ABBAN SOJOJI TAKUN TSAKIYA 2 BY BOSS BATURE.txt

Author :  Boss Bature Category :  Arewa Pen

Chapter   37 / 80

108K to 111K   out of 238K words

shi, babban abunda take fargaba shine kada su fara zarginta akan abunda ba laifinta bane, yanzu kuma duk ranar da sgr ya tuna da wannan abun daya faru a tsakaninsu dole ya tuhume ta, batasan wane irin kallo zaiyi mata ba,😖
"Ashe so yayi ya kashe ni !" ta furta cikin sanyin murya, "ni bansan me nayi mashi ba, ya Allah ka kare ni daga sharrin shi, ya Allah kada ka bashi nasara akaina,"
tana cikin wannan tunanin sam bata ji takon tafiyarshi ba, fitowarshi kenan daga part dinsa ya kimtsa cikin suits farare ba ƙaramin kyau suka yi mashi ba,
tsayawa yayi yana kallon ikon Allah yarinyar da yake ta faman jira ta gyara mashi bedroom dinshi itace zuƙunne tana shessheƙar kuka, cike da mamaki ya ƙarasa har inda sehrish take sam bata zaci ganin shi ba, sai dae taga ƙafafunshi masu sanye da haɗaɗɗun takalma, gabanta ne taji yayi wani irin bugu duk da bata san wanene ba amma tana da tabbacin cewa shi neeee saboda ƙamshin turaren nan nashi,
ƙara ƙanƙame jikinta tayi tana faman zazzare ido a tsorace, muryarshi ce ta ratsa kunnanta da cewa"ke tashi tsaye,"
cikin sauri sehrish ta miƙe tsaye jikinta na kerma kamar wadda taga wani horror sam taƙi yarda ta kalli fuskarshi saboda ta tsorata dashi,
shiru ya ɗanyi baice komai ba tamkar mai nazarin wani abu, hannunta yabi da kallo sai faman kerma yatsun hannun suke yi,
"Are u okey"? ya tambayeta,cikin sauri tace"eh"
"Okey agyaramin bedroom ɗina," yana faɗin hakan ya kama hanya ya wuce,
Sam takasa janye idanunta daga kallon bayanshi har sai da ya 6ace ma ganinta, sannan ta wuce part din nashi, lokacin data shiga bedroom dinshi ba komai ta tuna ba face abunda ya faru atsakaninsu daren jiya, bin shimfiɗeɗen gadon shi tayi da kallo har yanzu zanin gadon a cukuikuye yake, saboda damben da suka sha jiya, hannu takai tare da yaye bedsheets ɗin nashi ta rungumo shi a kirjinta tana shinshina ƙamshin turarensa, ita kaɗae tasan irin yanayin da tashiga a wannan lokacin duk da firgicin da take ci amma hakan bai hanata jin wannan yanayin ba.............💋😉

*💋Boss💖Bature❤*✍️

A galabaice take hura wutar murhun wani irin uban hayaƙi yake fitowa baƙiƙƙirin duk ya cika kitchen din, idanunta sunyi jawur kamar na mai shan taba, matashiyar yarinyace da bazata wuce shekara goma sha huɗu ba aduniya, a wani matsakaicin gida na masu rufin asiri, jikinta na sanye da koɗaɗɗen zani na atampha tayi ɗaurin gaba dashi, duk ya yayyage jikinshi yayi baƙiƙƙirin saboda dauɗa, gaba ɗaya ita kanta yarinyar abun ban tausayi ce, ta bushe ta rame ta ƙanjame yadda kasan skelaton haka take, saboda kasusuwan wuyanta da suka firfito mata waje kamar zasu fito daga fatar jikinta saboda tsabar rama, saboda koɗewar da fatar jikinta tayi baza ma a iya tantace launin fatarta ba, fara ce ko baƙa 😢

sai faman goho take yi agaban murfin tana hura wutar da bakinta amma wutar taƙi kama wa, zuƙunnawa tayi gaban murhun ta zabga uban tagumi hawaye na faman kwararowa daga idanunta, cikin murya kuka ta soma cewa"Ya Allah ka kawomin karshen wahalar da nake sha acikin gidan nan........'
Muryar mammynsu ce ta katse ta da cewa"AMAL!! wai uban wa kike so yayi wankin nan ne? zaki fito kiyi shi ko saina maki dukan tsiya ne? Hankali atashe tace"mammy iccen girkin ne ɗanye baya ci, tun ɗazu nake faman wahalar hura shi amma yaƙi ruruwa,"
Uban tsoki matar ta buga tare da cewa"wannan ba damuwa ta bace ba, ki tabbatar da kin hura wutar ta kama,sannan ki fito ki wanke mana kayan mu, bayan kin gama kuma ki share gidan,"
cikin ƙunar rai ta amsa mata da "toh,"
Sannan taci gaba da hura wutar don ta kama,
cigaba da magana matar tayi tana cewa"Yayarki nacan gidan hutu, ta manta dake gaki nan a wulaƙance kin zama tamkar baiwa a wurin mu, da ace tana sonki ae bazata barki a hannun mu ba,"
Shiru Amal tayi hawaye na zuba daga idonta, har yau tagaza yarda cewa yayarta zata iya yi mata hakan, saboda me zata tafi tabarta hannun waɗannan mugayen? Ta tambayi kanta,
muryar mammyn tasu ce ta sake katse ta da cewa"hmmm dama tsiyar talaka kenan anyi mata hanyar arziƙi amma ta manta da mutane, baƙin halinku iri ɗaya dana uwarku, ae duk laifin laila ne ko uban waya faɗa mata ana yiwa ƴa'ƴan kishiya abun arziƙi," tana zaune saman gujera ƴar tsugunno sai faman sambatu takeyi kamar zautacciya, wata tsamurarriyar mata ce fara siririya ta fara tsufa don gashin kanta harya fara hurhura, jikinta na sanye da atampa riga da zane, ta tsoge ɗaurin ɗankwalin nan ture kaga tsire, hannunta na ruƙe da aswaki sae faman kwalkwalar haƙoranta takeyi wadanda sukayi jawur saboda tsabar cin goro, kai kana ganin ta zaka shaida cewa ba ƙaramar jarababbiya bace, irin tsaffin nan da basa gajiya da mita,
daƙer Amal tasamu wutar ta huru, sannan ta fito agalabaice, kai tsaye ta wuce inda uban kayan wankin suke dila guda,gaba ɗaya kayan sawarsu ne su duka dana uwar dana su abra da hayam, ga zannuwan gado da barguna duk sun tara mata su don ta wanke, abun babu imani acikin shi, babu irin wahalar rayuwar da yarinyar bata shaba,uƙuba iri iri suke yi mata, ko bacci bata samu, in ma tayi baccin da duka suke tashinta, ko kuma taji saukar ruwa bokiti guda ajikinta, fatar jikinta duk cizon sauro ne gashinan ruɗu ruɗu saboda awaje take kwana, su kuma su shige ɗaki sai ita kaɗai ga tsora da Allah yayi mata, kullum cikin zullumin mai zai faru da ita take yi, duk yarda taso su haɗu da yayarta abun yaci tura, a halin da ake ciki ita kanta Amani batasan cewa yarinyar na raye ba, tun wani zuwa da tayi suka sanar da ita cewa yarinyar ta 6ace an neme ta an rasa, hankalinta ba ƙaramin tashi yayi ba, a lokacin tasha kuka sosai wurin neman yarinyar amma babu ita babu alamarta, tun tana sanyawa a nemo mata ita har tagaji ta daina saboda kullum babu labarin anga yarinyar shiyasa ta fidda rai da ita, ashe lokacin 6oye yarinyar sukayi a gidan makwabtansu acikin wani ɗaki aka rufe ta kamar akuya, duk in amani zataso maiduguri sai su kaita can gidan ajiya har tazo ta tafi bazata sani ba, hakan yasa basu ta6a haɗuwa da ita ba tun auranta da Abbas na wata takwas a lokacin abun ya faru, taso ta ɗauki yarinyar ta zauna a wurinta amma saboda baƙin hali irin nasu sun hanata ganin ƴar uwarta....😭
"Maza ki hanzarta ki wanke mana kayan," muryar mammynce ta katse ta,
Hannu tasa ta ɗauki bokitin dake ajiye awurin kayan, sannan ta wuce izuwa inda fanfonsu yake,ruwa ta tarbo acikin shi sannn ta ɗauke shi tadawo ta ajiye, ledar klin ta dauka tare da fasawa ta zazzaga aciki sannan tashiga tsoma kayan aciki tana wankewa idonta na zubar da kwalla,
suna cikin wannan zaman suka ji ƙarar dirar mota a ƙofar gidan, washe baki mammy tashiga yi tana cewa"ƴar albarka ta iso, nasan tadawo mana da abun arziƙi, ni dae naji daɗi ƴa'ƴana badae farin jini ba........' bata ƙarasa maganar ba Hayaam tashigo cikin gidan, jikinta na sanye da swiss lace ash colour, doguwar riga akayi mata dashi, ta matse ta tsam tamkar in tayi motsi rigar zata yage, ta kashe ɗaurin kallabi nan, mayafin kuma ta aza shi a kafaɗa,
fuskarta ɗauke da murmushi ta ƙarasa wurin mammyn tasu, tashi tayi ta rungumeta tana cewa"ƴar albarka sai yau zan saki a idona"?
Murmushi hayamm tasaki tare da cewa"Ammi yau ɗin ma sa'a kika ci, ki gode ma Allah da kika ganni yau, domin kuwa gobe zan wuce abuja nazo ne nayi maki bankwana saboda zan koma can da zama ina fata Aunty laila ta sanar dake game da komawa ta can? Ta tambaya tana kallonta,
gaba ɗaya Amal ta kasa kunne tana sauraronsu,
Washe baki tayi tare da cewa"ta sanar dani mana, ae ba ƙaramin daɗi naji ba kwara ki tattara ki tafican kema ki shafo mana arziƙi,"
Fari da ido hayaam tayi tare da cewa"baki da damuwa in dae nice mommy, arziƙi mun gama yin shi, muddin burina ya cika tuni zan canza maku tamfatsetsen gida na kece raini, na siya maku manyan motoci na alfarma sannan na biya maki aikin hajji, mommy kuɗi fa har sai kin gaji dasu wlh," ta faɗi tana faman sakin murmushi,
Cike da farin ciki mammy tace"Allah?
"wlh kuwa mommy," hayamm ta bata amsa,
ganin amal na kallonsu yasa mammyn kwatsa mata tsawa tace"zaki mayar da hankalin ki kan kayan da kike wankewa ko saina zo nan na karya maki wuya, magulmaciyar banza ƴar sa ido," jiki na rawa amal ta mayar da hankalinta kan kayan da take wanke wa,
ruƙo hannun hayamm mammyn tayi sannan tajata suka shige cikin ɗakinsu, don kar taji me zasu ce,
a hankali take wanke kayan tunani iri iri na zuwa mata aranta, tana yawan jin suna ambaton abuja abuja, kodai can aunty amani take zaune ne? Ta tambayi kanta, jinjina kai tayi tare da cewa"ina da tabbacin cewa auntyna tana zaune acan itama, dole na nemi mafita bazan zauna su kashe ni ba, zan gudu ne batare da saninsu ba," ta fadi tare da tsame rigar da ta sanya acikin ruwan wankin..........'😳

****************
A 6angaren su hossana kuwa saboda damuwar da suka shiga na jin cewa ya Omar ɗinsu na da aure gaba ɗayansu ba wanda yayi breakfast saboda damuwa, su kansu sun rasa gane dalilin dayasa suke jin kishin matar shi data kirasu a waya, abincin da jahad ta shirya masu har yayi sanyi saboda tun safe yake ajiye saman dining table babu wanda ya ta6a shi, gashi har ƙarfe ɗaya yanzu yayi na rana,
A tare suke kabbara sallah bayan sun kammala suka zauna suna addu'o'i, shiru jahad tayi tana sauraron addu'ar hossana da take yi,
"Ya Allah kasa mafarki ne ba gaske ba na cewa ya Omar yana da mata, in ma dagaske ne ya Allah kasa ya sake ta su rabu, zuciya ta tafarfasa takeyi mun bazan iya jurewa ba........'
katse ta Jahad tayi da cewa"hossana kina a hayyacinki kuwa? ya sake ta fa kika ce? Idan yana son matar shi fa?
harara hossana ta jefa mata tare da cewa"waya faɗa maki yana sonta? Auren dole ne akayi masu, da ace yana sonta ae da bai 6oye mana cewa yana da mata ba har da ciki...'
Itama jahad ɗin harar ta mayar mata tare da cewa"baki da hankali wlh,dagaske ɗin ke zararriya ce, yaya omar yana son matarshi, ke bakiji muryarta ba yarda take magana daga gani tana cikin kwanciyar hankali, kuma tana samun soyayyar mijinta tunda gashi har tana da ciki zata haifa mashi baby..........' jahad bata ƙarasa maganar ba, hossana takai ma wuyan hijabinta cakuma tana cewa"Ni ce zararriya? ɗaga kai jahad tayi alamar e,
Bugu hossana tashiga kai mata, ganin bazata iya jurewa ba yasa suka kacame da faɗa, abu kamar wasa sai da dukkansu suka sha kuka, dama ransu a6ace yake, duk don saboda matar Omar,
(Sehrish tayi tsiya)

tsaf ta kammala gyara mashi bedroom dinshi da toilet dinshi da falonsa duka ko'ina a kimtse tabar mashi shi, fitowa tayi ta sauko down stairs a lokacin duk sun kammala yin breakfast ɗin nasu babu kowa a falon, kai tsaye ta wuce bedroom ɗin Haroon gabanta na faduwa rass rass, ƙopar a rufe take don haka saita sanya hannu tare da yin knocking ɗinta, daga cikin ɗakin tajiyo muryarshi yana cewa"Wanene"?
"Ni ce," ta bashi amsa cike da ƙarfin guiwa,
buɗe mata ƙopar yayi fuskar nan ɗauke da murmushi, jikinshi na sanye da singlet fara tare da shorts baƙi,
"shigo daga ciki mana," ya faɗi yana nuna mata hanya, kallon shi kawai takeyi , sa kai tayi ta shiga ciki daga tsaye ta tsaya tana kallon shi, rufe ƙopar yayi sannan ya juyo ya kalle ta yace "wlh har naji sanyi araina dana ganki cikin ƙoshin lafiya,ae nayi tunanin e warhaka kina asibitin kwance magashiyyan rai hannun Allah.....' bai ƙarasa maganar tashi ba tace"me nayi maka? Meyasa kake son kashe ni? saboda me ka bani wannan allurar?
tafi yayi da hannunshi yana dariya, wuce ta yayi tare da samun wuri daga gefen gadonshi ya zauna yana facing ɗinta yace"Ko da ace zan iya kashe kowa a duniyar nan, ni bazan iya kashe abunda raina ke so ba!!! nasan cewa ba zaki mutu ba, akwai wanda zaizo ya taimake ki shiyasa nayi hakan ! kinfiye taurin kai shiyasa na gwada maki kaɗan daga cikin shaiɗancina, kin manta maganar da kika faɗa mun nacewa NAMIJI kike kallo? Shiyasa na haɗaki da namijin...........' ƙarasa maganar yayi yana faman tiƙar dariya, sakin baki sehrish tayi tana kallon shi. Da ƙyar ya tsagaita da maganar tashi yana kashe mata ido yace"Yarinya taji maza,baki ban labari ba ya kuka ƙare jiya?
shiru tayi tana kallon shi kawai saboda abun yafi ƙarfinta haroon ba ƙaramin shaiɗani bane,
ta6e bakin shi yayi yana kallonta sannan yaci gaba da cewa"wannan allurar da na baki, miyagu irina suke amfani da ita, aduk lokacin da mutun yayiwa kanshi allurar nan, imanin shi gaba ɗaya take cire wa, zai iya yi ma mata sama da goma sha biyar raping a lokaci guda batare da ya gaji ba tamkar engine zai dinga aiki, sannan koda ace mahaifiyarshi ce akusa dashi itama hakan ce zata faru da ita ba zai iya tantance fari ba balle baƙi, saboda gaba ɗaya take tayarwa mutun da wata irin jarababbiyar shawa'a da kuma ƙarfi na ban mamaki, kuma muddin a lokacin bai samu ya kawar da sha'awarnan ba, to fa zuciyarshi zata iya bugawa nan take,.......'
tunda ya soma bayani sehrish ke kallon shi cikin tsananin tashin hankali har sai da yakai ƙarshe sannan cikin sanyin murya tace"me yasa ka fita daban acikinsu ne? Saboda me kake son cutar da shi ne? idan ni nayi maka laifi saboda me laifin zai shafe shi?
shu'umin murmushi haroon ya saki kafin yace"tun ina yaro nake da son yin mugunta, ni ko dariya ban cika yi ba sai in anyi abun mugunta sannan take zuwa mun, burina kawai naga kowa cikin masifa da tashin hankali,natsani inga ana ta rayuwar farin ciki mai ɗaurewa, wannan ne dalilin dayasa nakeson in kawo canji acikin gidan nan,". Hankali kwance haroon ke kora mata bayani batare da nuna alamun wasa ba,
tuni taji idonta sun ciko da kwalla cike da takaici tace "tausayinka nake ji ! kana bani tausayi saboda kai abun tausayi ne, ban ta6a tunanin cewa a jinin abba za'a samu mai irin waɗannan mugayen ɗabi'un da halayen irin naka ba, saboda me yasa kai ba zaka yi koyi da sauran ba? ka zama mutumin kirki tamkar sauran"?
tasowa haroon yayi daga zaunen da yake ya ƙarasa dab da inda take a wannan karan fuskarshi babu wasa acikinta yace"kina so in shiryu ne? In zama mutumin kirki?
ɗaga mashi kai tayi alamar eh,
Murmushi haroon yayi kafin yace"kece mutun ta biyu, da kikayi mun fatan shiriya arayuwata, sai dae kash hakan bazai ta6a yiyuwa ba sehrish ni ba cikakken mutun bane kamar yarda kike tunanin....................' a wani irin firgice sehrish ta ɗago tana kallon cikin idanunshi fuskarta cike da tsoro tace"kana nufin kai ba mutun bane"?
dariya ya ɗanyi kafin yace"kona faɗa maki ba zaki yarda ba, amma bari na sanar dake wani abu da baki sani ba, ni da kaina na turo marshal Omar ɗakin sgr domin ya taimake ki ! kuma ni ne nan na hana ki furta sunana agaban Omar, na shaƙe maki maƙoshinki na hana sautin fita daga bakin ki, shin bakiyi mamakin taya akai duk nasan da wannan ba !!!!!!!!!!!
Zazzare ido sehrish tayi gabanta na faɗuwa, tuni zufa ta soma tsattsafo mata, ja da baya da baya tadinga yi tana kallon shi.....
dariya sosai haroon yayi kafin yace"Shiyasa nace ki nemi tsari daga sharrina wlh ni shaiɗanin aljani ne ba mutun ba..........'
tunkan ya ƙarasa maganar tashi Da gudun gaske sehrish ta juya tare da buɗe ƙopar ɗakin nashi ta fuce ji kake garam !!!! Ƙopar ta datse,
Fashewa da dariya haroon yayi hada dafe cikin shi, daga bisani kuma ya ɗan tsagaita da dariya tare da cewa "Yarinyar tana da kyau, shiyasa na tsoratar da ita saboda inga kyawawan idanuwan nan nata masu kashe mun zuciya," ya furta tare da kai hannun shi saitin zuciyarshi yana faman sakin murmushi...............😳 tashin hankali anya kuwa haroon 👹😈


86.
Ko kallon gabanta ba tayi saboda gudun da take yi gaba ɗaya ta gama firgita da haroon, bata yi wani aune ba ta faɗama junaid wanda ya nufo part din nasu, aikuwa gaba ɗaya suka faɗa ƙasa a manne da juna, atare zuciyoyinsu ke bugawa, musamman sehrish yana jin yarda zuciyarta ke faman bugawa da ƙarfi da ƙarfi, sun jima a haka kusan 8 mins sannan junaid ya ambaci sunanta "Sehrish,"
lamo tayi a jikinshi tana faman sauke ajiyar zuciya sai da ta samu natsuwa sosai sannan ta ɗago daga jikinshi,tayi gefe guda zaune dirshan tana kallon shi, tasowa yayi daga kwancen da yake yana faman sakar mata murmushi, tun safe yakeson ganin ta amma basu haɗu ba sai yanzu, shima zama yayi suna

37 / 80