ABBAN SOJOJI TAKUN TSAKIYA 2 BY BOSS BATURE.txt

Author :  Boss Bature Category :  Arewa Pen

Chapter   23 / 80

66K to 69K   out of 238K words

a duniyar nan saboda na kashe shi,kuma na ɗauko hoton gawarsa don na nuna ma hossana,"
  Wani irin murmushi jahad ta saki har ta gaza rufe bakinta don murna,shima Omar ɗin murmushi yakeyi yana kallonta,

  Nasan dayawa za suyi mamakin yarda akai hakan ta kasance,abun da ya faru shine cikin sojojin dake gadin gidan general ishaq akwai wani matashi Abokin major ne, a lokacin da suka kawo su hussana da jahad gidan Omar ya shiga tare da su ciki , A nan major suka haɗe da wannan saurayin abokinsa ne tun suna yara ,sunan Shi Osman bayan sun gaisa Osman ke cewa "Abokina waɗancan yaran fa? dana ga ka shiga ciki dasu ƴa'yan wanene? ko dai ogan naku ne yayi aure matar ta haihuwa,
Dariya Major yayi tare da cewa "Wai dama Osman har yanzu kana nan da shegen sa idon nan naka? Haba no wonder shiyasa Allah yabarka a matsayin mai gadi, in banda abun ka ina ogan mu yakai shekarun da zai iya ajiye ƴa'ƴa kamar waɗancan? shima fa ba wani babba bane duka shekarunsa bazasu wuce 28 years, matsayi ne kawai Allah ya bashi," jin haka yasa osman ɗan zaro ido tare da cewa "ka ce ashe shima ɗan shila ne, amma dan Allah tun yaushe nake ta fama dakai ka taimaka ka sama mun aiki a ƙarƙashinsa amma ka ƙiya, kafi son kaita ganina a matsayin mai gadin gidan genar, kalli fa yarda na rame nayi baƙi, kai kuwa har wani tumbi kafara ajiyewa saboda jin daɗin rayuwa, wlh abota bata ce haka ba," ya faɗi yana tsuke fuska, dafa kafaɗarsa Major yayi tare da cewa "Ina sane da wannan Osman, kuma insha Allah zanyi ƙoƙari na sama maka gurbi a kusa dashi, mutumin kirki ne sosai yana da sauƙin kai kuma ina jin daɗin aikin dashi,yana kyautatamun domin kuwa kafin ƙarshen wata yayi ina samun ninkin ba ninkin abunda nake samu a albashina wurinsa," jinjina kai Osaman yayi zugudun yayi masa fuskar tausayi kafin yace "Kaji daɗi mutumina,ni dai zan jira naji daga wurinka don Allah karka manta kasa ma mun kusanci dashi, nima na dangwali arxiki,"
Major yace"baka da damuwa, yanzu ma haka ga wani aiki ka samu, waɗancan yaran da kake gani ogan mu yana sonsu sosai, bashi da alaƙar komai dasu hasalima a asibiti ya taimake su,ya kawo su nan ne domin su zauna tare da matar yayansa ishaq, to ni hakan bai kwanta mun araina ba, shi ne nakeso ka sanya mun ido akansu! ka zama tamkar ɗan leƙen asiri duk da nasan hakan ya sa6ama dokar aikin ku amma inaso kayimun wannan Osman,ka lura da duk wani motsinsu acikin gidan nan, so nake kayi aiki tamkar jami'in sirri! dalilin dayasa nayi hakan saboda bana son duk wani abu da zai cutar dasu don na lura da yadda ogan mu ke tsananin ƙaunar yaran,ni kuma bana son duk wani abu da zai 6ata masa rai, ta6a yaran nan tamkar ta6a masa zuciya ne," ya ƙarasa maganar yana kallon osaman da yayi kasaƙai, daga bisani yace "Na amince zanyi hakan, amma wlh ka sani duk ranar da asirina ya tonu, sunanka na ciki ! don ba zan shiga haɗari ni kaɗai ba,"
  dariya major yayi sannan yace"Ai ni babu wanda ya isa ya ta6ani muddin ina tare da Marshal, don haka kaima ka kwantar da hankalinka, ba abunda zai same ka face alkhairi,tunda ka amince zaka yi ɗin, inaso duk wani hali da suke ciki ka tabbatar da ka kira wayata ka sanar mun,"
  Osman ya amsa masa da "toh," daga nan su kayi sallama, a lokacin marshal Omar ya fito daga cikin gidan jikinsa asanyaye suka shiga cikin mota su ka tafi,
  tun daga wannan lokacin Osman ya zaman ɗan leƙen asiri duk wani hali da su hossana ke ciki yana sane dashi kaf, kuma duk rana yana kiran major ya sanar dashi halin da suke ciki, Major bai ta6a sanar da marshal Omar ba, saboda gudun karya shiga tsakanin shi da matar yayansa ishaq,kullum yana sanar da osman cewa yaci gaba da sa musu ido,
  Idan har masu karatu zasu iya tunawa akwai lokacin da Aunty babba tayima su hussana da jahad bugun mutuwar nan, har suka kaisu asibiti bayan sun dawo suka shige cikin gida ita da hafsat suka bar jahad tsaye gaban motar tana kuka saboda hossana na'a cikin motar kwance rai hannun Allah gashi bata iya ɗaukarta bare tashiga da ita cikin gidan, a lokacin idan zaku tuna akwai wani soja daya zo yana tambayarta meke faruwane, take ce masa ƴar uwartace acikin motar kwance bata lafiya kuma bazata iya ɗaukarta ba, sai sojan yace maza "Can i help," take ce masa eh, yasa hannu ya ɗauki hossana ya shigar mata da ita ciki, ya kwantar da ita saman doguwar kujera, yayin da jahad tabisu, to wannan sojan ba kowa bane face Osman abokin major ɗan leƙen asirinsa, ko lokacin da zai fita daga falon bayan ya kwantar da hossana sai da ya ɗan tsaya daga bakin ƙopar ya juyo yana kallon jahad dake zukunne saman guiwarta agaban hossana tana yi mata addu'a tana kuka, jinjina kansa yayi tare da fuce wa bayan yafita, ya ɗauko wayarsa tare da buga ma major kira, bayan ya ɗaga kiran yake sanar dashi abunda ke faruwa, nace wa shifa yana zargin cewa Matar ishaq tayima yaran mugun bugu har ma ɗaya daga cikinsu ta jigita sosai tamkar ba zata rayuwa,don haka ya hanzarta sanar da ogansu Omar yazo ya kwashi yaran tunkan ta kashe su, har lokacin major bai sanar da Omar ba game da wannan ma, saboda yana tunanin koya faɗi masa daker ya yarda kuma yasan makircin mata, abun zai iya dawowa kansa,

Tun da farar safiya Anty Babba ta saka su Jahad wanki, kasa samun natsuwa Osman yayi saboda haka ya tashi ya karasa inda suke wayarsa na kare a kunne tamkar yana waya, ashe video yake yi masu, bayan ya kamamla yin video ne yana turawa major donya gani" Ba karamin tsorata Major yayi ba ganin irin uƙubar da yaran suke a cikin gidan General.

Bayan wannan lokacin kuma sai salon ya canza, duk osman na zuba ido yana kallon ikon Allah, na yarda hafsat ke nuna ma yaran soyayya, aduk lokacin da hafsat ta fita dasu cikin motarta sai osman ya bisu da machine ɗinsa dom yaga ina zata dasu, dashi suke yin duk wani yawo batare da sun san yana tare da su ba, duk inda zasu osman na biye dasu a sirrince,
  A lokacin daya kira Major ya sanar dashi abunda ke faru na cewa yaran fa yanzu suna samun kulawa sosai a wurin mutanen gidan, sai major yace mashi "Wannan salon da suka canza,alama ce dake nuni da cewa sun kusa salwantar da yaran,ina da tabbacin cewa so suke su zubar dasu kaci gaba dasa musu ido,daga yanzu banaso ko bacci ka dunga yi osman, saboda wannan lokacin ne mafi haɗari, aduk lokacin da maƙiyin ka ya canza maka salo na soyayya to kaji tsoransa domin yana daf da halaka"
Tun daga lokacin da Major ya sanar dashi haka, bawan Allah osman bai ƙara yin bacci ba, koda bashi ke akan duty ba, yana nan yana lura da shige da ficen da hafsat keyi dasu hossana,

A ranar da baba alamu zai tafi dasu hossana, akan idon osman Aunty babba ta fito tare da su jahad ta saka su a cikin motar hafsat, duk yana zaune yana kallon duk abinda ke fruwa. Daga bisani kuma sai yaga hafsat tafito hannunta ɗauke da trolley hakan na nufin wani ne zaiyi balaguro, bayan hafsat ta shiga cikin motar taja tafite dasu daga cikin gidan, cikin sauri osman ya hau mashine ɗinsa da yake ajiyesa acikin gidan yabi bayansu, a hankali yake tuƙa mashin ɗin don kar su ganshi, da hafsat ta tsayar da motar abakin titi tana jiran ƙarasowar baba alamu, sai osman ya dakata da tukin mashin ɗinsa, cikin sauri ya sauka tare da samun wuri ya cire rigar jikinsa ta kakin sojoji ya 6oyeta a ƙarƙashin wani benci dake agaban wani shago, sannan ya tu6e wandon jikinsa ma ya ajiyesa a ƙarkashin bencin, bakomai yasa shi yin hakan ba face don karsu ganshi da kakin sojoji yana binsu Asirin shi ya tonu.
   Sai daya rage daga shi sai farar shirt da gajeran wando ajikinsa a lokacin motar baba alamu taƙaraso,cikin sauri Osman ya zuƙunna agaban mashin ɗin tamkar ya samu matsala yana gyaransa, alhalin nan duk salon dabaru ne na jami'ae,
   yana gyaran mashin ɗin yana satar kallonsu, akan idonshi hafsat ta buɗe ma jahad da hossana mota suka fito sannan ta ɗauko masu trolley ɗinsu da food basket ɗinsu ta basu,bayan hafsat ta tafi, baba alamu ya amshi akwatin ya wurga cikin boot ɗin motarsa, daga nan jahad da hossana suka shiga cikin motar, shima ya shiga tare da tashin motar suka tafi, cikin sauri Osman ya haye mashin ɗinsa tare da tashinsa yabi bayan motar baba alamu da gudun gaske, amma bai bari ya ƙurewa motarsa ba kasancewar Motar baba alamu glass ɗin jikinta duk ya fashe, domin muddin osaman ya ƙurewa motar tofa zai iya hango shi, hakan yasa ya basu tazara sosai, yana cikin tuƙin mashin ɗin ya ɗan jinkirta tare da zura hannu cikin aljihun wandonsa ya zaro wayarsa tare da bugama major kira, bayan ya ɗaga yake sanar dashi duk abunda ke faruwa,
Hankali tashe major yace "Osman kada ka bari ya kubce maka, kaci gaba da bin motarsa, sannan kabar wayarka a kunne zamu biyo diddigin layinka har mu zo inda kuke," bayan osman ya amsa masa ya mayar da wayar, sannan ya ƙara ma mashin ɗinsa gudu, a lokacin da motar baba alamu tashiga dajin da gudun gaske, jahad na ƙoƙarin fitowa tana ihu, bayan ta samu nasarar balle murfin motar ya buɗe, sai baba alamu ya girgiza motar da mugunta, ta faɗo ƙasa timmmm goshinta ya bugu, ta taso da gudu tana bin motar tana kiran sunan hossana daga bisani ta yanke jiki ta faɗi, adai-dai lokacin shi kuma osman ya ƙaraso ba komai yasa shi yin jinkiri ba fa ce wayar da yayi da major shiyasa bai ƙaraso akan lokaci ba har baba alamu ya kubce mashi,
ganin jahad da yayi yashe a ƙasa ga kuma jini na zuba a goshinta ya sashi razana, cikin hanzari yayi wurgi da mashin ɗinsa ya nufeta, zuƙunawa yayi a gabanta yana faɗin "ke!ke!! tashi ki tashi dan Allah, kada ki mutu,"
Adai-dai lokacin kuma motarsu Marshal Omar ta faso cikin dajin ta hanyar tracking layin osman da sukayi yasa har suka ci nasarar cimma inda yake,
Osman na ganin motarsu Marshal yasan cewa sune aciki, a lokacin omar ya zuge glass ɗin motar a tsorace ganin jahad kwance duk jini a goshinta, harya harzuƙa zai fito daga cikin motar, cikin sauri Osman yace "yalla6ai ya gudu da ɗayar, gashi can ya miƙi hanyar dama da ita, don Allah ku ceci rayuwarta," jin haka yasa Omar fasa fitowa daga cikin motar, cikin sauri major yaja motar da gudun gaske suka bi motar baba alamu a lokacin ya ɗanyi masu nisa, hayaƙin da bayan motar baba alamu ke fitarwa shine yasa suka gane hanyar da yabi,
suna isa basu tsaya buɗe kopar katakon gidan gonar ba, kai tsaye major yabi ta ƙopar atsiyace ya tarwatse.

*Wannan shine abunda ya faru taƙaice kenan*

"Ya omar ina hossana take ita'? Omar yace"hossana tana cikin ƙoshin lafiya, itama ƙarin jini akeyi mata, yanzu haka bacci take sha tana a kusa da ɗakin nan," ajiyar zuciya jahad ta saki kafin ta kuma cewa "ya omar kullum hossana saita ambaci sunanka, komai akayi sai tace "ya Omar fa," ita bata son rabuwa da yaya omar ɗinta,"
Murmushi Omar ya saki jin abunda jahad tace,
"Amma ya Omar ba zaka ƙara rabuwa damu ba ko? dan Allah kada ka haɗamu da kowa kabarmu kawai a wurin ka, kai kaɗai ke son mu," tayi maganar idonta akansa tana jiran amsar shi,
Omar yace "ko wancan time ɗin bada son raina nabar ku ba, jahad you're always in my mind ina jin ku araina,amma yanzu komai ya wuce just forget about the past, ku ƙaddara cewa wani abu bai ta6a faruwa da rayuwarku ba na ƙunci, saboda yaya omar ɗinku ya shirya maku kyakkyawar rayuwa ta jin daɗi da walwala, masarauta ce wadda ku kaɗai zaku mulketa sai yadda kuka ga dama zakuyi acikinta, hatta yaya omar ɗinku zai zama tamkar bawa agare ku,"
dariya kawai jahad ke faman tiƙa saboda murnar jin abunda omar ke cewa, hatta dr Emran da Camila dake tsaye murmushi kawai suke saki, shima major dake tsaye daga ƙopar ɗakin murmushi ne a fuskarsa, ƙarasa shigowa ciki yayi yana cewa "Sir idan ba damuwa inaso a bani muƙami acikin masarautar nan, zanso na zama sojan dake kula da princesss ɗin dake acikinta, bama ni kaɗai ba ga abokina osman nan shima yana roƙon gimbiya jahad da ta bashi damar zama ɗaya daga cikin masu kula dasu,"
Abun sai ya zama tamkar shirin wasan kwaikwayo gaba ɗayansu dariya ce a fuskarsu, hakan ba ƙaramin farantawa omar rai yayi ba ganin yadda jahad ke faman tiƙar dariya, sai yaji sanyi aransa sam ya gaza janye idonsa akanta,
Muryar Camila (kameela) ce ta katse su da cewa "Yalla6ai nima idan ba damuwa ina neman alfarmar zama ɗaya daga cikin masu yi ma gimbiya jahad hidima, ko da a matsayin jakadiya ne mafi kusanci dasu,"
Fashewa da dariya jahad ta ƙara yi daga kwancen da take har omar na cewa "Bi a sannu my baby, kada ki shaƙe,"
gaba ɗayansu sun natsu sai raha akeyi, suka ji Muryar hosana kamar daga sama tace"YA OMAR,"
Atare suka juya suna kallonta, tsaye take a bakin ƙopar ɗakin daker take buɗe idanunta tana kallonsu, hannu tasa ta murza idonta sannan ta ƙara buɗe su da kyau donta tabbatar da abunda idonta ke gane mata, tabbas kuwa shine wato yaya Omar ɗinta,
tsananin farin ciki ne yasa hossana ƙarasa shigewa ciki da gudun gaske tana isa inda Omar yake ta zube saman guiwowinta tare da kifa kanta asaman laps ɗinsa tana kuka,
Shiru su kayi gaba ɗayansu na wani lokaci suna sauraren kukan da hossana ke yi, gaba ɗaya jikin omar ya gama mutuwa saboda yasan yarda yarinyar ke tsananin ƙaunarsa dole tayi kewarsa, hannu omar yasa tare da shafa gashin kan hossana cikin muryar lallashi yace "Am so sorry hossana,nasan nayi laifi ban ma san da wane baki zan iya baki haƙuri ba,"
Maimakon ta ɗago sai ta daddage ta gartsa mashi ciwo a laps ɗinsa, runtse ido omar yayi saboda yaji zafin cizon, babu wanda ya lura da abunda ke faruwa sai jahad, tun da taga omar ya runtse ido tasan cewa Hossana Cizon shi tayi,

tayi mashi hakan ne don yasan irin raɗaɗin da suka ji acikin zuciyoyinsu na ƙin zuwan da yayi ya tafi dasu,
buɗe idonsa yayi a hankali yana sauke ajiyar zuciya ya kalle ta, a lokacin itama ta ɗago tana faman huci ta ɗaure masa fuska tare da haɗe masa girar ƙasa da sama tana kallon shi,
Cikin sanyin murya ya sake maimaita "Am sorry again," ya furta tare da kai hannunsa a fuskarta yana share mata hawayenta dake kwaranyowa daga idonta,
Cikin kuka tace "Ya omar yanzu ka kyauta abunda kayi mana? ka tafi kabarmu cikin tashin hankali ko waiwayon mu, ba kayi ba yanzu da mun mutu shikenan bazan sake ganin Ka ba sai dai a lahira ko?
ƴar dariya omar yayi tare da cewa "Amma ae yanzun baku mutu ba ko? Kuna raye kuma ga yaya Omar ɗinku atare daku, mai yayi saura yanzu"? ya tambaya yana kallonta
Hossana tace "sai ka kaimu gidan ku inda kake rayuwa, don wlh duk inda zaka je, ƙafarka ƙafarmu, mu da kai mutu ka raba takalmin kaza," ta ƙare maganar tana zumbura baki,
Gaba ɗayansu na cikin ɗakin dariya kawai suke yi, Kallon dr emran omar yayi kafin yace "yanzu mai ya rage dr?yaushe kake tunanin za'a sallame su, in yaso sai acigaba da basu kulawa acan gida?
dr emran yace "zuwa night, ae jikinsu yayi ƙarfi yanzu saboda ƙarin jinin da akayi masu, idan ma ba damuwa Camila zata iya cigaba da kula da lafiyarsu, in har kana buƙatar hakan, tunda dama naji tace tana son zama hadimar princess ɗin naka,"
Murmushi suka saki gaba ɗayansu banda hossana don batasan zancen ba, tuni ta mayar da kanta akan laps dinsa tana faman sauke ajiyar zuciya,

dukkan tsanani yana tare da sauƙi, mahaƙurci kuma mawadaci ne wata rana, babu wani yanayi na rayuwa da yake kasance wa na dundundun, Innallaha ma'assabirin tabbas wannan haka yake, iya haƙuri dae su hossana sunyi kuma sun jurema duk wata jarabawa da suka fuskanta na ƙuncin rayuwa, basu fasa yin addu'a ba suna kai kukan su ga Allah ba kuma basu fidda rai da cewa Allah zai kawo masu ɗauki ba, idan muka sa haƙuri kowa zai cimma nasara, gashi yanzu zamu iya cewa Masha Allah 😍👑

**************Twins *******************
daker suka samu suka yi wanka suka canza kaya izuwa jeans da t-shirt suka fito wuraren ƙarfe 5 na yamma, tafiya suke yi gabansu na faduwa tsoransu kar suci karo da haroon don yanzu ya zamar masu tamkar dodo, suna cikin tafiya sai ga Junaid ya fito daga upstairs yana ganinsu ya ɗan zaro ido cike da murna yace "Yaya Jahan ina kuka shiga inata neman ku, naga da safe ko breakfast ba kuyi ba, duk na shiga damuwa," ya yi maganar tare da ƙarasa saukowa down ɗin yayi ya tunkaresu, suna tsaye baki asake suna kallon shi saboda neman shi suke yi ruwa a jallo,
yana ƙarasawa yabi su ɗaya bayan ɗaya yayi hugging ɗinsu tare da manna musu kiss a gefen fuskarsu, irin gaisuwar da suka saba,
Ganin sun zuba mashi ido batare da sunyi mashi magana ba yasa shi bubbuga ƙafarsa tare da cewa "Dan Allah wai menene haka duk kun Canzamin, ko magana

23 / 80