ABBAN SOJOJI TAKUN TSAKIYA 2 BY BOSS BATURE.txt

Author :  Boss Bature Category :  Arewa Pen

Chapter   80 / 80

237K to 238K   out of 238K words

kuka,a ƙopar gidan ta tsaya tana faman ambaton sunan baba buzu tana cewa babana ka kashe mun ka raba shi da ranshi,ka kashe mun babana ko,kuma zaka rabani da ƴa'ƴana suma ka kashe su ko......'haka ta dinga sambatu ita kaɗae,
  Tun daga wannan lokacin abu ta haukace ta miƙi santa tana faman sambatu,

Wannan shine silar rabuwarsu da mahaifiyarsu basu ƙara sanin inda take ba,

Abunda kuma yayi silar komawarsu katsina,labarin neman da mahaifinsu yake yi masu don ya kashe su kamar yadda ya fada ma abu,ya isar masu maman sadeeq,ko aikin ba'ayi ma hosana ba,amma ta miƙe saidae babu hankali ko kaɗan,da taimakon Mijin maman sadeeq ya sanyasu a mota tare da damka ma direban amanarsu,bayan yasa anyi ma hosana allurar bacci ya bama Sehrish address ɗin gidan tsohuwar nan,wadda ta kasance kishiyar mahaifiyarshi ce anan suke zaune,tsohuwa mai kirki koda yayi mata bayanin halin da yaran suke ciki ta tausaya masu sosae ta kuma ce zata rike su da tsakani da Allah,shima kuma yayi alkawarin zai rinka turo da dan abunda Allah ya hore,
  Da daddare suka isa unguwar ba tare da sanin kowa ba,sai da aka taimaka masu kafin aka samu suka shiga da hosana gidan,a ɗaki ake rufeta saboda haukan da takeyi,na bugun mutane da jefe jefe,tsaf zata iya kashe mutun,
   Wannan shine silar komawarsu gidan tsohuwar nan,tayi masu halarci arayuwa,ita ta dinga nema masu tallafi don a maida hosana asibiti ayi mata aiki,haka sehrish ma bata zauna ba,har wankau suke yi suyi guga itada jahad suna tara kuɗin da za'a kai hosana aiki,kafin tsotsai ya ritsa da jahad,
     Akwai wani lokaci da suka je gidan wani ɗan majalissa jin labarin cewa yana taimaka ma marasa lafiya waɗanda ake buƙatar kuɗin da za'ayi masu aiki,tsohuwa da sehrish suka je gidan mutumin,yayin da suka bar jahad a gida tana aikin wanki,
  Tana cikin yin wankin nan ta dinga jin kukan hosana gwanin ban tausayi tana cewa dan Allah su buɗe mata ƙopa su taimaki rayuwarta mutuwa za tayi,tana son ganin ƴan uwanta,me yasa kullum suke ƙumsheta a ɗaki,zafi ya isheta,itafa tana da hankalinta,ba mahaukaciya ce ita ba,tana da hankalinta,
  Natsuwa jahad tayi tana sauraranta,yanayin yadda hosana ke kalamanta yasa tayi tunanin cewa kodai ta samu lafiya ne,tun tana tsoran buɗe mata ƙopar har dae tausayinta ya kamata sosai,da sauri taje ta buɗe mata ƙopar,
  Kamar jira take a buɗe da ƙarfi ta damƙi wuyan jahad da hannunta,ta janyota cikin ɗakin,tana cewa"dama kece kika sace ni ko?kika rufe ni acikin ɗakin nan kina cutar dani!yau Allah ya kamaki!wlh saina rama,
  Duk yadda jahad taso ta kwaci kanta a hannun hosana abun yaci tura saboda wani irin mahaukacin ƙarfi ne ke gareta,buga kan jahad tashiga yi ajikin bango,jahad ta fasa ihu saboda azabar da taji,nan take jini ya shiga bulbulowa daga goshinta,kuma hakan baisa hosana ta daina bugunta ba,har saida taga jahad ta daina motsi sannan ta saketa,
Adai dai lokacin tsohuwa da sehrish suka dawo cikin gidan,da gudu suka faɗo ɗakin da hosana take ganinshi a buɗe nan suka samu jahad wanwar ƙasa jini na zuba,itama hosanar tana baje ƙasa sai faman mirgina-mirgina takeyi numfashinta na fita sama sama,
Wannan shine silar da aka kwantar da hosana da jahad asibiti,har akayi ma jahad ƙarin jini,ita za ayi mata aiki,
  Inda Allah ya taimakesu asibitin suna da wata ƙungiya wadda manyan masu kuɗi ke tallafawa marasa lafiyan da za'ayi ma aiki da wani parcentage,sun samu kuɗin amma akwai cikon da zasu yi dubu ɗari tara likitocin suka buƙata a wurinsu,
   Sehrish tasha wahala sosai wurin neman cikon kuɗin nan,duk inda taje neman taimako sae an nemi ta bada kanta sannan abata kuɗin,anan ne wata mata dake jinyar wata a ward din da aka kwantar dasu hosana take ba sehrish labarin hajjaju dake ɗaukar ƴan aiki tana samo masu aikatau suna yi kuma suna samun alheri dayawa,saboda gidajen manyan masu kuɗi take samo masu aiki,matar tace in taci sa'a ma,aranar da tafara zuwa aiki sai tace ma masu gidan su bata kuɗin aikinta na shekera ko biyu ne,in aka dace zasu bata kuɗin,bayan matar ta bata address din gidan,tun daga ranar sehrish kullum sai taje ƙopar gidan hajjaju nemanta,har Allah yasa ta samu ganinta,

Atakaice tarihin su sehrish hosana da jahad kenan,duk da bakomai aka fayyace ba, amma mutun zai gane inda aka dosa,

💋Boss Bature💋

Jikin kowa yayi mugun sanyi,masu raunin zuciya acikinsu tuni sun soma zubar da hawaye,hatta jahan dake da taurin kai sai da ya matse kwalla,Abusufyan kuwa tuni ya fashe da kuka,haka gwaggon katsina kamar ƙaramar yarinya haka ta dinga kuka tana fadin"Allah ka tsine ma Sayyadi da duk zuri'arshi!Allah ya wulaƙanta rayuwarshi kamar yadda ya wulakanta rayuwar ƴa'ƴan abusufyan ɗina,

Hatta Abbansu sae da ya matse kwalla shi da Abbas da su fawan,kowa ya harzuƙa ransu yayi mugun 6aci,tsananin tausayin su Jahad hosana da sehrish ne ya kamasu,marshal Omar kuwa sunnar da kanshi ƙasa yayi idanunshi sunyi jawur jikinshi sai kerma yake yi,zuciyarshi har wani tafarfasa takeyi saboda tsabar 6acin rai,
  Sehrish kuwa lokacin da Jahad ta kammala bada labarin tasa kuka ita da Hosana,
  Nan take ta miƙe daga jikin Sgr,hankali a matuƙar tashe take kallonsu yayin da zuciyarta ke bugawa da ƙarfi da ƙarfi,kowa zuba mata ido yayi yana kallonta ganin yadda jikinta ke rawa tana kallonsu hosana da jahad,
  Muryarta na rawa ta ambaci sunansu"Hosana jahad kune.........'tana faɗin hakan ta yanke jiki ta faɗi asume,
  Da sauri abusufyan da hajiya azeema sukayo kanta hada su jahad ɗin,
  Sam Sgr bazai iya jurewa ba,yunƙurawa yayi azafafe ya juya tare da nufar upstairs ya koma bedroom ɗinshi,agaban mirror ya tsaya yana kallon fuskarshi wadda take daure tamau,gaba daya jikinshi sae kerma yake yi saboda tsabar 6acin ran da yake ciki,wata irin zufa ce tashiga gangaro mashi daga gefe da gefen fuskarshi,tabbas idonshi Idon Sayyadi...............................


80 / 80