ABBAN SOJOJI TAKUN TSAKIYA 2 BY BOSS BATURE.txt

Author :  Boss Bature Category :  Arewa Pen

Chapter   21 / 80

60K to 63K   out of 238K words

sanya ba, ƙirjinta gaba ɗaya sun fito, hannunta ta sanya ta tarbesu tana kuka kuma hakan baisa ta daina tunkarar ƙopar ba,

Bin ta baba alamu yayi da gudun gaske saboda ya ruƙo ta jikinsa don ya idasa nufinsa,
Sai dae ina kafin yayi wani kwakkwan yunƙuri tuni anyi ma ƙopar ɗakin wani irin kwakkwaran Naushi nan take katakon jikinta ya farfashe gaba ɗaya ta buɗe,
A tsorace baba alamu ya dakata yana faman zazzare ido don son ganin wanene wannan ya faɗo masa cikin gidan gonarsa !!!!!!!!!!!!
Ita kanta hussana ta firgita tsayawa tayi jikinta na wani irin kerma ga zazza6i daya lullu6e ta, har lokacin hannunta na tarbe da ƙirjinta,
Duro ƙafarsa yayi cikin ɗakin tamkar damusa wani irin kakkarfa ne mai ban tsoro, jikinsa na sanye da Jacket baƙa daga ciki kuma farar t*shirt ce wadda ta bayyana ƙirar ƙarfinsa, Sai dogon wando baƙi,
bai bamu damar muga fuskarsa ba domin kuwa tana sanye cikin face mask baƙi, idonsa kuma na sanye da baƙin glass,
gaban hussana ba ƙaramin faɗuwa yayi ba duk ta gama tsorata, baba alamu kuwa murya na rawa yashiga cewa "kai...Wai Wanene kai ! daga ina kake? Mai ya kawoka gidan gonata ! ya tambaya yana tada jijiyoyin wuya,
Har lokacin bai da alamar yin magana, a hankali ya sanya hannunsa tare da ruƙo jaket ɗin dake ajikinsa ya cire ta gaba ɗaya yayi wurgi da ita, sannan ya mayar da hannun nasa ya tu6e t-shirt ɗin dake ajikinsa ya rage babu riga ajikinsa,
Hankalin baba alamu ba ƙaramin tashi yayi ba ganin irin damtsen hannunsa a murmuɗe ga ƙirjinsa dake motsi abun gwanin ban tsoro,
tuni zuciyar hussana tayi wani irin bugu nan take ta tafi zata sulale ƙasa, da Hanzari ya tarbota jikinsa gaba ɗaya tafaɗa a faffaɗan ƙirjinsa,
hakan ya bashi damar zura mata t-shirt ɗinsa ajikinta donya rufe mata jikinta, bayan ya kammala sanya mata rigar,
ya buɗe bakinsa ta cikin face mask ɗin yayi fito mai sautin gaske har saida baba alamu ya firgita yana faman kwalala ido,
Da gudun gaske wani Saurayi ya shigo ya tunkare sa, batare da yace komi ba ya miƙe masa Hussana, cikin sauri yasa hannu ya ɗauketa tare da azata a kafaɗarsa ya fuce da ita,
sai lokacin Yasa hannu ya cire glass ɗin fuskarsa tare da yin wurgi dashi, Azazafe ya sanya kyawawan idanuwansa waɗanda suka Canza Launi izuwa ja saboda tsananin 6acin rai, gadan gadan ya tunkari Baba alamu wanda ke shirin guduwa, hannunsa yakai tare da damƙar wuyan rigarsa ya ɗaga shi sama, ya dawo dashi ƙasa ya buga kansa jikin bulo nan take haƙora biyu daga bakin sa suka fito Jaga-jaga da Jini, saboda tsananin azaba da raɗaɗi ya sanya Baba alamun sakin futsari a wando yana cewa "Innalallahi wa'inna ilaihirraji'un na bani na 6atare na lalace nashiga uku, Dan Allah ka ƙyale ni wlh nabi Allah nabi manzonsa .,...........
tsawa mutumin ya daka masa tare da cewa "Kasan da Allah kake ƙoƙarin aikata ma ƙaramar yarinya faɗe tsofe tsofe dakai!! mutun mara imani da tausayi irinka wanda baisan darajar ƴa' mace ba Sam bai cancanta daya cigaba da rayuwa ba,'
ɗagowa baba alamu yayi yana ja da baya da baya idonsa jawur, jini na kwaranyowa daga bakinsa yana cewa "Dan Allah kada ka kashe ni ! Kabarni a haka naji jiki sosai, ina da ƴa'ƴa da mata in ka kashe ni zasu shiga wani hali.....' bai bari ya ƙarasa maganar ba, yakai masa wata irin mahangul6a da hanunsa nan take yasake fasa ihu,
"Karka kuskura ka sake buɗe wannan ƙazamin bakin naka da sunan zakayi mun bayani ! Bani da lokacin sauraron jawabin Ka, har kana da bakin da zakace mun kana da ƴa'ƴa da mata, don ubanka su yaran daka ɗauko donka lalata ma rayuwa daga sama suka faɗo? Ko su basu da dangi ne da zasuyi kuka in sun rasa su? Idan ka lalata masu rayuwa kana da tabbacin zasu ƙara numfashi ne ko baza suyi ba ? Ka yi tunanin hakan? ! idan wani ya lalata rayuwar ƴarka yaya zaka ji? Ka ƙiyasta yaya raɗaɗin yake azuciya............yana faɗin hakan yasa hannu ya rarumesa tare da wujijjiga shi ya sake buga kanshi ajikin bulo ɗin nan take kansa ya fashe jini ya soma kwaranya, ko shurawa baiyi ba nan take ya mutu a mace............
(Yanzu ina amfanin irin wannan rayuwar? Ka mutu kana aikata irin wannan mummunan zunubin batare da ka shiryu ba? Shin mai zaka ce ma Ubangiji? mutum baison lokacin mutuwarsa ba, shiyasa ake so koda yaushe mutun ya kansance cikin shiri kuma ya kasance yana aikata abun kirkiri, sam baba alamu baisan cewa yau wa'adinsa zai cika ba, Ga yarda ƙarshem shi takasance Ya Allah kasa muyi kyakkyawan ƙarshe, kuma ka kare mu daga aikata aikin dana sani 🙏😥

duk da ya mutu amma hakan bai masa ba saboda raɗaɗin da yake ji azuciyarsa, hannu yasa ya rarumi ƙaton dutsin dake ajiye a ƙasan wurin zai rotsa masa kai, cikin sauri matashin nan daya fita da husana ya faɗo ɗakin ya tunkaresa tare da hanzarin ruƙo hannunsa yana cewa "Yalla6ai kabarshi haka mana, ya riga daya mutu," fisge hannunsa yayi yayin da idonsa ke cike tab da hawaye da wani irin huci yake cewa "Kabarni kawai na tarwatsa kansa ko zuciyata ta samu salama, kasan yarda nake ji acikin zuciyata kuwa, tamkar ana rura garwashin wuta acikinta saboda tsantsar baƙin cikin da nake ji, WANNAN MUTUMIN YA SHIGA HURUMINA !!!!!!!!!!!!!!!!!!!! ⁉️❗‼️❗❓❓❓❓❓❓
*SHIN WANENE WANNAN MUTUMIN DAYA FARMAKI BABA ALAMU ACIKIN GIDAN GONARSA AYAYIN DA YAKE ƘOƘARIN KETA HADDIN HUSANA*❓⁉️
*WANENE SHI*❓❓
_*amsar tana a wurin hafsat Bature muhammad Boss Lady domin son sanin wanene wannan sai ku antaya kuɗinku naira 300 kacal Vip kuma 700 a wannan acct number ɗin 3196407426 first bank Bature hafsat Muhammad ku tura shaidar biya ta wannan layin da kuma masu tura recharge card 08103884440 kada ku bari abaku labari 👍👏*

Alhamdulillah finally na kammala free pages



*🪩🪩🪩ABBA SOJOJI🪩🪩🪩*•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®️_* ✍️
──────────────
ﻗﺼﺔ ﺣﺐ ﺭﻭﻣﺎﻧﺴﻴﺔ ﺑﻴﻦ ﺳﺤﺮﻳﺶ ﻭﺍﻟﺠﺮﺍﺡ ﺍﻟﻌﺎﻡ ﺭﺍﻓﻴﺖ💋❤️

Book 2 Page 28

•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•
rarumar dutsen ya ƙarayi zai rotsa masa kai cikin sauri MAJOR ya sake ruƙo hannunsa tare da cewa"Sorry Sir! Nasan Abun da ciwo, Amma mu gode ma Allah da muka ƙaraso akan Lokaci batare daya kai ga Cutar da ita ba" huci kawai yake yi yana kallonsa da idanuwansa waɗanda suka canza Launi bakomai yake tunawa ba fa ce yarda Baba alamu ya yayyaga ma Husana rigar jikinta, in ya tuna wannan abun zuciyarsa Tafarfasa take yi saboda 6acin rai, muryar major ce ta katse shi da cewa" Allah ya huci zuciyarka yakamata mu hanzarta barin gidan gonar nan domin muyi gaggawar kai su asibiti,
Jin hakan yasa shi yin saurin zura hannu tare da curo wayarsa daga aljihun wandonsa, nan take ya shiga camera tare da saita gawar baba Alamu ya ɗauke ta hoto da kyau, bayan ya ammala ya mayar da wayar cikin aljihun sannan ya kalli Major yace "Duba min aljihun wandonsa kona rigarsa kaga ko za'a samu waya,"
Cikin hanzari Major ya zura hannunsa cikin aljihun baba alamu daker ya lalubo wata ƙaramar waya nokia, taji duniya don bala'e batteryn wayar saida aka sanya robali sannan aka ɗaure shi baya cikon da akayi masa,duk ta rakwakkwa6e wayar,
"Sir ga wayar," ya faɗi tare da miƙa masa, bai kar6a ba bin wayr yayi da kallo kafin yace "Major cewa nayi ka ɗauko mun wayarsa ba wannan abun ba," ya faɗi yana nuna wayar hannun major ɗin
Ƙiris ya rage major ya fashe da dariya saboda ya lura cewa Boss Man ɗin nasa baya cikin hankalinsa,
"Sir wannan itace wayar, ka duba da kyau ta tsufa ne sosae shiya sanya ka ganta hakan,"
Ajiyar zuciya ya saki tare da cewa "Keep it in ur place, zan neme ta," yana faɗin hakan yakama hanyar fita daga ɗakin,
Muryar Major ce ta dakatar dashi da cewa "yalla6ai rigar fa? zan iya ɗauko maka ita," ya tambaya yana jiran amsa ,
Bai amsa mashi ba ya fuce kawai cikin sauri major ya ɗauko Jacket ɗinsa da yayi wurgi da ita sannan ya fito daga ɗakin ruƙe da ita a hannunsa a lokacin har yakai wurin motarsu da suka zo da ita, kai kana ganin yarda sukayi parking ɗinta kasancewa a tsiyace suka shigo da ita, domin kuwa har katakon ƙopar gidan gonar duk sun tarwatsa shi,
Cikin sauri Major ya rufa masa rigar abayansa shi kuma ya ƙara gyarata ajikinsa sannan ya zuge zeep ɗinta, buɗe motar yayi sannan ya shige back seat ɗin shikuma major ya shige driver seat sannan ya tayar da motar yayi baya² da ita kafin ya karya kwana ya fito daga gidan gonar da gudun gaske yake driving ɗinsu,
Sam ya gaza ɗauke idonsa akan hosana dake langwa6e asume kusa dashi, duk gashin kanta ya gama tarwatsewa dama a hargitse yake sai kuma aka ƙara hargitsar dashi, duk ya rufe mata fuskarta, lumshe idonsa kawai yayi har lokacin yana mamakin yarda akai wannan Lamarin ya afku amma yana da tabbacin cewa major yana da masaniya akan hakan,"
adai dai hanyar da baba alamu yayi wurgi da jahad Major yayi parking ɗin motar, cikin sauri ya buɗe motar ya fito gabansa ne kawai ke faɗuwa tsoranshi kar ace ta mutu,
wani saurayi ne zuƙunne a inda jahad take yashe, da alama ba ƙaramin taimako yayi mata ba, domin kuwa ya ciccire mata ƙayoyin da suka soki ƙafarta sannan kuma yayi amfani da Mayafinta wurin kekketa shi izuwa kashi uku, ya ɗaure mata goshinta sannan kuma ya naɗe mata ƙafafunta dake zubar da jini,
Fitowa major yayi shima yana kallonsa,
"Major karfa ace yarinyar nan ta mutu," ya faɗi a tsananin tsorace
"Sir she's still alive, suma ce kawai," ya bashi amsa,
saurayin yace"yalla6ai tana buƙatar taimakon gaggawa saboda jinin dake bleeding a goshinta da kuma tafin ƙafarta,"
Cikin tsananin tashin hankali ya ƙarasa tare dasa dukkan hannayensa ya tallabo JAHAD ya ɗaukota da sauri Major ya buɗe masa motar ya shigar da ita a kusa da Hossana ya zunar da ita a sume, sannan shima yashiga motar, zuge glass ɗin yayi tare da kallon saurayin yace"Ka shiga mu tafi tare,"
saurayin yace"yalla6ai machine ɗina fa"?
tunkan ya bashi amsa major yayi saurin cewa"daraban kayima arziƙi ƙulli ana maganar arziƙi wake ta wani machine"?
Jin haka yasa saurayin tasowa sai da ya bari major yashiga, sannan shima ya shiga kusa dashi ya zauna, rufe motar su kayi sannan da gudu suka bar dajin suka miƙi santalelen titin da zai sadasu da inda suka dosa
Kallonsu kawai yake yi ransa na ƙara ƙuna ganin irin jigatar da yaran su kayi yaran daya kai Amana, sam kwalwarsa ta rikice yarasa gane kan wannan lamarin ba komai yake son ji ba face yarda akai har tsohon can ya ɗauko yaran izuwa cikin gidan gonarsa don ya lalata rayuwarsu! taya akai ya fito dasu daga gidan general Ishaq? taya akai Aunty laila tayi gangancin da har wani zaizo ya ɗauki twins ɗinsa? da sa hannun wa akayi wannan ƙulla-ƙullar, tabbas kowaye bazai ƙyale shi ba muddin ya gano gaskiyar lamarin!!, ya ƙarasa zancen zucin nasa adai² lokacin da suka ƙetaro Abuja, kai tsaye suka wuce dasu izuwa katafaren asibitin SGR,
***************SEHRISH***************
Sam bata gane mai ake koyarwa acikin class ɗin saboda wata irin yunwa dake jibgarta ga wani irin bacci da take ji, sai faman hamma take yi tana lumshe ido,
Wuraren ƙarfe tara da rabi, time ɗin break yayi gaba ɗaya ƴan class ɗin sai fita suke yi don suje cin abinci, Sehrish na kwance saman desk ɗin gabanta sai faman sharar bacci takeyi,
juyowa Amrish tayi daga seat ɗinta tana kallonta, murmushi ta saki tare da sa hannunta taɗan bubbigi bayan sehrish tace "Get up baby ! time ɗin break yayi yakamata mu fita,"
daker sehrish ta buɗe ido tare da ɗago kanta daga saman desk ɗin tana kallonta biji², miƙewa Amrish tayi ta fito daga seat ɗinta, sannan ta ruƙo hannun sehrish tana cewa"Get up mana Let's go,ko bakya jin yunwa ne"?
ta tambaya tana kallonta, miƙewa sehrish tayi tare da biyota suka fito daga Class ɗin gabanta nata faɗuwa tsoranta kar ace siyen abincin zasuyi don ko sisi bata fito dasu ba, babu wanda ya bata kuɗi,
saukowa sukayi daga saman benen duk inda suka bi sai an samu wanda zai yi ma Amrish magana, kuma yawanci akan Sehrish suke tambayarta ko ƴar uwarta ce, sai dae kawai tace musu eh, saboda tasan son jin gulma ne kawai,
Hanya suka miƙa bada jimawa ba suka ƙaraso Lunch room ɗin makarantar wurin cin abincinsu, lokacin da suka shiga wurin mamaki ya kama sehrish ganin ɗalibai aciki kowa zazzaune saman dining tables masu mazaunin mutun 4, kowa wanne gabansa cike shaƙe da abinci sai ci suke yi,
Ruƙo hannunta Amrish tayi adai² wani tebur da bakowa tace ma sehrish tazauna sai faman zare ido take yi gabanta na faɗuwa tsoranta kar ace tabada kuɗin abinci,
"Me kike so na amso mana muci"? Amrish ta tambaya tana kallonta daga tsaye, zuru sehrish tayi tana tunanin yarda za tace ma Amrish bata da ko sisi,'
"Kin yi shiru baki ce komai ba"? Amrish ta tambaya a ƙagare, murya na rawa Sehrish tace "Ni bana jin yunwa, a ƙoshe nake,"
Cikin mamaki amrish tace "but alamu fa sun nuna cewa kamar kina jin yunwa? Yakamata ko Coffee ne kisha taya zaki zauna da yunwa acikin ki"?
sehrish tace"kada ki damu bana jin yunwa ne kawai," jinjina kai amrish tayi tare da cewa "its ok bazan takura maki ba, tunda kince bakya jin yunwa, ni bari naje na amso abunda zanci," tana faɗin hakan ta wuce wurin masu zuba masu abincin,
ɗagowa sehrish tayi tana kallon students ɗin dake zazzaune suna faman cin abinci hankalinsu akwance, haɗiyar miyau tashiga yi ganin yarda suke Cusa pancakes da zuma abakinsu,
sunnar da kai tayi gaba ɗaya tarasa yaya zatayi ga yunwa tana ji amma tana tsoran taci musu abinci ba kuɗin biya, tana cikin wannan tunanin sai ga Amrish tadawo hannunta ɗauke da plate guda biyu da murmushi afuskarta, ta ajiye su saman table ɗin sannan ta juya ta koma domin amso masu abunsha,
Zuru sehrish tayi tana kallon plate ɗin mai ɗauke da banƙararriyar kaza ta gasu sosai hada ƙaramar knife wadda mutun zai yanka yaci, ɗayan plate ɗin kuma Snacks ne acikinsa shaƙe, runtse ido tayi tana ji tamkar takai ma plate ɗin hari, sai faman cixon la66a takeyi,
dawowa Amrish tayi hannunta ruƙe da Laca sera mai sanyin gaske roba biyu, wuri tasamu tana fuskantar sehrish tazauna tana cewa "Wai haryanzu kina akan bakan ki na ba zaki ci komai ba"? tun yanzu zamu fara haka dake?
ɗan murmushin yaƙe Sehrish ta saki tare da cewa "ba haka bane just bana jin yunwa ne shiyasa," ta faɗi tamkar zatayi kuka, Ido ya gani rai naso,
Murmushi kawai Amrish tayi kafin tasa hannu ta ɗauki ƙaramar wuƙar dake ajiye saman kazar tashiga yankar naman tana ci,
Ƙiris ya rage sehrish tasaki miyau saboda tsabagen kwaɗaituwa da tayi cikin sauri ta gyara natsuwarta gudun kar tayi abun kunya agaban sabuwar ƙawarta,
Muryar amrish ce ta katse ta da cewa "Ko lemun ba zaki sha ba"? Cikin sauri tace"eh a ƙoshe nake," giɗa kai tayi sannan taci gaba da cin abunta, suna cikin zaman nan sai gasu Naja'at da parveena sun shigo, kai tsaye wurinsu suka nufa suka samu wuri suka zazzauna,
Naja'at tace "Wlh da wata irin yunwa na fito Class ɗin can, sam bana gane ma karatun, dama can nifa ba gane math nake ba,' tayi maganar tare da sa hannu ta ɗauki robar lacasera tare da buɗeta ta kwafa abakinta tana kwankwaɗa, hankalin sehrish ba ƙaramin tashi yayi ba ganin tashanye mata lacasera ɗin da Amrish ta kawo masu, Ana cikin haka parveena ta tsoma hannu suka cigaba da cin roasted chicken ɗin da Amrish ta kawo masu, kafin kace mai tuni sun kwamushe komai, duk tana zaune tana faman haɗiyar yawu, sai da suka kammala sannan ma suka lura da ita, parveena tace "Au! Wai dama Yarinyar nan tana a wurin nan? Yo aini yunwa tasa nagaza gane ku nawa ne zaune a table ɗin muka tarar," ta faɗi da mamaki Naja'at ma tace"ko ni ban lura da ita ba, sai da kikayi magana Allah, sannu ko? Meyasa ke bakici komai ba ne,"
Tamke fuska sehrish tayi rai a6ace tace "bana jin yunwa," jinjina kai su kayi atare naja'at tace "halan kinyi breakfast dayawa ne a gida"?
A ƙule sehrish tace "Bansani ba," acikin zuciyarta tayi maganar a fili kuma tace "eh,"
daganan suka ci gaba da firar su har Parveena ta ƙaro masu abincin duk tana zaune suka zauna suka lamushe suka bar rishi da tanɗar baki, da lokacin komawa Class yayi kowa ya wuce Ajinsu naja'at da parveena class ɗinsu ɗaya don haka suka wuce atare, ita kuma tabi Amrish izuwa nasu Class ɗin,

Sehrish ba ƙaramin jiki taji ba, saboda azabar yunwa har wani jiri take gani, dishi² ta runƙa gani a idonta sam batasan me aka koya masu bama,
Lokacin da suka taso daga school tunani ta soma yi wa zai zo ya ɗauke ta, ga school bus tashigo cikin makarantar amma tsoranta kar ace kuɗi za'a biya,tsayawa tayi hannunta ruƙe da school bag ɗinta sai faman lullumshe ido take yi, suna cikin tsayuwar nan sai ga drivern

21 / 80