Author : Boss Bature Category : Arewa Pen
gaske ta nufi motarta saboda tunawa da tayi da Motar da tagani ta gifta ɗazu da kukan yarinya acikinta,
buɗe motar tayi tare da shigewa ciki taja ta da gudun gaske,tana jiyo muryar waɗannan matasan suna cewa"Aunty Allah tsare hanya,"
***************************
SEHRISH
Sam ta hana idanunta bacci saboda jiran dawowar babban yaya,yau harya haura lokacin daya saba dawowa hakan ba ƙaramar damuwa ya jefata ba,harta sauya kayan jikinta izuwa na bacci riga da wando masu laushin gaske orange colour,tun wuraren ƙarfe sha biyu daidai takai mashi fruit a ɗakinshi,Coffee ne kawai bata kai mashi ba saboda tasan cewa bazai shaba idan ya salafce,don ta lura cewa yafi buƙatar shi da zafi zafinshi,don wani sa'en har yana tururi yake shan shi,
sai faman safa da marwa takeyi acikin ɗakin har sai da ƙafafunta suka soma yi mata raɗaɗi sannan ta koma tare da samun wuri gefen gadonta ta zauna,lokaci guda kuma ta soma sakin hammar bacci,duk yarda sehrish taso ta hana kanta bacci amma abun yaci tura,sai gata kwance abaje tana ta faman sharar bacci asaman gadonta,
da yake ta sama ranta abun sai gashi ta farka wuraren ƙarfe daya na dare,daƙyar ta iya mikewa tsaye tana kallon clock ganin ɗaya ta buga yasa taji gabanta ya faɗi rasss,tsoranta kar ace ya dawo tana cikin sharar baccin nan,
Cikin sauri ta taka izuwa wurin window ɗinta,hannu tasa tare da janye curtains din sannan ta zuge glass ɗin tana hangen wajen harabar ajiye motocinsu,anan ta hangi motarshi ajiye alamar ya dawo kenan,
dafe saitin zuciyarta tayi gabanta na faduwa a fili tace"Nashiga uku ashe ya dawo,yanzu ya zanyi kenan nasan ranshi zai iya 6aci akan ban kai mashi coffee ɗin ba,"
cike da takaici taja guntun tsoki tare da cewa"duk wannan baccin ne daya ɗauke ni,da hakan bata faru ba,yanzu ya zanyi kenan gashi dare ma yayi sosai,in naƙi kai mashi matsala, in nakai mashi ma hakan zai iya jamin wani abun kuma,"
taƙarasa maganar tare da yanke shawarar takai mashi kawai,hannu takai tare da daukar mayafinta,ta rufe kanta dashi,sannan ta zura silifa aƙafarta,a hankali ta buɗe ƙopar ɗakin kamar mara gaskiya haka ta dinga tafiya har ta isa kitchen,shiga ciki tayi tare da wuce wa kai tsaye wurin cupboard,hannu tasa tare da curo cup ɗin data ware mashi nashan coffee ɗinshi,batare da 6ata lokaci ba ta zuba mashi coffee ɗin da zafin shi aciki cup,asaman plate ta aza mashi kofin sannan ta nufi hanyar fita,tana ƙoƙarin fita daga cikin kitchen ɗin sai ga Hayaam ta faɗo ciki,ba ƙaramin tsorata Sehrish tayi ba don har saida takusa zubar da coffeen dake hannunta,ido azare take kallonta don bata tsammaci mutum ba adai dai irin wannan lokacin,
tun da tazo gidan take ƙumshe aɗakinta tana baccin lalaci,koda ta farka bata fito waje ba,sai yanzu Allah yayi ta samu ta fito,short gown ɗin nan ce ta ɗazu ajikinta,kan nan nata ko arziƙin dankwali babu balle mayafi,sai dai gashin kanta data ɗaure abayanta,
Murya a sanyaye sehrish tace"Sannu da fitowa,ya gajiyar tafiya,"
Ƙayataccen murmushi hayaam ta saki tare da cewa"yawwa ƴan mata,gajiya tabi jiki yanzu ina jina normal,"
Ta ƙarasa maganar tare da kallon cup din dake ruke a hannun sehrish tace"Wannan fa?ke zaki sha ne"?
girgiza kai sehrish tayi tace"a'a banawa bane,babban yaya zan kaimawa ne,"
yamutsa fuska Hayam tayi tare da cewa"Oh ashe ya dawo cikin gidan kenan,"
Sehrish tace"eh,ya dawo,"
"ra'ayin kanki ne kai mashi coffeen ko kuma shi ya buƙata ne"?ta kuma jifarta da tambaya,
"Ai shi ba'a yi masa katsalandan,shi yace na rinƙa kai mashi a kullum wuraren ƙarfe sha biyu idan sun dawo daga aiki," ta bata amsa tare da kama hanya zata wuce,
Cikin sauri hayaam ta sake shan gabanta tare da cewa"gaskiya bai kamata ace ƙaramar yarinya kamarki tana kai mashi abunsha adai dai irin wannan lokacin ba,sam wannan tsarin baiyi ba,yakamata ace yanzu kina kwance kina bacci ko don saboda zuwa school yana da kyau ki rinƙa yin bacci da wuri,"
..murmushin yaƙe sehrish tayi sannan tace"nagode da shawararki,amma wannan aikina ne kula dashi,kuma nasaba da yin hakan"
ganin hayaam zata 6ata mata lokaci yasa tayi saurin wuce wa batare da ta saurari sauran abunda zata ce mata ba,
jinjina kai hayaam tayi tare da cewa"yarinya dani kike magana,wato har wani faɗamun take itace mai kula dashi,shisshigi kawai da kutsi," ta faɗi hakan tare da jan dogon tsoki ta wuce bedroom ɗinta,
lokacin data ƙarasa part ɗinshi baya acikin falon hakan yasa kai tsaye ta wuce bedroom ɗinshi,sallama tayi mashi amma shiru ba'a amsa mata ba,almost 4 times tana zabga mashi sallama amma tsit babu alamar za'a amsa mata,
saurarawa tayi don taji ko zata ji motsin shi aciki,nan ma shiru ranta ne ya bata cewa kawai tashiga cikin bedroom ɗin nashi,
ƙafa tasa tare da shigewa ciki,nan take ƙamshin turaren nan nashi ya daki hancinta har saida ta ɗan ja da baya saboda yarda ƙamshin ya shigeta kai tsaye,sauke ajiyar zuciya tayi tare da ware idanunta tana bin bedroom ɗin nashi da kallo,wayamm tagani babu shi acikin ɗakin,tsayawa tayi tana tunanin ko'ina ya shiga ne,kodai bai dawo bane?amma kuma ae ga motarsu can awaje alamar sun dawo,har ta yanke shawarar barin ɗakin,zata juya kenan eyes ɗinta suka sauka akan fruits ɗin da takai mashi,wanda ta ajiye mashi asaman table din dake kusa da gadonshi,a rufe takai mashi kayan marmarin amma sai taga an cire plate din data rufe su dashi,alamar ya fara shan fruits ɗin kuma ya dakata,ranta ne ya bata cewa may be yana acikin toilet ne,
murmushi ta ɗanyi sannan ta ƙarasa wurin table ɗin tare da ajiye mashi cup of coffee din agefen kayan marmarin,
tsayawa tayi tana tunanin ko dae ta tsaya ya fito daga cikin toilet ɗin wata'ƙil zai buƙaci wani abun bayan wannan,wata zuciyar kuma ta bata shawarar cewa ta tafi kawai tabar dakin saboda dare yayi sosai,
tana cikin wannan tunanin,sgr ya fito daga cikin toilet,waist ɗinshi na ɗaure da short towel wanda bai kai guiwar ƙafafunshi ba da alama wanka yayi aciki,
sam bai lura da mutum a cikin bedroom ɗin nashi ba,gadan gadan ya tunkari wurin dressing mirror ɗinshi,cikin rashin sani tafin ƙafarshi ya hau saman 6awon ayabar daya ci ɗazu, daya maƙale masa a jikin shirt ɗinsa saida zai shiga wanka ne ya lura dashi yasa hannu ya ka6e shi ya faɗi anan ƙasa,aikuwa nan take wani irin mugun sul6i ya kwashe shi bazato ba tsammani, gaba ɗaya ya tafi a burkice zai faɗi,a firgice sehrish ta juya tare da yin ƙoƙarin taimaka mashi cikin sauri ta ruƙo shi nan take ƙarfin shi ya rinjayi nata gaba daya suka faɗa saman shimfiɗeɗen gadonshi manne da juna,tashin hankali da ba'a sama shi date,
wata irin nauyayyiyar azuciyar zuciya Sgr yashiga saukewa,tabbas ya ɗan firgita saboda bai tsammaci hakan ba,bai ta6a yin irin wannan gangancin ba,hada ƙarin sam ya manta da 6awon ayabar a wurin bai jefa shi dustbin ba,da ace sehrish bata ruƙo shi ba awannan lokacin da ba ƙaramin buguwa zaiyi ba yanda yake dogon nan,
atare zuciyoyinsu suka shiga bugawa da ƙarfi da ƙarfi,gaba ɗaya sehrish ta gama tsorata, don jin abun tamkar a amafarki take ganin shi,ta gaza yarda cewa itace tare da Surgeon general Rafayet kwance asaman gado ɗaya kuma amanne da juna,
gaba ɗaya jikinshi ya rufe nata hatta face ɗinta tana a saitin wide chest ɗinshi,tana jin yarda yake ta faman sauke ajiyar zuciya,da kuma yarda heart ɗinshi ke beating very fast,
tsit kake ji daga ita harshi an rasa mai wani kwakkwaran motsi,danshin ruwan dake ajikinshi ba ƙaramin sanyaya mata jikinta yayi ba,daƙyar take iya breathing saboda hancinta daya manne da fatar ƙirjinsa,haka la66anta ma suna manne da fatarshi,
Boss man ɗin fa ya gaza ɗago da jikinshi daga nata,ba don komai ba sai don yarda abun yazo mashi unexpected,ba ƙaramin jinjinawa lamarin yayi ba shi kanshi,
Jin yarda yarinyar keta kokawa wurin fitar da numfashinta,yasa ya daure tare da yunkurawa zai tashi daga jikinta,baiyi wani aune ba towel din dake ɗaure a qugunshi ya shiga warwarewa gaba daya dama daurin ya saki,
Shi kanshi baisan lokacin daya mayar da jikinshi asaman nata ba ya kwantar da kanshi a saman left shoulder dinta,bakomai ne yasa yayi hakan ba face gudun kar towel din jikinshi ya saki agabanta,don muddin hakan ta faru tofa wannan karon ba sume mashi zatayi ba,zuciyarta ce zata buga tabar duniyar saboda tsabar firgici don ya lura yarinyar ba ƙaramar matsoraciya ba ce,
wani irin yanayi mara misaltuwa taji atattare da ita,jikinta yayi wani irin sanyi sanyi kasala kasala haka,sam bata jin nauyin jikinshi akan nata sai ma yanayin da hakan ya jefa ta,
idanunta na'a rufe sam tagaza buɗesu ba don komai ba sai don tsoran abunda zai biyo baya,a matuƙar tsorace take hakan yasa ko kwakkwaran motsi tagaza yi,lumshe idanunshi yayi yayin da hancinshi ke gogar fatar wuyanta,fragrance ɗin turarenta ne yake kaimashi ziyara acikin hancinshi,ƙamshin ba ƙaramin daɗi yayi mashi ba,har lokacin tana jin yarda numfashinshi ke fita afatar jikinta,
almost 15mins suna cikin wannan yanayin, a hankali ya hannunshi daidai kugunshi don ya gyara ɗaurin towel din, moving ya runka yi da hannunshi yana gogar jikinta, wanda hakan da yake yi ba ƙaramin kashe mata jiki yayi ba, ji tayi ta shiga wani irin yanayi mara misaltuwa...
sai da ya samu ya ɗaure towel ɗin sannan a ƙaro na biyu ya ɗago da kanshi don ya raba jikinshi daga nata,nan take sehrish ta saki wata irin razananniyar ƙara da ta gigita shi,ashe dan kunnen tane sargafo gashin kanshi, wannan ɗagawar da zaiyi ajikinta shine sumar kanshi taja ɗan kunnan nata da ƙarfi wannan ne dalilin dayasa ta fasa ƙara,cikin sauri Sgr ya mayar da kanshi tare da kwantar dashi agafen fuskarta,fashewa da kuka sehrish tayi sosai saboda ba ƙaramin zafi taji ba,don wurin harya fara fidda ɗigon jini,a hankali ya buɗe blue eyes ɗinshi tare da bin kunnan nata da kallo yarda sumar kan nashi ta harɗe acikin earring ɗin shine yafi komai bashi mamaki,tunani ya soma yi taya za'ai ya cire gashin nashi acikin ɗan kunnan nata?dole akwai buƙatar yabi a hankali wurin zagayo da hannun na dama don ya cire shi,
A hankali ya ɗago da fuskarshi daga gefen fuskarta,ya kasance cewa suna facing ɗin juna sosai,hatta numfashinsu yana haɗewa dana juna,wannan shessheƙar kukan da takeyi ne yaja hankalinshi wurin kallon fuskarta,la66anta har kerma sukeyi yayin da idanunta ke arufe,
Muryar shi ce ta katseta da cewa"I don't wanna hear that sound again,"
Cikin sauri sehrish ta tsagaita dayin kukan gaba daya,ta koma tana faman sauke ajiyar zuciya,
buɗe idanunta tashiga yi waɗanda ke cike tab da ruwan hawaye,tun kafin ta ƙarasa ware idanun nata take hangen hasken blue ɗin kwayar idanun shi,a hankali ta ƙarasa buɗe idanun sosai akan kyakkyawar fuskarshi dake fuskantar tata,duk da irin bugun zuciyar da take ji amma hakan baisa ta mayar da idanunta ba ta rufe su,
A natse ta soma bin pink lips ɗinshi da kallo shape ɗinsu ba ƙaramin kyau ne dasu ba, mayar da eyes ɗinta tayi akan dogon hancin shi da tsinin ke dab da nata hancin,ta jima tana kallon hancin nashi daga bisani kuma a hankali ta aza idanunta acikin nashi nan take taji wani irin bugun zuciya,
sai faman lumshe idanunshi yake yana kuma opening ɗinsu saboda baccin da yake ji,dama agajiye ya dawo cikin gidan,a hankali yake ɗan waresu akan idanunta,anatse yake bin long eyes lashes din idonta da kallo,har yanzu akwai sauran tears dake dripping a cikin idonta.
Eyes balls ɗinta yabi da kallo a lokacin itama nata na'a kan kwayar idon tashi tana ƙarewa launin idon nashi kallo,kasa janye idanunshi yayi acikin nata,kamar yarda itama tagaza janye nata acikin nashi duk da tsoran kwayar idon nashi da take ji,
Suna cikin wannan yanayin a hankali ya zagayo da right hand ɗinshi ta saman kanta,ya ƙaraso dashi wurin ɗan kunnan nata sannan ya haɗa da hannun shi na hagu ya shiga ƙoƙarin cire gashin nashi da yake jikin dan kunnen nata,
runste ido sehrish tayi saboda zafin da take ɗan ji a wurin,ganin hakan yasa ya haɗe fuskokinsu awuri guda,jin yarda lips ɗinsa suka manne da nata tamkar zaiyi kissing ɗinta ya sana rasa nutsuwarta.
duk yarda yaso ya cire gashin daga jikin ɗan kunnan abun ya gagara ganin hakan zai 6ata mashi lokaci yasa yayi deciding tsinka gashin kan nashi daga jikin dan kunnen.
Cikin sa'a ya katse gashin nashi yabar mata sauran siraran da suka ruƙo dan kunnan nata,
Sai da ya raba ɗan kunnan sannan yaji wata irin kasala ta baibaye shi,lokaci guda ya rasa karfin janye jikinshi daga nata,ya dai samu ya ɗan janye face ɗin shi daga nata,sai dai kuma ya koma asaman boobs ɗinta,lamo yayi yana jin wani irin yanayin da bai ta6a ji ba arayuwarshi har wani bacci sosai ya dinga fisgarshi,sehrish kuwa tuni bacci yayi awon gaba da ita don bazata iya jurewa wannan yanayin ba,hannunta na asaman kugunshi ta ƙankame shi sosai ajikinta,hada ƙarin hakan ya ƙara kashe mashi nashi jikin,
Mamakine ya kama hayaam ganin cewa har yanzu Yarinyar bata fito daga part ɗin sgr ba,ashe tun bayan da sukayi magana da sehrish ta koma bedroom ɗinta sam tagaza samun natsuwa shine ta dinga leƙowa don taga ko yarinyar ta fito daga part ɗin nashi,amma shiru babu alamar cewa ma zata fito,hakan ba ƙaramin ƙona mata rai yayi ba,nan tashiga zargi kala kala acikin zuciyarta tana cewa"ko uban mi ya tsayar da ita ɗakin shi a irin wannan lokacin,ni dama banyarda da yarinyar can ba,daga ganinta irin sumu-sumu kasau ɗinnan ne,wlh saina yi maganinta bazan bari taci gaba da shiga sashen shi ba,
tun tana sa ran fitowar sehrish harta haƙura ta koma bedroom ɗin data sauka,shiga ciki tayi tana ta faman sambatu kamar wata zararra duk akan sehrish ne take wannan 6acin ran,
******************
*Junaid Romeo*
Bacci yake yi amma gaba ɗaya jikin shi kerma yake yi sosai da sosai,sai faman mutsu mutsu yake yi da alama baijin daɗin jikin shi,wata irin Zufa ce take tsattsafowa daga jikin shi saƙo da lungu na jikinshi gaba ɗaya ya kasance ajiƙe yake sharkaf,a wani irin firgice Junaid ya farka arazane yana faman zazzare manyan idanunshi da suke cike tab da kwalla,
Yana ƙoƙarin kai hannu ya tashi Abbansu dake kwance a gefen shi,sai ga wani baƙin hayaƙi ya fito daga Cikin mirror ɗin ɗaƙin mai yawan gaske baƙi wulik,bin hayaƙin junaid yayi da idonshi yana kallon shi a matuƙar tsorace,tattarewa hayaƙin yayi wuri guda kai tsaye ya nufi wurin shi,gaba ɗaya ya tunkare shi,ganin hakan yasa junaid faɗawa jikin abban nasu tare da ƙanƙame shi gaba ɗaya duk yabi ya firgice,kafin Abban nasu ya farka tuni wannan baƙin hayaƙin ya mamaye jikin junaid ta ƙofar hancin shi yabi ya dinga kurɗaɗawa cikin jikinshi,fashewa da matsanancin kuka junaid yayi yana ambaton sunan abban nasu,"Abba ka tashi dan Allah,abba pls ka tashi,bansan meke shirin faruwa dani ba,Abba ka tashi kaga halin da baby junaid ɗinka yake ciki",
duk wannan koke koken da junaid keyi abun mamaki ko motsi Abban nasu baiyi ba,sosai junaid ya dinga jijjiga jikinshi yana ambaton sunan shi amma shuru bai farka ba,babu alamar cewa zai farkama,
Allah sarki,sun sangartar da junaid sosai wanda hakan yasa bai iya ambaton wata addu'a acikin bakin shi ba,sai ihu da yake yi yana koke koke,ko addu'ar bacci wannan junaid bai ta6a yi ma kanshi ba,saboda ya saba kullum in Abbansu na nan shike yi masu addu'ar su kwanta atare,in kuwa abbansu bai nan anyhow yake baccin shi batare da tunanin yin addu'a ba,tsantsar son da suke yi mashi ne yasa basu son ya wahala ko kaɗan,junaid bai ta6a zuwa islamiyya ba don koyon wani abu na addini,amma Abbansu da kuma ƴan uwanshi suna zaunar dashi su koyar dashi wasu abubuwan sosai,a kwanakin baya har malami abbansu ya samo wanda zai dinga koya mashi karatu,tun rana ta farko da malamin yazo zai koya mashi karatu basu ƙara ganinshi ba,6at aka neme shi aka rasa,kusan sau huɗu hakan na faru duk in Abbansu ya samo malamin da zai koyar dashi addini daga yazo sau ɗaya sai a neme shi arasa,hakan yasa daga baya ya haƙura da neman malaman da zasu koyar dashi,musamman da yaga ƴan uwanshi na koyar dashi acikin gidan sai hankalinshi ya kwanta da hakan,abun da baisani ba kosu da suke koya mashi agabansu yake nuna ya fahimta kuma ya gane karatun amma da zarar yabar wurin karatun tofa komai ya zube acikin kanshi,yadawo zero 0
Wani irin sanyine ya gauraye ko'ina na sassan jikinshi,lamo yayi abayan abban nasu yana faman sauke ajiyar zuciya,a wannan yanayin kuma bacci yayi awon gaba dashi,🥺
Meke shirin faruwa ne!?
96.
A hankali ta soma buɗe idanunta dake ɗauke da bacci biji biji ta soma gani kafin daga bisani suka washe ta dinga ganin komai normal,jin babu nauyin mutum akanta yasa ta gane cewa sgr ya bar jikinta,cikin sauri ta miƙe zaune tare da kai idanunta inda yake kwance yana bacci,zuba mashi ido tayi tana kallon shi,yanayin yarda yake baccin zai tabbatar maka da cewa yana cikin kwanciyar hankali da natsuwa,
A hankali takai hannu tare da jan blanket ɗinshi ta rufe mashi jikin shi har wurin wuyan shi sannan ta saki bargon,
tamkar karta tafi tabarshi haka ta dinga ji,hannu takai tare da ruƙo sumar kanshi mai laushin gaske,ta tattare mashi ita tare da yin gefe guda da Ita,hakan ne ya bata damar kallon kyakkyawar fuskarshi sosai,
Cikin sanyin murya tace"inason farin ciki ya cigaba da wanzuwa a wannan kyakkyawar fuskar taka,kuma insha Allah zan tabbatar da hakan,zan cigaba da addu'a akan Allah ya mallakamin kai amatsayin abokin rayuwata,duk da nasan cewa zaiyi wuya hakan tafaru saboda kafi ƙarfina sosai nesa ba kusa ba"
Jiki asanyaye taƙarasa maganar yayin da ta juya tare da saukowa daga saman gadon nashi,sai da tafara kashe mashi hasken ɗakin sannan ta fuce daga part ɗin nashi,
A 6angaren Amani kuwa tunda tabi bayan motarsu da gudun gaske,bata ci nasarar taddo tasu motar ba saboda suma gudun sukeyi tuni sun 6ace ma ganinta,jiki asanyaye tayi parking ɗin motarta agafen titi,tamkar zata fashe da kuka haka ta dinga ji,hannu takai tare