ABBAN SOJOJI TAKUN TSAKIYA 2 BY BOSS BATURE.txt

Author :  Boss Bature Category :  Arewa Pen

Chapter   16 / 80

45K to 48K   out of 238K words

yarda hafsat ta amince yanzu komai zai fi zuwa mata da sauƙi,
taci gaba da cewa "Hafsat duk yarda zamuyi kada mu bari Abban ki yasan da yaran nan har izuwa gobe, Akwai wanda nayi ma magana zai zo gobe insha Allah, Shi zai kai su gidan marayun, Sannan maganar Omar tunda har yakai yanzu bai zo ba, inajin cewa tabbas akwai abunda ya tsaida shi wannan ba matsala bace kibar mun komai a hannuna ni nasan yarda zance mashi ya yarda..................
Jinjina kai hafsat tayi jikinta a matuƙar mace saboda sabon da tayi da Su hussana da jahad sam batason rabuwa dasu amma kuma babu yarda zatayi this is the Only solution !!!
Ajiyar zuciya ta saki tare da kallon Mommyn nata tace "Shikenan Mommy, ni zan wuce ɗaki sai naji ki ............ Muryarta na rawa take magana cikin sauri ta ƴunƙura tare da miƙewa ta nufi hanyar fita ɗakin tana jin Muryar Aunty babba tana cewa "Yanzu zan tura maki da kuɗin ki mayar mata abunta, kar taja mana bala'e
Hafsat bata ce komai ba saboda yanayin da ta shiga, cikin sauri ta fuce kai tsaye ta shiga bedroom ɗinta,
Lokacin da ta shiga ta samu su hussana da jahad zaune saman darduma suna karatun Al'qur'ani da kansu, sai taji zuciyarta ta ƙara karaya, cikin sauri ta faɗa toilet tare da rufo ƙopa tana faman shessheƙar kukan rabuwa dasu.........................................

__________________SEHRISH__________

Sam bakin ta yaƙi rufuwa don Murya, tun ɗazu ta shimafiɗa uniform ɗinta saman gadonta tare da sandal ɗinta da kuma school bag ɗin duka, ta tasa su gaba sai kallonsu take yi,bakomai take tunani ba face yarda zata fara shiga school gobe Talata, irin wankan da zata ɗauka,tana daga zuƙunne saman gadon nata sae faman sakin murmushi takeyi, hannu tasa tare da shafa uniform ɗin data jera tana cewa "daga gani zasuyi mun kyau,oh ni reeshi yanzu zanyi new friends a makaranta, da na banza da na kirki, Allah dae ya haɗa ni dana gari, ba wanda zasu canza min tunani na ba, ina ƴar talaka dani," ta faɗi da ƴar dariya,
Turo ƙopar Azmee tayi tare da shigowa tana cewa "Da alama yau sehrish kin manta da shiga kitchen ko? kin barni da aiki narasa dalilin dayasa kika zubama kayan makarantar nan naki ido,sai kace ba mallakin ki ba"?
   tayi maganar yayin da take ƙarasawa ciki, ɗagowa sehrish tayi ta kalle ta fuskarta washe tace "Am sorry aunty azmee, Yanzun nan nake shirin fitowa wlh, na kammala salla ne shine nake ɗan ƙara binsu da kallo,
   girgiza kai Azmee ta ɗan yi kafin tace "maza ki tattara kayan nan, ki mayar dasu cikin wardrobe, Kizo maza mu kama aiki,'
   Sehrish ta amsa mata da Toh sannan ta miƙe cikin sauri ta sauko daga saman gadon, Tattara kayan Uniform ɗin tayi takai su cikin wardrobe, bayan ta kammala ta ɗauki mayafinta saman gadonta, tayarfa shi akanta dama riga da skirt ne ajikinta,
   Cikin sauri tabi bayan Azmee suka fuce izuwa kitchen,
  Cikin hanzari suka soma shirye shiryen fara girkin dare, suna cikin aiki Azmee nagaban gas tana tafasa nama, yayin da sehrish ke ta faman fere kayan lambu asaman Chopping board,
   Faɗowa junaid yayi cikin kitchen ɗin jikinsa na sanye da Kayan ball yellow sai faman zufa yake yi da alama shigowarsa kenan daga wurin ball, sam yagaza rufe bakinsa sai faman murmushi yake yi,
  "Wlh harka ban tsoro junaid, yarda ka faɗo suddenly,jibi jikin ka sai faman zufa kake yi," Sehrish ta faɗi tana nuna sa da wuƙar dake hannunta,
  Juyowa azmee tayi tana kallonsa batare da tace komai ba,
  "Zuwa nayi in tunasar maki cewa, gobe ni zan kai ki school da mota ta," ya faɗi yana faman sauke ajiyar zuciya,.
Sai lokacin azmee tace "Salon wahalar da kai junaid, ka bari tahau school Bus mana,ƙwara tasa ba da bin motar makaranta tun yanzu, amma in kace zaka runƙa kai ta ɗawainiyar zatayi yawa, kuma kasan sarai Babban yayan ku baya so kana fita ko?.ta faɗi tana kallonsa,.
  turo baki junaid yayi tare da ɗan buga ƙafarsa yace "Nidai Aunty azmee zan kaita, just for tomorrow cos this is the first time da zata fara zuwa school ɗin yakamata tasan wasu abubuwan inaso zan nuna mata ne, tun da ni nasan school ɗin sosai...."
  gaba ɗaya kallon shi suke yi yarda yake magana cikin shagwa6a, yana faman bubbuga ƙafa
Dariya azmee tayi don ta Lura rigimarsa ce ta tashi, dama aduk lokacin daya buga ball sosai yagaji alokacin rigimarsa tafi tashi,
  Sehrish tace "Shikenan junaid gobe kai zaka kaini school, amma yanzu kana buƙatar yin wanka ka ɗan huta,,"
   ɗan murmushi yayi jin abunda tace "Amma ina jin yunwa fa sosai," ya faɗi yana kallonta
  "Shikenan kada kadamu yanzun nan zan kawo maka abinci,"
  "Yawwa My lovely sis," ya faɗi tare da kama hanya ya wuce upstairs room ɗinsa,
   A tray ta shirya masa coffee tare da snacks, sannan ta fito ta wuce upstair domin takai masa, tana hawa saman stairs ɗin sai ga SGR shi da Marshal Omar suna nufo stair ɗin, ganin su zo dab da benen yasa ta saukowa gaba ɗaya don tabasu wuri su wuce, dukansu suna sanye da jean da t-shirt, sai faman sauri suke alamar akwai wani Uzuri dake gare su, suna ƙarasowa inda take tsaye tayi saurin cewa "ina yinin ku," Omar ne kawai yasamu damar Amsa mata, amma shi SGR sam ko kallo ma hasalima baisan da mutun a wurin ba, gabanta ne ya faɗi don alamu sun nuna cewa ba ƙaramin abubane ganin yanayin fuskar kowannansu Especially Omar da ta sani, Kullum cikin sakar mata fuska yake duk in suka haɗu amma yau dakyar ya amsa mata gaisuwarta,
  Bin su tayi da kallo, yayin da suka wuce kai tsaye hanyar fita falon suka nufa, har sun kusa fita Omar ya juyo ya kalle ta, bakomai yasa Shi juyowa ba fa ce tuna Hussana da jahad yau tsawon wata kenan baije ya dubo su, saboda busy ɗin daya shiga, yana da burin zuwa ɗaukosu amma aiyuka sun hana shi, Ajiyar zuciya yasaki tare da mayar da kansa suka sa kai suka fuce,
   sam sehrish tagaza yin motsi da ƙafafunta, hakanan ta dunga jin gabanta na faɗuwa, bata kai ga hawa benen ba, taji dirar motoci cikin gidan nan take ta sake jin faɗuwar gaba, cikin sauri ta haye upstairs ɗin da hanzari ta shiga bedroom ɗin junaid a lokacin yana cikin toilet yana wanka, ajiye masa tray ɗin tayi saman table, sannan tafito da sauri-sauri ta fito daga babban falon ta tsaya abakin ƙofar shigarsa, . 
  Kamar dai ranar da SGR da Omar suka zo Nigeria tare da uban security guards na sojoji haka yau ma, tsoro ne yakama sehrish gudun kar ace US zasu  koma, 
   Tana ganin lokacin da suka shiga cikin motocinsu kuma nan take motocin ajere suka nufi dogon titin da zai fidda ka daga cikin gidan,
   Komawa ciki tayi da gudun gaske ta faɗa kitchen tana faman kwalama aunty azmee kira, a ɗan razane azmee ta juyo ta kalle ta tare da cewa "Sehrish lafiya kuwa kike ta faman kwalamun kira haka!?
  Cikin tsananin tashin hankali tace "Aunty azmee meke faruwa ne? Yanzun nan naga Babban yaya tare da Yaya Omar, sun fito fuskokinsu ba annuri kuma ga tarin motoci can sun fita dasu,"
   tsayawa azmee taɗan yi jimmmmmmm tana ɗan tunani kafin tace "Tabbas ina hasashen cewa Us zasu tafi Saboda ɗazu da safe naji ƙishin-ƙishin ɗin cewa Momynsu matar Uncle ɗinsu donald tana fama da blood cancer, To ina da tabbacin cewa kodae ta rasu ne...........'
   Zaro ido sehrish tayi cikin tsananin tashin hankali take furta "Innalallahi wa'inna ilairaji'un Allah yasa bata mutu ba, Yanzu shikenan in suka koma ko yaushe zasu dawo.....'
   Murmushi Azmee tayi kafin tace "naga kin tayar da hankalin ki, nasan saboda Tafiyarsu Rafayet ne bawai don jin mutuwar ba,
    Hannu sehrish tasa tare da rufe fuska saboda hawaye da taji sun tafo mata,
   bin ta da kallo kawai azmee tayi cike da mamakin ganin  tana shessheƙar kuka,
   Matsawa tayi kusa da ita tare da dafa ta tace"Sehrish !! Wannan kukan na menene? Ba dai don tafiyarsu bane?
   shiru kawai tayi batare da tace komai ba, ita kaɗai tasan me take ji aranta, gaba ɗaya fuskarta ta damuje da hawaye,
    Jinjina kai azmee tayi tare da cewa "Ki koma ɗaki ki kwanta kawai,"
  Cikin kuka sehrish tace "a'a aunty azmee zanyi aikin,"
   Azmee tace "a'a banaso ki tafi kawai zan ƙarasa abuna,"
   Juyawa sehrish tayi tare da fuce wa daga kitchen ɗin ta koma bedroom ɗinta, saman gado tafaɗa tare da cigaba da kukan, To fa sehrish komai yasata yin kuka? Allah wa'alamu,
  Azmee kuwa ta jima tana mamakin dalilin kukan Sehrish tarasa gane mata, aranta tana cewa "Badai saboda tafiyar SGR take kuka ba? Don ta lura da yadda sehrish ke matuƙar ƙaunarsa, sam bata iya fira batare da ta, Amabaci sunan shi ba ita dae kawai tafison jin Ana maganarsa,nan zakaga sakewarta,
   "Lallai ne akwai Babbar Matsala, muddin abunda nake zargi ya tabbata,ya zama dole in ja ma Sehrish burki, don gujema kamuwa da CIWON ZUCIYA,"!! Azmee ta faɗi acikin ranta,
  _______________________

Sehrish kuwa Tuni wani Irin zazza6i taji ya rufe ta lokaci guda, jikinta har kerma yake yi wurin janyo bargonta dake asaman gadonta ta lullu6e jikinta dashi, tana faman fidda numfashi mai zafin gaske, sam tarasa ina zata tsoma ranta ita kaɗai tasan irin raɗaɗin da take ji acikin zuciyarta

Har wuraren Sallar Magrib sehrish bata motsa ba, tana nan yarda take ƙudundune cikin barko,tamkar mai bacci alhalin nan Idonta biyu jikinta ne kawai da bayayi mata daɗi, Acan ciki kuwa fitowa junaid yayi bayan yasha baccin sa, ya sauya kayan jikinsa izuwa riga da wando, lokacin daya sakko down yayi mamakin ganin Azmee ita kaɗai tana faman jera masu dinner a dining, ƙarasawa yayi cikin sauri yana cewa"Aunty Azmee ina sehrish ɗin ne? Ita bazata fito ta tayaki ba? Azmee ta ɗan ɗago ta kallesa tare da cewa "Junaid ni kaina bansan meke damun Sehrish ba, Lafiya lou fa muke aiki da Ita, amma tunda tazo ta tambaye ni game da babban yayanku da Omar da taga sun fito fuskarsu cikin wani irin yanayi, kuma taga Sun fita tare da motoci dayawa, shine nake ce mata may be Us zasu je, tunda ɗazu da safe naji ƙishin ƙishin ɗin cewa Matar Uncle ɗinku donald tana fama da blood cancer may be ta rasu ne.....shine fa kawai sehrish takama kuka har nace mata ta koma ɗakinta kawai ni zanyi aikin," ta ƙarasa maganar cikin damuwa, Junaid kuwa shiru yayi hankalinsa ya rabu gida biyu, sam ya rasa gane inda maganar Azmee ta dosa, cikin mamaki yace "Us kuma? Taya babban yayan mu zaibar ƙasar nan batare da sani na ba? Anya kuwa aunty Azmee am just doubting about it bana tunani Us zasu je, kuma Matar uncle donald bana tunanin ta rasu gaskiya, tunda da naji ko a wurin Abban mu ne, Ni dai Allah yasa ba wani abu bane ya faru mummuna," ya faɗi cikin tashin hankali kafin ya wuce yana cewa "Bari naje wurin Sehrish ɗin naji meke damunta,"
Azmee tace "to shikenan,"

A hankali ya tura ƙopar ɗakin yashiga da sallama, tsayawa yayi yana kallonta yarda take ƙudundune cikin bargo, A hankali ya kira sunanta "Sehrish..........' shiru bata amsa masa ba, ƙarasawa yayi izuwa gab da gadon nata yaɗan zauna gefe tare da sa hannu ya yaye mata bargon dake jikinta, dogon numfashi taja tare da cewa "Junaid ka mayar mun da bargona, Sanyi nake ji," Junaid yace "Reesh wai meke damunki ne? Aunty azmee ta faɗamun cewa kinbar kitchen kina faman kuka? Cikin kuka tace "Junaid wai dagaske ne cewa Babban yaya da Yaya Omar us zasu koma yau? Sakin baki junaid yayi yana kallonta cikin tsananin mamaki amma bai kawo ma ransa komai ba sai cewa yayi "Sehrish dama akan wannan kika shiga damuwa? to ki kwantar da hankalin ki, Yaya Omar da yaya Rafayet bana tunanin sun bar ƙasar nan ne, Aunty azmee ce kawai tace maki hakan a hasashen ta, just calm down ur mind My lovely sis... . ...........jin abunda junaid yace yasa ta sauke ajiyar zuciya tare da miƙewa zaune daga saman gadon tana cewa "ngde da jin hakan junaid, naji ma anata kiran sallar magrib bari naje nayi alwala," junaid yace "to shikenan nima bari naje nayi salla,pls reesh karki ƙara sa damuwa irin haka, kuma in kin kammala sallar, ki fito muyi dinner atare," Murmushi ta sakar masa tare da cewa "Ok my lovely bro, da zarar nayi sallah zan fito nima," lumshe ido junaid yayi tare da buɗe su akanta fuskar nan ɗauke da Murmushi, sai da yaga sehrish tashiga toilet sannan yafuce hankalinsa a kwance..........................❤
remain 2 pages free su ƙare, wanda baiyi payment ba ya hanxarta Yi, Abban Sojoji 300 ne, discount da nayi na Abbban sojoji fans group ne kawai 200, Vip kuma 700, bank details ɗin da za'a tura,3196407426 First bank, Bature Hafsat Muhammd Evidence of payment 08103884440


*💋💋💋ABBAN SOJOJI💋💋💋*
•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
──────────────EPISODE 23-24

ﻗﺼﺔ ﺣﺐ ﺭﻭﻣﺎﻧﺴﻴﺔ ﺑﻴﻦ ﺳﺤﺮﻳﺶ ﻭﺍﻟﺠﺮﺍﺡ ﺍﻟﻌﺎﻡ
ﺭﺍﻓﻴﺖ💋❤️

*Mallakin Hafsat Bature Moh'd*
~BossBature~
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·• Fitowa tayi tana faman yarfar da ruwan alwalar dake hannunta,hijab da sallaya ta ɗauka a wardrobe, ta shimfiɗasu tare da kabbara sallah,bayan ta kammala tabar darduman anan saboda in an kira isha'e, hijab ɗin ta cire tare da ajiye shi saman gadon sai ta ɗauki Mayafinta, ta yafa shi akanta,
Fitowa tayi kai tsaye ta wuce dining, a lokacin junaid ma yana a wurin tare da Haroon sai kanal Yusif duk suna zaune, yayin da Azmee ke faman ɗawainiyar Zuba masu abinci,
   Ƙarasawa tayi tare da cewa "Sannu da aiki Aunty Azmee,"
Juyowa azmee tayi tare da kallonta tace"Yawwa mutuniyar sarkin kuka, Lamarinki naban mamaki kamar me iska,"
   Sunnar da kai Sehrish tayi tana ɗan Murmushi kafin daga bisani ta gaishe da Kanal yusif da fara'arsa yace "Our Princess,duk yau ban saki a idona ba, Yakamata ace kina sakewa da ƴan uwanki sosai,"
   Murmushi kawai Sehrish tayi tare da zama kusa da junaid suna facing ɗin kanal yusif da haroon ta hannun dama,
   Zuba mata abinci azmee ta soma yi a plate, junaid dake a gefenta yace"Da ace baki fito ba ko, da bazanci komai ba Allah,"
   Kafin sehrish tace wani abu haroon yayi saurin cewa "Saboda ciki ɗaya kuka fito ko? murmushi junaid yayi tare da cewa "Yaya Haroon yadda na ɗauƙi Sehrish ta wuce haka a wurina," ta6e baki Haroon yayi yana kallonta, Harara Sehrish taɗan wurga masa tare da murguɗa masa baki, jinjina kansa yayi tare da cewa "An fa samu freedom of sitting the same table da Ƴa'ƴan masu gida dole ayi iya shege,
   Jin wannan maganar ta Haroon ta sanya junaid ɗaure fuska lokaci guda yace "Yaya haroon me kake nufi da hakan?
   Haroon yace "Abunda ranka yabaka"
  Dakatawa kanal yusif yayi daga cin abincin da yakeyi ya ɗan bubbuga plate ɗin dake gabansa da cokalin hannunsa ya bada sauti sannan ya aza idonsa akan na Haroon, Ganin irin kallon da kanal yusif ya jefa masa ne yasa shi, yin tsit ya shiga taitayinsa,
   Mayar da idonsa yayi kan Sehrish yace"Sister Yaushe ne zaki fara zuwa school ɗin? yayi hakan ne donya mantar da ita maganar haroon, ganin yarda tayi sanyi lokaci guda,
  daƙyar ta ƙaƙaro murmushi tare da cewa "Gobe ne insha Allah,"
  Kanal yusif yace "Masha Allah,A matsayina na yayan ki, akwai wani jan hankali da nakeso nayi maki, kin ga gobe zaki fara zuwa, kuma zaki fara haɗuwa da sababbin ƙawaye iri-iri,akwai good friends waɗanda zasu dunga ƙarfafa maki guiwa akan karatu ta hanyar baki shawarwari masu kyau,bayan su kuma akwai bad friends gur6atattu waɗanda majority ɗinsu ba karatu ya kaisu ba,Asarar kuɗin iyayensu kawai suke yi, basa karatu ƴan abi yarima asha kiɗane,babban ma tashin hankalin yanzu majority na irin waɗannan ƙawayen ƴan Lesbian ne,fitsararru marasa kunya waɗanda suka gagari iyayensu da malamansu, burinsu kawai su 6ata tarbiyyar wasu, bana so ki kasance ɗaya daga cikin irin waɗannan ko kusa, dayawa wasu suna kuskuren yin abota da irin waɗannan bad friends ɗin, sai suce ae basu suke aikatawa ba,sun manta cewa zama da maɗaukin kanwa shi ke kawo farin kai,to koda gigin wasa bana so ko fira ta haɗaki da irin waɗan gur6atattun balle harku ƙulla Abota, Ina gargaɗin ki akan hakan ! And i want u to know that Ke yanzu kina ɗaya daga cikin Mutuncin gidan nan!! Kuma kinsan yarda sunan family ɗinmu ya karaɗe ko'ina, ba inda ba'asan Jinin SALAHUDDEEN HUSSEIN ba, don haka yazama dole ki kiyaye mutuncin family ɗinmu da kuma ƙimarsa, ina fata kina fahimtar abunda nake cewa"? Ya tambaya yana kallon sehrish wadda ta natsu tana sauraronsa cikin sauri tace "Ina fahimtar duk wani abu da kace yaya yusif, kuma insha Allah zan kiyaye faruwar hakan,kuma naji daɗi sosai harma baxan iya misaltawa ba,saboda na samu ɗan uwa nagari wanda yake mun nasiha akan na tsira da mutunci,babu wanda ya tunasar dani akan hakan sai kai, kuma insha Allah bazan ta6a baku kunya ba, zan kasance ɗaya daga cikin abun Alfaharin gidan nan,"
  taƙarasa maganar yayin da idonta suka ciko da kwalla, gaba ɗaya Azmee da Junaid sun kasa kunne suna sauraron maganar tasu, dukansu babu wanda baiji daɗin maganar Kanal yusif ba, Illa mutun ɗaya Wato Haroon wanda ke ta faman tur6une fuska yana faman hura hanci aransa yana cewa "Insha Allah ni kuma bazan taba barin ki ki xama abun alfaharin gidan nan ba, balle har

16 / 80