na ɗan bugawa.Na san Ummah na bayar da magani,wani sa'in ma ba sai ka tambaye ta ba a'a haka kawai a hanya ma in ta haɗu da kai sai ta baka magani amma ban taɓa sanin cewa iliminta har ya kai iya ta hoto ma tana iya hango matsala.
Na zo dab da ita ina mai cewa “halan meke da hoton ?”
“Zo mu sauka ƙasa ki ci abinci ” ta sauya zancen,haka na ajiye hoton ƙasan pilow na take mata baya.Ammy na zaune a falo,gaishe ta na yi sannan na zuba abinci na soma ci ta miƙo mini wayata sai na ga miss call ɗin Mujahida.Sanin yanzu tana cikin aji yasa ban maida mata ba sai text na yi mata,ai kuwa ta maido mini har take shaida mini cewa Sheikh Rayyadeen ya bulalaye ta saboda ta yi ƙaryar banda lafiya,dariya na shiga yi kafin kuma na yi tsit sakamakon zuciyata da ta raya mini ‘ jiya ai na yi wannan mafarkin ’ babu shiri na ajiye plate ɗin na haura sama,ina jin Ummah na tambayar lafiya amma ban juya ba.Zaune na yi na soma rubutawa Mujahida kaf irin mafarkin da na yi a daren jiya,ita kuma ta tabbatar mini da za ta zo gidanmu in an tashi daga makaranta.
Haka kuwa aka yi,ta cika alƙawari bayan ta zo ɗakina muka shige na ciro hoton Sheikh Rayyadeen na miƙa mata ina mai cewa “kin gansa”
Shiru ta yi tare da karɓa tana dubawa kafin ta ce “kuma kin tabbata ba wani ne ya baki hoton nan ba?”
Na ce “wani wa? Mujahida ni fa na fara jin tsoro kar dai a ce ni ma Rashida ta saka ni cikin group ɗinsu na Mayu ”
Sai da ta sheƙe da wata dariya kafin ta ce “ke fa matsala ta da ke hauka,yanzu dai abin da za a yi kawai mu shirya mu je gidansu Sheikh ɗin sai mu kaiwa mahaifiyarsa hoton” ba tare da wani tunani ba kuwa na amince,muka fito lokacin har duhun magarib ya fara shigowa wannan yasa Ammy da Ummah duk ba su falo.
Muna fita na karɓi key ɗin mota ga direba,haka na tuƙa mu har zuwa gidansu Sheikh Rayyadeen.A bakin ƙofa na yi parking,na cewa Mujahida “yanzu in muka shiga me za mu ce?”
“Wurin Ammy muka zo ” ta bani amsa sai muka fito,ni ke gaba ita kuma tana baya bakin get ɗin babu kowa hakan yasa muka shiga kai tsaye.Ina shirin shiga falon na ci karo da shi har kaina na dukan ƙirjinsa,ruwan gemunsa suka ɗiga kan fuskata da wani matsanancin bugawar zuciya na yi baya saura ƙiris na faɗi Mujahida ta taro ni sai muka yi cirko-cirko muna ƴar kallon mu da Sheikh Rayyadeen.....
Group biyu ne normal 300 , VIP kuma 500 via 2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank DM +22795045822 .Kamar tun a talla na faɗa muku wannan sabon salo ne sabuwar sheƙa to haka take,nan duk shimfiɗa ce ba mu ma fara labarin ba.
[14/12 15:15] MRS SADAUKI: *MAFARKI*👁️🦋🦋🦋
🦋🦋🦋
🦋🦋
Mallakar : 🦋
Chamsiya Laouali Rabo
```MRS SADAUKI 💫✍️```
06
Ban san me yasa yake yi mini ƙwarjini ba a duk lokacin da babu gilashi a idonsa,sai na dinga ganinsu tsirararsu girma da kyawunsu ya ƙara fitowa uwa uba wani abu da nake gani kwance a cikinsu mai ɗaga mini hankali da kaɗa hantar cikina.
Mujahida ce ta yi ƙarfin halin gaishe shi “barka da warhaka Sheikh ”
Bai amsa ba sai ni da yake kallo,ƙila gaisuwar tawa yake jira.Kai na sunne ina mai ƙara jimƙe hotonsa da ke hannuna.Bai ce mana kanzil ba saboda kiran sallar da aka ƙwala a masjid ɗin gidansu,yayi gaba yana jifata da mugun kallo yayin da ni kuma na ja wata ajiyar zuciya ta murna ina mai shigewa cikin falon .
Ko ina tsaf yake sai ƙamshi ke tashi,kamar wacce ta san gidan haka na bi na tafi wancan sashen na jiya sai a lokacin ma na farga da Mujahida ba ta biyo ni ba.Zan juya kenan Ammy ta fito tana cewa “wa ke nan?” da sauri na juyo ina kallonta,a kunyace na gaishe ta ita kuma ta amsa mini da murmushinta tana ambaton sunana daga ƙarshe,babu wata magana don duk a daburce nake na ciro hoton Sheikh ɗin na miƙa mata.Sai ta karɓa ta duba tare da kallona da mamaki,“ina kika samu wannan hoton?” ta jefo mini tambayar.
Shiru na yi,sai ma a wannan lokacin na ga wautata.Kame-kame na fara kafin daga ƙarshe na shaida mata mafarkin da na yi,duk illahirin jikinta ne na ga yana kyarma kafin ta ce “ MAFARKI?”
Na jinjina mata kai,sai ta ja hannuna ta kai ni ɗakinta ta zaunar da ni tana mai cewa “zauna na yi sallah” banda wani zaɓin haka na zauna,yadda ta jima a sujidar ƙarshe yasa na ji ina ƙaunarta don na tabbata addu'a ce take yi.
“Ammy?” na ji muryar Sheikh daga can falo,bai tsaya da kiran sunan nata ba yadda na ji amon muryarsa na tunkaro nan shi yasa na tashi da mugun sauri na buɗe wata ƙofa na shige ina dafe zuciya da tunanin na tsira sai dai nan ɗin ma wani tashin hankali na ci karo da shi .Fuskar tsohuwar nan Grand-Maa ce zaune raɗam a mirror ɗin toilet,babban tashin hankalin shi ne iya kanta ne kawai ya bayyana kuma a gundile babu gangar jiki.
“Yiiiii!” ta girgiza gashin kanta tana bani tsoro na fasa ihu tare da banko ƙofar na fito,sam idona sun rufe da tsoro ban gansa ba haka na je na faɗa jikinsa tare da ƙanƙame shi gam ina kuka tare da rumtse idona ina cewa “aljana! Aljana!“
Kiciniyar hakice ni yake yi,sai dai sam na ƙi basa wannan damar don ba mugun riƙo na yi masa.Sai da Ammy ta yi magana ne sannan nutsuwata ta fara dawowa,“Khadeejatu?” ta furta tana mai jawo ni ta baya,na ɗan jan numfashi kafin a hankali na buɗe idona akan gemun Sheikh suka sauka,zuciyata na ɗan bugawa na soma sassauta riƙon da na yi masa ina mai ɗaga kai na dube shi.Idonsa ne na ga sun kaɗa sun yi ja,sai na ƙara ruɗe na ƙi sakin gefen cikinsa da na cikuikuye,kamar wani wanda bai da hankali haka yasa tafukan hannuwansa kan ƙirjina ya wani tura ni baya,saura ƙiris na faɗi amma Ammy ta tare ni.A zuciye ya fita ko sakan biyu bai ƙara ba,wani kuka ne ya zo mini wanda ban san na mene ne ba.
Ammy ta fara rarrashina sai bayan na yi shiru sannan ta kamo hannuna ta ce “zo mu je ki nuna mini daidai ina ne kika tukunyar ” haka na bi bayanta muka je can bayan ɗakunansu na nuna mata wurin.Ta ja numfashi tana mai cewa “ Khadeejatu kin san wani mafarkin gaskiya ne,ta hanyarsa ce Allah subhanahu wata'ala yake nunawa muminai abin da ke faruwa a rayuwarsu.Ban san me lokaci ya tanadar muku ke da Deeni ba da har ƙaddararsa ta faɗo a tafin hannunki,ga shi ke ce za ki zamo silar warware wani baƙin ƙulli na rayuwarsa”
Saurarenta kawai na yi amma ban ce komai ba,sai ta ci gaba da cewa “ki tsaya nan bari na je na dawo” kai na jinjina mata ta tafi ta bar ni nan.
Tuna wa na yi yadda hannuwan Sheikh suka sauka a ƙirjina,duk da na san a bisa kuskure ne amma haka nake jin haushi .Ina nan tsaye Ammy ta dawo da abin haka rame,da sauri na karɓa na buga daidai wurin da aka nuna mini a mafarki.Bugu guda ne na yi amma sai ƙasar ta soma buɗewa da kanta, Ammy ta duƙa ta sa hannu ta soma janye sauran ƙasar da ke bakin rame cm.Hannunta na rawa ta ciro tukunyar tana mai ambaton sunan Ubangiji ,a gabana ta buɗe ta a ciki mun samu wandon Sheikh tun yana ɗan yaro sai kuma wani ƙwai mai kamar na jimina sai wasu tarkacen.
Ƴar kallon-kallon muka soma yi ni da Ammy kafin na ji wata idea haka kawai ban san daga ina ta fito ba,“ki ƙona komai ni kuma ki bani tukunyar da kuma ƙwan na tafi da su” wani abin mamaki shi ne ko kaɗan Ammy ba ta yi gardama ba hakan kuwa ta yi ta miƙo mini tukunyar wacce ƙwai ke ciki na ɓoye ta a hijabi ,a haka muka rabu na fita waje sai dai babu key ɗin mota a hannuna kuma ban san inda yake ba.
Don dole na koma can cikin gida,falon Ammy na shiga na kuwa same ta tuni ta zuba tarkacen a cikin kasko ta ƙyarta musu ashana.
“Ammy makullin motata” na furta,haka aka ta bincikensa amma ba a gani ba.
Ta ce “bari na kira Sheikh ya sauke ki” ba ta ma bari na furta wata kalma ba ta fita.
Ammy na shiga ɗakinsa ta same shi a kwance gorar ruwan sanyi a hannunsa,yana jan numfashi duk da ta san abin da ke saka shi a wannan halin amma wannan karon sai ta ƙi nuna damuwarta ta ce “ka taso ka sauke Khadeejatu gida”
Ya ɗago da sauri yana kallon Ammyn wacce ta haɗe rai ,kamar wani maraya cike da tausayin kansa ya ce “to”
Sai ta fita ta barsa yana jin kamar ya kama da wuta ko kuma ya fasa ihu ƙila zai ji sassauci.Ya miƙe yana masifa yana cewa “ke ɗin ba masifa ba ce a gare ni a'a ke kanki matsala ce,a kullum banda fitina babu abin da kike kawowa a rayuwata duk in mun haɗu daga kina gudu sai kin faɗo jikina mtswww!” ya ja dogon tsaki kafin ya ci gaba da cewa “na tsane ki!” haka ya fita can farfajiya ya buɗe motarsa ya shiga yana jiran fitowarta.
Ina nan tsaye Ammy ta shigo ta kama hannuna muka fito,sai ta sa key ta rufe ɗakinta kafin mu fito babban falo.Karo muka ci da Grand-Maa,cike da girmamawa Ammy ta gaishe ta amma tsabar munafurci irin nata sai cewa ta yi “Khadi wannan fa wace ce?”
“Ƴata ce Maa ta kawo mini ziyara ne za ta koma gida” Ammy ta bata amsa.
“Amma kamar na ganta a jiya”
Ammy ta dube ni kafin ta ce “eh ta zo”
“Tun da ta zo jiya ,yanzu kuma me ya maido ta? Munafurci ko me?” Ammy na jin haka ba ta ƙara tankata ba ta ja ni zuwa waje,idon Grand-Maa ƙur kaina tana kallon hijabina da dukkan alamu so take yi ta san mene ne ciki.
Muna zuwa kusan motarsa Ammy ta buɗe mini gidan gaba,kasa shiga na yi na girgiza mata kai tare da buɗe baya na zauna.Ta yi murmushi ta ce “sai da safe Deejar Ammy ki gaishe mini da mamarki”
A hankali na ce “to Ammyna” wata irin waigowa Sheikh yayi da sauri yana yi mini kallon mamaki mai cike da tsana kafin ya soma jan motar.
Sai da muka hau kan titi ya ce “wace unguwa?” maimakon na basa amsa sai na soma leƙen fuskarsa,rai a ɗan ɓace ya sake tambayata sai a lokacin na shaida masa.Da muka shigo layin kuma na soma nuna masa har muka iso ƙofar gida,gabana ne ya faɗi rasss ganin duk ahalin gidan a waje har da masu gadi.
Murya na rawa na cewa Sheikh “don girman Allah ka fita ka yi wa Daddyna bayani ko ƙarya ce ka yi masa ka ce daga makaranta nake motata ce ta lalace shi yasa ka ɗauko mu ni da Mujahida ”
Wani irin rumtse ido Sheikh yayi yana jin zuciyarsa na azalzala,shi da yake hukunta ɗalibai akan in sun yi ƙarya amma yau shi ne ɗalibarsa ke son ya yi ƙarya.Fita ya yi ya je ya gaishe da su Daddy,ban san me ya faɗa musu ba sai na ga duk sun shiga cikin gida.Sai a lokacin ya buɗe mini na fito,na yi tsaye ina kallonsa yadda haiba da ƙwarjininsa suka fito.Motarsa ya rufe sannan ya yi gaba na dinga take masa baya,cike da mamaki nake kallon yadda yake sa kai ciki.Muna shiga falo sai na ga Momy har wani rawar jiki take yi wurin kawo ruwan sha,yayin da shi kuma Daddy ya nunawa Sheikh wurin zama .Ban wani jinkirta ba na haura can sama inda ɗakina yake,ƙarƙashin bed na ajiye tukunyar kafin na cire hijabina.Toilet na shiga na haɗa ruwan ɗumi na yi wanka na canza pad,yunwa nake ji amma kasa fita na yi ƙasa don na san bai tafi ba,har yanzu kuma ban bar mamakin dalilin da yasa Daddy bai ce mini komai ba alhalin yana da zafi sosai.
A can falo kuwa cike da mutunta wa suke kula da Sheikh Rayyadeen,wanda shi ɗin ba ɓoyayye ba ne a wurinsu musamman ma Daddy wanda suke cikin association Islamic ta ƙasar Nijar shi da Sheikh ɗin.Ammy ita kuwa ta san shi a tv da kuma bakin mijinta in yana yi mata hirar addini,ko kaɗan Daddy hankalinsa bai tashi ba da Sheikh Rayyadeen ya fito ya shaida musu cewa ya kawo Khadeejatu ne gida a bisa umarnin mahaifiyarsa,sai dai yana mamakin meke haɗin Deejar da Ammy ɗin.
Ummah dai na zaune tana kallon Sheikh Rayyadeen don ita ba ta san shi ba,amma sosai take mamakin ta ya babban malami kamar shi yake ɗauke da ƙulli-ƙulli na asiri a jikinsa.Hirar addini kawai suke yi kafin ya miƙe ya ce “ni zan koma” Daddy ne ya yi masa rakiya har zuwa ƙofar gida sannan ya dawo ciki, ya dubi Momy ya ce “je ki kirawo mini Ummita”
Ina kwance ina wasiƙar jaki Momy ta shigo,da sauri na sunne kai ina jin gabana na faɗuwa.“Ki taso Daddynki na kira” shi ne kawai abin da ta faɗa ta fice,jiki babu ƙwari na zumbula hijabi na sauka.Kusa da Ummah na zauna ina mai kwantawa a jikinta,“daga ina kike? ” Daddy ya watso mini tambayar da ta tabbatar mini cewa Sheikh bai sanar da su komai ba.Wannan yasa na gyara zama na shararo ƙarya,“daga makaranta muke Daddy,motar da na ɗauka ce ta lalace ka san an kai mu ajin ƙarshe shi ne Mujahida ta zo muka tafi can don mu yi exercises ”
“Amma shi Sheikh ce mini yayi Ammynsa tasa ya kawo ki gida”
“Eh suna tare ne lokacin da suka haɗu da mu a hanya,ka san wani abu Daddy Ammynsa nada kirki sosai ” na faɗa ina murmushin ƙarfin hali don zuciyata cike take da fargaba.
“Ina motar take yanzu?”
“An kira mai gyara ya tafi da ita ,Ammy ta ce in an gyara za a kawo mini har gida” na basa amsa.A yadda na ga Daddy ya gamsu da hujjojina shi ya kwantar mini da hankali har na nemi abinci na ci.
Ummah ta miƙe ta nufi ɗakinta tana mai cewa “ƙawali ki zo ki yi mini tausar ƙafa”
Sarai na san halin Ummah babu wata tausa da zan yi mata ,tambayoyi ne za ta yi mini amma saboda ban jin tsoro ko shakkar sanar da ita sirrina kawai na miƙe na bi bayanta.
Ina shiga kuwa ta jawo ni ta zaunar tare da tsura mini ido,na ja ɗan numfashi kafin na ce “gidansu ne na tafi Ummah ,kin san kusan shekara uku kenan nake ciwon son Sheikh Rayyadeen amma ban taɓa furta masa ba.Jiya kuma na yi wani mafarki da ya tsorata ni shi ne na je na shaidawa Ammynsa ”
Ta ja numfashi kafin ta ce “ƙawali ba ki ganin mutumin nan yayi miki girma? Dube shi fa gudan dattijo da me Daddynki ya girme masa?”
Na turo baki na ce “to ni ina ruwana da girmansa tun da ba goya shi zan yi ba na yi yawo?”
Ta yi ƴar dariya kafin ta ce “lokaci yayi za ki fahimci abin da nake nufi.Matansa nawa?”
“Bai taɓa aure ba” na bata amsa,ta ce “amma hotonsa ne na gani a hannunki ko?” na jinjina mata kai,ba ta ce komai ba sai jakarta da ta jawo.Magani ta kaɗa mini ta bani na sha,kafin na fita na koma ɗakina.Wayata na ɗauka na kira Mujahida,tana ɗauka na soma yi mata masifa.Ta sheƙe da dariya ta ce “ke ba fa zan tsaya ba Sheikh yayi dambuna ah to,kin ga yadda yake hararenmu kuwa?”
Na ja tsuki ina mai cewa “to ai shi ya kawo ni gida” cike da mamaki ta ce “da gaske?” nan fa na bata labarin duk abin da ya faru.
Ta ja numfashi ta ce “yanzu tukunyar na nan wurinki?”
“Eh bari duk ranar da kika zo zan nuna miki ” na faɗa ina mai jingina jikin pilowe da na ɗora a baya,haka muka yi waya sosai ni da ita kafin mu yi sallama.Na cije leɓena na ƙasa ina mamakin maganar da na furtawa babban malami kamar Sheikh Rayyadeen,sai yanzu ma na ji kunya na rufe fuskata da tafin hannu ina mai cewa “ oh Khadeeja me ya shiga kanki da har za ki cewa Sheikh ya furta kalaman ƙarya?” sai kuma na ji tsoro kar ya ɗauke ni wata iri wacce ba ta da tarbiyya.Karon farko da na ji cewa ya zama dole na samu lambarsa,sai dai duk iya binciken shafinsa ban ga inda ya taɓa ɗora lambar ba a dole na haƙura na shiga rungume pilow ban san