MAFARKI Love and Horror Story By Mrs Sadauki.txt

Author :  Mrs Sadauki Category :  Hausa Read

Chapter   2 / 18

3K to 6K   out of 53.5K words

ta tambaya,sai Sheikh Rayyadeen yayi tsuru-tsuru kamar wani ƙaramin yaro.Shi sam bai farga da abin da ya yi ba sai yanzu,cike da jin nauyi yayi saurin nufar step yana hawa bibbiyu don tserewa kallon tuhumar da Ammy ke yi masa.Ita kuwa ta ɗaga murya tana mai cewa “in ka yi wanka ka fito da wuri don yau a part ɗina za mu sha ruwa” ya tsaya cak tare da juyowa ya kalle ta,ya san dalilinta na yin haka wato so take yi ta yi masa tambayoyi game da yarinyar da yayi suɓutar baki ya yi maganarta.....
[11/12 11:59] MRS SADAUKI: *MAFARKI*🦋🦋🦋
🦋🦋🦋
🦋🦋
Mallakar : 🦋
Chamsiya Laouali Rabo
```MRS SADAUKI 💫✍️```

02



Yana shiga ɗakinsa ya wuce can bedroom ,kan bed ya haye yana tunanin me zai cewa Ammy shi da tuni ya ajiye azuminsa a bisa larurarsa da ta motsa .Ji yayi ya ƙara jin tsanar Khadeeja saboda a kanta zai yi wa Ammy ƙarya ya je su yi buɗa baki tare,don bai ji zai iya sanar mata ya aje azumin ba duk da cewa kuwa bayan ya sha ruwan babu wani abu da ya ƙara sakawa bakinsa.Ya miƙe dakyar ya rage kayan jikinsa sannan ya shiga toilet,wanka yayi haɗi da alwala da ya fito jallabiya ya saka ya fesa turare kafin ya sauka ya nufi can falon Ammy,yayi sallama ta amsa sai faman haɗa Lipton take yi a kofi biyu.
Gefenta ya zauna tare da yin shiru,ta ɗan dube shi kafin ta ce “yau ba za ka yi addu'o'in ba? Saura ƙiris lokaci ya cika” ya ɗan murmusa kafin ya soma yin istigfar“Ya Allah ka yafe mini a bisa kuskuren da na yi, sannan ka kawo mini sauƙin wannan larrurar da nake fama da ita , in aure bai cikin ƙaddarar da shimfiɗa mini Ya Rabb ka cire mini sha'awa gaba ɗaya”


Tamkar Ammy ta san abin da yake ransa sai cewa ta yi ,“Allah dai ya nuna mini aurenka Sheikh Rayyadeen ɗina” murya can ƙasan moƙoshi ya amsa da “amin!” amma fa tuni ya ji a ransa kawai yana cikin mutanen da Allah ya jarabta da hanawa aure .Ana yin kiran sallah suka fara buɗa bakin har suka kammala shi ya wuce masjid ita kuma ta miƙe ta yi sallarta a nan.
Sai bayan sallar isha'i sannan ya dawo gida , lokacin tuni ahalin gidan duk sun hallara falo domin cin abincin dare kamar yadda tsarin yake.

A mutumce duk suka gaishe shi ya amsa cikin sakin fuska yana mai tambayar Aliya,“me yasa yau ba ki je makaranta ba?”

Ta sunkuye kai kafin ta ce “na tafi can babban gida ne ” wato gidan kakarta ta wajen uwa tana rufe bakinta Mama wacce ta kasance ƙishiyar Ammy ta yi caraf ta ce “ni ce na aike ta”

Ya dube ta kafin ya ce “amma ai da bari kika yi sai ranar da babu makaranta Mama”

Ta ɗan washe baki kafin ta ce “gaba za a kiyaye”

Abba wanda yake fitowa daga ɗakinsa duk ya ji abin da suke tattauna wa,har ƙasan ransa yake jin daɗin yadda ahalinsa ke mu'amulantar junansu amma duk da haka yana jin babu daɗi in ya tuna wani sa'in Grand-Maa na yin ƴar tsama da babban ɗansa mafi soyuwa a kaf ƴaƴan nasa.

Da sallama ya iso wurin,duk ƴar rige-rigen gaishe shi suka fara in ka cire Sheikh Rayyadeen da ya miƙe tsaye yana mai zuwa gun Abban ya amsa masa sallamar tasa tare da miƙa masa hannu suka yi musafaha.

Grand-Maa wacce ke zaune kan kujera ta ja tsuki tana mai cewa “in ba zuwan ƙarshen zamani ba da lalacewa ta ina ɗa zai tunkari ubansa ya miƙa masa hannu suna gaisawa sai ka ce wasu turawa,in kuma ka yi magana a ce ma ai shi ma addini ne”

Abba ne ya tanka ta don shi Sheikh ko kallon inda take bai yi ba.
“Maa wannan fa ba wani abu ba ne,ya ƙarfin jikin naki?” Abba ya tambaye ta cike da kulawa.

Kamar wata ƙaramar yarinya haka ta kwaɓe baki tana kukan dole haɗi matso ƙwalla.“Ta ya zan ji sauƙi alhalin kullum a gidan nan ni ce mai laifi,ka ga haka ɗazu uwarsa ta hana ni abinci wai ya kamata na dinga yin azumi tun da ban wani tsufa ba”


Abba ya dubi Ammy ransa a ɗan ɓace,ita kuma baiwar Allah sai ta fara ƙoƙarin kare kanta.

“Abban yara wallahi ban faɗa da wata manufa ba,gani na yi tun safe ba ta ci komai ba sai ruwan shayi shi ne na ce inda ma azumi ta yi ya fi ta zauna da yunwar nan ”



“Khadi a gidan nan wa yake sayen abinci?” Abba ya tambaye ta,idonta suka ciko da ƙwalla murya na ɗan rawa ta ce “kai ne”

“A kaf gidan nan wa yake da iko a kaina yayi mini faɗa har duka ma in ta kama?”

Ta basa amsa da “Grand-Maa”

“A ƙarƙashin wa kike a gidan nan?”

Kafin ta amsa masa tambayar Sheikh Rayyadeen ya tari numfashinta ,cike da nutsuwa ya ce “Abba don Allah ku bar maganar girma da ikon nan,cin abinci ya tara mu a nan amma kuma kuna shirin saka abincin ya fita ranmu ”

Abba ya ja numfashi tare da kawar da kai, Grand-Maa ta harari Sheikh kamar idonta za su faɗo yayin da ta yi wa Ammy mugun kallo sai dai suna haɗa ido da Mama sai ta sha jinin jikinta.Duk Sheikh na kallon komai ,har zuwa yanzu ya rasa dalilin da yasa Grand-Maa ke shakkar Mama amma kuma ta tsani mahaifiyarsa.


Ammy ce ta zuba wa kowa kamar yadda tsarin yake ranar girkinka kaina za ka yi haka.
Sheikh ya ɗan yi gyaran murya kafin ya ce “Aliya ke sai yaushe ne za ki fara taya iyayenmu aiki? Ko sai an kai ki gidanki ba ki iya komai ba?”

Duk sai suka kalle ta,Aliyu wanda ya kasance Yayanta uwarsu guda sai cewa yayi “wai wannan ce za ta yi girki mu ci? Allah ya tsari gawa da dariya”

Ammy ta yi ƴar dariya ta ce “Gadanga kar fa ka zo kana santi ”

Ya ce “haba dai Ammy wannan yarinyar ce za ta yi abinci mu ci? Ku dai barta da kwalliya da saka jan baki”

Ammy ta ce “in sha Allah duk ranar weekend tare da ita za mu dinga shiga kitchen ,zan sa kuma Saude ta koya miki girke-girken gargajiya”

Grand-Maa ta yi caraf ta ce “to sannu ƴar boko,ai gara na gargajiyar kan uwar fulawar da kike bamu kullum muna ci”

Ammy ta ce “yi haƙuri Ammy in sha Allah za a dinga yi miki girkinki daban,sai ki dinga faɗar abin da kike so”

Mama ta ce “haba dai Khadi wasa fa Grand-Maa ke yi miki amma tana son abubuwan da suka shafi fulawa ko Maa?” ta ƙarashe faɗa tana mai tsura mata ido, Grand-Maa duk da ranta ya ɓace haka ta daure ta yi murmushin yaƙe, Sheikh ya tsure ta da ido yana nazarinta kafin kuma ya ture plate ɗin gabansa ya ce “sai da safenku ”

“Tun yanzu za ka kwanta?” Ammy ta tambaye shi,sanin dalilin da yasa take tambayar tasa yasa ya ce “ban jin daɗin jikina ne Ammy,yau na gaji sosai”

“To ka sha maganinka kafin ka kwanta,in na tashi zan shiga na duba ka” Ammy ta faɗa cike da kulawa.

Ya ce “to Ammyna” sai yayi gaba,Abba ya dube ta ita kuma ta sunne kai tana jin fa ita ba ta ga dalilin da zai sa ta bar nunawa ɗanta kulawa ba.Duk shekarunsa ita a yaro take ganinsa,sauran ne suka tashi Aliyu da Aliya sai wurin ya yi saura Abba, Grand-Maa da Mama da Ammy.




“Mahmuda ya kamata ka yi wa matarka faɗa,shishigin da take yi wa mai gemu(cewa da Sheikh Rayyadeen) ya fara yin yawa,yanzu mene ne na tafiya duba shi? Ƙaramin yaro ne da za ta shayar ko me ? ”wannan ƙorafin na Grand-Maa ya fi shuren masaki da ta yi shi,don haka ba wani baƙon abu ba ne gun Ammy shi yasa ma ba ta wani damu ba.


Mama ce ta amsa mata madadin shi Abban,ta ce “Grand-Maa kin san tsakanin uwa da ɗa sai Allah,kamar ke ce da Abban yara kin ga duk da ya tsufa da ƴaƴansa haka wani zubin kike basa kulawa kamar ƙaramin yaro,in ba ki manta ba in ya jinkirta zuwa har cewa kike a kira miki shi a waya”

Cike da jin haushin katsalandan ɗin da take yi mata a lammuranta Grand-Maa ta ce “amma ai ni tsohuwa ce,ita kuma fa ba ki da sauran ƙurciyarta”

Mama ta ce “to mene ne aibu a ciki?”

Idon Grand-Maa ma suka kaɗa suka yi ja tsabar takaici,daga ƙarshe ta miƙe ta bar wurin.Mama ta ita ma ta miƙe da sauri tana cewa “ku jira kar dai a ce fushi Maa ta yi da ni ” sai kuma ta tafi da sauri,tana dab da shiga ɗakinta Mama ta ƙaraso tana mai cewa “wane sabon abu ne kuma kika tsiro Maa?”

Ta juyo cike da takaici ta ce “Ramma ki fita daga idona na rufe”

Mama ta zo ta ida tura Maa cikin ɗakin ita ma ta shiga ta dantse ƙofar kafin ta ce “me kike nufi? Kar dai ki ce mini zuciyar ƙurciya Sheikh Rayyadeen take so? Ke yanzu ba ki jin kunya cewa jikanki kike so? Wannan kuma wane irin salon tsafi ne?”


Grand-Maa ba ta bata amsa ba,sai shaƙe wuyan Mama da ta yi tana wani juya idonta suka rikiɗe kamar garwashin wuta yayin da akaifunta suka ƙara tsayi zaƙo-zaƙo.
Mama ta fiddo nata kayan aikin,wata ƴar siririyar tsutsa ce da ke cikin jijiyar wuyanta tana fitowa idon Grand-Maa ta cabka,babu shiri kuwa ta saki wuyan Mama ta yi baya tana dafe gun.

Mama ta shafi wuyanta tsutsar ta koma kafin ta ce “har abada ba zan bari ki cutar da Sheikh ba”

Ita kuwa Grand-Maa sai cewa ta yi “da ni da ke shege ka fasa” ba tare da ta ƙara cewa komai ba ta fice,ko da ta koma can falo tuni kowa ya watse.



Sheikh Rayyadeen na zuwa part ɗinsa sai ya shiga toilet ya haɗa ruwan wanka masu ɗumi ya shiga cikin bahon ya kwanta tare da ɗan lumshe idonsa.Wata irin kasala yake ji ga wani yanayi kamar wanda zazzaɓi zai damƙa,a duk lokacin da fuskar Khadeeja ta faɗo cikin magijin ganinsa sai ya ji wani abu ya tsarga masa wanda hakan yake ƙara hura wutar kasalar da ta aure shi.Dakyar ya fito ya ɗauro towel ya fito,yanayin ɗakin ya fara canzawa ya kunna na'urar ɗumama guri sannan ya tsane jikinsa tare da saka kayan bacci masu ɗan nauyi.Kan bed ya kwanta amma bai kashe fitila ba saboda sanin Ammy ta yi masa alƙawarin za ta zo ta duba shi.

Babu jimawa kuwa ta buga ƙofa ya ce ta shigo,ta tura ƙofar da sallama da sauri shi kuma ya tashi zaune yana mai daɗa jan blanket ɗin sama yana rufe jikinsa.


Tana zuwa gefen wuyansa ta taɓa ta ji da zafi,cikin muryar tausayi take cewa “jikinka da zazzaɓi shi ne ka yi wanka? Ka sha maganin da na baka?”

Ido ya tsura mata na wani lokaci kafin ya girgiza kai,ta ce “ don me? Ai ko addini bai hana a sha maganin gargajiya ba,me yasa ba za ka sha ba tun da har ka ga na baka bai kamata ka yi sakaci da shi ba.A ina ka ajiye shi?”

Ya shagwaɓe fuska kafin ya ce “Ammy ba fa abin da ke damuna kawai ɗan zazzaɓi ne”

“Shi mugu da kake ganinsa wayo ne da shi,a sannu a hankali yake kama ka har ya damƙe ka duka” ta faɗa tare da soma duba inda za ta ga maganin.


Can kuwa ta gansa,da kanta ta kaɗa madara sannan ta zuba maganin ta basa ya sha ba don ya so ba sai don yi mata biyayya.Yana gama sha ya koma ya kwanta yana mai lumshe ido,nan take kuma yadda Khadeeja ta faɗa ƙirjinsa a bisa kuskure ya faɗo masa,da sauri ya cije leɓe yana jin kamar ya ƙurma ihu .


“Me sunan yarinyar ta ɗazu da ka fara yi mini magana?” ya tsinkayo muryar Ammy,a hankali ya ɗan buɗe idonsa da suka yi masa nauyi yana kallonta kafin ya mayar da su ya rufe ruf.


“Deeni!” Ammy ta kira sunansa,wanda wannan sunayen ya kasance keɓaɓe ba ta kiransa da shi sai in tana son nuna masa shi ɗin yaro ne ƙarami a idonta har yanzu bai wuce ta yi masa duka ko kuma wani abu da uwa ce kawai za ta iya yi wa ɗanta shi.


Kamar zai yi kuka ya ce “Ammy ba fa sonta nake yi ba”

“Na sani,amma ai ita ce silar ciwonka ”

“Wane ciwo kuma Ammy?”

“Deeni ni fa ba ƙaramar yarinya ba ce,kar ka manta ni na ɗauki cikinka na tsawon wata tara,na haife ka sannan na raine ka.Babu wani hali naka da ban sani ba,hatta Maa da ke kakarka ta gane da yau ka haɗu da wata budurwa sai ni ce ba zan fahimta ba?”


Shiru ya yi kafin ya ce “Ammy na faɗa miki ba sonta nake yi ba,kawai tsautsayi ne yasa ta shigo hanyata”

“Na ji ba ka sonta mene sunanta?”

“Sunan mai darajata ne da ita” ya faɗa kamar zai fasa ihu,Ammy ta yi ɗan murmushi ta ce “takwarata ce kenan?”

“Eh!” ya bata amsa,idon Ammy suka ciko da ƙwalla tana mai yin addu'a a zuciya ‘ Allah yasa wannan ɗin ita ce abokiyar rayuwarka’ sai kuma ta fice ta barsa cikin duniyar tunani.



★KHADEEJA

Muna gaba buɗa baki na wuce sashena,sallar magarib na yi sannan na soma yin azkhar na maraice ina zaune kan sallaya lokacin isha'i yayi na miƙe na gabatar.Bayan na gama na yi wanka na saka kayan bacci pink riga da wando ne masu hulla,sai na ɗora ɗan madaidain hijabi a sama na fita zuwa falo.Soyayyen dankali na zauna na ci ina kallon Arewa24 da suke nuna shirin rayuwata,duk abin da jaruman ke yi sai nake hango kanmu ni da Sheikh wannan yasa na zauna ni ɗaya ina ta murmushi.

“Ke lafiyarki?” na ji muryar Yaya Hamza,da sauri na nutsu ina mai cewa “lafiya lau Yaya Barka da shan ruwa ka ga Daddy? Yau ba ka zo muka yi buɗa baki tare ba halan gidansu Mujahida ka sha ruwa?”

Ya ja dogon tsaki yana mai cewa “ke me yasa kin cika surutun tsiya ne,a yi mutum kamar Aku cacacaaa babu hutu sai zubo shi kike yi”

Na turo baki na ce “ai Mujahida ta koya mini” ya banko mini harara kafin ya ce “ba Mujahid ba?”

Na tuntsire da dariya kafin na ce “ka san kuwa haka ƙawata ta ce mini wai inda ma Yayanta Mujahid na aura shikenan mun yi masayar yayyu ”

Ya ɗan murmusa kafin ya ɗan dungure mini kai ya ce “ina mai tabbatar miki da cikin sati biyu kacal zai maido ki gida saboda ya tsani surutu”

Na sheƙe da dariya na ce “ai kuwa saurayina ma shi ma shiru-shiru yake kullum bakinsa a rufe kamar mai ciwon haƙori”

Yaya Hamza ya shiga yin dariya kafin ya ce “Allah ya shirye ki auta,kullum har tambayar kaina nake ko wane bawan Allah zai auri shirmamar ƙanwata?”

Na yi murmushi mai fiddo tsantsar farin cikin da ya fito daga zuciya sannan na basa amsa da “wani mai ilimi ne,mai nutsuwa, kyakkyawa ɗan gayu ,yana da cikar haiba da ƙwarjini.Bari na faɗa maka Yaya Hamza kaf makarantarmu kowa tsoronsa yake ji,hatta malamai fa ” sai kuma na tuntsire da dariya kafin na ci gaba da cewa “ɗazu fa malamin saura ƙiris zuciyarsa ta buga da Sheikh ya shigo ajinmu ” sai kuma na yi shiru ina tuna irin yadda ƙirjinmu ya haɗu da na juna.

Kamar wacce aka tsikara sai kuma na miƙe na nufi ɗakina ba tare da na yi wa yaya Hamza sallama ba.Ina shiga kawai na haye bed tare da jawo pilow na ƙanƙame na soma yin hawaye tuna cewa babu tabbas ya karɓi soyayyata.Ba tare da na shirya yin bacci ba na ji wani abu mai kamar rumfa ya luluɓe ni,kawai kwatsam sai na tsinci kaina a duniyar mafarki sai dai ba irin mafarkin da mutane suke yi ba a'a nawa na daban ne.

Cikin wani babban gida ne na tsinci kaina mai hoton ahali,ɗaya bayan ɗaya haka nake kallon hoton har idona ya sauka kan na Sheikh da na yi gaba kuma sai ya na ci karo da na wata mata,sosai suke kama da Sheikh tamkar ƴan biyu sai dai za ta girme masa.Ina shirin janye idona sai hoton ya soma yi mini magana.

“Kar ki tafi ba ki ji labarina ba” tana faɗa mini haka sai kuma na ƙara tsintar kaina wani wurin,sai dai wannan tare nake da ita.

“Ina ne nan?” na tambaye ta.
Ta bani amsa da “maƙabartar rayayyu ce”
“Rayayyu kuma?”
“Eh! Ni ma saura ƙiris na bi ayarin waɗanda za a binne da ransu” ta bani amsa tana goge hawayen jini.Kafin ta ci gaba da cewa “ni mace ce mai addini,na taso gidan malamai duk da ba su suka haife ni ba amma a can na girma tun ina ƴar shekara uku a duniya ƙanwar Mamana ta ɗauke ni riƙo.A can gidan aka yi mini aure,sai dai ban taɓa haihuwa ba.Farkon matsalata ta soma ne a wata rana da na bincika wayar mijina na samu shaidar yana cin amanata shi da wata mace a waje,da na tunkare shi da zancen sam bai yi mini gardama ba ya karɓi laifinsa tare da neman yafiya ni ma sai na haƙura na yafe masa.Sai dai a bisa tsautsayi ko na ce ƙaddara,sai na ƙara duba wayar tasa na ga dai ashe har yanzu bai goge komai nata ba sai na je can facebook na binciko sunanta tare da following nata.Na ɗauki tsawon sati biyu ina bibiyar duk wani abu da za ta yi posting a page ɗinta amma ko sau ɗaya ban ga mijina yayi comments ba,duk da cewa mafi akasari hotunanta ne masu

2 / 18