MAFARKI Love and Horror Story By Mrs Sadauki.txt

Author :  Mrs Sadauki Category :  Hausa Read

Chapter   12 / 18

33K to 36K   out of 53.5K words

yadda ake gudanar da baƙin tsafi da wasu dangin asirai.Yadda ake yin hadaya da jinin bil'adama,da kuma yadda ake ƙulla harƙalla tsakanin jinsi biyu.Cikin firgici na farka jikina duk ya jiƙe da gumi,idona kan littafin da na ɓoye a cikin kayana ya sauka amma a yanzu kan table na gansa kuma a buɗe.Da na ɗauke shi sai na ga sak irin abin da na gani cikin mafarki ne,wato ya buɗe kansa da kansa yana karanto mini labarin da ke ƙumshe a ciki ne.Waje na fita na yi rame can bayan ɗaki na binne shi da tunanin hakan shi ne kawai mafita,ina komawa ɗaki na sake tarar da littafin ya buɗe shafi na gaba.Zaman ƴan bori na yi tare da yin tagumi,wata murya na ji tana cewa “littafi ya zaɓi wanda zai karanta shi,tun da kuma ya zaɓe ka to har abada ba zai taɓa barinka ba” kamar wani mahaukaci haka na matsa kusa da shi na ce “to na ji ni ne ka zaɓa amma sai ka bari har lokacin da na buƙaci karanta ka ni ne da kaina zan ɗauko ka na karanta don haka yanzu ka koma ma'ajiyarka ta farko” abin mamaki ina gama rufe bakina na ga ya ɓata kamar walƙiya yayin da kuma jakar kayana ta yi wani motsi tana rawa alamun dai ya shiga ciki ya zauna.

Kan shimfiɗata na kwanta na shiga yin wasiƙar jaki,ƴan magana na cewa bacci ɓarawo ne to shi ne yayi nasara sace ni a karo na biyu sai dai sam ban yi mugayen mafarkai ba a wannan karon.
Ina tsaka da yin baccin da ban samu na yi ba na ji muryar Abba kaina yana kuma jijiga ni alamun na tashi,ina buɗe ido na ga sai yaƙar haƙora yake kamar gonar auduga.

“David tashi! Tashi ka ga waɗanda suka zo gidanmu.Taso suna son ganinka” Abba ya faɗa cikin murna,yadda ya riƙe mini hannu gam shi ya sa na tashi don dole na biyo bayansa.A cikin rumfarmu ta kara na hangi dattawan garinmu a zaune ko wannensu ya ƙure ƙofar ɗakina da kallo,cike da mamakin abin da ya kawo su na ƙarasa na gaishe su.Bakunansu har rawa suke wurin amsawa kafin ɗaya daga cikinsu ya ce “Jakob ka ɗan bamu wuri muna son yin magana da ɗanmu” Abba ya washe baki yana kallona kafin ya ce “David wannan shi ne pasto ɗin Cochinmu ka saurare shi da kyau,su kuma waɗannan ai ka san su tun da kana shiga gari” yana gama faɗa ya tafi.

Tambayoyi ne suka fara yi mini waɗanda sam ban san mene ne alaƙata da su ba,amma da na ajiye hankali sai nake ganin kamar sun san na taɓa littafin nan na sirri.Shiru kawai na yi ban iya ce musu komai ba,da suka gaji don kansu suka yi wa Abba sallama suka yi tafiyarsu.



Ina shirin shiga ɗaki Ummah ta fito kamar wata munafuka ta ce “Davido wacce maganar ce waɗan can mutanen suka yi da kai?” kallonta na yi da kyau,sai na ga duk wasu alamomin rashin gaskiya sun bayyana a fuskarta.

“Babu komai Ummah” na bata amsa tare da yin gaba.A tsakiyar ɗakina na yi tsaye ina kallon akwatin kayana ina son ɗauko littafin sirri ina kuma jin tsoron kar wani ya shigo ya ganni da shi.
Daga nan inda nake a tsaye na soma jin wani irin yanayi kamar kasala kamar gajiya,idona na ɗan rufewa na soma jan ƙafata na je na kwanta kan shimfiɗata.Ba bacci nake ba kuma ba idona biyu ba,ina cikin wani lamari ne mai wuyar fassarawa.Adaidai nan wata kyakkyawar mace ta bayyana a gare ni cikin shigar fararen kaya,tsawon lokaci tana yi mini wani kallo kafin ta zumbule suturarta nan siffar jikinta ta bayyana a gare ni,haka na ci gaba da kallonta kafin ta tako zuwa gare ni.Abubuwan da suka faru a tsakaninmu,ba zan iya furta su ba saboda yadda ta shagaltar da ni ta saka ni cikin wani hali da babu shi a duniyata ta zahiri.Sai bayan ta gama mu'amalantata sannan ta bi ta jikin bango ta fice daidai nan kuma control ɗin kaina ya dawo.Yadda na samu duk na ɓata jikina shi ya tursasa mini zuwa na cika bokiti na yi wanka,bayan na fito na ɗauki tsintsiya na share ɗakina wanda kuma hakan sam ba tabi'ata ba ce Jowel ce ke yi mini gyaran ɗaki amma yau dai haka na ji ina ra'ayin yin kayana.


Ba tare da na yi wa kowa sallama ba na fice,wurin da muke haɗuwa na je a yau ni ne na zauna domin jiransu.Ina nan zaune sai ga wata tsohuwa ta zo wucewa,sunana ta ambata wanda kuma ba iyayena ne suka raɗa mini shi ba a'a hasali ma ba na wannan duniyar ne ba amma a hakan na fahimci sunana ne.


“Mikiya!” ta sake furtawa a karo na biyu,sai a lokacin kuma na saka idona cikin nata wanda hakan ya bani damar yin kutse a cikin ruhinta.Babbar matsafiya ce wacce ta laƙanci aikinta na bokanci da tsafi,ta kwashe kusan ƙarni biyu a doron duniya tana rayuwa ta hanyar fatalwar ruhinta.


“Ba sunana Mikiya ba! David ne sunana” na faɗa murya a ɗan dake.Ta yi wani murmushi wanda ya ida fito da sauran muguntarta ta ce “sai yaushe ne za ka yarda? Sai zuwa yaushe ne za ka ɗauki ƙaddararka a hannu? Kai Mikiya ce mai yi wa dukkan abin da ya tunkaro ka dirar sauri,kar ka hana ikonka yin aiki akan nauyin da ke kanka” ba tare da na fahimci abin da take nufi ba na ce “na ji na yarda! Za ki iya tafiya”

“Wannan salo naka ya burge ni sak irin jarumtar mahaifinka sarki Alfanso”tana gama faɗar haka ta ɓace cikin iska, maimakon na ɗauki ƙarshen furicinta da muhimmanci sai na watsar.Ina nan zaune sai abokaina suka zo a tare lokaci guda,yanayinsu kawai na duba na fahimci yau ba su fito da niyyar yin dako ba.

“Ina za ku je haka?” na tambaye su ba tare da na yi nauyin baki ba.

Isa ya bani amsa da “za mu je mu kai takardunmu ne ko Allah zai sa mu dace a ɗauke mu aiki ka ga shikenan sai mu huta da yin dako”

“Yaushe aka yanke wannan shawarar ba tare da sanina ba?” na faɗa ina jin wani iri alamun babu daɗi don duk abin da ɗaya zai yi to dole ya shawarci sauran.

“Saboda mun ga ba ka yi wani dogon karatu ba ne shi yasa,amma ba wai da wata manufa ba” Abdul ya faɗa .

“Okay!” shi ne abin da na faɗa kafin na miƙe na kama hanyar kasuwa,tafiya nake cike da ɓacin rai ina jin ya zama dole ma na yi karatun boko tun da har an fara yi mini gori sai dai ta ina zan fara ? Ban sani ba.Da isata kasuwa na soma yin dako cikin zafin rai,wanda sam ban san na yi aikin mai yawa ba da Alhajin ya zo biyana sai ya bani kuɗi na ban mamaki.Cike da murna na koma gida,sai kuma ta koma ciki tarar da mutane da na yi a tsakar gidanmu fuskokinsu cike da alhini haka na ratsa na isa gaban Ummah wacce ke ta gumurzun kuka.

“Ummah?” shi ne kawai abin da na iya cewa,ta ɗago kanta ta dube ni da idonta da suka yi mugun ja kafin kuma ta sake rushewa da wani kukan.

“Meke faruwa ne wai?” na sake tambaya,da hannu ta yi mini nuni da ɗaki haka na tunkari ɗakin zuciyata na yi mini matsanancin bugawa.Cak na yi tsaye ina kallon tashin hankalin da na ci karo da shi,gangar jikin Joy ce a kwance cikin ɗaki babu numfashi .Fuskarsa babu ido an cire su haka ma daidai wuyansa an yi masa wani rame da dukkan alamu wani abu aka cire daga jikinsa.


Ta maza na yi na ƙarasa na zube gwiwaina ƙasa tare da tallabo kansa,wani abu na ji ya caki idona mai bala'in zafi da raɗaɗi a dole ban shirya ba na rumtse ido gam.Kamar magiji haka aka nuno mini ta yadda aka yi abin ya faru da shi.Yana zaune cikin ajinsu aka aiko kiransa,bayan ya fito sai ya ga su Isa ne da Abdul.A mutumce suka gaisa kafin su ja hankalinsa sosai ta hanyar yi masa ƙaryar cewa ya zo ni ne ke nemansa cikin gaggawa .Suna fitowa daga cikin makaranta wata mota suka shiga da shi suka saka shi a tsakiya,suna tsaka da yin gudu suka shaƙa masa hodar bacci a haka suka isa wani gida inda suka yi masa kisan gilla,da farko wuyansa suka caka da wuƙa wanda zafi da raɗaɗi yasa ya dawo hayyacinsa kafin kuma su cire masa idanuwa duka biyun. Daidai nan kuma wasu mutane masu baƙaƙen kaya suka shigo suka zagaye Joy,wata hoda ce ɗaya daga cikinsu ya zuba a jikin Joy ɗin yana yin wasu kalamai waɗanda ba na wannan duniyar ba ne amma sarai na fahimce su.Nan take gawar Joy ta ɓata ta zo nan inda yake kwance a tsakiyar ɗaki,sai kuma na ga lokacin da Ummah ta shigo ɗakin da kuma yadda ta tsorata saboda cin karo da ta yi da wannan lukutar masifar.

Idona na buɗe waɗanda nake jin sun yi mini wani mugun nauyi da zafi,har wani yaji nake ji suna yi mini feshi. Jiki na ɗan rawa na miƙe tsaye da niyyar fita sai dai wani jiri ne na ji ya soma kwasa ta,da sauri na dafa bango ina jan numfashina da ke barazanar ɗaukewa gaba ɗaya.Amma da yake ina da ƙarfin hali haka na ƙoƙarta na fito ina rangaji,wata irin runguma Ummah ta zo ta yi mini tana mai kiran sunana tashin hankalin da nake tsinkayowa a cikin amonta kamar ma ya fi na mutuwar Joy.


Damtsena na ji shigar wani abu kamar mashi,amma ba shi ne ba yatsan Ummah ne.Wani furici take yi mai shige da wancan ɗin wanda ya kasance na ƙarnin baya sai dai wannan sam ban fahimta.Kamar yadda in an zuba wa wuta ruwa take mutuwa murus,to haka na ji duk zafin kaina da ɓacin raina sun sauka.Baya na ɗan yi ina kallon Ummah wacce take yi mini wani kallo ita ma,kafin cikin ɓacin rai ta ce “mene ne wannan Davido? Ina za ka je da wannan ɓacin ran? Wuce ka tafi ɗakinka,yanzun nan Abbanku zai zo”

‘Wace ce ke?’ ita ce tambayar da zuciyata ke son yi mata amma kamar wanda aka tsafe na kasa furtawa,ɗakina na koma na yi tsaye ina kallon akwatin kayana inda na ajiye littafin sirri.Ina son yin bincike a cikinsa sai dai shock ɗin mutuwar Joy ya ƙi barina dole na haƙura,babu jimawa kuwa Abba ya shigo ya kira ni da kansa.Gawar Joy muka ɗauka muka kai can gidan gawa kafin mu fara shirya yadda jana'izar za ta kasance don sai an yi bikin binne shi,domin yin haka kuma muna buƙatar kuɗi masu ɗan yawa .Na sayen akwatin gawa,da kuma abincin da mutane za su ci da kuma kuɗin da za a bai wa makaɗa da pastocin da za su yi masa addu'o'i.


Tun a hanyar komawa gida Abba ya ce mini “ David ya kake gani game da bikin binne Joy? Ka ga dai ni banda kuɗi kai ne za ka yi komai,kana ganin sai mun yi gayyata dayawa ko kuwa?”


Na dubi Abba cike da takaici na ce “kai ba ka damu da irin yadda ka samu gawar ɗanka ba a'a ta yadda za a rufe shi kake ? Abba ka cire ran zan bari a rufe Joy ba tare da na binciko su wane ne suka yi masa wannan kisan gillar ba suka raba shi da sassan gangar jikinsa”


Sake da baki Abba ke kallona kafin ya ce “wane irin sassan jiki kuma? Ciwon ciki ne fa ya kashe shi ko?”

Ni ma da mamakin na dube shi,kafin na yi wa kaina tambayar ‘ kenan shi Abba bai ga gawar Joy an cire mata ido ba?’ amma don sake tabbatarwa haka na buƙaci mu koma can mutuware.


Da muka je muka shiga ciki na buɗe gawar Joy tare da tsure Abba da ido kafin na ce “ka gani ko?”

“Me?” ya tambaye ni,“ba ka ga komai ba?” na tambaye shi ni ma.Ya ce “ka ga David mu je gida” ba tare da na ce komai ba na rufe gawar muka fito.Ko da muka dawo gida mun tarar da Joyel na yin kuka kamar ranta zai fita ,tana ganina ta zo ta faɗa jikina.Ban iya rarrashinta ba kawai na bar ta tana ta yin kukan har ta gaji don kanta ta je ta zube kan tabarma.Mutane sai shigowa suke yi suna taya mu jaje har cikin dare kuwa,sai da daren ya tsananta sannan ƙafa ta ɗaga.Na je na rufe ɗaki tare da shiga ɗakinsu Ummah na yi zaune kamar yadda su ma ɗin suke zaune in aka cire Joyel da ke bacci.

So nake mu haɗa ido da Ummah amma ta ƙi yarda da hakan,da na gaji don kaina na miƙe na fita.Sai da na watsa ruwa na ɗan ji sanyi kafin na shige ɗakina,bayan na rufe ƙofa na ɗauko littafin sirri na ajiye kan table.


A hankali ya soma buɗe kansa har aka zo a page ɗin da na tsaya,idona ya sauka kan rubutun da ya shafi nasabata.

“BABU WANDA ZAI IYA MALLAKAR LITTAFIN NAN SAI SARKI KO KUMA MAI SHIRIN ZAMA SARKI! DOMIN SANIN DALILI KA BUƊE PAGE TA GABA” shi ne abin da yake a rubuce, wannan karon da kaina na buɗe page ɗin ta gaba sai dai wayam take babu rubutun komai a cikinta haushi na ji kawai na rufe shi na mayar.

Na ja tsuki kafin na kwanta ina shirin lumshe idona na soma jin yanayin iskan ɗakin na canzawa.A nan take na fahimci ta zo,babu jimawa kuwa na soma jin ana shafar jikina tare da sarrafa ni kafin ta mu'amulance ni bayan nan sai na ji wata irin gajiya da ciwon jiki amma ban iya ko da motsi ba ne a haka bacci ya ɗauke ni.

Wannan karon a wata unguwar nakassu duniyar mafarkin tawa ta kai ni,ko ta ina makafi ne da kurame da guragu da duk wata irin nakasa.Cike da ƙyanƙyami nake ratsa wurin wanda yake cike da datti da ƙanzata iri-iri,daga bayana na ji an dafa ni.Na juyo da sauri nan na yi arba da wata yarinya wacce ba za ta wuce shekara goma ba a duniya ,fara ce tasss ban taɓa ganin mutum mai irin farinta ba.Gashin kanta kuma wani iri ne kamar na gingiya,idanuwanta blue ne masu ɗan girma duk da kuwa yadda take ta ƙoƙarin ƙanƙantar da su,laɓanta jajaye ne sirara.

“Ina ne nan?” na tambaye ta.

“Daular Alfanso !” ta bani amsa tare da miƙo mini wani ɗan itaciya wanda shi ma ban taɓa ganinsa ba,hannunta na bi da kallo wanda yake da datti duk laka ta ɓata shi .Na girgiza mata kai na ce “a'a ban ci”

“Ka karɓa dai za ka ji daɗinsa” ta faɗa tana yi mini dariya wacce ta bank damar ganin haƙoranta waɗanda suka sha banban da na mutane don kuwa ba farare ba ne a'a kamar chocolat haka suke da duhu amma wani abin mamaki sosai suka yi mata kyau ƙila don saboda kalar fatarta.Na kai hannu kenan zan karɓa na ji muryar Ummah “Davido?” kamar tsawa haka na ji sautin,da mugun sauri na tashi ina ware ido a kallon farko sai na ga Ummah da wata siffa kanta kamar na Tinkiya amma da na murje idona sai na ga ta dawo normal.


Kafin na kai ga cewa wani abu ta ce “ka tashi ka yi mini rakiya can mutuware ina son ganin gawar ɗana kafin a rufe shi”

Na ce “an samo kuɗin bikin jana'izar ne? ”

“Ka same ni a ƙofar gida” ta faɗa tare da ficewa,a dole na fita na yi wanka na zo na shirya.Sai da na shiga ɗakinsu,a zaune na hango Joyel ta rakuɓe kamar wata marainiya,tausayinta ne na ji ya ratsa ni amma ban iya yi mata magana ba na fice na samu Ummah a ƙofar gida.Gaishe ta na yi amma ba ta amsa ba,taxi na samo mana muka shiga.Har muka isa babu wanda ya yi magana,sai da na nuna takardar shaida sannan aka buɗe mana mutuwaren.Wani irin iska ne mai haɗe da hucin ruhika ya tarbe mu,da sauri muka kalli juna ni da Ummah kafin kuma mu ida shiga.

Gawar Joy na nuna mata,ta buɗe tana shafar fuskarsa.A yanayinta kawai na fahimci ita idonta suna gane mata abin da ni ma na gani a tattare da gawar saɓanin Abba.

“Je ka biya kuɗin wanka a zo a yi masa mu wuce da shi,ba zan bari ya ƙara kwana ɗaya ba a nan” Ummah ta faɗa .

Na ce “akwatin gawa fa? Ina za a samu?”

“Ka yi abin da na ce” ta faɗa cikin ƙaraji,wani irin tsoron Ummah ne na ji ya ɗarsar mini a ƙahon zuciya wanda ban taɓa jin makamancinsa ba,da sauri kuwa na je na nemi mai gadi na sanar da shi tare kuma da biyan kuɗi.

Wani matashin saurayi ne aka turo domin yi masa wankan,Ummah ta fita yayin da ni kuma na tsaya.Almakashi yasa ya yage suturar Joy sannan ya luluɓa masa wani zanen,ya ɗago da niyyar yi mini magana sai kuma na ga ya yi shiru tare da kafe ni da ido har sai da na tsargu na ce “Me?”

“Babu komai! Ammm.. na ce ka taɓa ganin an yi wankan gawa irin wannan ko kuwa yau ne farko?” ya faɗa .

Na ce “ban gane irin wannan ba?”

Sai da ya sake dubana da kyau kafin ya ce “kar ka nuna kamar ba ka san abin da nake nufi ba, alhalin ga alamun baiwar da ke tattare da kai nan a bayyane”

Na ja ajiyar zuciya don na fahimci abin da yake nufi, wannan yasa na basa amsar tambayar tasa na ce “yau ne farko”

Ina faɗar haka sai ya miƙo mini auduga ya ce “ka cusa wannan a ƙofofin hancinka ” na dube shi har zan yi tambaya amma kuma sai na karɓa tare da yin yadda ya ce ɗin ,yana fara zuba ruwa a gawar Joy sai na ga gawar ta yi motsi.Murya na ɗan rawa na ce “kamar fa ya motsa” ya ce “ba kama ba ce motsin ne ya yi” sai kuma ya ci gaba da yin wankan,can sai ga gawar Joy ta tashi zaune kan ƙugunsa.Matashin sai

12 / 18