Author : Boss Bature Category : Arewa Pen
Amanin da kika sani ada ba ita bace ayanzu ba,ashirye nake dana kwance dukkan wasu notikan kanki,zan mayar dake kamar wata zararra,ita kuma hayaam zanyi amfani da wannan damar wurin ganin na canza mata halittar jikinta,kamar yarda kuka canzawa Amal kamanni ta tsotse ta rame ta ƙanjame haka itama nakeson ta koma,dama ance ramuwar gayya tafi ta gayyar zafi,that's my plan!
Tana faɗin hakan ta juya tare da komawa wurin Amal ta zauna,kallonta Amal tayi tare da cewa"Aunty amani,dan Allah kiyi haƙuri da abunda zan faɗa maki,bansan ko zai 6ata maki rai ba,nasan cewa su mammy sun cutar damu sosai,amma kada kice zaki ɗauki fansa,mubarsu da Allah kawai shi zai saka mana,sannan in zamu iya mu taimaki mahaifinmu don yana cikin mawuyacin hali"
Shuru kawai amani tayi batace mata komai ba,amma fa har yanzu tana akan bakanta,maganar mahaifinsu kuwa tasan matukar mammy na numfashi bazata barshi ya sarara ba,don ba karamar shedaniyar mata bace,ita kanta yanzu tana shakkun in don Allah aka hadata da Abbas.
_💋Boss Bature💋_
______________________tunda yadawo daga masallaci yake jin jikinshi wani irin yanayi mara daɗi,bedroom dinshi ya shiga tare da nufan saman gadonshi ya haye yana faman sauke ajiyar zuciya,pillow ya jawo tare da aza kanshi a saman shi yana faman lumshe ido,yana cikin wannan yanayin yaji fitar wani abu daga hancinshi mai ruwa ruwa,cikin sauri junaid ya tashi daga zaune yana kallon pillown nashi,zuba ido yayi yana kallon jinin daya ɗigo daga hancinsa,abun yayi matuƙar ɗaure mashi kai,kafin yayi wani yunƙuri sai ga wani ɗigon jinin ya sake fitowa daga ƙopan hancinshi,abu kamar wasa jinin ya dinga ɗiɗɗigowa saman bedsheet ɗinshi,
Hankali tashe junaid ya sauko daga saman gadon da saurin gaske ya faɗa cikin toilet ɗinsa,kai tsaye ya nufi wash basin,dafa shi yayi yana kallon fuskarshi acikin mirror ɗin,hancin shi yabi da kallo ganin yarda hancinshi ke cigaba da bleeding,sam bai damu ba saboda yasan cewa yana yawan yin nose bleeding,don haka tunaninshi ha6o ne kawai,
Hannu yakai tare da kunna tap ɗin,ruwa ya soma shararowa da gudun gaske,tarba hannunshi yayi tare da ɗebo ruwan ya watsa a fuskarshi yana wanke blood ɗin,murzar wurin ya shiga yi don jinin ya tsaya amma yaƙi daina zuba,ya kusan 15mins a haka sannan jinin ya dakata da ɗigowa,ajiyar zuciya ya saki tare da kai hannu ya kashe tap din,
Sannan ya fito daga cikin toilet ɗin,yana ƙoƙarin ɗaga ƙafarshi ya nufi gadonshi,wani irin jiri ya kwashe shi,hannu ya aza asaman kanshi tare da ambaton sunan Allah,yayin da idanunshi ke ganin mashi biji biji,
Yana cikin wannan yanayin Sehrish ta faɗo cikin ɗakin ambaton sunanshi ta shiga yi "junaid, junaid.....,"
ganin shi atsaye abakin ƙopar toilet ya sata tsayawa tana kallonshi tare da cewa"baby junaid meya faru ne naganka haka?baka jin daɗine,"
Jin muryarta yadinga yi acikin kanshi tamkar ana buga ganga,hakan yasa ya yanke jiki zai faɗi gadan gadan,
A wani irin slow sehrish ta ƙarasa wurin da sauri ta ruƙo shi suka faɗi ƙasa atare,hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba jin yarda yake kokowar fitar da numfashinsa,hankali a matuƙar tashe take faɗin"Innalillahi_!junaid!meke faruwa dakaine!me yake damunka ne?ka faɗamun dan Allah,
Ko iya ɗaga la66ansa ba yayi bare ya iya furta mata wata kalma,hannunshi dake kerma yasa tare da ƙara ƙanƙameta sosai ya kwantar da kanshi asaman ƙirjinta yana cigaba da ƙoƙarin fitar da numfashinsa,hankalin sehrish ba ƙaramin tashi yayi ba,tuni ta soma fitar da ƴan matan hawaye,yanke shawarar zuwa ta sanar ma wani tayi don a hanzarta zuwa aga halin da yake ciki,ƙoƙarin janye jikinta tayi daga nashi,tamkar zata rabashi da ranshi haka yaji,ƙanƙameta ya kuma yi sosai da sosai sai lokacin ya iya furta"rishi kada ki tafi ki barni a yanayin da nake ji zan iya mutuwa,"
Cikin shessheƙar kuka take cewa"junaid ka bari inje in sanar dasu,idan wani abu ya same ka fa"?
"A'a nidai kada ki tafi kibarni,"ya ambaci hakan da wata irin kasalalliyar murya,tsananin tausayinshi ne ya kamata,mayar da hannunta tayi abayanshi tare da ƙara rungumo shi ajikinta tana tofa masa addu'a,lamo yayi ajikinta yana faman sauke ajiyar zuciya,lokaci guda kuma numfashin ya daidaita kamar yarda yake ada,komai nashi yadawo normal,wani irin sanyine ya ratsa zuciyarshi,idonshi na arufe yake shaƙar ƙamshin turaren rishi ɗinsa,gaba ɗaya ya shiga yanayin da bai ta6a shigar irinsa ba,
Muryarta ce ta katse shi da cewa"junaid kana lafiya kuwa?naji ka tsit"?
shiru yayi mata,saboda bayason tasan cewa ya dawo cikin hayyacinsa,baison ta raba jikinta da nashi,ɗumin jikinta ba ƙaramin daɗi yayi mashi ba,yaushe rabon da yaji ɗumin mace haka akusa dashi tun yana da kananun shekaru,tunda mommynshi tabarshi,Aunty azmee ta ɗaura da shayar dashi,shima ɗin da zarar ta kammala bashi nono ƴan uwanshi ke ɗauke shi daga wurinta,don basu son rabuwa dashi kona minti ɗaya,ya saba da jikin abban shi,dana ƴan uwanshi yayi missing wannan feeling ɗin,
Jin yarda junaid ya lafe mata ajikinta kamar jinjiri,yasa tayi tunanin cewa kodai ya cika ne,cikin sauri takai hannu tare da ɗago da kanshi tana kallon fuskarshi,waro ido waje tayi ganin yarda yake ta faman sakin murmushin nan nashi,ranta ne ya bata cewa Dama duk plan ne ya tsara mata don ya tsoratar da ita,ɗaure fuska tayi tare da cewa"janaid wannan duk shirinka ne ko? don ka tsoratar dani,"
Buɗe idanunshi yayi a hankali yana kallon fuskarta data zuba mashi ido,tana mashi kallon Tuhuma,
Murmushi ya kuma saki tare da cewa"dan Allah rishi ki mayar dani a jikinki na kwanta,ba kiji wani irin daɗi dana ji ba,daɗi kamar nayi bacci,"ya ƙarasa maganar yana lumshe mata ido,tsuke fuska sehrish tayi tare da cewa"amma ka rainamin wayau junaid!wai meyasa ka fiye shiririta ne,kalli fa, ka gani hada hawaye na soma zubarma saboda halin da na sameka aciki,ashe duk plan ne ko"?
girgiza mata kai yayi tare da cewa"ba haka bane reesh,kona faɗa maki gaskiya ba zaki yarda ba,"
102.
A hankali ta kwantar mashi da kanshi ƙasa,sannan ta matsa tare da saita fuskarta akan tashi tana kallon shi,shima binta yayi da kallo yarda ta duƙo da fuskarta asaman tashi, yayin da gashin kanta kuma tayi masu rumfa.
"Junaid waye uncle Abusufyan?naji abbanku na cewa zaizo nigeria,kodai shima ɗin yayanku ne"?
girgiza mata kai yayi alamar a'a yace"uncle ɗinmu ne,ƙanin mahaifinmu dake zaune a ƙasar turkey"
jinjina kanta ta ɗanyi kafin ta kuma cewa"bayan shi kuma naji Abbanku yana cewa,Mommynku zata zo itama,tare da wata goggonku ta katsina da kuma Ammi da Aunty azeema,duk zasu zo,"
Sai da ya bari takai ƙarshen maganarta sannan ya ɗan harareta tare da cewa"Ashe dama jin gulma ne ya kawoki ɗakin"?
Murmushi tayi tace"no ba haka bane junaid,inason nasansu ne saboda na koyi zama da kowannansu,bana so na samu matsala da kowa acikin family ɗinku,"
"Zan faɗa maki halin kowannansu amma bisa sharaɗi ɗaya'?ya jefa mata tambaya,
Tace"ina sauraronka wane sharaɗine wannan"?_
murmushi ya saki tare da kai hannunshi ya nuna mata red lips ɗinsa yace"kiss on lips,if u agree then saina faɗa maki,"
hannu tasa tare da ɗan buge bakinshi tace"pls junaid banason wasa fa,in zaka faɗamun ka faɗamun kawai,in ba haka ba zan tashi inyi tafiyata,"
tayi maganar tare da yunƙurawa zata miƙe cikin sauri ya ruƙo hannunta tare da cewa"rishi mommyn mu bata da sauƙi,nima haka naji ana faɗa,amma in har zaki iya zama da babban yayanmu to wannan bazai maki wuya ba,bambancin ita mace ce kinsan ku mata da tsiwa kuke,
Dariya tayi tana sauraronshi
"Uncle ɗinmu kuma Abusufyan,wayayyen mutun ne,idan yazo zakiji daɗin zama dashi,bafa wani babba bane autansu daddynmu ne,yana da sauƙin kai sosai amma idan mutun bai kwanta mashi araiba hmmmmm bazasu ta6a jituwa ba,Aunty azeema kuma kamar abbanmu take wurin faran faran da mutane ga son ƴa'ƴa,zakisha mamaki idan tazo ta ganki sosai zata jaki ajikinta,goggon katsina kuwa......"bai ƙarasa ba ya kama dariya,
Murmushi ta saki tare da cewa"me tayi ita?ko batasan mutane"?
Girgiza kai yayi tare da cewa"a'a tanason mutane sosai,matsalarta ɗaya tana da mental illness.......'
Tunda junaid ya ambaci mental illness taji gabanta ya ɗan faɗi kaɗan kamar maison tuna wani abu acikin brain ɗinta,
"tana da ban dariya sosai,tana fa iya ganinki tace ke ɗiyar wani ce acikin family ɗinmu kuma dole ki yarda da hakan in ba haka ba ta sanya rigima hada kuka ma,'
Sai faman zuba junaid yake yi yana korama sehrish jawabi,ita kuwa tuni tayi nisa cikin tunaninta,kalmar da ya faɗi na cutar ta6in hankali ta tsaya mata arai,so take ta tuna waye ta ta6a sani da irin wannan lallurar amma sam tagaza tuna hakan,
Ganin ta tafi duniyar tunani yasa junaid kai hannu ya janyo sumar kanta yana cewa"wai menene haka reeeshi,kin barni ina ta zuba kamar rediyon da bata da saiti,"
Firgita ta ɗanyi tare da kallon shi har lokacin yana daga kwance tace"junaid thanks for the information,zan koma bedroom ɗina naji ana kiran sallar isha,kaima ka tashi kaje kayi sallar,'
Ba musu ya amsa mata da cewa"bari nayi alwala sai mu fita atare,"
Amsa mashi tayi da toh sannan ta miƙe tare da juyawa ta ɗauko mayafinta daya faɗi kasa ta rufe kanta dashi,toilet junaid ya shiga shaf shaf yayi alwala,bayan ya fito atare da ita suka saukko downstairs,
Anan ya haɗu dasu Irfan zasu masallacin suma yabi bayansu suka tafi,
Komawa bedroom ɗinta tayi kai tsaye ta fada toilet ta ɗauro alwala,bayan ta fito ta ƙarasa wurin wardrobe dinta tare da ɗaukar hijabinta da sallaya ta shimfiɗa tare da kabbara salla,anatse ta kammala sallar,fitowa tayi daga dakin nata sannan ta wuce kitchen don ta shirya ma kanta abincin da zata ci saboda yunwar data taso mata,
_💋Boss Bature💋_
A hankali Motarsu tashiga babban gate din gidan Abusufyan,major ne ke driving dinshi yayin da Omar ke hakimce a seat ɗin baya,sai faman zullumin haɗuwarshi da hossana yake saboda yasan cewa ba ƙaramin fushi take dashi ba,saboda ƙin zuwan da yayi,
Parking ɗin motar major yayi sannan ya fito tare da buɗe mashi motar,a hankali Omar yasa ƙafa tare da fitowa daga ciki,sannan cikin sauri batare da 6ata lokaci ba ya wuce cikin gidan,
Tunkan yasa ƙafarshi cikin parlourn nasu yajiyo shessheƙar kukan hossana,tsayawa ya ɗanyi yana sauraron abunda suke cewa,
"Hossana wai ba zaki daina kukannan ba?salon ki 6ata kwalliyarki ko"?
"Jahad ba zaki gane bane,bakisan yarda nake ji bane,saboda ya omar nayi kwalliyar nan,amma ta tashi a banza,yau ma bazaizo wurin mu ba...'cikin shessheƙar kuka ta ƙarasa maganar,
ƙayataccen murmushi Omar ya saki a fuskarshi,kafin yasa kai tare da shiga cikin palourn,samunsu yayi zaune asaman 3 seater,hossana ta kwantar da kanta asaman hannun sofa ɗin,yayin da jahad ke gefenta tana rarrashinta,gaba daya duk sunyi wanka sun canza kayan jikinsu,riga da skirt ne ajikin jahad,hossana kuma gown ce mai kyan gaske,
jin alamar motsin mutum yasa jahad ɗagowa tana kallon shi,cike da mamaki ta buɗe baki zatayi mashi magana,da hanzarin gaske ya dakatar da ita ta hanyar yi mata nuni da hannunshi alamar ta tashi ta tafi,murmushi jahad tayi tare da miƙewa cikin sanɗa tabar saman sofa ɗin ta koma saman 1 seater ta zauna tana kallon dramar da ya Omar ɗinsu zai shirya,cikin sanɗa ya lalla6a tare da komawa wurin da jahad ta tashi ya zauna,sannan yakai hannunshi tare da ɗan janyo wutsiyar gashinta,
A fusace tace"dan Allah jahad ki rabu dani inji da abunda ke damuna,ki tashi kiban wuri,"
Murmushi Omar yayi tare da cewa"zan tafi amma ki fara faɗamun meyasa kika damu da yaya Omar ɗinki har haka"?
Sam hossana bata gane voice ɗinshi ba saboda ranta a6ace yake,
"Saboda inason shi sosai,jahad nasan ni kawai nake haukana,yana can wurin hayatyn shi,suna shan soyayya.....'
Katse ta Omar yayi da cewa"kina kishi ne"?
A faɗace tace"saboda me bazanyi kishi ba,nima ae zuciyata ce a ƙirjina ba dutse ba,"
Wannan maganar ta hossana ba ƙaramin dariya taba marshal Omar ba,hatta jahad sai da ta murmusa daga inda take,
Kwantar da kanshi ya ɗanyi abayanta yana cewa"am really sorry babyn Omar,nayi missing ɗinki sosai,nasan nayi laifi ayimun afwa bazan ƙara ba..."jin muryar Omar raɗau a kunnanta yasa tayi hanzarin ɗagowa tana kallonshi da idanunta da suka cicciko da kwalla,
Waro ido Omar yayi yana kallonta ba ƙaramin tsorata yayi ba da ganin makeup ɗin da ke a fuskarta,ta dambara Uwar foundation kamar wata aljana,Jan bakin da ta shafa ya 6ata fuskarta har wurin cheeks ɗinta saboda uban kukan da tasha,ga maskara ta zazzago mata a ƙasan idonta,
Hankali tashe Omar yace"subhanallahi,kuke ganinmu bamu muke ganinku ba,Babyn Omar wannan kwalliyar fa?dama itace kwalliyar da ake cewa anyimun don inzo in gani,"cike da zolaya yayi maganar,amma tamkar ya tunzura hossana nan take ta 6are baki tare da fashewa da wani sabon kukan,
Dariya jahad ta dinga tiƙa kamar kamar me har tagaza dakatar da kanta,
Yama rasa ta inda zai fara shawo kanta don ya lallashe ta,hakan ya ƙara hasalata,kamar wata ƙaramar yarinya,ba ƙaramin tausayi ta bashi ba yasan duk don saboda rashin zuwan shi ne,hannu yasa tare da janyota jikinshi yayi hugging ɗinta sosai yana ɗan bubbuga bayanta,lokaci guda ta nemi kukan da takeyi ta rasa,sai gata tana faman sauke ajiyar zuciya,
a hankali ya furta"am really sorry hossana,bazan ƙara 6ata maki rai ba,kullum zan dinga zuwa idan ma bansamu halin zuwa ba zan kira ku awaya mu gaisa,"
Ya ƙarasa maganar tare da cewa"kin yafe mun"?
ƙasa ƙasa tace"na yafe maka,amma karka ƙara,"
murmushi yayi tare da ɗagota daga jikinshi yana kallon fuskarta,sai faman cin magani takeyi tana haɗe mashi fuska,
"Kin ci abinci kuwa"?
"A'a banci ba,"
"Why"? Ya tambaya yana kallon bakinta da take ta faman turowa irin na shagwa6a66u,
"Kai nake jira kazo ka bani abaki,"
"Really"? ɗaga mashi kai tayi alamar eh,
Juyawa ya ɗanyi tare da kallon jahad dake zaune tana kallonsu gwanin burgewa yace"dagaske hossana bata ci komai ba"?_
Amsa mashi tayi da eh,jinjina kai yayi sannan yace"ki kawo mata dinner ɗinta anan,sai na tabbatar da taci ta ƙoshi sannan zan tafi,"
Murmushi jahad tayi tare da miƙewa ta wuce downstairs don pta shiryo masu dinner din,"
_💋Boss Bature💋_
Yau da wuri suka dawo cikin gidan wuraren karfe goma dai dai,wani irin tsoro da fargaba sehrish taji,musamman da azmee ta sanar da ita cewa ga dinner ɗin sgr can taje takai mashi,bakomai ya faɗo mata arai ba face abunda ya faru ɗazu tasan cewa dole ya tuhumeta saboda ita kaɗai ce macen da take shiga part ɗinsa,sai faman zarya takeyi acikin bedroom ɗinta,tana tunanin yarda zata tunkare shi ayau ɗinnan,
Hayaaam
Tafiya takeyi cikin sanɗa tana waige waigen ko akwai wani a main palour din cikin sa'a taga babu kowa,murmushin mugunta ta saki tare da nufar kitchen din,tana shiga tayi arba da tray na abincin da Azmee ta shirya ma Sgr,asaman dogon table na kitchen ɗin ta ajiye mata,jinjina kai hayaam tayi tare da cewa"hmmmmm yarinya kenan yau zaki fara sanin koni wacece wurin iya makirci,"
Tana faɗin hakan ta shiga ciki kai tsaye ta tsaya wurin tray din,hannu tasa tare da buɗe warmer ɗin dake ɗauke da chicken ppr soup,sai faman ƙamshi yake yi,murmushi hayaam tasaki tare da kai hannu cikin sumar kanta,ta cinko gashin kanta sannan ta jefa acikin chicken ɗin tare da sa hannu ta motsashi aciki,sannan ta rufe murfin,duk hakan bai mata ba sai da tabi komai na abincin ta sanya gashi aciki,sannan cikin sanɗa tabar kitchen ɗin,tana faman sakin dariya don tasan cewa da zarar sgr yaga gashin nan yarda yake da tsaftar nan ba ƙaramin ƙyamatar yarinyar zaiyi ba,kuma tasan dole ya koreta daga yi mashi aiki,bama wannan ba dole ya hukuntata.
💋💋💋
Fitowa sehrish tayi bayan ta gama zullumin nata,kitchen ɗin ta nufa batare da 6ata lokaci ba ta ɗauko tray ɗin a hannunta tare da wuce wa upstairs,hakanan tadinga jin gabanta na faɗuwa kamar wani mummunan abu zai faru da ita,tsayawa tayi abakin ƙopar shiga falon nashi,sai da ta dai²ta natsuwarta sannan ta zabga sallama,tana jiran jin amsawar shi,
Jin shiru yasa ta ƙara maimaita sallamar,har kusan sau uku ana huɗun ne tajiyo muryarshi yace"Come in,"
Ae tunda taji Voice ɗinsa jikinta ya shiga yin kerma,addu'o'in neman tsari tashiga karantowa abakinta,ta jima atsaye tana faman zullumin abun da zaibiyo baya kafin daga bisani ta daure tare da shiga cikin falon nashi,ƙamshin turaren nan nasa ne ya wanko mata hancinta har saida ta lumshe idanunta,tunkan taƙarasa ta hango shi kwance ya miƙe kafafunshi asaman 3 seater,jikinshi na sanye da pyjamas yellow,ba ƙaramin kyau su kayi mashi ba,kunnanshi na kare da wayarshi alamar waya yake yi,
Gabanta na faɗuwa haka ta nufe shi tare da ajiye mashi tray ɗin asaman table dinsa,saboda tsabar rashin gaskiya,tana ajiye tray ɗin ta juya cikin sauri zata bar parlourn nashi,kamar daga sama taji anyi ma mayafinta kwakkwaran ruƙo ta baya,nan take mayafin ya sulale daga jikinta,zazzare ido waje sehrish tayi jikinta na kerma,nan take tashiga haɗiyar yawu,tsayawa tayi tana jiran maizo biya baya,
Jin alamun motsin shi abayanta ya tabbatar mata da cewa shine yaja mayafinta daga jikinta,tsayawa tayi tana ambaton sunan Allah abakinta,ganin kusan minti biyar bata ji ya ƙara motsawa ba yasa tayi hanzarin juyawa a wani irin firgice sam bata tsammaci yana tsaye abayanta ba, sai dai kawai taji ta kai mashi karo,ja da baya ta ɗanyi tana faman zare ido,tunkan ya tambayeta ta shiga cewa"dan Allah kayi haƙuri,nasan na 6ata maka rai,wlh nima bada son raina hakan ya faru ba,nashiga na gyara maka bedroom ɗinka ne,bayan na kammala shine na ɗan cire mayafina na ajiye asaman gadonka don naji daɗin yin aikin,ashe kafin na fito daga cikin toilet ɗin ka dawo,shine na same ka akwance kana bacci saman mayafina,saboda ina tsoran ka farka ka ganshi yasa nayi ƙoƙarin janshi daga jikinka,shine...cikin bacci batare da saninka ba ka...........'kasa ƙarasa maganar tayi saboda jin yatsun hannunshi da tayi asaman lips ɗinta,alamar tayi mashi shiru,sannan ya hankali ya ɗan ware eyes ɗin nashi akan fuskarta............
A tsananin tsorace take kallon fuskarshi ganin ya ware idanunshi yana kallon fuskarta,a hankali ya zame finger ɗinshi daga saman tausasan la66anta dake ta faman kerma,sai faman haɗiyar yawu take yi tsoranta wane hukunci zaiyi mata,sau biyu yana ƙoƙarin buɗe mouth ɗinsa zaiyi magana amma ya kasa,saboda ya rasa me zaiyi ma yarinyar,tun da yake wata ƴa mace bata ta6a