MAFARKI Love and Horror Story By Mrs Sadauki.txt

Author :  Mrs Sadauki Category :  Hausa Read

Chapter   17 / 18

48K to 51K   out of 53.5K words

tsaya ya buɗe sannan ya ci gaba da nuno mini abubuwan da suka shuɗe.


Ta ƙarfin tsafi ne a wancan lokaci Alfanso ya jawo ragamar hankalin gimbiya Janaki ta zo har a nan cikin kurkuku ta kawo masa kanta ya yi tarayya da ita wacce ta sauya ƙaddararsu shi da ita.

Ina kawowa nan na yi wa littafin magana cikin sigar raɗa na ce “ka bani wani tarihin ban son wannan,in lokaci ya yi iyayena da kansu za su bani gwagwarmayar da suka sha” ai kuwa ina gama rufe bakina sai pages ɗin suka fara yin ƙarrrr suna ta gudu haɗi da buɗe kansu,har aka zo kan wata page mai ɗauke da wasu ahali.Uba mahaifi ,uwa da kuma wata ƴar babynsu a hannu ita ma tana riƙe da ƴar tsanar roba.

Na kai hannu na shafi hoton babyn,girrr na ji wani shock ya kama ni da sauri na rufe littafin ina jin kamar na taɓa jin makamancinsa abin da na ji sai dai ko da wasa ban kawo a kaina wai moments ɗinmu ne na ɗazu ni da baiwa Izzatu.


Ina shirin kwanciya bacci na soma jin yanayin iskan nan na kaɗawa,wato matar mafarkina ce za ta bayyana.Wani irin sanyi ne ya soma luluɓe ni yana saukar mini da kasala,idanuwana sun yi mini nauyin da yasa dole na soma rufe su a daidai kuma wannan lokacin ne ta bayyana a gare ni cikin shigar tsaraici.Tana shirin kai hannu jikina wani irin haske da ban san daga ina ya fito ba ya taso ya luluɓe ni tare da yi mini iyaka da ita.Na ja wani numfashin farin ciki kafin wani daddaɗan bacci ya ɗauke ni mai ɗauke da mafarkin prophecy ɗina wanda ababen bauta suka zaɓe ni matsayin wanda zai cika musu wani buri wanda tun lokacin baya suka fara gina shi.


★IZZATU

Ko da ta fita daga sashen Yarima David direct can ɓangarensu na bayi ta nufa.Tana shiga ta soma cire kayan jikinta ta jawo wani tsohon zane ta yi ɗaurin ƙirji kafin ta fara kiran sunan Kakarta “Dadda? Dadda?” daga can cikin wani ɗan ɗaki mai kamar akurkin kaji wata dattijuwa ta fito tana cewa “shalele har kin dawo?” da mugun sauri Izzatu ta ƙarasa wurinta tana cewa “kin ga Dadda ruwan wankin ƙafafun Yarima sun shigar mini ido kuma an zuba musu sanadarai dayawa”


Wani irin kallo ne Dadda ke yi wa Izzatun mai cike da tsoro,shakku da kuma zargi kafin can ta nisa ta ce “je ki kwanta kan gado na duba idon” ba tare da ta musa ba ta je ta kwanta ɗin,Dadda ta ɗauko wata ƴar ƙaramar fitilar hannu wacce a baɗininta wani busashen maciji ne da ya yi zamani wajen ƙarni uku.


Idon Izzatu ta soma dubawa bugun zuciyarta na sake tsananta tana jiye wa ƴar jikarta tsoron abin da tarihi ya tanadar mata.Yadda take gumi ya saka Izzatu cikin damuwa ta ce “Dadda ko dai makancewa zan yi ?”

Dadda ta ajiye fitilar tana mai cewa “a'a zan saka miki magani sai a ɗaure idon”

Izzatu ta ce “to bari na yi alwala tukun ” sai da ta je ta yi alwala ta dawo sannan Dadda ta saka mata maganin ta ɗaure idon sai ta zauna gefenta tana kallon face ɗinta sannan ta ce “ya yariman yake a zubin halitta? Ɗazu na ji gangami amma ban fita ba ballantana na gansa”


Izzatu ta saki wani murmushi wanda kana jin sautinsa za ka fahimci tun daga ƙasan zuciyarta yake,ta ce “dogo ne mai cikar zati,yana da manyan idanuwa da ɗan madaidaicin saje,fuskarsa babu walwala amma yana da kirki”

Dadda dai ido kawai ta tsura mata can ta miƙe ba tare da ta ce komai ba ta shiga haɗa wasu magunguna tana yi tana yin wasu siddabaru tana zuba wasu kalolin ruwa da aka tatso daga jikin wasu dabbobin masu dafi.

Bayan ta gama sai ta zuba maganin cikin kofi ta bai wa Izzatun da kanta,duk da babu daɗi haka ta daure ta sha.Magungunan sai suka saka ta bacci wanda hakan ya bai wa Dadda yin wani tsafi wanda ta jawo wasu tsoffin ruhika da zamaninsu ya shuɗe.Kamar wasu likitoci haka suka zagaye Izzatu kowanne yana nasa aikin sai dai sam sun ƙi yin nasara game da abin da suke buri a dole suka haƙura.

Lokacin sallar azahar na yi Izzatu ta farka ta je ta yi,haka ta wuni tana tunanin irin yadda Yarima David ya bushe mata ido ita ɗaya kuma sai ta yi ta murmushi a haka dare ya same ta.Bayan ta gama shafa'i da witiri sai ta yi zaune kan sallaya idonta na rufe da bandejin da Dadda ta saka mata.Tasbihi ne take ta jerowa haɗi da kirari ga Ubangijin talikai tana jin wata nutsuwa na ratsa ta,a daidai lokacin ne kuma aljanar Yarima David ta yi ƙoƙarin kusantarsa sai dai kash addu'ar kariya da neman Allah ya saka hannu a lamurran sarkin daularsu na gobe yasa ta kasa mu'amulantarsa.

A wannan daren sam Izzatu ba ta yi bacci ba,wani irin sabon yanayi take ji yana bijiro mata wanda ba taɓa sanin kanta da shi ba.A hankali ta tashi kamar makauniya ta soma yin lalube sai kuma wani abin mamaki sai ta ga wani haske ya fito mata a tsakiyar goshi wanda ke bata damar gani duk da idonta a rufe suke.Sam ko kaɗan tunaninta bai bata cewa ido uku ne gare ta ba,biyu na normal mutum ɗayan kuma wanda ababen bautar kakanni da iyayenta ne suka tsaga mata ita wacce za ta dinga bata damar ganin abin da mayafin sirri ya ɓoye.Cak ta yi tsaye tana kallon Dadda wacce ta sharar baccinta da gibjejen kanta irin na Saniya,yadda zuciyarta ta soma bugawa a tsiyace shi ya bai wa masu kula da idon goshin saurin rufe mata ita sai ta bar ganin komai.Ji ta yi wani abu ya matsar da ita shuuu ya kai ta dab da ɗan madaidaicin gadonta na itace,babu shiri ta kwanta tare da soma karanta “hasbunallahu wa ni'imal wakil!” cikin ikon Ubangiji ta samu salamar ruhi ta yi baccinta.



★A can ɓangaren EZRA kuwa duk da Yarima David ya bada umarnin a damƙo ahalin gidansu hakan bai sa dakaru sun rufe ta ba. Gida ta koma ta je ta yi tsaye gaban baƙar rijiyar tsafin da mahaifiyarta ta nuna mata ita da kuma yadda ake amfani da ita.Cikin ƙwarewa a wurin tsafi ta soma kiran baƙaƙen ruwan da ke kwance a rijiyar,nan suka fara yin zillo suna tumbatsa sai dai fa sam ta kasa taɓuka komai game da Yarima David saboda shi ne zaɓin ababen bautarsu.

Duk da haka EZRA ba ta karaya ba da dare ya yi sai da ta ƙara gwada sa'arta sai dai wannan karon garkuwar da ke bai wa Yarima kariya ta sha banban don kuwa wannan garkuwar hasken rahama ce .Cike da tsoro da firgici ta soma kiran ruhin Goggoji wato aljanarsu babu jimawa wata baƙar siffa marar kyawun gani ta fito daga can ƙasan rijiyar tana mai bata amsar abin da take son sanin cikin wata irin murya ce marar daɗin amo sannan a Yaren mutanen farko take cewa “garkuwar Yarima tana cikin Daular Alfanso,ba iya garkuwa ba ce ita ce sarauniyar gobe muddin ba ki yi wani abu ba to za ta hana ki cikar burinki da na mahaifiyarki”


Cikin ɓacin rai EZRA ta yi wani ihu wanda ya haifar da rikiɗewar harshenta ya koma wani baƙin maciji,idonta ma suka juye suka dawo wasu kore kafin ta fara aman furicin ɗaukar fansa tare da alwashin ko wace ce mai bai wa Yarima kariya ita ce za ta zamo ajalinta......



My book is only 500 via

2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank

DM +22795045822
[18/12 13:06] MRS SADAUKI: *INUWAR ALJAN*👻



```LoVe aNd HoRrOr story```👽


By
Chamsiya Laouali Rabo
{MRS SADAUKI💫✍️}



*SADAUKARWA:* Ga Rachida Mamar ƴan biyu, alherin Allah ya luluɓe ki . Ubangijin rahama ya kula da lamurranki👏🏻

*FCWA*☀️

________________________

BONUS

Daga yau Laraba bonus zai tsaya da zarar na saki page 10 to 500 ne,yanzu kuma bonus za ki tura 300 VIA 2670215530
ZULFAU YAHAYA
Ecobank DM +22795045822 .

09

#Yarima David

Tsawon kwana biyu ban saka baiwa Izzatu a idona ba,tun ranar da ta zo wanke mini ƙafafuwa sabulu ya shigar mata a ido.Duk yadda na so kuma na watsar da zancen nata sai na ji na kasa ina son jin labarinta.Yau rana ta uku kamar yadda na samu canjin wacce ke zuwa tana yin ayyukan da baiwa Izzatu ke yi,tana shigowa ta gaishe ni cike da ladabi tana shirin kwasar kayan wanki na ce “ina waccan baiwar?”

Ba tare da ta ɗago ba ta bani amsa da “ba ta da lafiya,idonta ya samu matsala ”

Haka kawai na ji ƙirjina ya buga,na ce “makancewa ta yi ko me?”

“Eh to hakan dai na ji ana faɗa amma ban tabbatar ba” ta bani amsa kanta na ƙasa har yanzu.

“Okay! Ki yi mata jagora zuwa nan ɗin” na faɗa cikin wata irin izza da ban san yaushe ta ratsa jinina ba.Sai da ta ɗan rusuna kafin ta ce “an gama ranka shi daɗe ” sai ta fice.


Bakin window na je na yi tsaye ina kallon yadda bayi ke ta kai komo a cikin katafariyar farfajiyar masarautar.Yadda nakasa ba ta hana wasu daga cikin bayin aiki ba shi ya fi komai burge ni,saboda ina son mutum mai jarumta.Ina nan tsaye na ji suna neman izini,ba tare da na juyo ba na ce “ku shigo!”

Da sauri kuma na lumshe ido jin amon muryartar na furta kalmomin amincin Ubangijinta a gare ni,duk da cewa ni ɗin ba musulmi ne ba amma na ji daɗin haka sosai.A hankali na juyo,idona suka yi tozali da ita tana sanye cikin wani pink ɗin hijabi har ƙasa idonta na naɗe da wani jan ƙyalle.Ɗayar baiwar na kalla,da mugun sauri ta fice har tana tuntuɓe.

“Ga ni ranka shi daɗe ” ta furta cikin wata irin sanyin murya tana ƙanƙame jikinta da alamu kamar sanyi take ji,a hankali na soma takawa zuwa gare ta har na isa gabanta na tsaya.Ba tare da na ce mata komai ba na kai hannu zan cire bandejin sai dai ya ƙi fita ba tare da wani tunani ba na ja wuyan hijabinta baya kanta ya fito.Na ɗan ranƙwafa tare kai hannuwana baya ina kuma kallo na kwance ƙullin tare da cire ƙyallen duka.


“Buɗe idon na gani!” na furta cikin bayar da umarni,kai ta girgiza wanda ya bai wa baƙar sumar kanta damar motsawa.Zuciyata na ɗan dokawa na soma motsa bakina ina karanto wasu ɗalasima haɗi da hura mata iskan bakina a fuska.Babu shiri ta buɗe idon,sai dai a tashin farko sun canza daga na normal mutum saboda wata irin kalar haske da suke fitarwa.Ɗayan idon ya zama kamar hasken rana yayin da kuma ɗayan ya ɗauki siffar na mage yana fitar da wani blue haske.

A hankali kuma ta ƙara mayar da su ta rufe,da sauri ni kuma na sa hannu ina ƙoƙarin buɗe su sai ga Nelson ya turo ƙofa ya shigo.Cak ya yi tsaye yana kallon mu kafin yayi gyaran murya,baiwa Izzatu ta nufi ƙofa za ta fita amma na dakatar da ita “ke!” cak ta tsaya ba tare da juyo ba.

“Kina iya tafiya ke ɗaya ne ba tare da ƴar jagoro ba?” na tambaye ta ina kallon yadda hijabinta ke jan ƙasa.“Eh ranka shi daɗe zan iya”

“Okay!” na furta,tana fita Nelson ya matso yana cewa “meke tsakaninka da wannan baiwar? Ka rasa wacce za ka ƙulla alaƙa sai wacce ba ta da wasu taurari masu haske?”


Wani irin kallo na yi masa kafin na ce “na yi maka kama da wanda zai yi mu'amalar banza da mace ? Yawwa dama ina son yi maka wata magana,me yasa ka kusanci Nadiya sannan kuma ka kashe ta?”


Babu wata kunya Nelson ya bani amsa da “saboda ina son samun ƙarfin power,ita ɗin ƴa ce ga wani matsafi ya saka mata abubuwan tsafi sosai su ne na sace sai kuma aka samu akasi ajalinta ya yi”

Na taɓe baki kawai tare da komawa bakin window na yi tsaye.

“Yarima faɗa mini mana shin namiji ne kai?” na ji wata tambayar rainin hankali Nelson ya jefo mini.

A zuciye na ce “a'a mace ce ni ! Ai ka ɗan kwali a kaina”

Ya yi wata irin dariya sannan ya zo kusa da ni ya tsaya yana mai cewa “ba haka nake nufi ba,tambaya nake yi in ka taɓa jin feeling akan mace”

Da sauri na kalle shi ina jin bugun zuciyata na canza sheƙa,na haɗiye wasu yawu ina mai ci gaba da kallonsa.Yayin da shi kuma ya ɗora da cewa “kar ka ji kunyata,ni abokinka ne sannan kuma mataimakinka ban yi maka wannan tambayar don rainin wayo ba a'a sai don ina son isar maka da wani saƙo mai muhimmanci ”

“Wane irin saƙo?” na tambaye shi.

Ya ce “duk wanda ke ɗauke da rigar prophecy ana killace masa sha'awa har zuwa wani tsaunin nasara,ba zai kasance namiji ba har sai in ya haɗu da macen da ababen bauta suka zaɓa masa wacce ita kanta ba normal mutum ba ce tana ɗauke da wani muƙamin ƙarfin iko ne wanda zai taimaka maka ka tura motar burinka ga ci”


Na kawar da kai gefe ina mai cewa “sam ban fahimci abin da kake son faɗa ba”

Nelson ya ce “ka fahimta sarai Yarima kawai ba ka son sanar da ni amsar tambayata ta farko,sai dai ka sani nan kaɗan zan samo ta ba ni ɗaya ba har da mai girma sarki Alfanso ”



Na juyo da sauri ina kallonsa,ya jinjina kai yana mai ci gaba da cewa “a ranar da ka zo masarautar nan in ba ka manta ba ka suma,a lokacin ne kuma aka gudanar da bikin ƙaddamar da kai.Aka yi maka wankan ruwan tsafi wanda ba a samu damar yi maka shi ba lokacin da aka haife ka, sannan an yi maka sabon shayi wanda za a tabbatar da ingancinsa nan da kwana uku ”

“Shayi? Ni ɗin ne aka yi wa sabuwar kaciya? Hahaha” na yi wata irin dariya saboda maganar tasa ta fi kama da rainin wayo.

Ya ɗaga gira ya ce “tabbas an yi maka sabon shayi Yarima.Kuma ƴan matan lorori ne za su tabbatar in kai namiji ne ko kuwa dai...” mugun kallon da na watso masa ya saka shi yin shiru .


“Kana iya tafiya!” na furta ina jin wani nauyi a zuciyata.Nelson ya ɗan bubuga kafaɗata ya ce “ka huta lafiya sarkinmu na gobe” har zai fice na dakatar da shi ta hanyar cewa “an kawo iyalan wannan matsafin?”

“Matarsa na rufe a kurkuku ko ka manta? Sai ƴarsa ce kawai EZRA Albino girl ”

“A je a tawo da ita” na faɗa cikin bayar da umarni,ya ce “an gama” sai ya fice na bi bayansa da kallo ina maimaita kalaman da ya furta mini a game da nagartata ta ɗa namiji.In da akwai wacce zan gwada sanin ni ɗin a wane sahu nake cikin jerin maza to EZRA ce,yarinyar mafarkina matar da zuciyata ta zaɓa.


Ina nan a tsaye bakin window na tsinkayi Nelson shi da wasu dakarun sun haɗu wuri guda suna yin wasu alamo na tsafi,kafin ƙyaftawar ido suka ɓata cikin wata ƙura da ta turniƙe wurin ta haifar da guguwa.


Ba a kuma ɗauki lokaci ba suka bayyana suna riƙe da EZRA,sai ƙoƙarin ƙwacewa take .Nelson ya ɗago kansa saitin benen da nake,duk nisan tazararmu kuma bai hana mu ganin ƙwayar idon juna ba har muka yi magana irin tamu ta matsafa.


Cikin sauri na je ƙara kimtsawa na ɗora babbar rigar ƴaƴan sarakai kafin na fita.Ina tafe wasu ɓoyayyun ruhika na take mini sawu har na isa wani sashen sirri wanda aka ware domin ni,ban jima a cikinsa ba aka kawo mini EZRA hannuwanta ɗaure da kacocin tsafi waɗanda nata tsafin ya gagara ya kwance su.


A gabana suka gurfanar da ita kafin su fice su bar Nelson shi kaɗai yana kallona.
“Zan neme ka daga baya” na furta,ya jinjina kai kafin ya fice.

Na maida dukkan hankalina a kanta ina jin wutar sonta na ƙara ruruwa a birnin zuciyata.

“Mene ne sunanki?” na tambaye ta.

Cikin zafin kai na matsafiya ta ce “ka juya ƴaƴan wurinka domin samo sunan”

“Ni ba boka ba ne matsafi ne!” na bata amsa ina mai ɗauke ta da wani gigitacen mari wanda ainahinsa ba daga gare ni ya fito ba a'a kawai na samu kaina da yinsa ne.


Ta goge bakinta da ke fitar da jini kafin ta ɗago tana kallona da idon sharri,kunnuwanta kuma suna daɗa yin tsayi sosai har suna mai hudu dogon gashin kanta wanda yake kamar zaren kwakwa.


“Ki yi ƙoƙarin mayar da waɗannan siffofin naki kafin raina ya ƙara ɓaci na sauke miki waɗannan kunnuwan masu kamar na Zomo ” na furta tare da kallon tsakiyar idonta da nawa idon muguntar.

Ta saki wata razananiyar ƙara tana mai rumtse idonta gam,nan take kuma suka fara shatatar da jini.Rai a ɓace na ce “dakaru!” suka wani buɗo ƙofa da ƙarfi suka shigo,“ku ɗauke ta ku kai ta can inda aka ajiye mahaifinta ƙila in ta ga irin azabar da ake yi masa ta yi hankali ta saurare ni a nutse ” na furta cikin amon ɗaga murya.

Ƙiiii suka ja ta suka fice da ita,ni ma fita na yi na koma sashena na fiddo littafin sirrina.Hoton nan dai ne na ƴar babyn nan mai ɗauke da ƴar tsanar roba.Zama na gyara na soma gwada yin siddabaru don nuna mini abin da babyn ta zama a yanzu sai dai kashhh iya wani zane kawai na iya gani da ke manne gefen wuyanta.



★ BAIWA IZZATU

A daren ranar da ta ga Dadda da kan Saniya a wannan daren ne prophecy ɗinta ta soma.A washegari sam ba ta tada wa Dadda zancen ba ita kuma a nata ɓangaren sai ƙoƙarin ganin ta rufewa Izzatun idanuwanta take don kar ta ƙara yin tozali da Yarima David sai dai kuma aka samu akasi yau Yariman da kansa ya turo wata baiwa kan ta zo ta tafi da ita.Duk yadda Dadda ta so hana Izzatun tafiya amma kasa samun ƙwarin gwiwar yin haka ta yi a dole ta bar ta suka tafi.

Ita kuwa IZZATU banda bugawar zuci babu abin da take yi har lokacin da suka isa can ɗin.A sa'ilin da Yarima ya samu kusanci da ita sosai ji ta yi numfashinta na

17 / 18