Author : Boss Bature Category : Arewa Pen
ethiopia," Jahad ta bata amsa atakaice, kafin hossana ta ƙara cewa wani abu, sai ga Camila tafi to daga toilet din daga ita sai ɗan pant da bra, cikin sauri suka sanya tafukan hannayensu tare da rufe fuskokinsu cikin jin kunya,
tsayawa tayi tana kallonsu cikin mamaki take cewa"why are u hidding ur face pls? Can i know
Jahad tace"mun ji kunya ne,"
Murmushi camilla tayi tare da girgiza kai tace"kuna da kunya sosai,in dae haka ne kam ba zaku iya rayuwa a ƙasar mu ba,"
"Wata ƙasa ce"? Hossana ta tambaya,
Camila tace "Mexico,"
Jinjina kai tayi tare da cewa"ni ko sunan ƙasar ma ban ta6a ji ba gsky...."jahad ce ta katse ta da cewa "hossana zoki wuce kije kiyi wankan kema,"
Amsa mata tayi da toh sannan ta wuce cikin toilet ɗin,
Ita kuma jahad ta kama hanyar fita daga ɗakin har lokacin fuskarta na rufe da tafin hannayenta, abun sai ya ba camilla dariya sosai,
Sai da ta fita daga bedroom ɗin sannan ta soma sauke ajiyar zuciya, shiga cikin falon tayi, tana ƙare masa kallo, zagaye shi ta shiga yi tana tatta6a dogayen curtains ɗin dake kewaye dashi,
Sallamar Osman ce ta dakatar da ita, cikin sauri ta amsa mashi da wa'alaikum salam,sai da ya fara tambayar iznin shiga daga ciki, ta amsa mashi sannan yasa kai cikin falon,
Hannun shi na ruƙe da manya ledoji na abincin da yayi masu oder a restaurant,yarda yaga jahad ta kimtsa tamkar ba ita bace ya gani acikin daji ba sume cikin ciyayi,ba don akwai dressing na ciwo a forhead dinta ba, da bazai iya shaida taba,
.murmushi kawai yayi tare da miƙa mata ledojin hannun shi, cikin sauri tasa hannu ta kar6a tana yi masa godiya,
Har ya juya zai fita sai kuma ya juyo ya kalle ta yace"pls game da abunda ya faru da ku a gidan yayan Omar,wurin matar yayan shi kada ku sanar dashi komai don nasan zai tambaye ku ne,
Murmushi jahad tayi tace"insha Allah ba zamu sanar mashi ba,"
"Yawwa" ya faɗi tare da juyawa yasa kai ya fuce,
Ajiyar zuciya ta sauke tare da ajiye ledojin a saman table,tana jiran su kammala kimtsa wa su fito suci atare,
Goya hannayenta tayi a ƙirjinta tana faman sakin murmushi,bakowa ne ke faɗo mata aranta ba face yaya Omar dinsu,ta ƙosa ta sashi a idonta saboda tayi mashi godiya sosai,kuma tayi missing din wannan kyakkyawar fuskar tashi,
tana cikin wannan tsayuwar sai ga Camila ta fito fes abunta har ta canza kayan jikinta,v neck shirt ce ajikinta fara sai wando jeans, ta ɗaure sumar kanta da ribbom,fuskarta asake ta ƙaraso tare da samun wuri saman 3 seater ta zauna tana kallon jahad tace"kina so ciwon naki ya dawo sabo mu koma asibiti gobe ko?
Girgiza kai jahad tayi tare da cewa"a'a bansan na take ta bane,ciwon bai mun zafi yanzu ina ji kamar naji sauƙi ma,"
Tace "duk da haka yakama ki kula just in case,"
Amsa mata tayi da toh sannan tace "ga abinci nan,an aiko mana shi," ta fadi tare da ƙarasawa wurin table ɗin ta matsar mata dashi kusa da kujerar da take zaune,
Sannan itama ta samu wuri ta zauna a kusa da ita,hannu camila tasa ta buɗe ledar ta farkon,kayan ciye ciye ne gasu nan chips, bugger, shawarma da sauran wasu tarkacen, ɗayar ledar kuma da ta bude masu fried meat ne (tsiren nama) mai yawan gaske yaji kayan haɗi sai ƙamshi yake yi,
Dole ne su buƙaci plate don haka jahad ta tashi tare da cewa "bari na ɗauko mana plate," camila tace "plate yayi kaɗan tray zaki samo mana,"
Amsa mata tayi sannan ta tunkari doors din dake a cikin falon tana neman kitchen babu alamar kitchen na a wurin,
"Ki duba down stairs baza arasa acan ba," acewar camila,
Cikin sauri jahad ta hau benen da zai sauke ta a dowm stairs tana sauka cikin sittingroom din ta hango kitchen ɗin, tasha mamakin ganin yarda aka ƙawata ɗakin,
Cikin hanzari ta wuce kitchen ɗin an tsara shi sosai,ƙarasawa tayi jikin kitchen shelves anan ta samu trays a jere ta ɗauki ɗaya,komai na cikinsa sabone wasu acikin kwalinsu wasu kuma a buɗe suke, tare da cokali ta haɗo masu da knife saboda taga tsiren naman basu zuge shi ba acikin tsinken shi yake,zasu buƙaci su yayyanka shi in zasu ci,
Fitowa tayi daga kitchen ɗin sannan ta koma upstairs ɗin, tunkan ta ƙarasawa ta samu hossana zaune agefen camila hannunta ɗauke da tsiren naman nan ta tura abaki sai ci take kamar kura,hankalinta kwance, bakomai bane ya burge jahad ba face ganin yarda hossana tayi wani irin kyau cikin gajeran skirt mini tare da riga ƴar t shirt tabi shape din jikinta, hada ƴar hoda ta shafa ma fuskarta da jan baki,
Ganin jahad ta soma washe mata baki, girgiza kai jahad tayi tare da cewa "dama nasan dole kiyi ƙara'e hossana irin wannan ɗaukar wanka haka,"
"Kaɗan kika fara gani ma,aunty camila ma tace in ta samu hutun aiki zata kaimu saloon a gyara mana gashi tare da ƙunshi ma duka za'a yi mana,"
murmushi jahad tayi a lokacin taƙarasa wurin table ɗin, aza tray ɗin tayi asaman shi sannan ta samu wuri ta zauna itama suka saka Camilla a tsakiyarsu,
ita ta baje masu tsiren acikin tray ɗin ta jera masu shi,sannan ta zuba masu chips ɗin daga gefe,
Nan fa suka gyara zama duka ukun suka tasar ma kayan lashe lashen, ba baka sai kunne, ba kaji komai sai sautin taunar shi da suke abakinsu,
78.
**********************SEHRISH
tun da english teacher ɗinsu ta fita daga class ɗin, sehrish ta kifa kanta asaman desk din gabanta tana ta sharar bacci, har amrish ta gane mata daga jiya izuwa yau sam bata gajiya da yin bacci,alamu ma sun nuna cewa bata fahimtar komai kanta dashi da kwankwon ashana duk ɗaya suke,tashi amrish tayi tare da nufo inda sehrish ɗin take, hannu tasa tare da bubbuga bayan sehrish tace"ki tashi mu tafi time ɗin break yayi," kusan sau uku tana tashinta daƙer ta buɗe idonta da suka canza launi saboda bacci, miƙa tayi tare da yin hamma alamar yunwa take ji ga baccin ma bai isheta ba, fitowa tayi daga seat ɗin nata tana cewa"ashe har lokacin break yayi "
Amrish tace"taya za'ae ki sani, bayan baccinki kawai kike tasha, ni anya kuwa ma kina yin bacci a gida? Ta tambaya tana kallonta a yayin da suke fita daga class ɗin,
"Ina yin bacci mana sosai,"_
"To meyasa kike yin bacci a class?ko karatu ma bakya saurara salon azo yin test ko exam kiyi ta baza idanu kina kallon question paper kina cizon biro ko? Ta fadi fuskarta ɗauke da dariya, itama sehrish din dariya tayi tana cewa "insha Allah hakan ma bazata faru ba,kafin lokacin zanyi karatu sosai,"
Suna tafiya suna fira har suka isa Lunch room ɗin nasu atare suka shiga ciki rike da hannun juna, students duk sun hallara kowa sai break fast dinsa yake yi.
Sake ruƙo hannun sehrish tayi tare da kaita gaban table ɗin da zasu zauna,sai da rishi ta zauna saman table chairs din sannan amrish ta wuce ciki don ta amso masu abunda zasu ci,
Ajiyar zuciya sehrish ta saki tana kallon students din dake zaune a wurin suna cin abincinsu suna shan fira abunsu,zahiri su take kallo amma abaɗi ba komai take tunawa ba face fuskar SGR ɗinta,murmushi ta saki aranta tana cewa "koyana ina yanzu?me yake yi?ko yaci abincinsa?Allah yasa dae baibar cikin shi da yunwa ba,
babu mai bata amsar tambayarta, cigaba da cewa tayi"bani da wani burin daya wuce naganshi cikin nishaɗi batare da wata damuwa ba,amma narasa dalilin dayasa kullum fuskarshi aɗaure baison yin fara'a,inaso na kawo sauyi a cikin zuciyar shi, ya Allah ka bani wannan damar da zan zama ɗaya daga cikin farin cikin ran shi,"
Gaba ɗaya tayi nisa acikin tunaninta, batasan meke wakana ba, kwatsam taji hannun mutun a ƙirjinta an shafa mata, a wani irin firgice ta buɗe idanunta gabanta na faɗuwa,
Bin su da kallo tayi atsananin tsorace, kai kana ganinsu kasan tantiran ƴan iska ne, mata ne su jikinsu na sanye da uniform riga da wannan mini skirt, kai kace ba musulmai bane saboda ko dan kwali babu akansu, iya gashi ne kawai suka ɗaure abayansu shima ɗin na ƙari ne, ga uban bleaching sun sha abun dae kawai ba'a magana,.
Kallon juna su kayi suna dariya kafin ɗayar tace "wow gaskiya an mana nisa, Sofia tun yaushe aka kawo wannan zazzafar a school ɗinmu batare da sanin mu ba"? ta tambaya tana faman sakin murmushi gefen fuska, tuni jikin sehrish yayi mugun sanyi bakomai ta tuna ba face nasihar da kanal yusuf yayi mata kafin tafara zuwa school,
wadda ta kira da sofia tace"ni kaina bansani ba, amma yanzu tunda Allah ya haɗamu da ita, zatayi mana bayani ne, ta faɗi tana kallon sehrish tare da kashe mata ido ɗaya tace"ƴan mata,naga kin ɗaure fuska may be don na shafa chest ɗinki ne batare da izninki ba,ae mun afwa irin salon tamu gaisuwar kenan,ya sunanki ne"?
ƙara tamke fuska sehrish tayi jikinta na rawa Allah Allah take yi Amrish tadawo don tasan ita zata iya dasu,
ɗan ta6e baki zeenat tayi tare da cewa"Can't u talk to us? May be don baki son ko mu su wanene ba a school ɗin nan ba,zamu yi maki uziri ne," ta faɗi tana yarfa hannunta, yatsun zira zira da du anyi fixing nails dogaye.
shiru sehrish tayi burinta amrish ta ƙaraso in ba haka ba tashi zatayi tabar musu table din gaba ɗaya ta koma Class, duk da yunwar da take ji acikinta,
Suna cikin zaman ne sai ga Amrish ta ƙaraso fuskar nan ɗauke da murmushi ta ruƙo tray a hannunta mai ɗauke da plate biyu na abincinsu tare da coke,
Sehrish na ganinta ta shiga sauke ajiyar zuciya,amma abunda ya daure mata kai time ɗin da amrish ta ƙaraso kai tsaye bayan ta ajiye masu tray ɗin asaman table din, sai ta miƙa ma Zeenat hannu suka gaisa tare da cewa"Am really glad to see u guys, nayi missing ɗinki sosai my zeenat," murmushi zeenat tayi tare da cewa"nayi missing ɗinki nima,bcox of u na matsa wa mommy sai mun dawo nigeria sbd a ƙagare nake da na haɗu dake ko fa isasshen bacci bana samu saboda rashinki,"
bin su da kallo kawai sehrish takeyi baki asake, yarda suke magana tamkar irin mace da namijin nan,
Muryar sofia ce ta katse su da cewa "oh ni ba'a ma ta tawa ko Amrish? Zeenat kaɗai kika gani shikenan bari na tafi," ta faɗi tana ƙoƙarin tashi, cikin sauri Amrish tayi holding hands dinta tana cewa"am sorry kada ki tashi pls, in naga zeenat ina mantawa da komai ne,"
ɗaure fuska sofia tayi tace"i can't stay here,cos am getting jealous bazan iya jure yarda kike son Zeenat ba,
Dariya zeenat tayi tana cewa"in dai akan Soyayyata da amrish ne ke 6ata maki rai sai dae ki mutu,"
ta faɗi tana mayar da idonta akan sehrish da tayi zugudun tana kallon ikon Allah,
wuri Amrish tasamu ta zauna, kusa da sehrish suna facing ɗin su Sofia da zeenat,
ɗan kallonta amrish tayi tare da cewa"am sorry my friend nabarki da yunwa ko"? ta faɗi tana kallon Sehrish wadda jikinta ya gama mutuwa,
"A'a" ta bata amsa a takaice,
Mayar da idonta tayi kansu zeenat tace"bansan zaku zo ba ae dana haɗo mana abincin tare,amma bari na tashi yanzu naje na ƙaro mana yadda zai ishe mu,"
cikin sauri zeenat tace"no ba sai kinje ba its ok ba mu jin yunwa a ƙoshe muke,"
murmushi amrish ta saki tare da kallon sehrish tace"bismillah mufara ci time ɗin komawa class ya kusa,"
Gaba daya hannunta kerma yakeyi a haka ta ɗauki spoon ɗin zata fara cin fried rice din da takawo masu shaqe da plate,tana ɗebowa shinkafar na zube wa saboda rashin natsuwar da take ciki ba don komai ba sai don zeenat data tsare ta da waɗannan manyan idanun nata masu zubin na karuwai a tsaitsaye suke ga eye lashes da tayi fixing sinsu kamar ɗiyar roba,
Ganin yarda hannun sehrish ke kerma ta kasa kai koda one spoon ne yasa Amrish ɗagowa ta kalli zeenat wadda ta zuba mata ido ko kyafta su bata yi,
ɗan gyaran murya Amrish tayi tare da cewa"Zeeta pls kidaina kallonta hakan na hana ta samun natsuwa,class mate ɗina ce jiya tafara zuwa school bata saba da kowa ba,"
ƙayataccen murmushi zeenat ta saki tare da cewa"its okey,ashe new comer ce, tayi mun kyau ne shiyasa nagaza janye idona akanta,ina fata kin sanar da ita komai game da zama cikin team ɗin mu?
Cikin sauri amrish tace"a'a pls mubar maganar nan,ita ba'a team ɗinmu take ba kawai class muka haɗa da ita,"
zeenat tace"that's impossible amrish tun da har kina yawo da ita a school dole ta zama ɗaya daga cikin mu,not only that yarinyar ta burgeni sosai........'kasa ƙarasa maganar tayi saboda ƙarar cokalin amrish data bugi gefen plate dinta dashi tace"Zeeenat! Nace kidaina wannan maganar agabanta bana so," rai a6ace tayi maganar sannan ta mayar da idonta kan sehrish tace"pls ki ci abincin ki,"
gyaɗa kai sehrish tayi tare da mayar da hankalinta akan abincin dake gabanta,ci take amma batasan inda abincin ke zuwa ba,saboda tsoro da ruɗin da ta shiga,
yunƙurawa su kayi su biyun atare suka miƙe, cikin sanyin murya amrish tace"Am sorry zeenat i don't mean to hurts u,just bana son muna wannan maganar agabanta ne,saboda batasan komai ba ko mutane batason shiga cikinsu," hankali atashe take maganar tana kallon su,
atare suka yatsina fuska sannan zeenat tace,kinsan bana fushi dake amrish shiyasa kike mun duk abunda kika ga dama,amma ina so ki sani 6ata mun rai tamkar 6atawa mommynki raine, kuma kinsan mai zo biyu baya ya zama dole kibi umarnin duk abunda nace, don haka wannan yarinyar dole tashiga team ɗin mu !!!
tana gama faɗin hakan taja hannun sofiya suka fuce daga lunch room din
ita dae sehrish zuru tayi tana kallon ikon Allah bayan sun fuce ta mayar da idonta kan amrish wadda jikinta yayi mugun sanyi tuni kuma idonta sun cicciko da kwalla, amma bata bari sun zubo mata ba, sai ma kallon sehrish da tayi tare da ƙaƙaro murmushi tace"ki ci gaba da cin abincin ki mana,naga kin tsaya,"
jiki asanyaye sehrish ta mayar da hankalinta kan abincin tana ci amma zuciyarta ajagule saboda halin da taga Amrish ta shiga akan waɗannan ƴan matan da suka zo,ko su wanene oho,
Ta tambayi kanta,
***************************Twins
Fitowarsu kenan daga wanka atare kamar yarda suka saba kwatsam sai ga haroon ya turo ƙopar ɗakin nasu fuskarshi ɗauke da wannan shu'umin murmushin nashi, tsayawa yayi yana binsu da wani irin kallo jikinshi na sanye da Crazy jeans tare da wata figaggar riga daya sanya, ya tada kwalar rigar tsaye,sam haroon baya kama da musulmai ko a fuska, balle ma daya kasance yana sanya chain a wuyan shi da kuma earrings irin yarda jigunannun ƴan iska ke sakawa,
Kallon juna su kayi atare kafin suka mayar da idanunsu akanshi,tuni ran Jahan ya 6aci ganin yarda yake bin jikinsu da kallo kamar wani tsohon maye, dama daga su sai short towels ajikinsu, farar surar ne mai jan hankali ta bayyana muraran,
ɗaure fuska jahan yayi tare da cewa "me ya kawo ka ɗakin mu? me kuma kake buƙata,indai kuɗi ne suna nan zamu baka,"
ta6e baki haroon yayi tare da yatsina fuska yace "yakamata kasan yarda zakayi magana dani with respect,ko don darajar wannan videon dake ajiye acikin wayata,'
tsuke fuska su kayi atare zuciyarsu na tafarfasa tamkar su rufe shi da bugu haka suke ji,
Cigaba da magana yayi "zuwa nayi don na ƙara tunasar daku, don na lura kamar kun manta da maganar dukiyata dake a wurinku, saboda waccan farin balbelen ɗan uwan naku da bai lfy na lura duk kun wani tashi hankali akanshi,'
Buga tsoki ayaan yayi yace "kada ka sake kiran shi da sunan balbela kadaina haɗa sunayen mu dana dabbobi domin kuwa mu bamuyin munayen ɗabi'un da za a haɗa sunan mu dana dabba, domin kuwa dabba yasan inda yake"
waro ido waje haroon yayi jin abunda ayaan yace a tsananin mamaki yace "Ayaan ni kake kira da sunan dabba"?! Ya tambaya a dan fusace
Cikin sauri jahan yace"kayi shiru ayaan kada kaja mana wani bala'en don na lura bai da Imani ko misƙala zarratin, tunda har bai damu da halin da ɗan uwansa ke ciki ba, burinsa kawai ya ƙuntata ma rayuwarmu," yayi maganar yana jefar haroon din da mugun kallo,
fashewa da dariya haroon yayi hada dafe cikinsa kafin yace "Waye kuma ɗan uwana? ae ni bana ɗaukarku jini na,ko ajinsi ku farare ne ni kuma baƙar fata ne, in fact ni bani da wata alaƙa daku, Uba fa kowa muka haɗa uwa kuma kowa da tashi, bayan shi kuma sai me?
shiru su kayi suna sauraron shi gaba ɗaya tsanarshi ƙara ninkuwa take yi acikin zuciyarsu,
juyawa yayi tare da cewa "Zan wuce ni ku huta lpy ƴan samari," yana faɗin hakan ya fuce yana sakin dariya kamar zautacce,
Mayar da ido ayaan yayi kan jahan yace "bro i ave an advise abt that bastard, why not mu kashe shi kawai kowa ya huta, cos i don't think ko mun bashi kuɗin zai goge videon,"
aɗan razane jahan ya kalle shi yace "ashe baka da hankali ayaan, kisa fa kace? Mu zamu kashe shi? In muka jefa kanmu cikin matsala fa? ya fadi yana kallon sa,
Ayaan yace "ba wata matsala jahan, just lettus kill him kowa ya huta !!!!!!!!!
"Mu bashi time in har muka bashi kuɗin bai goge videon ba, sai mu kashe shi kawai,don da abunda zai ta6a mutuncin family dinmu gwara abunda zai tada masu hankali na ɗan wani lokaci ya wuce" Acewar jahan,
Gaba daya sun amince da shawarar kashe haroon 😳
Duk mutanen da suka zo duba fawan duk sun ragu, har sun mai dashi daki sun kwantar dashi