Author : Mrs Sadauki Category : Hausa Read
ne? Ka koma ka bari zuwa dare”
“Inda zan komawa can ɗin yanzu dare ne,na yi tunanin nan ɗin ma haka ne.A takaice dai dole ki saurare ni” na faɗa ina mai ɗaga kaina sama tare da yin wata irin cara sai ga kowa da ke wurin ya ɓingire bacci in ka fidda Ummah.Ban kuma ɓata lokaci ba na sauko ƙasa,direct ɗakina na yi tsinke Ummah ta take mini sawu.A gabanta na canza siffata na dawo normal mutum,kamar wani ƙaramin yaro haka ta zo ta ci kwalar rigata tana cewa “Davido ba ka da hankali ne? Me ya maido ka nan bayan ka samu ka kuɓuce?”
Na sa dukkan hannuwana na cire nata kafin na kalle ta tsakiyar ido na ce “ki faɗa mini gaskiya wace ce ke? Mene ne dalilinki na kashe Abba?”
Cikin ƙaraji ta ce “ba Abbanka ba ne!” ni ma na tari numfashinta na ce “ko ma dai mene ne ai shi ya raine ni ya kuma yi ɗawainiya da ni”
Wani gigitacen mari ta ɗauke ni da shi kafin cikin wani yare da ba na Hausa ba ta ce “ ni ce na haife ka don haka dole ka saurare ni kuma ka yi abin da na ce” tana gama faɗar haka ta soma harhaɗa mini kayana tana buɗe akwatina nan ta yi kiciɓis da littafin sirri ta kai hannu za ta ɗauko shi amma na hana ta hanyar yin furucin tsafi littafin ya tashi sama ya zo hannuna.
Jikin Ummah na ɗan rawa ta ce “tun yaushe ka samu littafin sirri? Davido dama kana mafarkin samun prophecy amma shi ne ba ka taɓa sanar da ni ba? Faɗa mini ya siffarta take?”
Ido kawai na tsurawa Ummah jin tana magana kamar dama tun can asali ta san abin da ke faruwa a rayuwata ko kuma zai faru,amma daidai ɗaya rana ba mu taɓa zama ni da ita mun yi maganar fahimta ba.
Ganin na yi shiru sai ta ci gaba da cewa “haukan da abokinka ke yi kenan kai ne sila? Mutuwar Joy fa?” ta ƙarashe idonta na cikowa da ruwan hawaye.
Na yi wani murmushin gefen baki kafin na ce “Ummah me yasa kike son nuna mini kina da ƙawa zuci? Kar ki yi ɓarnar hawayenki don zuwa yanzu ban san wani abu wai shi tausayi ba,zuciyata ta ida ƙeƙashe na ɗauki alƙawarin yin rayuwata a salon yadda na gani ta dace da ni.Ban damu da sai kin sanar da ni wane ne mahaifina ba saboda na riga da na san shi ” ina gama faɗar haka na nufi ƙofar fita ina mai rungume da littafina.
“Ka kula da kanka, sannan ka yarda cewa Ummarka na ƙaunarka fiye da komai na duniya da ta mallaka” shi ne abin da ta furta ,duk da kalaman sun dake ni amma ban juya ba haka na fita tsakar gida a kuma take na ƙara ɗaukar siffar Mikiya na yi sama ina mai sakin carar da ta dawo da kowa cikin hayyacinsa sannan na yi gaba abina.
Sai da na yi shawagi sosai wanda ya ishe ni kafin juya idona ta hanyar tsafi na dira a Uganda wannan karon a karan kaina a kuma hayyacina.Gidan Sarki Alfanso na dira a bayan wata ƙatuwar bishiyar kuka wacce Hausawa ke yi mata laƙabi da uwar Aljanu .Ƙafafuwana na sauka ƙasa kamar tarko haka wata raga ta dabaibaye ni wacce ƙaryar idon mutum normal ya ganta saboda ta tsafi ce.
Sawun tawowar runduna da ya fara kawo mini farmaki yasa na yi saurin ɗaukar siffar bil'adama sai dai fa kash sam ƙafafuwa sun ƙi bani haɗin kai suna nan dai irin na tsuntsu.
Yadda inuwoyin siffofin mutanen suka kewaye ni yasa na ɗaga kai domin ganin su wane ne,sai dai sam kawunansu sumul suke babu ido,babu hanci babu baki .Cikin nasu kalar siddabarun suka cilla ni wata haɗaɗɗiyar fada,sai ga ni zube kan gwiwaina a gaban Sarki Alfanso wanda ke zaune daram kan kujerar sarauta.
Kaina a sunne yake hakan ya hana shi damar ganin fuskata sai ƙafafuwana waɗanda duk nake jin idanuwan dakarun a kansu.
“David?” na ji muryarsa cike da nutsuwa ta ambaci sunana yayin da kuma wurin ya ɗauki wata irin guɗa wacce kana ji ba matan bil'adama ne ke yinta ba sai dai na mutanen ɓoye.
Na ɗaga kaina muka yi ido huɗu da dattijon,ya sakar mini murmushi.Sam ban ga tahowarsa ba kawai dai na gansa tsudum a gabana,rungume ni yayi ƙam a ƙirjinsa nan take hasken idona ya ɗauke ban ƙara sanin abin da ya faru da ni ba sai tashi na yi na tsinci kaina kan gado na alfarma,a gefena kuma littafina ne na sirri.
“Barka da tashin asubah Yarima!” wata sanyayyar murya ta daki kunnena,a hankali na juya ɓangaren da na ji ta.Nan na yi tozali da wata baƙar yarinya mai masifar kyau da kyawun fasali,a ta cikin idonta kawai ka kalla za ka iya hango farin ruhinta mai cike da tausayi da kuma rauni.
Ta sakar mini murmushi wanda ya bayyana fararen haƙoranta masu ɗauke da ƴar siririya wushirya,ta ce “sunana Izzatu baiwarka ce ni wacce za ta dinga yi maka hidima”
Tana gama rufen bakinta aka buga wata irin ƙarar rawa mai mugun ƙara wacce ta karaɗe kaf illahirin masarautar.Wata irin zabura na ga ta yi haɗi kuma da tsorata,na ce “ƙarar mece ce wannan?”
Murya na ɗan rawa ta ce “in ka ji an buga ƙarar rawar nan to an samu wani hatsabin matsafi ko matsafi a daular nan ne”
A hankali na sauko daga kan gadon ina gyaran zaman wata rigar bacci da ban san yaushe aka saka mini ita ba.Kusan window na tsaya tare da yin tsaye na ɗan ɗaga labule ina kallon yadda aka jawo wani tsoho a tsiyace,“in an kama su wane irin hukunci ake yi musu?” na samu kaina da tambayarta.
Daga can inda take a tsaye ta ce “ana killace su ne domin yin hidima ga Masarauta ”
Na ɗan juyo na dube ta na ce “amma ya na ga kin tsorata?”
Ta yi ƙasa da kai ta kasa furta komai sai jikinta ne da ke ɗan yin rawa,tambayar tawa na sake maimaita wa hakan yasa ta ɗago fuska shaɓe-shaɓe da hawaye ta ce “ana yanka Musulmi guda ne matsayin hadaya ga ababen bautar Masarauta ”
“Musulmai? Su wane ne su?” na tambaya.
Cikin kuka ta ce “Addini ne da ya sha banban da sauran addinai, wannan dalili ne yasa ake yanka ɗaya daga cikinmu a cewarsu jinin musulmi tsarkake ne bai da wani rauni ko datti”
Ƙarar buɗe ƙofar ɗakin yasa na mayar da idona can,wa zan gani? Nelson ne cikin shigar dakaru.Ya shigo yana mai sakar mini murmushi,kallo guda ya yi wa baiwa Izzatu ta fita da sauri.
Zuwa ya yi ya rungume ni kafin ya ce “barka da shigowa Masarauta ! Ya kamata ka shiga ka yi wanka,a karo na farko za ka fita zuwa faɗa domin ƙaddamar da ƙarfin iko kan sabon matsafin da aka samu”
“Ta ya aka yi ka san har na zo nan?” na tambaye shi.Ya yi mini wani kallo kafin ya ce “ka san kuwa tun yaushe kake cikin masarautar nan? Kimanin awa takwas kenan,tun da ka zo ruhinka ya fita zuwa dajin ɗaukaka, kai dai mu je ka yi wanka daga baya za mu yi magana ”
Da taimakon Nelson na samu na yi wanka na shirya cikin kayan sarauta waɗanda ba a kawo su ɗakina ba sai da aka tsafe su ta yadda za su tafasa jinina .
Tun kafin na fita aka fara shelar Yarima David zai fito,ɗa ɗaya tilo ga Sarki Alfanso.Ba ka jin komai sai busar sarewa,a haka na ratso cikin dubban mutanen da suka hallara wurin taron bayyana ni da kuma na hukuncin da zan yanke.Kujera ta musamman aka ware mini na zauna yayin da kuma Nelson ya yi tsaye gefen damana.
Bayan kirari da sauran abubuwan da al'adu suka tanada mahaifin Nelson wanda ya kasance Sarkin yaƙi da kuma babban abokin sarki ya gabatar da ni.Kafin kuma a fito da tsohon da aka ce matsafi ne,ana gurfanar da shi ƴarsa ta rugo da gudu tana kururuwa sai dai ba a bata damar isa wurinsa ba aka dakatar da ita.A hankali na sauke idona kanta,yarinyar mafarkina ce wacce nake gani nake kuma jin ƙaunarta har ƙasan raina.
Daga can inda take tirjiya kan sai an sake ta domin zuwa ga mahaifinta,a inda take tsayen ta saka idonta cikin nawa tana yi mini wani irin kallo wanda na hango tsantsar ƙarfin baƙin tsafi da kuma muguntar da ruhinta ke ɗauke da shi.
Ban san lokacin da bakina ya furta “ku barta ta ƙaraso!” sakinta suka yi sai kuma ta yi tsaye tana mai ci gaba da kallona, wannan karon da ɗan tsoro a tattare da ita.
Ganin ba za ta iya ƙarasowar ba na mayar da dubana ga mahaifin nata cikin bayar da umarni na ce “maida siffarka daidai shekarunka” idonsa cike da nadama ya dawo normal don a zahiri bai wani tsufa ba.
Na miƙe tsaye ina mai kallon dubban mutanen da ke wurin na ce “daga rana irin ta yau,duk wanda aka kama yana gudanar da tsafi ba tare da neman izini ba,za a kashe shi yayin da kuma iyalansa za su zama bayin Masarauta.Wannan dokar za ta soma ne daga yau,dakaru ku ɗauki wannan matsafin ku kai shi kurkuku sannan ku je ku kwaso iyalansa ku maido su nan” ina gama faɗar haka na dubi Nelson shi kuma ya buga wata guduma kafin kuma ya ja ragamar tafiyata zuwa wani wurin.
Wani sashe ne mai ɗauke da symbol na tsafi da kuma wasu hotuna masu motsin rai.Sarki Alfanso na ganina ya yi saurin tashi cikin iska ya zo ya tsaya gabana yana mai cewa “ya za ka yanke wannan hukunci? Shin ba ka san cewa matsafa sun fi kowa daraja a wannan Daular ba? In an kashe su ta yaya za mu haɗa ƙarfin ikon da za mu tunkari abokan hamayya?”
Na yi wani guntun murmushi kafin na yi masa raɗa a kunne,ya ja numfashi tare da yin baya ya zauna .“Ka tabbata?” ya tambaye ni,na jinjina masa kai.Sai ya dubi Nelson ya ce “ka yi wa Yarima rakiya zuwa sashensa, sannan ka yi masa duk wani abu da ya kamata”
“An gama shugaba!” Nelson ya amsa tare da juyawa na take masa baya muka fito.Muna tafe muna hira har muka isa sashen nawa,shi ya taimaka mini na rage kayan jikina kafin kuma na zauna shi kuma ya fita.Can ba da jimawa ba baiwa Izzatu ta shigo hannunta ɗauke da wani ɗan madaidaicin baho,ƙasa ta ajiye shi kusa da ƙafafuna tana mai cewa “ranka shi daɗe za a yi ma wankin ƙafa ne” ba tare da na ce mata komai ba na ɗauki ƙafafun nawa na saka cikin ruwan sai na ga kamar tana jin tsoron saka hannun nata a ruwan ta wanke mini ƙafafun ba tare da na san dalili ba.
“Ni zan wanke da kaina?” na samu bakina da furtawa,da sauri ta girgiza kai ta ce “a'a ranka shi daɗe” sai kuma ta ɗago ta dube ni da manyan idonta masu kamar hasken gold har ta motsa baki kamar za ta yi magana sai kuma na ga yi shiru ta saka hannun nata cikin ruwan ta fara motsa su kamar mai yin wasa kafin na je ta kama tafin ƙafata.Wani yammm na ji haɗi da tsirgawar wani abu tun daga babban yatsana har tsakar kaina,yayin da kuma zuciyata ta soma matsanancin dokawa kamar wanda yayi gudun fanfalaƙi,babu shiri na ja fatun idona na rufe.Can kuma na tsinkayi muryartar na cewa “na ji daɗin hukuncin da ka yanke ranka shi daɗe,hakan da ka yi sai yasa na ji a raina wata rana mafarkina zai zama gaskiya”
A hankali na ɗan ware idona ina kallon yadda take murmushi har dimple ɗinta na lotsawa ,yadda kuma ta ci gaba da wanke ƙafafun ya kusa saka ni na suma don har wani tausa mini ƙafafun take tana cuɗa su kamar mai yi mini susa.Da wani bala'in sauri na ciro ƙafafun nawa sama wanda hakan ya haifar da faltsar ruwan suka shigar mata ido ,ta saki wani irin ihu tana kuka kamar wata yarinyar goye ni kuma na saki baki ina kallonta kamar na sheƙe da dariya.....
Waɗanda ba su da hali su tura 300 ,masu shi 500 hajiyoyi kuma 1k🌚 via 2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank DM +22795045822
[18/12 13:06] MRS SADAUKI: *INUWAR ALJAN*👻
```LoVe aNd HoRrOr story```👽
By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI💫✍️}
*SADAUKARWA:* Ga Rachida Mamar ƴan biyu, alherin Allah ya luluɓe ki . Ubangijin rahama ya kula da lamurranki👏🏻
*FCWA*☀️
________________________
08
A hankali na miƙe na yi tsaye gabanta sai na ga na kere ta tsayi sosai.Fuskarta na tallabo tare da gwale idonta na kai bakina ina bushe mata ruwan,sai ta ɗan ware idon alamun tana son ganin ko ya fita kafin ta ƙara rufe su gam tana yarfa hannu.Wani irin tausayi ta bani sai na ga kamar ƙanwata ce Joyel wannan yasa na ƙara mayar da hankali wurin bushe mata idon,sai kuma reshe ya juye da mujiya ta yi mini wani ƙwaƙwaran riƙo wanda ya kusan sumar da ni don kusan jikinta duk yana kan nawa.Wanda kuma shi ne karon farko da na taɓa samun kusanci da wata mace wacce ba muharamata ba.
Da sauri na ɗan ture ta saboda sam ba zan juri lantarki da nake jin yana jana ba,ita kuwa da wani mugun gudu ta nufi toilet har dogon mayafinta na faɗuwa wanda ya bani damar ganin baƙar sumarta wacce aka yi wa saƙar kitso .Ina nan tsaye nake jin ƙarar zubar ruwa,sama da minti biyar amma ta ƙi fitowa sai na ji kuma na damu a hankali kamar mai tsoron taka ƙasa na je na buɗe ƙofar.Cak na yi tsaye kamar wanda aka zubawa ruwa masu mugun sanyi ,yayin da ita kuma ta ƙara sunne kai tana wasa da yatsun hannunta.Cikin abin da bai fi sakan biyar ba na ƙarewa zubin halittar kallo ta saman jiƙaƙiyar rigarta wacce ta kwanta luf jikinta ta lafe,dakyar na iya yin baya na koma na duƙa na ɗauko mata mayafin nata wanda na yi imani rashinsa ne ya hana ta fitowa.
Ban ƙara shiga toilet ɗin ba,na dai miƙa mata shi ni kuma ina daga waje.“Ungo ki saka” na faɗa cikin wani irin sauti wanda ya fito daga ƙasan zuciyata ji nake kamar ina son kare mata wata daraja ce wacce ni kaina ban san dalili ba.
Ban sani ba ko har zuwa yanzu ba ta ɗago kan nata ba ne wannan yasa ta ɗan haɗa da hannuna ko mene ne,amma haka nake kyauta zato.Da sauri na sakar mata shi na nufi kujera na je na zauna,zuciyata na ɗan dokawa ta fito sululu kamar kazar da ƙwai ya fashewa a ciki.
Fuskarta nake son gani wannan yasa na ce “sabulun ya fita?”
Murya kamar ta yaro mai koyon magana ta ce “ba sabulu ba ne sinadarin tattalin lafiyar ƙafafu ne” sai kuma ta kai gefen mayafinta ta goge ƙwalla.
Raina ne na ji babu daɗi na ce “zo zauna bari na fita na ga Nelson ko zai samu wanda zai duba miki idon” da wani irin sauri ta ɗago tana girgiza kai ta ce “ka rufa mini asiri ni ɗin baiwa ce kawai,in na je gida Kakata za ta duba mini ita ɗin likitar gargajiya ce”
Cike da jin haushin kaina na ce “ok” sai ta zo ta ɗauki bahon ta fice,yayin da ni kuma na shiga jan tsuki ina jin wani irin takaici na rufe ni amma Nelson na shigowa sai na wani manta da wata baiwa Izzatu.
Masarauta muka zagaya Nelson na nuna mini komai da ke cikinta da kuma yadda ake gudanar da lamurra har muka zo kurkuku.Nelson ya ce “wannan shi ne kurkukun sirri wanda ake ɓoye wasu daga cikin matsafan da ake shakku akan tsafinsu ” yana furucin ne tare da kamo hannuna yasa wuƙa ya tsaga shi,jini ya soma zuba sai ya ɗora shi jikin ƙofar yana mai ci gaba da cewa “manyan Aljanai ne suka tsafe ƙofar nan ta yadda babu wanda zai iya buɗe ƙofar nan sai jinin mutum uku,na farko mahaifinka na biyun kuma mahaifina sai kuma kai”
Ba tare da na ce komai ba na ratsa baƙar ƙofar wacce ba irin normal ƙofa ba ce,Nelson ya take mini baya.Kejin farko idona ya fara sauka,wata mata ce fara sol idonta na tsiyayar da ruwan hawaye yayin da kuma gundulalun yatsunta ke share su.Muna haɗa ido da ita ta wani zabura irin kamar Kare ya ga mutum yana son cizonsa,da ido kawai na kalli Nelson ya bani jawabinta.
“Matar matsafin nan ce ta ɗazu,an samu nasarar cabko ta ne a wani dare da bokayen Masarauta suka gano ita ce matsafiya ta farko da ta fara yin nasarar gurɓata ruwan da mutane ke sha ta silar haka ne adadin makafi ya yawaita a wannan Daular ”
Raina ne na ji yana azalzala sai na ce “kenan ita ce ta haifi Albino girl ɗin nan?”
“Eh ƴarta ce!” ya bani amsa.
Na ce “me ake jira to da ba a kashe ta ba?”
“Lokaci na zuwa”
Tafin hannuna na ji yana motsi wanda ko tantama babu tururuwa ce ke fitowa,ƙwaya biyu na jefa mata cikin kejin suka fara cizonta ta soma gurnanin wahala.Sai kuma muka yi gaba inda na samu wani tsoho mai ɗauke da ƙusumbi wanda kuma ba komai ne cikinsa ba sai macizan tsafinsa.
“Shi kuma wannan fa?” na tambaya.
“Shi ne farkon wanda ya taɓa shiga wannan kurkukun,shi ne ya yi silar ƙetarar da sarauniya Janaki daga wannan Daular zuwa wata ƙasar ya kuma rufe duk wata ƙofa da za ta sa ta ƙara shigowa nan saboda gallazawa sarkinmu”
Da ido na tsure shi nan take na fahimci shi ne bafaɗen wancan Sarkin mahaifin Ummana,na yunƙura zan kashe shi amma Nelson ya dakatar da ni ya rarrashe ni sannan muka fito.
Ko da dare yayi zama na musamman muka yi ni da sarki Alfanso wanda har zuwa wannan lokacin ban furta masa kalmar da ke nuni shi ne mahaifina ba.Bayan mun gama cin abinci muka tattauna game da abin da na gani a Masarauta kafin kuma mu yi sallama kowa ya tafi sashensa.
Cikin kayan bacci na alfarma na shirya ,na rage hasken ɗaki kafin na jawo littafin sirrina.A daidai page ɗin da na