Author : Boss Bature Category : Arewa Pen
fuskantar juna da ita, wankan jeans da t shirt red colour ne ajikinshi, sai faman ƙamshi yake yi,
"Me ya faru ne naga kina ta tiƙar gudu kodai motsa jiki kike yi ne? ae muna da wurin gym acikin gidan nan,'
Ya faɗi yana kallonta, tayi mashi zuru da ido,
Ganin bata da niyar yin magana yasa shi cewa "Labari mai daɗi "! cike da zumuɗi tace "dagaske ? Wani irin labari ne wannan,
"Mafarki nayi jiya,"
"Me ya faru acikin mafarkin"? ta tambaye shi cike da son ji,
gyara murya yayi tare da cewa" mafarki nayi da wani narkeken zaki acikin wani ƙurmin daji ya biyo ki da gudun gaske, kamar zaki tashi sama haka kika dinga gudu kina ihu, kinsan waye ya cece ki a wannan lokacin"? Ya jefa mata tambaya, hankali tashe tace "A'a," ƴar hararar ta yayi tare da cewa"Ni ne nan, nazo da suffar jemage na ɗauke ki da fika fiki na mukayi sama can cikin gajimare...........' ganin yarda sehrish ta fashe da dariya yasa shi dakatawa da labarin yana kallonta, nuna shi tayi ta yatsa tana cewa"junaid kaji tsoran Allah, jemage fa kace? taya jemage zai iya ɗaukar mutun ? sannu malam fesal ka feso mun ƙarya,
gaba ɗaya suka sanya dariya, ba ƙaramin nishaɗi junaid ya sanyata ba duk da fargabar da take ciki, sun jima a zaune ƙasa suna fira, kafin daga bisa ni suka tashi, shi ya wuce mosque ita kuma ta wuce bedroom ɗinta saboda tayi sallar itama,
**********
zaune take agaban mirror ta kammala shiryawa cikin doguwar rigar material blue colour mai kyan gaske, rigar tabi shape ɗin jikinta daga can ƙasa yayi ƴar baza tamkar mermaid haka shape ɗin ya bada,hoda ta ɗauka tana shafa ma fuskarta, bayan tagama ta ɗauki jan baki red colour ta murza, ba ƙaramin kyau tayi ba, set na brushes ɗinta ta ɗauko ta gyara eye brows ɗinta,bayan ta kammala gyara gashin giran, ta ɗauki ribbom ɗinta data ajiye saman mirror ɗin, tattara sumar kanta tayi tana kiciniyar ɗaure gashin amma sam tagaza saboda yawan da yayi,ita kanta tayi mamamkin yarda gashinta yake toho,ba ƙaramin tsayi yayi ba ga yawan gaske dami guda dashi,bakomai ya jawo hakan ba face mayukan da take amfani dasu na gyaran gashi sun amshi kanta sosai,
Sakin gashin tayi ya tarwatse a bayanta,saboda gajiyar da tayi da ruƙon shi,hannu takai cikin jerin perfumes dinta ta dauki kwalbar turaren flower bomb wanda junaid ya ɗaukar mata a lokacin da suka je siyayya saboda shima yana da irin shi, shiyasa ya haɗa mata dashi don suyi anko,
feshe jikinta tayi da turaren ko'ina ya ji, nan take daddaɗan ƙamshinsa ya gaure ko'ina na ɗakin gaba ɗaya,mayar da kawalbar turaren tayi bayan ta kammala fesa wa, sannan ta zuba ma madubin ido tana kallon fuskarta,fuskar sgr ta dinga gani acikin mirror ɗin,nan take ta tuna lokacin da ta watsa a guje zata bar ɗakin ya biyota da gudun gaske tare da ruƙota a jikinshi,tafin hannunta tasa tare da rufe fuskarta tana faman sakin murmushi,sake tunawa tayi da lokacin da ya yage rigar jikinta kai tsaye ya afka mata,nan take taji wani irin sanyi da kasala sun rufar mata,gaba ɗaya fa sehrish ta shiga yanayi cike da shauƙi take tariyo duk wani abu da ya faru da ita a daren jiyan ta shagala sosai, taji knocking daga waje, muryarta cike da kasala tace"Wanene"?
.muryar Azmee tajiyo tana cewa"Auntynki ce," jin hakan yasa sehrish tashi tare da ƙarasawa ta buɗe mata ƙopar,tana a tsaye jikinta sanye da jallabiya ta mata maroon colour, ta yafa mayafi akanta ba ƙaramin kyau tayi ba,
sakin baki tayi tana kallon Sehrish kafin tace"Masha Allah, irin wannan kyau haka? sai kace sabuwar amarya,kinyi kyau sosai,"murmushi kawai sehrish ke saki,
matsa mata hanya tayi tare da cewa"Aunty azmee ki shigo daga ciki mana,"
"A'a basai nashigo ba, dama nazo naji ya kuka ƙare da Omar?ina fata kin sanar dashi gaskiya?
shiru sehrish tayi tana tunanin amsar da zata bata,ranta ne ya bata cewa kawai ta amsa mata da eh,saboda tana da tabbacin cewa muddin ta faɗa mata cewa takasa furta sunan haroon agaban Omar to tabbas azmeen zata iya cewa zata sanar dashi ita da kanta,idan kuma hakan ya faru to tabbas itama azmeen zata fuskanci irin abunda sehrish ta fuskanta wurin Furta sunan Haroon,kuma bazata so hakan ya faru ba don ba ƙaramin raɗaɗi taji ba,.
Sam ta tafi duniyar tunani taji muryar azmee ta katsa ta da cewa"Lafiya kuwa naji kinyi shiru baki ban amsa ba"?.
cikin sauri sehrish tace"aunty azmee na sanar dashi gaskiya kuma yace zaiyi bincike akan haroon ɗin,"
"Kin tabbata"? ɗaga kai sehrish tari alamar eh,
Jinjina kai azmee tayi tare da cewa"kayan sunyi maki kyau sosai Allah," murmushi sehrish tayi tana sunnar dakai,
Azmee ta kuma cewa"Munyi magana da junaid akan kayan nan naki da aka kai ɗinki,yace mun tailor din ya kammala ɗinki shi zaije ya amso maki kayan," cike da farin ciki sehrish tace"ngde sosoe aunty azmee na,"
Murmushi azmee tayi tare da kai hannu taja kumatunta tace"bani zaki godemawa ba, ko kin manta waɗanda suka bada kuɗi akayi maki siyayyar ne"?
girgiza kai sehrish tayi tare da cewa"a'a ban manta ba,amma ina jin kunyar zuwa inyi masu godiya,"
"Gaskiya yakamata kije kam,zasu ji daɗi sosai su son cewa kinji daɗin abunda sukayi maki,ki same su kiyi masu godiya,"
"Insha Allah zanje," ta amsa mata, sakin kumatun nata tayi sannan ta juya zata futa, har ta ruƙe ƙopar zata buɗe ta jinkirta kamar mai tunanin wani abu, sake juyowa tayi tare da kallon Sehrish dake a tsaye tace"wai nikam akwai abunda nake taso in tambayeki tuntuni sai in ta mantawa,"
cike da kulawa sehrish take kallonta don jin me zata ce,
Cigaba da cewa tayi "a kwanakin baya kinyimun magana akan cewa kinason zuwa garinku domin ki duba ƴan uwanki da basa lafiya ko"? ta tambaya tana kallonta,
A ruɗe sehrish tace"ƴan uwana kuma aunty azmee? Su wa kenan ? ni ba muyi wannan maganar ba kodai kin manta ne"?
hararar wasa azmee tayi mata tare da cewa"banason wasa fa, kinsan me nake magana akai mana, nan kwanaki kikazomin kina kuka kina cewa in taimaka maki kije kiga ƴan uwanki shine kuma yanzu zaki ce mun har kin manta?
Hankali tashe sehrish tace"aunty azmee ni bani da wasu ƴan uwa, bani da kowa wlh, bansan akan me kike magana ba,"
mamaki ne ya kama azmee ganin yarda sehrish ta haƙiƙance akan cewa bata da wasu ƴan uwa kuma fuskarta babu alamun zolaya,bayan ita da kanta ta sanar da ita game dasu,
ɗaure mata fuska tayi tare da cewa"banason rainin hankali sehrish!kina nufin dama baki da wasu ƴan uwa!ƙarya ce kawai kika shirga mun?tun farkon zuwanki gidan nan aiki, kika sanar dani cewa ƴan uwanki ne basu da lafiya shiyasa kikazo neman kuɗin da za'ayi masu aiki, har na ranta maki kuɗi dubu ɗari tara domin ayi masu aiki a amatsayin kuɗin aikin ki na shekara ɗaya da rabi, shima wannan duk plan ne kika tsara mun !!!!? Rai a6ace azmee ke magana hakan ba ƙaramin ɗaga mata hankali yayi ba, tuni idonta suka soma zubar da hawaye saboda tagaza gane kan me azmeen ke magana akai,.
"Aunty azmee wlh ni duk bansan anyi wannan ba! Bamu ta6a magana dake akan cewa ina da wasu ƴan uwa ba,kuma ni ban amshi wasu kuɗi ba saboda ayi ma wasu aiki ba.....'
tunkan ta ƙarasa maganar azmee ta kwatsa mata tsawa tare da cewa"Ya isa haka Sehrish!!ashe dama ke maƙaryaciya ce!! kin cuce ni kinyi mun karyar cewa kina da ƴan uwa,ashe duk tsara ni kikayi saboda ki samu kuɗi,danasan haka kike da tunfarko ban yarda dake ba, wlh sehrish kinban mamaki kuma na gama yarda dake.......' tana kai ƙarshen maganarta, a fusace ta juya zata bar ɗakin cikin sauri sehrish ta ruƙo jallabiyar jikinta,muryarta na rawa cikin kuka tashiga cewa"wlh aunty azmee bansan komai game da abunda kike faɗa ba,na rantse maki da Allah wlh bani da wasu ƴan uwa aduniyar......'
girgiza kai azmee tashi ga yi tana cewa"wlh kin ban mamaki sehrish,bansan haka kike ba ae da tun farko ban bari kin fara aiki agidan nan ba!!kin cuce ni kin rushe duk wata yarda da nayi maki,sai faman rantse rantse kikeyi mun ko tsoran Allah bakiji," rai a6ace azmee tayi maganar tare da fusge rigarta daga riƙon da sehrish tayi mata, cikin sauri tasa kai ta fuce daga ɗakin,
A wani irin yanayi sehrish ta zube saman guiwowinta tana faman sharara kuka,mutun ɗaya da ta yarda da ita aduniyar nan ayau ta juya mata baya akan abunda batasan dashi ba,har ga Allah ita gaskiyarta take faɗi amma azmee taƙi fahimtarta,tuni zazza6i ya fara hawa jikinta,sam tagaza tashi daga kneel down din da tayi 😭
Tun da azmee ta fuce daga ɗakin sehrish, kai tsaye ta wuce nata bedroom ɗin, shiga ciki tayi tana faman safa da marwa,ranta ba ƙaramin sosuwa yayi ba,gaba ɗaya taji sehrish tafara fitar mata arai,saboda ƙaryar da ta shirga mata,cikin ƙunar rai take cewa"kin cuce ni sehrish,banta6a tunanin zakiyi mun haka ba,natsani makaryaci arayuwata, me yasa tunfarko bata fito fili ta faɗamun cewa kuɗi takeso ba,don me za tayi mun ƙarya?
tuni idon azmee sun cicciko da kwalla saboda ƙululun baƙin cikin daya tsaya mata arai,daƙyar ta iya samun wuri ta zauna daga gefen gadonta tana cigaba da tunani acikin ranta,
"ɗan adam kenan!yanzu duk yarda nake kyautatama yarinyar can sai da ta butulce mun,saboda farin cikinta nakeyin wasu abubuwan don na faranta mata,amma hakan bai hana tayi mun ƙarya ba!!idan har dagaske ne sehrish ba ta da wasu ƴan uwa ƙarya ne tayimun,TO WAYE TASA NA TURA MA KUƊIN!!!!!!? miƙewa azmee tayi lokaci guda gabanta yashiga faɗuwa tuni taji zufa tasoma tsattsafo mata,hankali tashe tace"nashiga uku!! tabbas na tafka kuskuren yarda da yarinyar can!! meyasa tunfarko najata ajikina?kada fa ace da wata manufa tazo cikin gidan nan!!!
abubuwa iri iri suka dinga zuwa mata acikin ranta game da SEHRISH,😥
Lamarin dae ba daɗin ji
💋BOSS BATURE💋
A 6angaren su hossana kuwa tun bayan da suka yi faɗan nan atsakaninsu,su kayi fushi da junansu,saman gado hossana ta haye tana baccin wahala bayan ta gama shan kukan nata,Jahad kuwa bayan sun gama faɗan toilet tashiga tayi wankanta,bayan ta fito ta shirya cikin riga fara off shoulder tare da dogon wando baƙi,ba ƙaramin kyau tayi ba,musamman gyaran gashin kanta wanda akayi masu a wurin saloon ya ƙara ƙawata ta sosai,
komawa tayi ta zauna daga gefen gadon kusa da hossana, bin ta da kallo tayi sai faman sharar bacci takeyi tana jan minshari,haryanzu kayan baccin nan ne ajikinta tun na daren jiya,
Hannu tasa tare da bubbuga bayanta a hankali tana cewa"hossana ki tashi!ko baki jin yunwa ne?
tsoki taja tare da juya mata ƙeya don karta takura mata, sake bugun bayanta jahad tayi tace"wai ba zaki tashi bane!?
buge hannunta hossana tayi tare da cewa"ki rabu dani, babu ruwanki dani,idan banyi wankan ba jikinki ne ko nawa?ko kin ta6a ganin zararre mara hankali yayi wanka ne? ni mahaukaciya ce kibarni inyi rayuwata.......'cikin kuka hossana ta ƙarasa maganar,da alama abun ya ta6a mata zuciya dama ta tsani akirata da zararriya,
Cike da lallashi jahad tace"am really sorry hossana nasan ban kyauta ba,raina ne ya 6aci shiyasa har na gaya maki hakan,bazan ƙara ba insha Allah,"
tayi maganar tare da ruko hannun hossana donta tashi,fisge hannunta tayi daga cikin nata tace"pls jahad leave me alone,zuciyata ba ta mun daɗi,yaya Omar kawai nake jira yazo,"
Murmushi jahad tayi tare da janyo gashin kan hossana tana wasa dashi a hannunta tace"faɗa mun gsky hossana kodae son yaya omar kike ne"?
juyowa hossana tayi tare da kallonta fuskarnan ɗauke da murmushi tace"eh ina son yaya omar sosai ke fa"?
jiki asanyaye jahad tace"Wani kalar so kike nufi? Na soyayya da aure? ta tambaya tana kallonta,
hossana tace"shi nake nufi,jahad inason ya omar sosai,"
shiru jahad tayi gabanta na faɗuwa tuni yanayin fuskarta ya canza izuwa matsananciyar damuwa,ganin hakan yasa hossana tashi zaune tana kallonta tace"jahad naga kamar fuskarki ta canza meya faru ne"?
cikin sauri ta basar tare da ƙaƙaro murmushi tace"bakomai hossana,ni zan wuce kitchen na shirya mana lunch," tana faɗin hakan ta miƙe da hanzari tabar bedroom ɗin nasu,saukowa daga saman gadon hossana tayi tare da wuce wa cikin toilet don tayi bath,
sam jahad tagaza jurewa tana fitowa daga bedroom ɗin ta wuce cikin falon tare da samun wuri saman 3 seater ta zauna jiki amace,
"dagaske ne hossana ya Omar take so?amma hossana ba ta da cikakken hankali bana tunanin tasan menene *SO* ya Allah kasa hakane saboda bazan iya jurewa ba......' ta furta tare da kai hannunta saman goshinta,bakomai bane ya faɗo mata aranta ba face farkon haɗuwarsu dashi a asibiti,lokacin ba ƙaramin tafiya yayi da zuciyarta ba saboda yarda yake acting dinsa,kyawawan ɗabi'unsa da halayansa sune suka sa jahad faɗawa tarkon shi, ita kanta bata tashi tabbatar da hakan ba sai ranar daya sanya handkerchief dinsa yana goge mata hawayenta..........."
tayi nisa cikin tunanin nata muryar hossana ta katse ta da cewa"jahad nayi tunanin zanzo na sameki a kitchen ne ashe kina nan zaune," firgit jahad tayi tana kallonta sai da ta dai²ta natsuwarta sannan tace"har kinyi wankan kenan," ta faɗi tana kallon hossana dake nufota jikinta na sanye da gown black colour, ta saki curly hairs ɗinta ya barbazo mata abayanta,
Amsa mata tayi da cewa"Eh baki ga har na canza kaya ba," ta faɗi tare da jujjuya mata donta gani,
Murmushi jahad tayi tare da cewa"kinyi kyau sosai," ta ƙarasa maganar tare da miƙewa tsaye tace"kizo muje kitchen ɗin atare saiki tayani aiki, muyi sauri mu kammala,"
Amsa mata tayi da toh, sannan suka wuce atare kitchen ɗin atare,
***************
Zaune yake acikin motarsu Ƙirar mercedes S450,ash colour,jikin shi na sanye da kakin sojoji,sai faman duba wrist watch ɗin dake hannun shi yake lokaci zuwa lokaci,gajiyar da yayi da jira ne yasa shi ɗauko wayarshi daga cikin trouser pocket dinsa ya buga ma Jahan kira nan take kiran ya shiga bada jimawa ba Ya ɗaga kiran, tsoki ayaan yaja tare da cewa"Wai kuɗin sunƙi fidduwa ne? Nifa nagaji da jira wlh," fuskarshi a yamutse yayi maganar,.
on the other hand jahan yace"Am sorry yanzu haka ma na fitowa daga bankin gani nan zuwa,"
katse kiran ayaan yayi tare da mayar da wayar inda ya ɗaukota ya ajiye,
Cikin ƴan mintuna saiga Jahan ya fito daga cikin bankin hannunshi ruƙe da jaka,
Yana ƙarasawa gaban motar ya buɗe back seat dinta tare da yin wurgi da jakar ciki, sannan ya rufe ya kuma buɗe front seat ɗin ya shiga ya zauna a gefen Ayaan dake zaune a driver seat,
"Yau dae zamu jefar da kwallon mangwaro mu huta da kuda," acewar Jahan,murmushi ayaan ya saki yana kallon shi yace"baka ji daɗin da nakeji ba wlh,saboda a ƙagare nake da mu bashi kuɗin nan mu huta da shegen nacin nan nashi,ya takurama rayuwarmu gaba ɗaya,Haroon bai da imani jahan," fuskarshi a yamutse yayi maganar.
"har yau in na tuna abunda yayi mana zuciyata tafarfasa takeyi mun saboda 6acin rai,haroon ya wulaƙanta arayuwarmu,Allah bazai ta6a barin shi ba, Insha Allah ƙarshen shi bazaiyi kyau ba," acewar jahan
Jinjina kai Ayaan yayi kafin yace"amma Jahan kana tunanin in muka bashi kuɗin nan zai goge video ɗin duka?am just doubting about it,don na lura ba ƙaramin shaiɗani bane,
jahan yace "ae ba zamu bashi kuɗin ba har sai mun tabbatar daya goge videon agabanmu mun gani,"
"Duk da haka nidae ina fargaba wlh," cike da damuwa ayaaan yayi maganar,
Sun jima suna magana kafin daga bisani Ayaan ya tashi motar suka miƙi hanyar gida,babu wanda ke ma wani magana acikin motar saboda duk sun tafi duniyar tunani, gaba ɗaya zulluminsu akan haroon,
Koda suka ƙarasa cikin gidan basu shiga da kuɗin ba,acikin motar suka barsu cikin jakar saboda tsaro, sun ajiyeta ne da nufin in dare yayi suzo su ɗauketa su kai mashi,
Bayan sun fito daga motar kaitsaye suka shiga cikin gidan tare da wucewa bedroom ɗinsu don rage gajiyar da suka kwaso,
Sehrish
Tasha kuka kamar kamar me,har sai da zazza6i da ciwon kai mai tsanani suka rufar mata sannan ta lalla6a ta haye saman gadonta ta kwanta,ta jima tana roƙon Allah akan yasa mafarki ne ba gaske ba,abunda ya faru tsakaninta da Aunty azmeenta,gaba ɗaya jikinta baya mata daɗi saboda dama can akwai fargar haroon dake damunta ga kuma wani ciwon kan ya taso mata na Azmee,duk ita kaɗae😢
ta jima tana juyi asaman gadon amma bacci yaƙi ɗaukarta sai ma ciwon nata dake ƙara gaba,fuskarta harta fara kumbura saboda kukan da tasha,dakyar ta lalla6a ta tashi jikinta na kerma ta wuce toilet jin an fara kiran sallar la'asar,bayan wasu ƴan mintina tafito daga ciki tana faman ƙanƙame jikinta saboda sanyin daya rufar mata gashi ta ta6a ruwa,
wurin wardrobe ɗinta ta wuce tare da buɗeta, ta zura hannu ta ɗauki hijab ɗinta ta zurata ajikinta sannan ta ɗauko carpet ta shimfiɗa,sam babu natsuwa ajikinta haka ta kabbara sallar tana karanta fatiha hawaye na wanko mata a fuskarta a haka ta kammala sallar tare da zama saman dardumar ta ɗaga hannayenta sama cikin shessheƙar kuka tashiga cewa"Ya Allah kasa aunty azmee tadawo cikin hayyacinta ta gane cewa ni ba ƙarya nake mata ba,bansan ya zanyi ba in ta juyamin baya,Ya Allah ka yayemun damuwar da nake ciki,ka kawomin sauƙi acikin rayuwata.........' sosai sehrish tashiga jera addu'o'i tana roƙon Allah akan abubuwan dake damunta,
87.
ta jima zaune saman dardumar tana tunanin maganganun aunty azmee,har lokacin tana kokwantan cewa anya Aunty azmee tana a cikin hayyacinta kuwa,
Har kusan ƙarfe biyar sehrish bata motsa ba tana zaune zugudun,sai da biyar da rabi ta yi sannan ta tashi jiki a mace ta cire hijabin tare da naɗe carpet ɗin duka ta haɗa ta jefa asaman gadonta,cikin toilet tashiga ta wanke fuskarta sannan ta fito ta ɗauki mayafi