Author : Mrs Sadauki Category : Hausa Read
bayyana tsaraici.Kwatsam wata rana sai ta wallafa zancen fyaɗe na wata yarinya da aka tozarta,kawai sai na yi mata magana pc na ƙirƙiro zancen ƙarya na ce ni ma da ina yarinya an taɓa yi mini fyaɗe,daga nan ne muka fara gaisawa fa har ta kai da mun yi masayar lambobin juna muka soma yin WhatsApp.Wata rana sai ta shirya mana haɗuwa a wani gidan cin abinci haka na kwashi jiki na je,a fili har ta fi kyau kan a zahiri tabbas ta yi haɗuwar da duk wani namiji mai lafiya zai so ya kasance da ita,tuni kishi ya turnuƙe ni amma na daure muka gaisa aka gabatar mana da abin sha da kuma abin motsa baki bayan nan kowacce ta kama gabanta.A wannan daren ne na ga ta saka video ɗinta a status jikinta babu wata suturar kirki,haka na kalla na sake kallo da na ji ban gaji da kallo ba kawai sai na yi saving nata.Tsabar yadda ta shiga raina yasa duk hankalina ya tashi,maimakon na je gun mijina a'a sai na ji tamkar wani baƙin ruhi na zuga ni a haka na yi amfani da kaina na biya wa kaina buƙata wacce a zahiri ni ɗaya ce amma a baɗini akwai sheɗani a tare da ni ” tana kawowa nan sai kuma ta dafe mararta tana cije haƙora,ina shirin yi mata magana alarm wanda ke tashina sallar dare ya soma ruri,na buɗe idona da suka yi mini nauyi kafin na miƙe dakyar na shiga toilet.Kan WC na hau na soma yin fitsari amma kamar abin tsiya haka na ji wani baccin na ƙara jana daga zaune....
[11/12 11:59] MRS SADAUKI: *MAFARKI*🦋🦋🦋
🦋🦋🦋
🦋🦋
Mallakar : 🦋
Chamsiya Laouali Rabo
```MRS SADAUKI 💫✍️```
03
Da sauri na kamo ta,sai ta ɗago ta dube ni da idonta da suka soma canza launi suna komawa kore kamar na maciji.Murya na ɗan rawa ta ci gaba da cewa “tun da nake ban taɓa yin auren hannu ba sai wannan ranar,abin mamaki kuma shi ne gamsuwar da na samu ta sha banban da irin wacce nake samu a wurin mijina sam ban fahimci abin da yake faru da ni ba.Sai na yi istigfari har da ma azumi uku ina ɗauke da na huɗun ne kwatsam ta aiko mini video a WhatsApp wannan karon babu sutura ko ɗaya a jikinta ko ɗan kamfai,fuskarta kuwa duk ta ɓace da dukkan alamu sun gama mu'amula ne da namiji sai ta yi tabi'arsu ta ƴan kwalta.In taƙaice miki dai nan take azumina ya zama gurgu,na mance da istigfarin da na yi na ƙara biyawa kaina buƙata a karo na biyu.Sai bayan na gama ne na yi ta kuka tare da goge video na kuma ja mata kunne kar ta sake in kuma ta ƙara zan yi blocking nata.Ta bani haƙuri muka wuce wurin,sai dai ba a wani ɗauki lokaci ba kamar abin tsafi haka na ƙara tsintar videon a wayata alhalin na goge ta.Sai kuma na sake komawa ruwa duk da kuwa na yi ƙoƙarin hana kaina ƙara kallon videaon amma yadda kika san akwai wani baƙin ruhi mai zuga ni haka na buɗe na kalla .Na riga da na hallaka,karuwar mijina tuni ta yi galaba a kaina don har da link ɗin groupe ɗinta ta aiko mini na shiga ba tare da na san wannan shi ne takun farkona a cikin duniyar matsafa.Duka-duka mu bakwai ne cikin groupe ɗin,babu wata hira da muke yi sai ta sex da kuma videon batsa wani sa'in ma video call muke yi muna biya wa juna buƙata,a cikin irin wannan shiriritar ce muka fara yin gasar mazajen bogi ta hanyoyin biyawa juna buƙata da kanmu.Wata daga cikinmu ta bani wani abu wanda ba zan ce miki mene ne ba,ta ƙalubalance ni muddin na yi amfani da shi matsayin mijin tarayya na kwana ɗaya kacal to za ta bani 500k.Haka na yi ɗin duk da ina jinsa har cikin marata yana tokare ni haka na haƙura na cuci kaina akan kuɗi,yayin da su kuma suke tsaye a zahiri suna kallona.Bayan na gama kuwa ta bani kuɗin,ba tare da na san cewa duk don su ƙara kwaɗaita mini zama cikinsu ba ne mu ci gaba da sheƙewa” sai ta yi shiru tana mai ɗan lumshe idonta.
Na ce “mijinki fa ya sani?”
Kai ta girgiza mini kafin ta ci gaba da cewa “da na samu kuɗin dai na saya masa agogo sabuwa yayi murna sosai,ɓangaren auratayyarmu kuwa sai abubuwa suka canza na soma tsiro da abubuwan sheɗanci ina yi masa da sunan gamsar da shi,abin mamaki kuwa sosai yake jin daɗin haka ya kuma ƙara sona har yake mamakin yadda ban ƙyanƙyaminsa da nake kai bakina a wurin da yake bahaya” sai ta buɗe ido tana murmushi mai ciwo.Can ta ɗora da “wata rana kamar a MAFARKI haka na tsinci kaina wata duniya.Ƙawayen sharholiya suka ja ni wani gun don mu huta mu cashe,sai kuma tsari ya canza muka soma shiririta kafin kuma duk su tsaya cak suna masu haɗin baki su ce “lokaci yayi” duk sai suka zube ƙasa suka kuma roƙe ni na yi yadda suka yi ɗin,haka ni ma na zube gwiwana ƙasa ba tare da na san dalili ba.Babu jimawa wata tsohuwa ta bayyana,sanye take da baƙaƙen kaya,gashin kanta a buɗe yake wanda yayi fari ƙal,idonta kuwa sun shige sosai can cikin gurbi ko ƙyaftawa ba ta yi haka ta kafe ni da su tana kallona,ni kuwa zuciyata sai matsanancin bugawa take yi kamar zan mutuwa.
Cikin masifa take yi wa sauran faɗa tana zaginsu don me yasa ba su samo wasu members dayawa ba alhalin ta faɗa musu wannan karon mutane sosai take so.Kafin kuma ta juya ga karuwar mijina wacce ita ce shugabar groupe ɗinmu,ta tozarta ta sannan ta ce “me yasa ba ki sanar da ita tun farko ba? ” ba ta iya cewa komai ba,sai tsohuwar ta dawo kaina tana mai tambaya ta “me sunan mahaifiyarki?” na shaida mata sai kawai ta rufe ido tana kiran sunan Mamana,babu jimawa na soma jin kukanta haɗi da kakari.Ko da na koma gida kiran farko da na samu shi ne don a sanar da ni mutuwar Mamana,tun daga wannan lokacin kuma na yi alƙawarin ko mutuwa zan yi ba zan yi musu biyayya ba kin ji kuma inda farkon wata izayar ta soma yanzu haka ina jin motsinta za ta kawo mini ziyara domin amsa mata tambayarta a karo na ƙarshe na yarda na yi wa baƙin ruhi hidima ko kuwa na zaɓi ta binne ni da raina kamar sauran da suka bijire” tana gama bani labarin na farka.
Yadda na tsinci kaina a toilet yayi matuƙar bani mamaki,haka na yi tsarki na je kusan pampo na yi alwala.Da na fito na duba agogo sai na ga tuni lokacin sallar asubah ma ya yi,haka na yi nafila tare da farillar kafin na zauna ina lazumi ina kuma tunanin mafarkin da na yi.
Bayan na gama sai na fita,ɗakin Momy na je na gaishe ta tare da tambayarta abin da za a yi na breakfast ta faɗa mini sai na wuce kitchen.Tare da taimakon ƴar aikinmu na haɗa komai , lokacin da na gama tuni ƙarfe bakwai da rabi ta gota.A gaggauce na je na yi wanka na yi shirin makaranta,abicina ma sai cikin kula na zuba shi na wuce direba ya kai ni.
Ina sauka abu na farko da na fara yi shi ne duba inda yake parking motarsa,wurin wayam yake babu motar sai na ji babu daɗi.Haka na wuce ajinmu,bayan mun gaisa da Mujahida ne nake bata labarin mafarkin da na yi kafin na ƙara da cewa “ sosai fa na ji tsoro,kar ki so ki ga yadda na yi ta murna tare da yi wa Allah godiya da yasa mafarki ne”
“Amma abin da mamaki yake,kuma duk da kin farka bayan kin koma wani baccin matar ta sake dawowa ta baki ci gaban labarin?” Mujahida ta tambaya.
Na ja numfashi kafin na ce “shi ne abin da ya fi bani tsoro,kuma fa ina zaune cikin toilet.Haka kawai nake ji a raina wannan ba kawai MAFARKI ne ba”
Ta ɗan bangaje ni ta ce “dalla can matsoraciya wa ya sani ma ko Film ne kika kalla kawai kin manta ne kin yi dubin mafarki ne”
Na yi ƴar dariya ina mai cewa “in akwai wanda ya raina ni duniyar nan bayanki yake” ba ta kai ga cewa komai ba malam Ibrahim ya shigo.Abu na farko da ya ce mu yi shi ne raba mana takardun da zamu zana jarabawa haɗi questions ɗin.
Haka muka soma yi,duk wanda ya gama sai ya kai masa.Ina kammalawa na miƙe na kai masa,sai ya ƙi karɓa tare da cewa “ya jikin naki?”
“Alhamdullah!” na basa amsa tare da ajiye takardar kan teburi na fice.Idona na ƙara kaiwa wurin parking special amma har yanzu dai babu motarsa,haka kawai na ji hankalina ya tashi.
Ina nan tsaye Mujahida ta fito tana mitar cewa ta gaji,ban kula ta ba sai ma zancen Sheikh da na ɗauko mata.“Yau mutumin bai zo ba Allah sa dai lafiya”
“Wane mutum?”
“Ke banza dubi babu motarsa” na faɗa tare da bangazarta.
Ta ja tsaki tana cewa “uban ƴan takura za ki ce,ashe bai zo ba shi yasa na ji makarantar ko ina hayaniya”
Na ɗan murmusa kafin na bata labarin abin da Yaya Hamza ya ce,sai da ta ci dariya kafin ta ce “kuma fa zamanku zai yi wuya kin ga dai shi bai son yawan magana,ke kuma ga ki kamar Akun kuturu” na dake ta na ce “ni ce Akun kuturun?” ita ma ta rama ta tabke ni sosai tare da rugawa tana cewa “eh ke ɗin” da gudu na bi ta don na rama ɗin wanda ya yi daidai da shigowar Sheikh Rayyadeen a ƙafa yake babu mota.Cak na tsaya ina mai kallon tsakiyar idonsa da suka yi ɗan ja,shi ne ya fara ɗauke kansa kafin ni kuma na juya masa baya ina dafe saitin zuciyata.
Daga bayana na ji Mujahida na cewa “to sai ki juyo don kuwa tuni ya tafi da dukkan alamu dai bai da lafiya don na ga abin ƙarin ruwa a hannunsa”
Na juyo ,na fara rama dukan da ta yi mini ina mai cewa “babu wani nan,so kike yi dai ki ɗaga mini hankali”
“Wallahi gaske don me zan yi miki wannan wasar,kin ga waccan ita ce ƙanwarsa” Mujahida ta faɗa tana yi mini nuni da wata budurwa wacce za mu iya yin sa'anni ko kuma ta girme mini da kaɗan.
“Amma ya na ganta ita baƙa?”
“Oho ni za ki tambaya,bari in Sheikh ya kai ki gidansu sai ki tambaye ta” ta faɗa tare da yin gaba,na tsayar da ita ina mai cewa “na fa kawo abinci daga gida yana can aji”
“Na sani ai,ruwa zan nemo” ta bani amsa,sai na take mata baya muka je ta samo ruwa muka dawo.Bayan kowa ya gama zana jarabawa muka shiga aji don cin abinci amma sam na kasa cin na kirki saboda tunanin abin da ke damun Sheikh .Wunin nan dai haka nan na yi shi duk babu daɗi,da na je gida ma haka sai da aka ga canji.
Abu kamar wasa sai ga shi wajen kwana uku Sheikh bai ƙara takowa makaranta ba,ga shi kuwa tuni an kai mu aji na gaba wanda ya kasance ajinsa.Ga baƙunta ga kuma tunani sai duk suka taru suka ramar da ni,yau ta kama Lahadi bayan mun fito shan iska tsoffin ƴan ajin Sheikh suka yanke shawarar zuwa duba shi haka ɗaiɗaiku daga cikinmu mu ma muka runguɗa muka bi ayari kasancewar da ƙanwarsa a ajin wannan yasa ba mu da damuwa ta fannin sanin gidansu.
Babu wani nisa sosai,tafiyar minti goma sha muka isa ƙaton gidan wanda ya ninka namu sau biyu.Tun da na ɗora ƙafa a ƙasar gidan jikina ya ɗau rawa zuciyata ta soma bugawa kamar za ta faɗo tsabar lugude.
Ita ƙanwar tasa mai suna Aliya ita ta yi mana iso zuwa babban falon gidan,kan lafiyayyen capet duk muka zubo sai wasu su biyu ne wanda alamu ya nuna ƙawayen Aliyar ne suka hau kujeru.
Babu jimawa ta sa aka fara kawo mana lemu mai sanyi,kafin ta ce “bari na je na kira shi” wani irin dam na ji zuciyata ta buga .
Can kuma ta dawo ita da wata mata wacce kallo ɗaya na yi mata na gano inda Sheikh ya samo kyawunsa,wato daga gare ta ne.Cike da girmamawa duk muka shiga gaishe ta,ita kuma tana amsawa cikin kulawa kafin ta ce “ku taso ku ƙaraso” haka duk muka miƙe muka take mata baya,wani falon muka ƙara ratsawa kafin kuma ta ƙara kai mu can cikin wani.Ido na lumshe jin yadda duk ƙamshinsa ya cika ɗakin,sai da Mujahida ta ɗan bangaje ni sannan na buɗe idona sai na ga tuni har sun zauna sai ni ce a tsaye kamar haure .Jikina ne ya hau rawa saura ƙiris na faɗi Allah ya gyara na samu wuri na zauna, Ammy ɗin ce ta kira sunansa “Sheikh Rayyadeen? Tashi ga su nan sun shigo”
Ta ƙasan ido na kalle shi,yana kwance kan kujera mai zaman mutum uku ya luluɓe da blanket.A hankali ya tashi ya zauna yana mai yi mana sallama,ni dai ban amsa ba sai ɗan kallon fuskarsa da na yi wacce ta ƙara yin haske .
Ƴar rige-rigen yi masa ya jiki suke yi shi kuma yana amsawa,tare da tambayar sabbin fuskokin da bai sani ba su kuma suna yi masa bayani ɗaliban da aka kawo ne sabbin zuwa.
A bisa tsautsa yi na ɗaga kai da niyyar satar kallonsa,karaf idonmu ya sarƙe cikin na juna da wani irin mugun sauri na sunne kai ina mai kama yatsuna ina wasa da zobena.
Ammy wacce ke tsaye duk tana kallon komai,dama burinta bai wuce ta ga wacce ta jefa ɗanta cikin wannan halin ba.Amma don sake tabbatarwa sai cewa ta yi “ma sha Allah nan dukkanku ajinsa kuke ?”
Cikin murna suka amsa da eh,Ammy ta ce “ina ga dai tun da shi malamin naku bai da lafiya ni zan je na ci gaba da koyar da ku” duk sai aka soma murna tare da nunawa eh ana so ta koya ɗin,ita kuwa Ammy sai cewa yi“ke ya sunanki?”
“Sadiya” ta bata amsa tana wani sunne kai,na dube ta ina mai cewa a zuci ‘ kina da kunya amma shi ne kika haye kujera daga zuwa gidan mutane’ haka Ammy ta dinga tambayar sunaye har ta kawo kaina ta ce “ke kuma me sunanki?”
Na ɗan dubi Sheikh kamar ba zan yi magana ba sai kuma na ce “Nana Khadeejatu” ina ganin lokacin da ya kawar da kai kamar na ambaci sunan kashi.Bayan ta gama jin sunayenmu cikin tsokana ta cewa Aliya “ke kuma fa?” duk sai aka sa dariya,nan dai ta fita Aliyar na take mata baya.
Sheikh Rayyadeen kuwa tambayoyi ya soma yi wa ɗaliban nasa suna basa amsa yadda ajin ya kasance bayan tafiyarsa .Duk da kaina na sunkuye amma lokaci zuwa lokaci ina jin kaifin idonsa a kaina,a hankali na kai hannu na taɓa Mujahida ta juyo ta dube ni tana mai tambayar “ya dai?”
“Ki tashi mu tafi” na furta kamar zan yi kuka,don wani irin yanayi ne nake ji yana ratsa ni ga kuma kallon Sheikh da nake ji a jikina.Hararar wasa ta yi mini tana shirin juyawa na ce “please ki zo mu fita waje to” kanzil ba ta ce mini ba sai ma yadda kusan kowa ya maido dubansa kaina sai na ji duk na tsargu,cikin ikon Allah Aliya ta sake shigo wa hannunta riƙe da faranti an yanka ƴaƴan fruits sai ta soma tsokanarsu tana cewa “yau dai za ku ci abinci a gidan malaminku duk wacce ta ƙi ci kuma bulala goma” hakan da ta yi ne yasa sai hankalinsu ya koma can.
Uwar iya yi Sadiya wacce na lura kamar kanta na rawa sai cewa ta yi “duk wanda ya yi habaici dai a kasuwa ya san da wanda yake” ɗayar ce wacce suka hau kujera a ɗazu ta karɓe da cewa “ai ban so kika kula ta ba Diya ”
Yadda suke raha a gabansa abin yayi matuƙar bani mamaki,ko da yake kawar da kai yayi gefe yana latsa waya.Ko kunya ba su ji haka wasu daga cikinsu suka sa hannu a faranti suna ɗauko fruit suna ci.
Aka yi sallama, Ammy ce da tare da wani mai farar rigar likitoci.Gaishe shi aka fara yi kafin shi kuma ya tambayi jikin Sheikh ɗin kamar wanda bai son yin magana ya ce “alhamdullah!”
Hannunsa ya kama don saka masa sabon tiyon ƙarin ruwa amma samun jijiya ya gagara sai sokarsa yake yi jini na zuba.Duk in ya tsake shi sai na rumtse ido don takaici,da na ji na kasa haƙuri ban san ina na samo jarumtar miƙewa ba na ce “kawo ka gani”
Ba Sheikh ba alamun mamaki ne ya bayyana a fuskokin kowa,duk yadda kuwa Mujahida ta so riƙe mini ƙafa ina tuni har na isa gabansa na karɓe allurar .Sai kuma a lokacin na dawo hayyacina,yadda Sheikh Rayyadeen ya kafe ni da ido shi ya saka jikina soma rawa.
Mahaifiyarsa ce ta matso tana cewa “bari kallonsa yi aikinki” sai da na ƙara kallon tsakiyar idonsa kafin na sunne kai,a cikin ledar magunguna na zaro safar hannu kafin a hankali hannu na yi mini rawa na soma jan hannun jallabiyarsa sama.Ɗaure damtsensa na yi gam ba a ɗauki lokaci ba kuwa jijiyarsa kore ta bayyana,da Bismillah na soka allurar ina mai ɗan ɗagowa na dube shi idonmu ya sarƙe cikin na juna kafin kuma ya kawar da kai gefe.Na ja numfashi ina mai kwance ɗaurin da na yi masa tare da cewa likitan “na nemo jijiyar”
Ya saki ɗan murmushi kafin ya zo ya ƙarasa aikinsa,ni kuwa ji na