Author : Boss Bature Category : Arewa Pen
zauna ayita taƙare kawai,in yaso sai jahad tayi mana bayanin komai tunda itace mai cikakken hankali acikinsu,Sehrish ita kanta bana tunanin tana acikin hayyacinta yanzu,
Kowa ya amince da maganar omar,batare da 6ata lokaci ba,suka wuje bedrooms ɗinsu domin yin alwala,hajiya azeema ce ta shigar da Gwaggon katsina cikin ɗakinta tare da saude kafin agyara masu inda zasu zauna,
Yau dae gidan Abban sojoji a hargitse yake,Wlh ni kaina a hargitse nake,sai addu'a kawai,
Abbansu na fitowa daga cikin toilet,junaid ya faɗo mashi acikin ranshi,nan fa gaban shi ya faɗi rasss,sae lokacin ya tuna da cewar babu junaid fa acikin gidan tun ɗazu,duk wannan budurin da akeyi babu shi acikinsu,
Hankalinshi amatuƙar tashe ya tunkari wayarshi dake ajiye saman side drawer ya dauketa,tare da lalubo numbar junaid ya danna mashi kira cikin sa'a wayar tashiga tana ringing amma ba'a ɗaga ba,kusan sau huɗu yana kira ba'a ɗagawa,
Ana biyar ɗinne aka ɗaga wayar,kara wayar yayi kunnanshi yana cewa"Junaid ina ka shiga ne!!"shiru yaji ba'a tanka mashi na,nan fa yabi ya rikice,
"Junaid wai baka jina ina magana ne?bazaka amsa mun ba?junaid kodae wani abu ya faru da kaine?
Nan ma shiru ba'a bashi amsa ba,
Muryarshi tamkar zaiyi kuka ya kuma cewa"don Allah babyn Abbanshi kayi mun magana mana!
Muryar mace ce ta amsa mashi da cewar"ka duba whatsapp ɗinka,zaka ga video mun tura maka,"
Jikinshi har kerma yakeyi wurin katse kiran ya shiga whatsapp ɗinshi,new number ya gani tayi mashi message da video,
Saboda tsabar fargaba,tun kafin ya buɗe video ɗin zufa tashiga gangarowa a fuskarshi,dukkan ilahirin jikinshi ya shiga yin kerma,idanunshi sukayi jawur tsoranshi kar a videon yaga junaid cikin wani yanayi,bazai iya jurar wannan ba,
Runtse idanunshi yayi yana karanto addu'o'i abakinshi,kafin daga bisani ya daure ya cije ya buɗe videon,
Zazzare idanunshi yayi waje tamkar kwayar idanunshi zata faɗo ƙasa,
A ƙarshe kuma ya fashe da dariya,tare da zubewa saman guiwowinshi yana tikar dariya,
Bakomai bane acikin video ɗin nan ba,face Mommynsu junaid Alexandra rungume da junaid asaman gado,suna kwance abunsu,da alama ma kamar bacci yake yi ajikinta.......
😔
Abunda ya faru,lokacin da wata mata ta kira junaid da sunan mommynshi don yazo ya ɗauketa a airport,jiki na rawa junaid ya shige cikin motarshi ya kama hanyar zuwa airport bayan ya fita daga gidanne ya tuna da tace in ya fito ya sanar da ita,fiddo wayarsa yayi da niyyar kiranta,tunanin taya zai kirata ma ba number ya shiga yi,adaidai lokacin ta sake kira tambayarshi tayi ya fito ne,ya amsa mata da eh yana a akan hanyar zuwa,cigaba da tafiya yayi zuciyarshi cike fal da son ganin mommynshi,driving yake yi yana ayyana farkon haɗuwarshi da mommynsu, baisan wani irin runguma zaiyi mata ba,yayi zurfi acikin tunaninshi kwatsam sae ga wasu jerin motoci sun kusa goma sha biyu,baƙaƙe kuma da black tinted,da gudun gaske suka nufo inda junaid yake,koda junaid ya lura da motocin nan fa hankalinshi yayi mugun tashi,ƙarasowarsu ke da wuya suka zagaye motar shi,yadda bazai iya kubce masu ba,nan fa hankalin junaid yayi mugun tashi,jikinshi ya shiga rawa,tsoranshi kar ace mutanen da mommy azeema ta sanar dashi cewa suna bibiyar rayuwarshi ne,zama yayi acikin motar hankali a matukar tashe,
ɗaya daga cikin motocin aka buɗe,sae ga wani gabjejen mutun faffaɗan gaske sanye cikin suits,kai tsaye ya nufi motar junaid hannu yasa tare da knocking glass ɗin motar,zuge glass ɗin junaid yayi atsorace yana kallonsu sae faman haɗiyar yawu yake yi da kyar,
kafin yayi wani yunƙuri Mutumin nan ya buɗe motar tashi,gaba ɗaya ya cakumi junaid ya toshe mashi baki,ya nufi cikin motarshi dashi,bayan ya sanyashi acikin motor,atare suka tashi motocin da gudun gaske suka bar wurin,
junaid dake a back seat na motar tuni ido ya raina fata,hawaye suka shiga wanke mashi face ɗinshi,muryar shi tamkar zaiyi kuka yace"Su wanene ku?laifin me na aikata maku?dan Allah kada ku rabani da rai na,inason na sake ganin Abbana.....'bai kai ƙarshen maganar tashi ba,ɗaya daga cikinsu ya daka mashi tsawa tare da cewa"Shut up!ko tari ka ƙara yi saina fille maka kai,"
Jin haka yasa junaid yayi tsit zuciyarshi na bugawa da ƙarfi da ƙarfi,
Wani katafaren gida suka shiga tare da shi,bayan sunyi parking ɗin motocin,ɗaya daga cikinsu ya buɗe motar tare da ɗauko junaid asaman kafaɗar shi,ya wuce dashi cikin gidan,a babban falon gidan ya sauke shi,sannan ya juya ya fuce,
To fa,tsayawa junaid yayi cikin tashin hankali yake kallon haɗaɗɗen falon komai a gyare tsaf,tunani ya shiga yi mai yasa suka kawo shi nan suka ajiye shi?ko dae kidnapping ɗinshi sukayi ne?hannu yasa yana share hawayen shi,bai kammala wiping ɗinsu ba,yajiyo takun takalmi kwas kwas,
A firgice ya ɗago don yaga wanene,zuba mata ido yayi yana kallonta,daga saman stairs take saukowa down,jikinta na sanye da doguwar riga fara mai shegen kyau tabi shape ɗin jikinta,ƙafafunta kuma na sanye da takalma high hills farare duk da tsayin da take dashi don sam ba gajera bace,ba ƙaramin kyau shigan tayi mata ba,kasancewarta farar fata,wuyanta na sanye da ziririyar sarƙa fara ta diamond,hannunta kuma na sanye da Zobe ɗaya kacal a middle finger,shima na diamond ne,ta ɗaure gashin kanta mai tsayi wanda laushi.
A hankali ta ƙarasa saukowa daga saman benen,sannan ta tsaya tana kallonshi daga inda yake tsaye,duk da akwai tazara atsakaninsu amma suna iya ganin juna sosai,ƙare mashi kallo tashiga yi,burinta junaid ya fara shaida ita wacece kafin ta sanar mashi,
hakanan ya dinga jin gabanshi na faɗuwa rass rasss,batare da jin tsoro ba ya tunkareta sai da ya kusa kaiwa inda take sannan ya tsaya yana kallonta,ƙwayar idanunta yabi da kallo blue colour wanda hakan ya tabbatar mashi da cewar mommynsu ce, dama kuma yasan ta a hoto,komai na fuskarta irin na Babban yayansu ne,duk da ta kwana biyu aduniya amma hakan bai 6oye kyawun fuskarta ba,tamkar ƴar shekara 30 haka fuskarta take,hatta jikinta yana nan yadda yake da kyau da kuma diri,
A hankali junaid ya furta"Mommy!is you?
jinjina mashi kai tayi alamar eh,da gudun gaske ya ƙarasa tare da faɗawa jikinta,sosai ya ƙankameta saboda tsabar farin ciki ya fashe mata da kuka,nan take itama kukan yazo mata atare suka shiga yin kukan babu mai lallashin wani,tamkar zasu haɗe jikin junansu su koma ɗaya haka suka ƙanƙame kansu,daƙyar Alexandra ta iya dakatar da kukan nata,ta sanya hannayenta tare da ɗago da fuskar junaid tana kallonshi,hawaye sun wanke mashi fuskarshi tass,
muryarta na rawa ta ambaci sunan shi"Ro..meo.ɗina,'
Cikin shessheƙar kuka junaid yace"Mommy,ashe zan sanyaki acikin idanuna,bansan da wasu kalmomin zan bayyana maki irin farin cikin da nake ciki ba,i luv u so much mom....'
Jikinta ba ƙaramin sanyi yayi ba,duk irin watsin da tayi dashi tabar Nigeria,hakan bai hana shi sonta ba,
Kwantar dashi ta sake yi asaman ƙirjinta,ta sanya hannayenta tana ɗan bubbuga bayanshi,kafin ta mayar da hannunta ɗaya acikin sumar kanshi,ta jima tana mamakin girman shi,ta tafi ta barshi a lokacin da yake ɗan jinjiri dashi,amma yanzu tadawo ta same shi ya girma ya zama babba,ba ƙaramin farin ciki taji ba,mara misaltuwa,
ɗago dashi ta kuma yi daga jikinta cikin sanyin murya tace"romeo ɗina,kayi haƙuri ka daina wannan kukan duk da nasan na farin cikin ganina ne,ni kaina bazan iya misalta farin cikin dana ji ba,wai yau ni ce tare da babyn dana bari yana jinjirinshi,ya girma ya zama babba,nayi danasanin tafiya nabarka romeo,nayi kewarka sosai,hakanan na raba kaina dakai,ba don bana sonka ba romeo,zan iya cewa nafi sonka fiye da kowa aduniyar nan.....na godema Allah daya nunamin wannan ranar....inaso na sake neman yafiya a wurinka saboda na cutar da rayuwarka sosai,ko wani yaro lokacin da yake jinjiri burinshi yaji dumin mahaifiyarshi,ya kasance atare da ita don samun kulawa daga gareta a koda yaushe,koda ace yana da uba,amma kai baka samu wannan gatancin ba,ka tashi hannun maza ba'a hannun mahaifiyarka ba,baka samu soyayyar nan ba,duk da mahaifinka yayi ƙoƙari sosai wurin gina rayuwarka tayi kyau,haka ƴan uwanka ma ba su bari ka zubar da hawayenka ba,amma duk da haka nasan abun ya jima yana maka Ciwo..."
Tana ƙarasa maganar,ta zube saman guiwowinta agabanshi,tana roƙon yafiyarshi,hakan ba ƙaramin tayar mashi da hankali yayi ba,cikin sauri shima ya zube saman guiwowinshi suna fuskantar juna ita dashi,
"Mommy dan Allah ki tashi,banason kina duƙamin,komai ya wuce yanzu tun da kin dawo wurinmu da ranki kuma da lafiyarki,har yanzu kina da sauran damar da zaki gyara kuskuren da kikayi abaya mommy," ashagwa6e ya ƙarasa maganar,murmushi ta saki tana kallonshi,ji take yi da tana da ikon da zata mayar dashi cikin cikinta,taƙara haifo shi da tayi,don kawai ta bashi wannan kulawar daya rasa,
Sun jima a wannan yanayin,kafin daga bisani suka miƙe tare,ta ruƙo hannunshi cikin nata,ta wuce dashi upstairs ɗaya daga cikin bedrooms ɗin dake a wurin suka shiga,ɗakin ya haɗu sosai,
"Mommy me yasa ba kije gidaba?wurinsu Abba su ganki? Yayi tambaryar yana kallonta,
"I just came because of u junaid,inaso mu samu lokaci sosai atare,ka ganni dakyau nima na ganka da kyau,tun yanzu in fara aikina na baka kyakkwayar kulawa kamar jariri,in yaso gobe zamu shiga gidan da safe ko?
Murmushin jin dadi junaid yayi tare da cewa"Eh,mommy,dama ni yakamata in fara ganinki tunda dama nine ban sanki ba a zahiri"
"Bansani ba ko kana jin yunwa,amma zansa akawo mana abinci,in baka abaki kaci ka ƙoshi,yau dae atare da babyna zamu kwana,'
Dariya junaid yayi,ba ƙaramin daɗin maganarta yaji ba,sosai mommynshi ta shiga bashi kulawa a wannan lokacin,
Kunji yadda akai junaid ya kasance tare da mommynshi,har ta ɗauko ma Abbansu video ɗinsu saman gado ta tura mashi,abunda yasa kuma Abban bai gane Voice ɗinta ba,shine da kanta tayi amfani da wayarta wurin canza muryarta don ta tsoratar da Abbansu.
💋Boss Bature💋
fitowa Abbansu yayi daga cikin ɗakin nashi fuskar nan tashi awashe saboda tsabar farin cikin dawowar Alexandra,bakomai yafi faranta mashi rae ba face Junaid daya gani rungume ajikinta,yaji daɗi sosai,ko ba komai Junaid dae ya haɗu da mommynshi,hankalinshi zai ƙara kwanciya,
Bai sanar masu da zuwan nata ba,saboda sunyi waya da ita ta sanar dashi cewar till tomorrow zasu shigo gidan don tana bukatar kasancewa da junaid don su kara fuskantar juna sosae,hakan yasa ya bari kawai sae goben sannan su ganta unexpected,duk da a kagare idanunshi suke da suyi tozali da ita.
Gaba daya suka haɗu atare suka wuce masallaci,
Jin shiru hayaam bata fito ba tsawon lokaci,yasa Azmee leƙawa ɗakinta,anan ta same ta zaune dirshan gefen gadon ta zabga uban tagumi,jin motsin mutun yasa ta ɗagowa fuskarnan a yamutse ta kalli azmee,
"Hayaam wai dama duk budurin nan da akeyi acikin gidan nan kina ɗaki ƙumshe"?
Jin abunda azmee tace yasa tace"hmmmm,to ina zani Aunty azmee?babban yaya ya kore ni daga gidan nan,nasan muddin na leƙa waje ya ganni sai yasa an kora ni daga gidan nan,'
Cike da mamaki azmee tace"Subhanallahi!taya akai hakan ya faru?laifin me kika aikata mashi da har ya koreki daga gidan nan?shi da ma bai damu da mutane ba"
ta6e baki hayaam tayi kafin tace"Ni banyi mashi laifin komai ba,Sehrish ce ta shiryamun makircin da yasa har ya kore ni,batare da nayi mashi laifin komai ba,"
Tunda tasoma magana azmee ke kallonta,ga rashin gaskiya nan ya bayyana ƙarara a fuskarta,taya akai ma Sgr yasan da zamanta da har zai kore ta?dole sai in itace tayi mashi shisshigin da yasa har ya ganeta kuma ya kore ta,
"Allah ya kyauta toh,!yanzu ya zakiyi kenan?kinfa san halin shi!dole fa ki tattara kibar gidan nan!in ba haka ba wlh zaki fuskanci mummunan hukunci daga wurinshi,'
Hankali tashe hayaam ta miƙe tsaye tana kallon Azmee tamkar za tayi kuka tace"don Allah aunty azmee ki taimaka mun,wlh banso in bar gidan nan!na saba da zama acikinshi,anan nake samun duk wani jin daɗin da nakeso,acan gidanmu duk babu waɗannan kayayyakin more rayuwar,nasan zaki taimaka mun,"
Dariya azmee tayi tana kallonta ko yaushe tazo da har zata ce tayi sabo da mutanen gidan ta ayyana a ranta,
"Aunty azmee dan Allah ki taimaka mun,in xauna acikin gidan nan,nasan yana jin maganarki,ki roƙa mun shi akan yabar ni in cigaba da zama,wlh bazan ƙara shiga shirgin kowa ba,zanyi rayuwata cikin salama,"
Azmee tace"Tabɗijancan!so kike kija mun bala'e ko?ina zaman lafiyata agidan nan,Wacece ni?da har kike tunanin Sgr zaiji maganata?kin manta matsayina ne acikin gidan nan?kefa kike da alaƙa dasu ko kin manta ne"? Da biyu azmee tayi mata maganar saboda wulaƙancin da hayaam tayi mata,
Magiya hayaam ta shiga yi mata tana roƙonta akan ta nema mata mafita tamkar zata zuƙunna mata saman guiwarta,don ita sam bata shirya barin gidan yanzu ba,tabb yo mima akai kenan"ta fada cikin ranta.
Sosai abun yaba azmee dariya,
"Hanya ɗaya ce hayaam in zaki iya!idan har kinason cigaba da zama acikin gidan nan"!
jiki na rawa hayaam tace"Ina sauraronki aunty azmee,wlh koma manene zan iya ni,"
Azmee taci gaba da cewa"daga yau zaki dinga yin shigar maza,kinasa gashin baki kamar yadda sehrish tayi a lokacin da tafara aiki acikin gidan nan kinga sai kizama kamar sabon mai tayani aiki"
Waro ido waje Hayaam tayi tare da cewa"Haba Aunty azmee ni zanyi shigar maza?so kike na ƙasƙantar da kaina har yarinyar can ta raina ni"
Azmee tace"that's the only solution,if not sai dae fa ki tattara kayanki ki bar gidan nan!"ta karasa maganar tana jiran jin ta bakin hayaam din don tasan da kyar zata amince dama shiyasa ta fadi mata hakan,
gyaɗa kai hayaam tayi tace"shikenan zanyi tunani in ga in zan iya,kafin nan zanci gaba da 6oye ma ganinshi"
Azmee tace"to shikenan kiyi yadda kika ga yafi maki,ni dai gaskiya ba ruwana,kuma fa dole ki rika futowa kina taya ni aiki,indai kina a cikin gidan nan, don bazai yiwu ba ki zaune a daki baki komae gaskia "
Hannu hayaam ta aza akanta tana faɗin"Nashiga uku!
dariya Azmee tayi kafin ta kuma cewa"hayaam zamanki fa bazaiyiyu acikin gidan nan ba,Sgr ya riga da ya kore ki!muddin ya sake ganin fuskarki dole ya hukuntaki,kuma kinga gwaggonsu ta katsina tazo,!matar nan bazata ta6a bari ki zauna acikin gidan nan ba,in har taji cewa ke ƙanwar matar yayyansu ce,nan zaki ga tashin hankali,sae ta kunyataki acikin jama'a,shiyasa nace kiyi shigar maza kawai,Ni zan taimaka maki muna yin aiki atare inyaso duk wanda ya tambayeni xance mashi abokin aiki ne na samo,nasan babu wanda zai zargi wani abu,
Komawa hayaam tayi ta zauna gefen gadon cike da damuwa,gaba ɗaya taji ta tsani kanta,da tana zaman lafiyarta acikin gidan,kwaɗayinta da zalamarta su suka ja mata,gashi ita gskia bata jin zata iya yin wani shigar maza wannan ai kaskanci ne,
123.
"Na manta ban sanar maki ba!"
Rai a6ace hayaam tace"Menene!"
Azmee tace"SEHRISH TAGA ƳAN UWANTA,ASHE ƳAN UKUNE SU,YANZU HAKA SUNA ACIKIN GIDAN NAN!BAKI GANSU BA,ABUN FARIN CIKI KAMANNINSU IRI ƊAYA SAK!BAKI TA6A BANBANTA SU,"
A razane Hayaam ta miƙe tsaye hannunta dafe da saitin zuciyarta tace"WAI DAGASKE AUNTY AZMEE?
AZMEE TACE"Zan maki ƙarya ne?yaran suna nan,kyawawan gaske,HOSANA DA JAHAD!!!!!"
Jiki amace hayaam ta koma ta zauna,gabanta na faɗuwa rasss rasss!tama rasa ina zata tsoma ranta taji dadi,
Murmushi azmee ta saki tare da juyawa ta kama hanyar fita daga ɗakin,buɗe kopar tayi tare da sa kai ta fuce,
Kamar jira take azmee ta fita,nan fa ta fashe da kuka kamar ranta zai fita,saboda tsabar 6acin rai,wani irin ƙululun baƙin ciki ne taji ya tokare mata maƙoshinta,komae ya jagule mata,tabbas tana bukatar tayi magana da Aunty laila,lokaci guda yadda sukai da yaya babbar ya shiga dawo mata, sambatu tashiga yi tana bugun bed mattress kamar wata zautacciya,
Bayan kammala sallar isha'e,atare suka dawo cikin gidan,a babban falon suka kuma zama kamar ɗazu dae,
Gyaran murya Abbansu yayi kafin yace"Ina yaran suke ne?wani yaje ya kira mana su,domin jin ta bakinsu"
Miƙewa fawan yayi kamar dama jira yake yi,wucewa ɗakin sehrish yayi bayan ya isa ya kwankwasa masu ƙopa,jahad ce ta buɗe mashi kopar jikinta na sanye da hijabi da alama bata jima da kammala salla ba,
Fuskarshi ɗauke da murmushi yace"Abba nason ganinku,idan ba damuwa ku fito mu tafi atare,"
Jahad tace"Toh,bari na kirasu,"ta fadi hakan tare da juyawa ciki ta kira hosana da sehrish wadda har lokacin bata motsaba,tana nan saman gadon ta ƙanƙame jikinta,
"Hosana kuzo Abbansu na son ganinmu!hada sehrish kema ki taso,"
Maƙe kafaɗa sehrish tayi alamar bazata taso ba,
"Sehrish dan Allah kidaina abunda kikeyi,nasan duk don saboda ganinmu ne,idan har baki so zuwanmu ba zamu bar gidan nan,"acewar jahad,
ɗaure fuska Sehrish tayi tare da kawar da fuskarta gefe tana faman hura hanci,
babu yadda basuyi ba akan sehrish tabiyo su amma taƙi binsu,har fawan sae da ya leko yayi mata magana amma ko kallo ma bai isheta ba,
A ƙarshe suka ƙyaleta,suka bi bayan fawan ya shiga babban falon tare dasu,
gaba daya hankalin kowa ya dawo kansu,musamman Abusufyan dake zaune agefen abbansu,ji yake kamar ya tashi ya rungumosu ajikinsa,su twins kuwa dasu irfan zuba masu ido kawai sukayi suna kallonsu,haka Omar da Abbas da kuma hajiya azeema,kowa burinshi yaran su tabbata ƴa'ƴan abusufyan ne,duk sun ƙagu suji cewa yaransa ne,tabbas da ba ƙaramin farin ciki zasu ji ba,
Sgr dae tunda ya ɗago ya kallesu ya gane cewa babu sehrish acikinsu,bayan yaji cewar dukansu Abbansu yace a kira mashi,
Abbansu ne yace"Ina ɗayar take ne?ni bana gane ma wacece babu acikin ku!
Omar yace"waɗannan hosana da jahad ne!sehrish ce babu acikinsu,"
Abbas yace"Masha Allah,gaskiya banta6a ganin yara masu kamanni irin nasu ba,Allah dae yasa mu tabbatar da abunda muke hasashe akansu....'
"Meya hanata zuwa"?muryar Sgr ce ta karaɗe kunnuwansu,har sae da su jahad suka ɗan tsorata dashi,dama tunda sukazo hankalinsu ke kanshi saboda launin kwayar idonshi ba ƙaramin ɗaukar hankali takeyi ba,
Fawan yace"Ba yadda bamu yi da ita ba,amma tace bazata zo ba,kamar tana cikin damuwa sosai,ko kallona fa batayi ba,da naje kiransu,'
A zafafe Sgr ya yunkura tare da miƙewa daga saman kujerar da