ABBAN SOJOJI TAKUN TSAKIYA 2 BY BOSS BATURE.txt

Author :  Boss Bature Category :  Arewa Pen

Chapter   27 / 80

78K to 81K   out of 238K words

yace "Yaya Abbas saboda me zaka ce kana fushi dani dan Allah, bakasan yarda na damu dakai ba koda yaushe inason zuwa amma shaiɗan ya hanani zuwa,' dariya sukayi gaba ɗayansu jin abunda junaid yace,
  ɗan gyaran murya amani tayi masa tare da cewa"Junaid ni baka ganni bane"?
  matsawa yayi tare da kai hannu zai rungumeta ajikin shi, ae kuwa a razane Abbas ya finciko rigarshi tare da janyo shi baya baya yana cewa "Sannu mati na mata,!matar tawa zaka rungume agabana? salon mu koma gida ta juya mun baya ko?"
  Fashewa da dariya Amani tayi shima junaid ɗin dariyar yake yi cikin jin kunya ya sunnar dakai, shi aganin shi ba wani abu bane don ya rungume matar yayan shi, duk cikin waye wa ne,
  Abbas ya kuma cewa "Oh ni junaid? Yanzu fa in na ƙyale ka sai ka rungume ta ko"?
  ɗaga mashi kai yayi alamar Eh, hannu abbas yasa tare da ɗan jan kunnan shi har yayi ƴar ƙara yana faɗin "wayyo yaya Abbas karka cire mun kunne na in rasa na jin magana,"
  "Hanzarta ka cire masa kunnan, hukuma ce zata raba ni dakai," acewar Abbansu wanda bai jima da fitowa ba ganin su yasa shi tunkaro su,
   Murmushi suka saki gaba ɗayansu, adai dai lokacin Sehrish tafito daga ɗakinta, harta sanya Sandals ɗinta taruƙo school bag ɗinta, ƙarasawa tayi inda suke,
  tunkan taƙaraso Amani ke kallonta cikin jin bugun zuciya, shi kanshi Abbas kallon matashiyar yarinyar yake yi cike da mamakin ina aka samu yarinya mace acikin gidan,
Ganin duk hankalinsu yadawo kanta yasa jikinta ya soma yin kerma, dakatawa tayi da tafiya sannan cikin en ina tace "umm....ina kwananan ku,"
  atare abbas da abbansu suka amsa mata banda Amani dake tsaye ƙiƙam tana kallonta cikin tashin hankali, ita kanta sehrish atsorace take da kallon da Amani ke yi mata,
  "Zonan My daughter nayi missing ɗin ganinki, gashi bakya zuwa kina gaishe da Abbanki ko"? Yayi maganar yana kallonta,
  Ƙarasawa sehrish tayi gab da Abban nasu ta tsaya tana faman ƙaƙume hannun jakarta da ta sargafo a kafaɗarta,
Hannu yasa tare da shafa gefen fuskarta yace"yaushe kika fara zuwa school ne ba'a sanar mun ba"?
....daker sehrish ta iya cewa "jiya ne nafara zuwa,"
Jinjina kansa yayi tare da cewa "okey,ki maida hankali sosai akaratun ki kinji ko? Banda biye ma ƙawaye
  "Insha Allah Abba," ta amsa mashi,
Baki asake Abbas yace "yakamata a wayar mun dakaina mana, ina aka samu yarinya kyakkyawa kodai daga cikin danginmu ne na damaturu ko zariyya"?
  Ya tambaya aɗan ruɗe yana kallon Abban nasu, tunkafin Abban nasu yace wani abu junaid yayi saurin cewa "ƙanwata ce yaya Abbas, sunanta Sehrish kuma abbane yayi mun ƙanwa da ita, itama ƴar Abban mu ce, ba'a jima da haihuwarta ba, nasan zakayi mamakin yarda tayi saurin girma har haka, ka tambayi Abba zaiyi maka bayanin komai,'
  yana faɗin haka yaja hannun sehrish suka bi ta gefensu suka fuce,
  Dariya kawai Abbansu ke saki hada shi Abbas ɗin,
  "Ji wata shiririta irinta junaid,hakanan kawai ya zabga mun ƙarya, ina na ajiye matar bare harna haifi ƴa kamar wannan,'
Ya fadi tare da yi masu alamar su shiga daga ciki, bin shi su kayi tare da samun wurin saman royal sofa mai mazaunin mutun uku suka zauna, Amani na kusa da Abbas yayin da Abban ke fuskantar su yace "sannun ku da zuwa,nayi mamakin ganinku da wuri haka,"
Abbas yace "tun jiya muka so muzo,amma dare yayi sosai lokacin, wlh sam nagaza samun natsuwa ne game da halin da naga fawan a asibiti, shine nace mata tashirya muzo har gida mu duba shi,"
  yayi maganar fuskarshi dauke da damuwa, Amani ma tace "Abba ya mai jiki? sai jiya da daddare yake faɗamun abunda ya faru dasu fawan hankali na ya tashi sosai, tun jiya nima naso ko wayane nakira na tambayi jikin shi amma duk layin dana kira ba'a ɗagawa,"

Abba yace "ae ba zaki same su ba, saboda duk muna cikin damuwa ne,bakowa ma yasan inda ya jefa wayarshi ba,abun ne ya tayar mana da hankali sosai,
Cikin sanyin murya tace "Allah sarki Allah ya bashi lafiya,ya tashi kafaɗun shi, su kuma waɗanda sukayi mashi wannan aika aikan Allah ya toni asirin su,"
  "Ameen Ameen," suka amsa mata
Daga bisani Abbas yace "bari mu shiga ciki mu dubo shi,"
  Miƙewa su kayi hada Abban yayi masu jagowa izuwa ɗakin da aka kwantar da fawan,
  Da sallama suka shiga ciki, har lokacin fawan na kwance sai faman sharar bacci yake yi, Abbas yace "masha Allah jikin nasa yafara sauƙi, tun da harya samu bacci,"
  "Ae tunjiya dana shigo ɗakin na same shi yana ta faman fisge-fisge yana cewa sun biyo shi zasu kashe shi,saina zauna wurin shi anan zaune muka kwana ni dashi da asuba ne nabar ɗakin," Abban nasu ne yayi maganar ayayin da yake samun wuri gefen gadon tare da zama yana kallon fawan ɗin dake kwance magashiyyan yana kwasar bacci,
  matsawa Abbas yayi shima tare da samun wurin kusa da Abban nasu ya zauna sannan yakai hannun shi ya dafa forehead din fawan yana cewa "Baƙaramin jiki yaji ba gaskiya,sun azabtar dashi sosai bawan Allah, amma asannu zai warware insha Allah,
  Kafin Abban nasu ya kuma cewa wani abu wayar Amani dake acikin handbag ɗinta tashiga yin ringing da ƙarfin gaske,
  Kallonta Abbas yayi tare da cewa "ki fita waje ki amsa wayar," cikin sauri ta amsa mashi da toh sannan ta fuce,
dama so take ta fita daga ɗakin saboda gulmar data ciyota kunsan mu mata abun ajinin mu yake,da zarar abun gulma ya samu nan take zaka ga jikin mutun har rawa yake yi don ya faɗama ɗan uwansa, (Amma fa ni bana gulma) 😒



76.
Cikin sauri Amani ta sauko down stairs jikinta har rawa yake yi ganin Azmee na jera masu breakfast a dining table, yasa cikin sauri ta wuce wurinta
  Azmee naganin ta ta soma sakin fara'a tana cewa "aaa yau kune agidan namu? saukar yaushe,"
Batare da Amani ta amsa mata ba tace "Yawwa Aunty azmee dama akwai abunda nakeso na tambaye ki,"!
  Cikin mamaki azmee tace "meke nan"?
  "Ga me da Yarinyar dana gani acikin gidan nan, wata ƴar matashiyya shin ita ɗin jinin su Abba ce?
  murmushi azmee ta saki aranta tace "Gulma ajali, in ba'ayi ba a mutu," a fili kuma tace "abokiyar aikina ce a aka kawo don ta runƙa tayani aiki,"
  yamutsa fuska amani tayi kan ta yagama ɗaurewa ta kuma cewa "ƴar aiki fa kika ce? But i was confused ya akai naganta cikin uniform kuma har junaid na kiranta da ƙanwarshi? Kuma naji Abba ma ya kirata da My daughter,duk kuma a matsayin mai aikin?
  dariya azmee tayi ganin yarda amani ta ɗaga hankalinta akan sehrish
  "tabbas mai aiki ce itama, amma abba ya mayar da ita tamkar ɗiyarsa,bata da banbanci da sauran ƴa'ƴanshi a yanzu, saboda yana son Yarinyar sosai,"
  Jin haka yasa Amani ɗan zaro ido waje bata ƙara cewa komai ba saboda wayarta da ta ƙara yin ringing, cikin sauri ta zura hannu tare da buɗe handbag din ta zaro wayarta, tare da duba screen din wayar don taga mai kiranta, sunan Aunty laila ne ya bayyana asama, kallon Azmee tayi tare da cewa "ina zuwa," tayi maganar tare da kama hanya ta danyi nesa da azmee sannan ta ɗaga kiran tare da kara wayar a kunnanta tana cewa "barka da safiyya Auntyna fatan kin tashi lafiya,"
Murmushi Aunty babba tasa ki daga can 6angaren tace "Lapiya lou Alhmdllh my sister, nazo maki da labari mai daɗi ina fata kina da kunnan saurara,"
  Amani tace "nima ae ina tafe da labari zazzafan gaske, amma bansan wa zai fara bada labarin shi ba acikin mu,"
  Saurarawa tayi tana jiyo dariyar aunty babba ta cikin wayar sai da ta tsagaita da dariyar sannan tace "ina tunanin labarina yafi naki daɗi kuma zaifi ƙayatarwa, bari dae ni nafara baki,"
  murmushi Amani tayi tamkar tana agabanta tace ina sauraronki auntyna,
  gyaran murya Aunty babba tayi sannan tace "ina yaran nan da nake baki labari Omar ya kawo mun gidana?
  Amani tace "eh nagane su,"
Aunty babba taci gaba da cewa "ae tuni nasa an kwashe su, an jefar mun dasu bayan gari,yanzu haka hankalina kwance na rabu da alaƙaƙai, yanzu banda wata sauran damuwa saura target ɗina nagaba nake jira...." tunkan taƙarasa maganar Amani ta kwashe da wata irin mahaukaciyar dariya,
Jin dariyar da amani keyi ne yasa aunty babba dakatawa da maganarta tana sauraronta ta cikin wayar, ganin cewa amani bata da alamar jinkirtawa da yin dariyar da takeyi ne yasata cewa "ke bana son iya shege, na ji kina mun dariya kodai daɗin labarina ne yasa ki jin daɗi har haka," ta tambaya tana jiran jin mai amani zata ce,
  daƙyar Amani ta tsagaita da yin dariyar sannan tace "Aunty laila an fa yanka ta tashi,labari da ɗumi ɗuminsa idan ma kina atsaye to wlh ki zauna don kar in sanar dake ki yanke jiki ki faɗi,"
  Jin maganar Amani yasa hankalin aunty babba ɗugunzuma,murya na rawa tace "ba atsaye nake ba,ina zaune saman 2 seater ne ina shan tea,dan Allah ki sanar mun wane irin labari ne wannan,"
  wani irin shu'umin murmushi amani tayi kafin ta soma cewa"Yanzun nan muka zo gidansu Abbas saboda mu duba jikin fawan da miyagu suka kai masu hari, ina fata kinsan wannan labarin"? Ta tambaya tamkar tana agabanta,
Aunty babba tace "eh nasani,ae muna nan muma zamu zo tare da ishaq don mu duba jikin shi,"
  Jinjina kai Amani tayi sannan taci gaba da cewa "Shin ko kinsan cewa akwai wata matashiyyar yarinya kyakkyawar gaske da muka tarar acikin gidan !!!'
  darammm !!!gaban aunty babba ya faɗi rasss a firgice ta saki cup ɗin dake hannunta ya tarwatse ƙasa, zumbur ta miƙe tsaye tana cewa "kamarya Amani ! Bangane abunda kike cewa ba anya ba kunne na bane suka jiyo mun hakan"?
  dariya amani tayi kafin tace "ba kunnanki bane Aunty laila,zahiran ne wannan nake faɗa maki, wlh da ido na naga yarinyar,kyakkyawar gaske har na tambayi azmee nake cewa wacece ita yarinyar kodai cikin danginsu Abba take, sai azmee ke sanar dani cewa house maid ce itama amma Abba ya mayar da ita tamkar ƴarsa, har fa school sun sanya yarinyar, babban abunda zai tayar maki da hankali sai kin ga yarda Abba ke kiranta da ɗiyarshi, yarinyar ba ƙaramin wuri ta samu ba.......
Fuska a damuje aunty babba tace "nifa hanyanzu ban fahimta ba, shin yarinyar ƙarama ce sosai ko babba"?
  Amani tace "ina fa, wlh balagagga ce nace maki fa matashiyar budurwa kyakkyawar gaske mai cikar sura,ni kaina dana kalle ta sai da gabana ya faɗi to ina ga matasan gidan da suka kasance maza ne dukansu,
  Jin wannan maganar yasa aunty babba dake atsaye tana zarya a falon nata, aza hannunta na dama akanta, ɗayan kuma na ruƙe da wayar tashiga cewa "Ae shikenan wlh an yanka ta tashi, ni ina nan sake da baki ina murnar rabuwa da waɗancan tagwayen da Omar ya kawo min ashe abanza ga wata can ta riga ƙetare iyakar da bana so aje,amma an gama dani wlh ya akai har takai wannan lokacin gidan baki sanar dani ba,"? ta tambaya a kiɗime,
  Amani tace "nafa ce maki ni kaina bansan da zamanta ba, yau ɗin nan muka ganta kwatsam tafito ɗas da ita cikin school uniform wlh abun ba'a magana yarinya haɗaɗɗiyar gaske,tasamu wuri fa sosai agidan, kuma yarda naga Abbansu na kiran sunanta da daughter dinshi kinga kuwa hakan na nufin nan gaba ma da sunan Surikata zai kirata,"
  ƙasa ƙasa amani ke sakin dariya tana sauraron aunty babba dake faman Zabga salati, dama dagangan take tunzurata don ta rikitar da ita,
"Nashiga ukuna,wannan masifar har ina matashiyar budurwa kuma agidan surikina, wlh hakan bazai ta6ayiyu ba, wlh saina son yarda zanyi na rabata da gidan, badai zamu zo da ishaq ba hmmmm zanganta ne !! zanga KOWACECE ITA 😳😳😳
  Sun jima suna waya da aunty laila kafin daga bisa ni sukayi sallama da juna amani ta koma daga ciki, ranta fess don tasan yau ko bacci aunty babba bazata iya yi ba har sai taganta a Abuja, gata ga yarinyar data bata labarinta,

Fitowa hafsat tayi daga bedroom ɗinta jikinta sanye da sleeping dress ganin mommyn nata tsaye tana ta faman zarya a falon tana zazzaga bala'e ita kaɗai kamar zararriya, hakan yasa hafsat ƙarasawa kusa da ita tana cewa "wai mommy lafiya kuwa kike ta faman tada jijiyoyin wuya duk akan wanene?
Uban tsoki Aunty babba ta saki sannan tace "wani mummunan labari amani ta sanar dani yanzun nan, wlh nagaza samun natsuwa, so nake kawai naganni a abuja wlh,"
  Wuri hafsat ta samu tare da zama saman 2 seater sannan tace "mommy wannan wane irin labari ne haka daya tayar maki da hankali haryasa kika fasa cup ɗin da kike shan tea dashi," tayi maganar ayayin da take kallon kofin da aunty babba ta saki ƙasa ya fashe,
  juyo tayi ta kalle ta rai a6ace tace "ba dole hankali na ya tashi ba, ina murnar rabuwa dasu hossana da jahad sai gashi yanzu Amani ta kirani awaya tana sanar dani cewa sunje gidan su Abba, sun tarar da wata matashiyar budurwa wai mai aikice fa, amma abba ya mayar da ita tamkar ɗiyar cikinsa," tayi maganar tana huci,
  Shiru hafsat ta ɗanyi na wani lokaci kafin daga bisa ni ta saki ƙayataccen murmushi tace "Mommy kenan, dama kina tunanin haƙƙinsu hossana da jahad zai barki ne? to inaso ki sani haƙƙinsu ne yafara bibiyarki, kuma ba zaki ta6a cin nasara ba akan wannan yarinyar da aka baki labarinta yanzu, saboda mommy sam baki kyauta ma rayuwar yaran nan ba, basu miki laifin komai ba kinsa an kwashe su,ki kayi mun ƙaryar cewa gidan marayu za'a kaisu ashe zubar dasu kikasa ayi,yanzu wayasan wani hali suke ciki.........' hawaye ne suka soma zarya a fuskarta saboda raɗaɗin da take ji aduk lokacin da ta tuna dasu hossana da jahad,tun jiya da aunty babba ta sanar da ita cewa ba gidan marayu tasa akaisu ba, zubar dasu tasa ayi bata ƙara samun kwanciyar hankali ba, abun namata ciwo azuciyarta
. kallonta kawai aunty babba keyi ganin yarda take zubar da tears ɗinta akan tsintattun yaran da bata haɗa alaƙar komai dasu ba,
  tsoki ta sake ja tare da cewa "kin dai ji haushin rayuwarki wlh, saboda waɗancan marasa galihun kike ta faman sharara kuka,har kina ikirarin haƙƙinsu ne ke bi na,to ki zuba ido ki gani saina sa anyi waje da waccen yarinyar da amani taban labarinta,"
  afusace hafsat ta miƙe tana kallonta tace "mommy! Ina miki fatan nasara," tana fadin hakan ta juya tare da komawa bedroom ɗinta,
  Jinjina kai aunty babba ta shiga yi tana faman sakin huci kamar zakayan, afili tace "Tabbas dole nasan kowacece wannan yarinyar dake ƙoƙarin tarwatsa mun plan ɗina, yakamata nasan abunyi dole na kira HAYAAM awaya in sanar da ita cewa ta tattaro kayanta itama ta koma gidan da zama, tunda har ƴar aiki ta samu irin wannan gatancin ina ga ita da take ƙanwata !!!!!!🤭
  Sai faman balbali bala'e take yi ita kaɗae tana ci gaba da zarya a falon,

*******************************

tun bayan da junaid ya sauke sehrish a school su kayi sallama ta shige ciki shi kuma yakama hanyar komawa gida, yana driving yana tunanin fuskar rishi ɗinsa, wani irin tsantsar sonta ne ke sanya shi jin wata irin kasala a jikinsa, lokacin da ya ƙaraso gida sai da gabanshi ya faɗi rass ganin dandazon motoci suna ta shiga gidan nasu,manya manyan mutane ne aminnan abbansu suke ta zuwa dubiyar fawan, wasu daga cikinsu manyan shuwagabannin sojoji ne da kuma mr president da kanshi ya tako yazo don duba jikin ɗan aminin nasa atare dashi hada mataimakinsa da kuma babban ɗansa Captain Shattima wanda ya kasance aboki ne ga Marshal Omar da SGR tun a U.s don acan shima yayi karatunsa na Airforce, halayyarsa da ɗabi'unsa sak irin nasu ne shiyasa tafiyar tasu tazo ɗaya, ƙwararre ne a6angaren aikin shi, sannan kuma shima mace sam bata gaban shi,tamkar dae su ɗin dae,
  Gida fa ya ɗinke ɗuff da mutane tamkar rasuwa akayi, ta ko'ina jinsin bil'adama ne ke ta shigowa,
  Hankalin junaid ba ƙaramin tashi yayi ba tunkan yayi parking ɗin motarsa yake ta faman sharar hawaye tsoran shi kar ace wani abune ya faru dasu fawan saboda yasan sune basa a gida anturasu aiki,a hankali ya tsayar da motar sannan ya buɗe murfin motar ya fito yana kallon mutanen dake shigowa,
...jingina bayansa yayi ajikin motar tashi sannan ya zura hannun shi cikin trouser pocket ɗinsa, wayar shi ya zaro tare da shiga contact ɗin wayarsa, lambar abbansu ya gano sannan ya buga masa waya,
  ta jima tana ringing kusan sau uku kafin Abban nasu ya ɗaga kiran,
  Kara wayar yayi a kunnansa tare da fashe mashi da kuka,
  Shiru Abbansu yayi yana sauraran kukan da junaid ke yi masa acikin wayar,
  Cikin shesshekar kuka yace "Abba......wanene ya mutu, naga dandazon mutane acikin gidan...'daker ya iya yin maganar zuciyar shi na faman bugawa,
   "Kana ina ne"? abban nasu ya tambaya
.."gani awaje abba, nakasa shigowa,ina jikin motata yanzu haka ban jima da shigowa gidan ba, saboda nakai sehrish school ne,"
  Ajiyar zuciya abbansu ya saki kafin yace "sauraran ni kaji da kyau, babu wanda ya mutu, nasan halinka ne shiyasa tun jiya ban sanar maka ba, amma yanzu zan faɗa maka, but promise me first cewa zaka daina kuka,"
  Ajiyar zuciya junaid ya shiga saukewa yana cewa "Okey, abba nadaina tell me pls,"
  gyaran murya abban nasu yayi tamkar yana agaban shi sannan yace "abunda ya faru shine, su irfan da aka tura aiki,miyagu suka farmake su amma alhmdllh duk suna cikin ƙoshin lafiya, fawan ne kawai suka samu nasarar cutar dashi harya zauce ssae tun shekaran jiya suna asibiti ana duba su sai jiya ne muka dawo gida tare da su............'
  tunkan abban nasu ya ƙarasa maganar tashi tuni Junaid ya saki wayar dake hannun shi sakamakon faduwar da yayi nan take ya sume...................dama abunda abbansu ke gudu kenan

hankali atashe yake cewa "junaid!junaid !!! Kana

27 / 80