ABBAN SOJOJI TAKUN TSAKIYA 2 BY BOSS BATURE.txt

Author :  Boss Bature Category :  Arewa Pen

Chapter   77 / 80

228K to 231K   out of 238K words

yake ya nufi sashensu Azmee,
"Kuzo ku xauna kusa dani,"hajiya azeema ce tayi masu magana yayin da takeyi masu nuni da hannunta,

Hannunsu ruƙe cikin na juna,suka ƙarasa wurin sofa ɗin da hajiya azeema take,a gefenta suka zauna,duk jikinsu asanyaye saboda basu saba dasu ba,tunda suka zauna jahad ke kallon Abusufyan,saboda tunawa da maganar gwaggon katsina da tayi ɗazu na cewa shine mahaifinsu,kanta ya gama ɗaurewa,tashiga tambayar kanta taya akai hakan zata kasance?meke shirin faruwa da rayuwarsu ne?dama suna da dangi ne?wai su wanene su?ya akai rayuwarsu take a birkice ne?
tambayoyi iri iri tashiga yi ma kanta waɗanda bata da amsar su,
ƙasa ƙasa hosana tayi da muryarta tare da kai bakinta saitin kunnan jahad tace"Wancan mutumin sai kallonmu yake yi jahad,ni duk nabi na tsargu wlh,tsoranshi nake ji,shi da wannan kyakkyawan mai wasu kalar kwayar idanu kaman aljani....'
"Dan Allah hosana ki daina mun magana a kunne na,wai ke bakya ganin mutanene kuma duk idanunsu na akanmu,ni kaina atsorace nake wlh,yaya Omar kaɗae nake kallo naji dan sauki,da ace baya a wurin nan da tuni na gudu...'jahad ce tayi wannan maganar,cikin raɗa tayi mata ita don kar aji su,

A lokacin da Sgr ya ƙarasa bedroom dinta,tura ƙopar yayi tare da faɗawa ciki,tsayawa yayi yana kallonta,ta takure kanta,jikinta sae kerma yakeyi yayin da hawaye ke saukowa daga cikin idanunta,sam bata lura dashi ba har sae da yayi gyaran murya,a firgice ta wurga idanunta akan fuskarshi,gabanta ne taji ya faɗi rass,nan take kermar jikinta ya ƙaru sosai,
"Taso muje"!babu wasa a fuskarshi yayi maganar,girgiza mashi kai tashiga yi tana cewa"bazan iya tafiya ba,ƙafafuna ciwo suke yi mun,dan Allah kuyi haƙuri ku ƙyaleni,inji da abunda ke damu na,'
Abun ya ɗaure mashi kai jin yadda take yi mashi jayayya,tabbas akwai matsala hakanan dae yarinyar bazata ƙi bin umarninshi ba,
Bai tsaya wani 6ata lokaci ba,ya ƙarasa shiga cikin ɗakin har saman gadonta ya bita,sai faman ja da baya takeyi,gaba daya ya ɗaukota tare da azata asaman kafaɗarshi ya fito da ita,sai kuka takeyi mashi tana cewa ya sauketa ita bazata je ba,su rabu da rayuwarta,suna ƙuntata mata,har bugun bayanshi ta dinga yi da hannayenta don ya sauketa,duk yana jinta,

tashin hankalin da ba'a sama shi date!

"Ga babban yaya nan ɗauke da sehrish din daman nasan sai dae ya ɗaukota,"acewar fawan,jin sautin kukanta yasa kowa yakai hankalinshi wurinsu,abun ba ƙaramin ɗaure masu kai yayi ba,ƙiri-ƙiri tana gudun ƴan uwanta,bayan duk alamu sun nuna cewa su ɗin fa ƴan ukune,

Koda Sgr ya ƙaraso wurinsu, a tsakiyar inda kowannansu yake,sai ya sauko da ita,Kamar dama jira takeyi ya sauke ta ƙasa da gudu ta kama hanya zata bar wurin,aikuwa a zafafe ya damƙo waist ɗinta da ƙarfi ya maido ta jikinshi,
Har Abbanshi na cewa"ka bi ta a hankali don Allah,ta tsorata sosai,bansan meke damunta bane, ko ƴan uwan nata ne ke batasan gani "abusufyan kuwa runtse idanunshi yayi,har cikin ranshi yake jin soyayyar yaran,
Cikin shessheƙar kuka take faɗin"Na bani,na shiga uku!Na lalace!dan Allah ku rabu dani!ku barni na tafi, banason ganinsu!ni ba ƴan uwana bane!ciwon kai suke sani idan ina kallonsu,raɗaɗi nake ji acikin zuciyata kamar ana ƙonata...."
Hankalinsu ba ƙaramin tashi yayi ba jin abunda sehrish ke cewa,yanayin yadda take maganar zai tabbatar maka da cewar da gaske take tana jin duk wani abu da ta faɗi,musamman Sgr daya ruƙota,yaji jikinta da wani irin Zafi,har shi kanshi zafin na shafar jikinshi,
Abusufyan ne yace"kuyi mata addu'a don Allah,zai iya yiyuwa akwai sihiri ajikinta,wani zai iya shiga tsakaninta da ƴan uwanta saboda ni shaidane akan yadda suke son junansu!nagani da idona,basa rabuwa da junansu kullum suna manne da juna,banta6a ganin ƴan uwa masu son junansu ba irin yaran nan,tun kafin su mallaki hankalinsu suke tsananin son junansu.....'
Cike da mamaki Abba yace"meyasa kake tunanin cewa akwai sihiri ajikinta?

kowa ya kasa kunne yana sauraronshi,
"In har da gaske sune ƴa'ƴana kamar yadda nake hasashe to tabbas an shiga tsakaninsu ne,saboda mutumin da suka taso awurinshi,nayi bincike akanshi,bama haka ba shi da kanshi ya rabani da bibiyar rayuwarsu da nake yi,kowa zaiyi mamakin taya nabar yaran rayuwarsu ta wulaƙanta batare dana taimaka ma rayuwarsu ba,ko kuma na sanar ma wani daga cikin dangina don a taimaki rayuwarsu,ba laifina bane tursasamun akayi........'
Kasa ƙarasa maganar yayi saboda hawayen da suka shiga kwaranyowa daga cikin idanunshi,

Abbas yace"Akwai sauran labari kenan, bari mu gyara zama don a idasa warware mana komai,"

ɗagowa yayi da idanunshi da suka yi jawur har sun dan fara kumbura ya kalli sgr tare da cewa"idan ba damuwa,inaso ka zauna tare da ita akusa dakai,saboda ka ruƙeta karta gudu,in yaso sai kayi mata addu'ar koda bata dawo hayyacinta ba,zataji sauƙin radaɗin ciwon kan da takeyi,

"Okey,"ya amsa tare da samun wuri ya xauna,asaman laps ɗinshi ya zaunar da Sehrish,sosai ya ruƙota jikinshi,tunda ta kwantar da kanta asaman wide chest ɗinshi,numfashinta ya fara daidaita,a hankali kuma zafin jikinta ya soma raguwa,saitin kunnanta yakai ƙaramin bakinshi yana karanta mata addu'o'i,bugun zuciyarta ne ya soma raguwa,jikinta kuma ya rage kermar nan da yake yi,

"Ina gwaggon take ne?naga bata fito ba inaso ayi komai agabanta tare da Dr haris kuma"abusufyan ne yayi maganar yana kallon Abban nasu
Fawan ne ya kuma miƙewa tare da cewa"Bari naje na kirasu,'
cike da zolaya jahan yace"Messenger,aikinka na kyau,"murmushi kawai yayi tare da wucewa ciki,ae yau ji yake kamar ya zuba ruwa ƙasa yasha don murna don kuwa ranshi ya gama bashi cewa su jahad din yan'uwansu ne.

Ba da jimawa ba,sae ga Gwaggon katsina ta fito har yanzu undin nan ne ajikinta Allah ma yasa irin dogon nan ne mai kauri,tana biye da bayan fawan tana dungurin keyarshi tana cewa"Shegen bisa,da kanshi kamar na tamola,baccin ma baza abar mutun yayi ba,matsalar mutun yazo gidan jikoki kenan duk subi su addabi rayuwarshi.....'
Muryar Abba ce ta katse ta da cewa"gwaggo ku samu wuri ku zauna,magana ce mai muhimmanci zamuyi,"
Har zata zauna idonta suka sauka karaf akan Sehrish dake zaune asaman laps ɗin Sgr,hankali tashe tace"mun shiga uku!yanzu agabanku ake wannan aika-aikar amma babu wanda ya tanka?hosana ce ko jahad?wacece acikinsu?wlh bazan bari a lalatamun ƴa'ƴan Abusufyan ɗina ba,dasu zamu koma katsina ayau.......'
..da sauri Haris ya katseta da cewa"Dan Allah gwaggo kidaina wannan sambatun naki,bakiji abunda abba yace ba!magana mai mahimmanci za'ayi,ki samu wuri ki zauna kuma kiyi shiru,'
Wurga mashi harara tayi kafin ta wuce tare da samun wuri ta zauna,shima haris ya zauna agefenta,sai da suka xauna sannan ta lura da hosana da jahad dake zaune gefen hajiya azeema,
Da sauri ta mayar da idonta kan sehrish don taga wacece ita,ko dae idanunta ne suka fara samun matsala don taga kamar kamanninsu iri ɗaya sak,
"Harisu,kana ganin abunda nake gani kuwa,wai yaran nan har nawa ne masu fuska iri ɗaya"?
A dan ƙule haris yace"Eh,su uku ne!ko kinmanta su nawa ne,na faɗa maku Abu ta haifa!wannan ae cikon ƴar ukun tasu ce,'
"Oh to,yanzu nagane"ta fadi tana faman gyara zamanta,

Sae da kowa ya natsu sannan abusufyan ya kalli su hosana da jahad yace"Ya sunan mahaifiyarku ne?kuma waye mahaifinku"? Yayi masu tambayar ne don ya fara tabbatar da cewar sune ɗin dai dagaske,
Har suna haɗa baki wurin cewa"Sunanta Zainab,amma anace mata abu ƴar buzuwa,sannan mahaifinmu kuma sunanshi Sayyadi.......'tunkan taƙarasa maganar kowanne daga cikinsu ya shiga sakin murmushi,jin sun ambaci dai dai da sunayen da abusufyan ya gama bada labari akansu,tunkan aje ko ina suka tabbatar da cewar sune dae ƴa'ƴan abusufyan ɗinsu,
"Ina mahaifiyarku take yanzu"?ya kuma tambayarsu,
Jahad tace"bamu son inda take ba,amma koma a ina take bata acikin hayyacinta,lokacin da tabarmu tasamu ta6in hankali,'
jiki asanyaye ta ƙarasa maganar,
"Yanzu zaki iya bamu labarin abubuwan da suka faru arayuwarku gaba daya,har izuwa lokacin da kuka rabu da junanku"?
ɗaga mashi kai tayi alamar eh,
Kafin abusufyan ya ƙara cewa wani abu,Abba ya katse mashi hanzarinshi da cewa"Yakamata,ka fara sanar dasu game da alaƙar da take tsakaninka da mahaifiyarsu"
Jinjina kai abusufyan yayi kafin yace"zaku iya tunawa da mutumin daya ta6a zuwa wurinku lokacin kuna ƴan ƙanana,har ya ɗauke ku hoto a wayarshi?lokacin da zan tafi kuka dinga kuka kuna cewa na tafi daku baku son zama da mahaifinku"?
A razane hosana da jahad suke kallonshi yayin da suke ƙoƙarin tunawa da wannan lokacin......'
Murmushi abusufyan yayi tare da cewa"nasan ba zaku iya tunawa da wannan lokacin ba!,amma mun sha haɗuwa daku wani lokacin kuna ku kadae,wani lokacin kuma tare da mahaifiyarku........'

Batare da 6ata lokaci ba,abusufyan ya basu labarin rayuwarshi da abu a takaice yadda zasu fahimta,sai lokacin suka san asalin mahaifinsu da kuma kakansu baba buzu daya rasu,da kuma irin rayuwar da abu tayi tare da abusufyan kafin su rabu,ta auri ya sayyadi,sunsha kuka sosai,aransu suna jin ƙuncin abunda mahaifiyarsu tayi masu,ashe duk itace taja masu bala'en da suka fuskanta,

Kowa yayi shiru na wani lokaci suna sauraron kukan dasu hosana da jahad sukeyi gwanin ban tausai,banda sehrish wanda tayi lamo ajikin Sgr,duk wani abu da suke faɗi acikin kunnanta,amma bata ɗago ta kallesu ba,har yanzu dae bata dawo dai dai ba,


Daƙyar su Omar suka lallashe su,kafin daga bisani Abbansu yace"Jahad yanzu ke muke sauraro!munaso muji irin rayuwar da kukayi a hannun mutumin nan!"

Duk wannan abun dake faruwa akan kunnan Haroon,ya jima da shigowa batare da sanin kowa ba ya la6e yana jin labarin da abusufyan ke ba su jahad,na rayuwarshi da mahaifiyarsu,hankalin shi yayi mugun tashi,gaba ɗaya ya tsorata ya rikice,wata irin zufa ce tashiga gangarowa a fuskarshi,bakomai ya razanar dashi ba face ganin Ƴan ukun gaba ɗayansu sun haɗu acikin gidan kuma ga Ubansu da kanshi ya gane cewa ƴa'ƴanshi ne wannan alama ce dake nuna cewar asirinsu ya kusa tonuwa,
Tuni zufa tasoma tsastsafo mashi acikin jikinshi,sharkaf ta jiƙa t shirt ɗin jikinshi duk kuwa da ba zafi,jan ƙafarshi yayi tare da lalla6awa cikin sanɗa ya wuce bedroom ɗinshi,
Zagaye ya shiga yi acikin ɗakin,gaba ɗaya jikinshi sae faman rawa yakeyi,yama rasa inda zai tsoma kanshi kamar wani zautacce haka ya koma,a fusace ya dunƙule hannunshi tare da kai ma madubin ɗakin naushi,nan take glass ɗin jikinshi ya tsastsage ya zube ƙasa,
Hannunshi ya shiga fitar da jini,ko kaɗan baiji xafin hakan ba,raɗaɗin da zuciyarshi ke yi mashi yafi raɗaɗin glass ɗin daya shige shi,
Da ƙarfi ya furta"That's impossible!ƙaryane ba gaske bane!!wlh bazan rasa rayuwata ba!dole na rayu ko da kowa zai rasa ranshi,zanyi komai zan yi don ganin na kwaci kaina!!
Yana magana yana sakin huci,idanuwan nan nashi sunyi jawur dasu luhu luhu,
Cikin sauri ya zura hannunshi tare da ciro wayarshi daga cikin aljihun jeans dinshi ya danna ma wata number kira,cikin sa'a aka ɗaga kiran!
Wata irin muryace ta karaɗe kunnanshi mai tsoratarwa"Ba saida nace maka karka sake kira na ba!Tun farko ya mukayi dakai?
hankali atashe haroon yace"Ni ba wannan maganar tasa na kira ka ba!ka faɗamun taya akai kukayi gangancin barin yaran nan har suka haɗu da danginsu!!!!!!!
"Wasu yara kenan!"
Haroon yace"Ƴan ukun nan!na gansu da idona acikin gidan nan!yanzu haka gasu can a falon gidan nan sun taru suna jin labarin rayuwar yaran nan!
Nan take muryar mutumin da suke waya dashi ta canza,
"Wai kana nufin hosana!jahad!sehrish!duk sun haɗu anan cikin gidan naku ko mi"?
A ƙule haroon yace"Eh mana!akansu nake magana,wlh kowa yayi ta kanshi!saboda yarinyar nan dole ta ambaci sunanka acikin labarin da zata bayar kuma kasan cewa muddin waɗannan namun dawan guda biyu sukaji mugayen abubuwan da kuka aikata dole su binciko ka duk inda ka shiga kuwa,kuma koda a ƙarƙashin ƙasa ka 6oye,!

Fashewa da dariya mutumin yayi kafin ya tsagaita da yin dariyar yace"Baza su ta6a iya gano ni ba!nafi ƙarfinsu nesa ba kusa ba!zanyi amfani da ƙarfin sihirina wurin dakatar da tunaninsu.......'
Tun kan ya ƙarasa maganar haroon ya daka mashi tsawa tare da cewa"Ya Isa haka!!zancen ku iri ɗaya da ita!daga kai har ita daga anyi magana sai kuce ƙarfin sihiri,zakuyi amfani da sihiri ku asirce mutun!angaya maku cewa kowane lokaci sihiri ke yin tasiri ne!sam babu Allah aran kowannanku don haka babu wanda zai tsira acikinmu!ko ka manta da irin mutuwar da mahaifinku yayi ne?duk wani sihiri da kuke taƙama dashi ae a wurinshi kuka gado shi,akan idon kowannanku yayi mummunar mutuwa sakamakon farmakar shi da kakanmu salahuddeen sukayi,ku baku da tunani ne?me yasa shi a lokacin baiyi amfani da ƙarfin sihirin shi ba don ya hana kanshi mutuwa?ko don saboda ya tsufa ne yasa nashi sihirin baiyi aiki bane?

Gaba daya haroon ya rufe shi da faɗa ta inda yake shiga batanan yake fita ba,ba don komai ba sai don saboda yasan cewa bazai kai labari ba,sun ja mashi bala'e da masifa,
Wata irin gigitacciyar tsawa mutumin ya daka mashi wadda tayi silar dawowarshi cikin hayyacinshi,yayi tsit yana faman sauke ajiyar zuciya,
"haroon!ya kamata ka iya bakinka!kasan dawa kake magana!duk wannan tada jijiyoyin wuyan da kakeyi bazai hana kaga mutuwarka ba!zaifi kyau ka mayar da hankali wurin ganin ka sama ma kanka abokan tafiya,kada ka yarda wannan abun ya tayar maka da hankalinka,babu wanda ya isa ya ta6a ka acikinsu,!abu ɗaya kawai mukeso awurinka!muddin ka aikata hakan komai yazo ƙarshe zaka tsira kuma muma zamu tsira,sannan farin cikin gidansu zai tarwatse na har abada,......................'
Natsuwa haroon yayi yana sauraron bayanan da mutumin yake kora mashi,sae amsa mashi yake yi da to,toh
Alamar ya amince da abunda suke so ya akaitan,


Acan main palour ɗin kuwa,kowa ya kasa kunne yana sauraron Jahad,

****

*CIGABAN LABARI*

Abu ba ƙaramar wahala tasha ba a hannun Ya sayyadi,daga ita har yaran bai raga masu ba,tun yana 6oye mata mugayen halayenshi,har ya fara bayyana mata su,babban tashin hankalin da ta fara fuskanta a wurinshi shine shigo mata da Manyan Alhazan da yake yi acikin gidansu,in suka shiga ɗaki sai suyi fiye da 6hrs basu fito ba,wani sa'in har gurnani take ji ya cika gidan tamkar namun dawa na yaƙi,wannan abun ba ƙaramin razanar da ita yake yi ba,kuma duk in ta tambayeshi me suke zuwa yi a wurinshi sai yace mata *Wala tajassasu*kuma ta tsaya a iya matsayinta kar tace zatayi mashi shisshigi irin na mahaifinta,tarasa uban me sukeyi acikin ɗakin,abun ba ƙaramin damunta yake yi ba,tun tana iya jurewa har dae wata rana ta yi masu la6e a window ɗin ɗakin shi,a ranar abu taga tashin hankalin da bata ta6a gani ba da idonta tunda uwarta ta haife ta,wani irin yunƙurin amai ne yazo mata da gudun gaske tabar leƙen sun da takeyi ta koma bakin fanfo tana kwarara amai tamkar ƴan hanjin cikinta zasu fito,agaban fanfon ta zuƙunna tare da fashewa da kuka,ta dafe kanta da hannunta saboda raɗaɗin da yake yi mata,gaba ɗaya rayuwarta ta shiga ƙunci taji ta tsani kanta,kamar ta kashe kanta haka ta dinga ji a lokacin,

ta jima abakin fanfon kafin ta koma cikin ɗakinta,a lokacin triplets ɗinta suna kwance sae sharar bacci sukeyi,komawa tayi daga gefen gadon ta zauna tare da ɗan russinawa dai dai saitin fuskokinsu tana kallonsu,yadda suke sharar baccin su zai tabbatar maka da cewar suna cikin kwanciyar hankali,tasa su gaba tayi tana faman shessheƙar kuka muryarta na rawa ta dinga cewa"Na cuci kaina!Kuma nacuci rayuwar ƴa'ƴana,Haƙƙin mahaifina kadae bazai ƙyale ni ba,na bijire mashi na ƙuntata mashi duk don saboda in auri sayyadi,haƙiƙa na tafka babban kuskuren da bazan ta6a gyarashi ba,Ni duk a zato na kowane mutun daya iya jan ayar kur'ani ya fassarata kuma yayi wa'azi abainar jama'a,mutumin kirki ne bai aikata zunubi tsarkakakke ne shi,ashe ba haka bane,ko acikin malaman akwai nagari akwai kuma na banza,wanda suke amfani da iliminsu na addini don su cutar da mutane,Mommy saida ta gargaɗe ni akan hakan amma na bijire mata saboda na makance akan soyayyar sayyadi,Ni ban tsaya nayi bincike akan rayuwarshi ba,kawai natashi na aure shi,kuma na ƙuntata ma mahaifina duk don saboda shi,na kuma ƙuntatama Mijina mai sona da gaskiya,wlh na cuci rayuwata....!kaicona.......'



124.
Sosai abu ke shassheƙar kukan,sautin kukan da takeyi ne ya farkar da Sehrish, sai faman mutsustsuka idanunta takeyi da hannayenta,hannu abu takai tare da ɗauko ta,ta zaunar da ita asaman cinyoyinta,shafa fuskarta tayi tare da cewa"Rishina kin farka?kina jin yunwa ne"?
  A hankali ta ware kyawawan idanuwanta akan fuskar mahaifiyarsu,koda taga hawaye na zuba a idanun oumman tasu,sae ta sanya tafin hannunta tana share mata su tana cewa"oum ki daina,banasho,nima inyi kuka,'tayi maganar da hausarta ta ƴan koyon magana,hada ta6e la66anta zatayi kuka,
Hakan da tayi yasa abu ta fashe da dariyar karfin hali tana kallonta,kwantar da kanta tayi asaman ƙirjinta tana shafa sumar kanta tace"na tambayeki kina jin yunwa baki faɗa mun ba,'
Cikin shagwa6a tace"inaji,amma tare dashu usana da johad anci.  '
  Abu tace"shikenan,bari mu jira su farka daga baccin sai in dafa maku ko indomie ce kuci,bayan kun gama ci sai inyi maku wanka,in shafa maku mai in canza maku kaya sannan in kaiku gidan maman sadeeq ku tayata fira,kina son zuwa ko?
  Inasho,ta bata amsa,
Suna cikin yin fira da ita sai ga sayyadi ya faɗo cikin ɗakin nata,tana ganinshi gabanta ya faɗi rass don yanzu yafi yi mata kama da ibliss,
  Yadda ya nufo ta a fusace yasa tayi saurin sauke sehrish daga jikinta ta miƙe tsaye tana kallonshi fuskarta da alamun tsoro,

Nuna ta yayi da hannunshi yana huci yace"Abu!uban me ya kaiki yin la6e aɗakin can!angaya maki banganki bane?duk wani motsin ki acikin gidan nan,acikin kunne na nake jinshi,basai da na faɗa maki cewa kada ki tsananta bincike akaina ba!
  duk da tsoranshi da take ji hakan bai hanata tanka mashi ba,
"Saboda baka da gaskiya shiyasa ka hana inyi bincike akanka!yau naga komai da idanuna ashe kai ba sayyadi bane!baƙin shaiɗan ne wanda ke 6oye mugayen halayansa!wlh nayi danasanin auranka sayyadi yafi sau aƙirga,banta6a sanin cewa kai dabba bane sae yau!wlh sai ka sake ni don bazan iya cigaba da zama da fasiƙin mutun irinka ba......'
  Tunkan ta ƙarasa maganar sayyad ya fashe da dariya hada dafe cikinshi,abun ba ƙaramin ɗaure mata kai yayi ba,shiru tayi tana kallonshi,
  Sai da ya gama tiƙar dariyarshi sannan ya sassauta muryarshi tamkar zai lallashe ta yace"My wife,yau da bakinki kike jifana da waɗannan munanan kalaman?nifa ne sayyadin nan naki da kika kwallafa rai

77 / 80