MAFARKI Love and Horror Story By Mrs Sadauki.txt

Author :  Mrs Sadauki Category :  Hausa Read

Chapter   8 / 18

21K to 24K   out of 53.5K words

hirami ja.Tsadadiyar agogo ya ɗaura a hannun dama,ya saka takalmi ƙafa ciki irin rigarsa wani turaren ya ƙara feshe jikinsa da gemu kafin ya ɗora farin gilashi ya sauko ƙasa.

A falo ya tarar da Ammy tana baiwa Rashida abinci,kusa da ita ya je ya tofa mata addu'a kafin ya yi wa Ammy sallama ya tafi.Tuni kuwa an wanke motarsa,ya shiga ya zauna bayan ya yi addu'a yana shirin tuƙawa Ammy ta fito tana tsayar da shi .
Ta ƙaraso tana mai cewa “ga key ɗin motar Deeja ka kai mata” yadda ta game fuska babu hanyar yi mata gardama yasa shi ya karɓa kafin ya wuce.

Ko da ya isa makaranta ƙarfe tara saura,sai da ya fara zuwa suka gaisa shi da malam Hafiz kafin ya je ya buɗe keɓaɓen ajin da yake tara malaman dukkan makarantar in yana son yin magana da su wanda su kuma ɗalibai suke yi wa lakaɓi da ajin hutun malamai.

Yana buɗewa ya ga wani baƙin abu yashe a ƙasa,ya duƙa ya dauƙa sai ya ga niƙafi ce.Da mamakin ta ya aka yi ta zo nan ya je ya ƙarasa ciki,shaf ya manta da an kawo masa Khadeeja har na cikin babu lafiya.Cikin wata jakarsa ya cilla niƙafin sannan ya soma bincike har ya nemo littafin da yake so.


★KHADEEJA

Ni ɗaya na buɗe alƙur'ani ina yin hadda,ban damu ba sam da ƙin zuwa a koyar da ni don ni ban ga wani aibun yin haka ba.Mujahidah kam an tafi ana ta yi mata gyara,sauran ɗaliban ma haka.A hankali na miƙe saboda yadda na ji zuciyata na tashi,bakin ƙofa na fito na tofar da yawu sai dai aka yi rashin sa'a suka sauka kan rigar Sheikh Rayyadeen wanda yake dab da ya shigo ajin,sam ban gansa ba .Na waro ido a tsorace ina kallon yadda ya wani ja burki yana kallon inda yawun nawa suka sauka......


Normal group 300, VIP 500 via
2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank

DM +22795045822

🚫 Waɗanda suka yi payment su yi mini magana na saka su group Please
[16/12 07:55] MRS SADAUKI: *MAFARKI*👁️🦋🦋🦋
🦋🦋🦋
🦋🦋
Mallakar : 🦋
Chamsiya Laouali Rabo
```MRS SADAUKI 💫✍️```

08

Dukkan illahirin jikina rawa yake,yadda Sheikh Rayyadeen ya wani haɗe fuska kai ka ce bai taɓa yin dariya ba.

“Biyo ni ” ya faɗa cikin tsananin fushi kafin ya juya,kamar zan faɗuwa haka na take masa baya har zuwa ajin malamai.Ya buɗe ya shiga ,kamar ba zan bisa ba sai kuma na ɗan shiga tare da tsayawa bakin ƙofa.

“Ban san wane sheɗani ne a kanki ba da har yake yi miki huɗuba ki yi mini abubuwa iri-iri,to ko ma uban waye ya tsaya iya kanki saboda in kuka shigo gonata sai na yi mugun baki mamaki.Ban son rashin kunya da tsaurin ido,duk wanda ya yi mini ɗaya daga cikinsu zane shi nake yi” ya ida furicin tare da juyowa rai ɓace hannunsa na gani riƙe da bulala.

Ko kaɗan ban taɓa tunanin zai doke ni ba,shauɗar da ya yi mini ita ta maido ni daga duniyar mamakin da na tsunduma.Na ƙara tare da sosa wurin,cike da masifar da ban san yana da ita ba ya ce “wato don kin ma raina ni ina yi miki magana hankalinki na wani wuri ,zaunaaa ” ya ƙarashe tare da sake shaɗa mini bulalar a karo na biyu.Babu shiri na zube kan gwiwaina,ya ɗaga zai yi mini ta uku na yi saurin kamo ƙafarsa cikin kuka na ce “don Allah Sheikh ka yi haƙuri ba zan sake ba,amma kar ka doke ni ban so” hannuwan nawa da na riƙe masa ƙafa ya shaɗe na sake shi da mugun sauri ina jin wani zafi yayin da shi kuma ya wani ja da baya yana jan numfashi kamar zai mutu.Ba tare da ya bani damar fita ba na tashi a guje na bar ajin na nufi namu inda muke karatu.Kamar an jefo ni haka na faɗa ciki ina matsanancin kuka, Mujahida da ke kusa da ni ce take cewa “a kullum ina faɗa miki ki rage wannan shagwaɓar taki nan makaranta ce ba komai ne za ki nuna ke ƴar Daddy ce ba amma ba ki saurarena.Waɗanda ke kusan window sun ga duk abin da ya faru,tun bayan fitarki ake cece-kuce don ma malam Hafiz ya shigo ya tsawatar ne da ƙila sun ta yi miki dariya”

Kanzil ban ce mata ba don baƙin ciki,ita da ya kamata ta yi rarrashina amma ta zo tana yi mini surutu.Na ɗauki kamar minti biyar kafin na ji sallamarsa,duk aka amsa masa kuwa.Gudun kar na yi wani laifin na gyara zamana ina shafar ido,tambayoyi ya fara nan uwar iya yi Sadiya ta shaida masa ni kaɗai ce na ƙi zuwa a koyar da ni.

Idonsa masu masifar tsoratar ni ya zubo mini,kamar daga sama na ji ya ce “zo ” kasa motsi na yi don duk a tunanina dukana zai yi.Duk ƴan ajin suka zubo mini ido,ina jin Mujahida na salalami “innalillahi!”

Wani abin mamaki yana cewa na je ɗin ya ɗauke idonsa a kaina ya soma buɗe alƙur'ani.Zuciyata na ɗan dokawa na tashi ,kamar mai koyon tafiya haka na ƙarasa kusa da babban teburin gabansa na ja na tsaya.



“Me yasa ba ki son yin karatun Alkur'ani? Ko ba ki iya komai ba kawai turo ki aka yi aji na gaba?” ya tambaye ni tare da ɗago kai,ni kuwa kayan jikinsa nake kallo yadda ya wani cire rigar sama kawai don na tofa masa yawu.

“Kwashi kayanki ki koma tsohon ajinku ” ya faɗa a hankali amma kana iya jin feshin wutar da zuciyarsa ke yi.

Sai a lokacin na yi magana “ka yi haƙuri na iya karatun ne”

Hannuwansa ya game wuri guda ya ɗora haɓarsa tare da tsura mini na mujiya kafin ya ce “ina jinki Malama koyar da ni”

Da sauri na sunne kai ina murmushi don na fahimci me yake nufi.Ya turo mini Alkur'ani wanda shi ne da kansa ya buɗe mini shafin,idona cikin nasa na jawo alƙur'anin tare da juyo shi gabana na soma karantawa cikin ƙira'ar da Daddyna ya koyar ni,sam ban taɓa sanin ainahinta ta Sheikh Rayyadeen ɗin ce ba saboda in banda cikin sallah ban taɓa jin yana koyar da karatu ba.


Daga can baya na ji muryar A'isha tana cewa “ma sha Allah! Yau dai mun ji wacce ta iya bin ƙira'ar Sheikh ” duk sai wasu suka shiga yin murmushi mai sauti.


Ni kuwa shi na kalla sai na ga ya ƙara haɗe rai kuma ko arzikin kallo ban ƙara samu ba haka ya dinga yi mini binciken karatun kamar wani makaho har ya kammala ya ce na je na zauna.

Ƙin tafiya na yi na sake cewa “don Allah malam ka yi haƙuri ka bar fushi da ni, wallahi muddin ka ci gaba da yi to ba zan samu sukuni ba har abinci ba zan ci ba”

Yadda duk mutane suka zubo masa ido suna kallo yasa shi cewa “na ji to tafi ki zauna”

Na ɗan yi murmushi na ce “da gaske ka haƙura?” ya jinjina mini kai cike da murna na je na koma wurina na ci gaba da kallonsa cike da so.Shi kuwa Sheikh Rayyadeen karatu ya soma koyar mana, lokaci zuwa lokaci haka nake tsintar idonsa cikin nawa a haka har aka fita shan iska.

Muna fita na rungume Mujahida tare da bata labarin yadda muka kwashi adashen tsiya ni da Sheikh bayan na tofa masa yawu daga ƙarshe na ƙara da cewa “wannan dukan da ya yi mini sosai na ji daɗinsa,kin ga yau zai wuni da tunanin abin”

Ta ja tsuki tana mai cewa “ni dai wuce mu tafi mu yi sauri mu dawo kar lokacin dawowa aji ya yi mu kuma muna can”

“Ina za mu tafi?” na tambaye ta,sai ta waro ido tana mai cewa “asibitin mahaukata ko kin manta?” ina shirin yin magana wani abu ya ɗauki hankalina yadda Sadiya da ƙawayenta suka tunkari aji alhalin Sheikh na ciki.

Da wani mugun sauri na ja hannun Mujahida muka zagaya bayan aji don ta can ne zan fi jin abin da za su yi wurin nasa.
Kunne na kasa ina saurare,ina jin lokacin da Sheikh ya ce “ina jinku me kuka zo yi?”

Kame-kame suka fara kafin ɗaya ta ce “dama...dama mun zo ne mu sanar da kai ɗaya daga cikinmu ce ke sonka shi ne kawai”

Na yi tunanin zai balbale su da masifa,zuciyata har wani bugawa ta yi jin ya ce “ita wacce ke son nawa ba ta da baki ne sai ke? ”

“A'a malam ba haka ba ne kunya take ji”

“To ku fita ku bani wuri” ya faɗa .

“Sadiya ki faɗa masa mana” na ƙara jin wata ta faɗa ,ƙiri-ƙiri Sadiya ta canza harshe zuwa larabci ta shaidawa Sheikh Rayyadeen tana sonsa har da su cewa in bai aure ta ba mutuwa za ta yi.


Ban san matakin fushi da kuma tashin hankalin da na tsinci kaina ba,sai da na ji ƙusoshin kaina na kwancewa yayin da wani abu ya soma yi mini motsi da mugun ƙarfi na ƙwala wata razananiyar ƙara wacce ta karaɗe dukkan makarantar.Duk wata bishiya da ke da kwai sai da ta kaɗa cike da razani, wannan karon hankalina bai gushe ba duka ina jin lokacin da Sheikh ya leƙo ta window yana tambayar Mujahida wacce ke faman riƙona.

Can kuma suka zagayo su duka huɗun,cikin bayar da umarni yasa aka kai ni ajin malamai.Karatu ya soma yi mini su kuma suna tsaye a kaina, Mujahida kawai ce ta riƙe ni.Kamar zan mutuwa haka nake ji,shigowar malam Ibrahim ce yasa sauran suka fita iya ƙawata ce kawai ta tsaya.

Wani abu ya shaƙa mini a hanci wanda ya kusa kai ni lahira ban shirya ba,wani irin ƙarfi ne ya zo mini na turo Mujahida zan gudu.Sheikh Rayyadeen ya riƙo ni da hannu ɗaya tare da mini wani riƙaƙen kamu wanda na kasa kubcewa,ci gaba yayi da karatun yana bugun tsakiyar bayana da hannunsa.

Kamar ana ruwa haka na soma jin wani sanyi na rufe ni,yayin da wani abu mai zafi da ke cikin jikina ke yin ƙasa.Kamar wata ƴarsa haka yake ganin Khadeeja,shi sam bai ma taɓa ganinta matsayin cikakkiyar budurwa ba duk in Ammy na yi masa zancen ya aure ta har mamaki yake ji.


“Khadeejatu?” muryar malam Ibrahim ta daki kunnena, lokacin tuni na ida samun cikakken hankalina.A hankali na sa hannuna kan na Sheikh Rayyadeen don cire nasa da yayi mini mugun riƙo don har wani zafi nake ji.Sai da ya kalli tsakiyar idona kafin ya sake ni,a hankali na miƙe kamar zan faɗi Mujahida ma ta tashi tana mai kamo hannuna.


“Ya jikin naki?” ya sake tambaya ta,ban basa amsa ba sai ma ƙeya da na sa na fice.

Sheikh Rayyadeen ji ya yi kamar ya haɗiye zuciya ya mutu don takaicin abin da ta yi wa malam Ibrahim shi kuwa da wani irin kallon so ya bi bayanta har ta fice.
Yana maido hankalinsa ga Sheikh ya sha jinin jikinsa saboda irin mugun kallon da ya ga yana yi masa.


“Khadeeja har yanzu yarinya ce,sai a hankali ” ya furta don ya ga da alamu ran Sheikh ɗin ya ɓace yadda ta tafi ba ta yi musu sallama ba haka kuma babu godiya.

“Kana iya tafiya” Sheikh ya faɗa a takaice.

Malam Ibrahim ya ce “don Allah ina neman alfarma ne,a yi haƙuri da ni son Khadeeja ya daɗe a zuciyata ne shi yasa na kasa controling kaina,na san haramun ne a bisa dokar makaranta yin soyayya da ɗaliba muddin dai ba a wajen nan ba ne za ku yi ta.Amma ina so ni dai a bani wannan damar zan dinga koyawa Khadeeja karatu duk in lokacin shan iska ya yi ta haka ne ƙila za ta yarda da ina sonta”


Tun da ya fara zuba Sheikh ya tsura masa na mujiya har ya dire,da sauri ya juyar da kai yana mai cewa “ka tambayi mahaifinta ni malaminta ne kawai,sannan wurin shugaban makaranta ya kamata ka nemi izini ba wurina ba”

Jikin malam Ibrahim ya yi sanyi kafin ya ce “to in sha Allah! ” sai ya juya ya fita, Sheikh ya bisa da wani mugun kallo kafin shi ma ya fita don lokaci ma tuni yayi.


Muna fita direct aji muka nufa,yau ɗin ma haka mutane suka yi mini caaa suna kallo yayin da Sadiya ke hararena kamar idonta za su faɗo.Samun kaina na yi da mayar mata da martani tare da jan tsuki,na furta “marar aji kawai” yadda ta waro ido shi ya tabbatar mini ta canki abin da bakina ya furta.Ni kuma raina sai yayi fari ƙal kafin na ɗauki ruwa na leƙa ta window na wanke fuskata juyowar ga da zan yi muka yi ido huɗu da Sheikh.Da wani mugun sauri na je wurina na zauna,shi kuma rubutu ya soma yi jikin babban allon aji kafin ya soma yi mana bayani kan tarihin rayuwar Annabi.Tsawon lokaci kafin ya tsaya a wani wurin sakamakon lokacin tashi da ya yi,haka aka fara fita amma ni da ke a gaba ko motsi ban yi ba.

“Tashi mu tafi Malama ni nan yunwa nake ji ban ci komai ba” cewar Mujahida.

Na ce “to sannu acici uwar sakawa ciki abinci,ni me ki ga na ci?”

“Na tafi don wallahi ba a gabana za ki sake yin wata tijarar ba” ta furta tare da ficewa,haka kowa ya fita aka bar ni a zaune ina kallon Sheikh Rayyadeen da ke faman latsa waya da dukkan alamu bai ma san ina nan ba.

Murmushi na ga yana yi wanda ya fito tsantsar kyawunsa,muryar Ammynsa na ji tana cewa “yau yarona ya yi kewata har haka ne shi yasa ya kira ni video call?”

A shagwaɓe ya ce “Ammy please kafin na iso a haɗa mini ruwan wanka kuma a sake gyara ɗakina don yau ina son na huta sosai”

Ta ce “tuni fa Saude ta yi komai,sai ka zo”

Ya shafi sajensa ya ce “ina jin yunwa kuma”

“Oh! Ni Khadi Allah ya nuna mini dai ranar da za ka kawo mai yi ma girki don ni na kusa gajiya.Yawwa ka baiwa Khadeeja key ɗin motarta ”

Ya dafe kai ya ce “ciwon kai dai,don Allah Ammy ki bar mini maganarta zuciyata ta tafasa take yi.Yanzu dai gani nan tafe yanzu in sha Allah ” yana gama faɗa haka ya kashe kiran,ni kuma da mugun sauri na yi kwance jikin table ina mai rera kuka a hankali.



Inuwarsa da na gani a tsaye yasa na fahimci ya farga da mutum a ajin.“Ke?” ya furta,a hankali na ɗan ɗago kai na dube shi.Ya haɗe fuska tamau kamar ba shi ba ne ya gama zuba shagwaɓa,“me kike yi nan?”

Ya tambaye ni,wani haushi ya rufe ni wato bai ma ga kukan da nake yi ba ballantana ya rarrashe ni.Ban ce masa komai ba,shi ma bai ƙara ba sai key ɗin motata da ya ajiye mini ya fice na bi bayansa da kallon mamaki kafin na tashi da mugun sauri na fita.


Sadiya na tsinkayo can nesa kusan inda yake ajiye mota,da sauri na ga ta nufe shi tare da karɓar jakarsa ta kai masa har mota.Bayan ya buɗe ya shiga ya zauna,ita ta yi tsaye ta riƙe murfi yayin da kuma suke yin maganar da ban san me suke cewa ba.Gudun kar baƙin ciki ya kashe ni na nufi masjid ɗin mata,ai kuwa a can na samu Mujahida tana waya ita da Yaya Hamza ko da muka haɗa ido taɓe baki ta yi tare da juya mini baya.


“Taso mu tafi ga key ɗin motata ya bani” na furta,ta juyo da sauri kafin ta kashe wayar ta ce “ da gaske?”

Nuna mata na yi,sai ta miƙe da sauri tana murmushi muka fito.Bakin hanya muka tsaya muka samu abin hawa ,duk da babu nisa haka muka je a taxi ɗin.Muna sauka kuwa na hangi motata,sai kuma na yi mamakin ta yaya aka yi har yanzu Sheikh bai zo ba.


Kasancewar a hanya duk na baiwa Mujahida abin da ya faru sai cewa ta yi “ko ya tafi kai matsiyaciyar nan ?”

Na yi shiru kafin na ce “ban iya na sani,amma tana yi yiwa motarsa na cikin gida”

Mujahida ta ce “to sai dai in ke ɗaya za ki je amma wallahi ni ba zan shiga ba” haka na je na gaishe da mai tsaron get na shaida masa motar da ke ƙofa tawa ce tun jiya na bar ta a nan sannan kuma ina son ganin Aliya saboda yau ba ta je makaranta ba.Ƙofar ya buɗe mini na shiga,sai dai a farfajiyar gidan ma babu motar Sheikh.Maimakon na juyo a'a sai wata zuciyar ta ce mini na shiga na gaida Ammy,ina dab da shiga falon na soma jin hayaniya da alamun kuma faɗa suke yi.

“Ba zan taɓa tafiya na maido Khadi ba saboda ba ni ne na ce ta tafi ba,ɗanta ne ya kwashe ta suka koma can saboda ya nuna mini isasshe ne shi sannan ya fi son mahaifiyarsa da ni.Ke kuma da ba ki kishin mijinki shi ne kike goya musu baya” murya babban mutum ce wacce nake kyautata zaton mahaifin su Sheikh ne.

“Abban yara sam wannan ba adalci ba ne,yadda Maa ke da haƙi a kanka mu ma matanka haka.Amma babu komai ni ma gidanka zan bar maka sai uwa da ɗa su zauna su kaɗai”

“Mahmuda in dai ni na haife ka to kar ka dakatar da Ramma ta yi ta tafiya,ai ba su kaɗai ba ne mata ni nan zan auro maka yarinyar ɗanyar sharrr” wannan karon kuma muryar wannan tsohuwar ce na ji wacce suke kira da Grand-Maa.

Da sauri na yi baya jin kamar za a taho,ina fita na buɗe mota muka shiga ni da Mujahida sai da muka hau titi ne ta tambaye ba'asi na kuwa labarta mata kafin na ce “kakarsu Sheikh ba ƙaramar sheɗaniya ba ce”

“Yanzu asibitin za mu je?”

“Eh saboda ina son ganin mahaukaciyar nan,ina ji a raina kamar akwai abin

8 / 18