Author : Boss Bature Category : Arewa Pen
Allah,kowani tsautsayin ne da ƙaddara suka kawo ta cikin gidan nan!Allah yasa ta kwanan mana biyu...." ya jinjina kai tare da cewa "tsuntsu daga sama gasasshee!"ya ƙarashe maganar tashi tare da zura hannun shi cikin aljihun jeans ɗin dake a jikinshi,wayar shi ya ciro tare da duba screen ɗin, missed calls aka mashi da wata hidden number,
shiru yayi yana tunanin taya zai bi kiran saboda kira ne mai mahimmanci a wurin shi gashi dole sai in shi mai 6oyayyiyar numbar ne ya kira ka,
Yana cikin wannan tunanin sai ga kiran ya sake shigowa,cikin sauri yayi picking call ɗin tare da kara wayar a kunnan yana jiran jin me za'a sanar dashi
Wata irin muryace ta irin hamshaqan matan nan waɗanda suka ji duniya ta soma magana"Haroon!kana shirin jamin bala'e ko?meyasa ka fiye shiririta ne?ko kamanta plan ɗin mu ne"?
nan take haroon yashiga en ina murya na rawa yace"ban manta ba,inaso nabi komai a hankali......'bata bari ya ƙarasa maganar ba ta kwatsa mashi tsawa"Ya isa Haka! kasani wlh akanka bazan bari nayi gangancin rasa damar da nake da ita ba!haroon zaka iya rasa ranka muddin kace zaka kawomin wasa acikin lamarina!kai kasan wacece NI!bani da imani,"
Wata irin zufa ce ta soma gangaro mashi daga cikin sumar kanshi,lokaci guda duk yabi ya rikice yashiga zazzare idanu,
sautin dariyarta ce ta karaɗe kunnan shi,tsagaitawa tayi da yin dariyar sannan ta sassauto da muryarta wurin cewa"Am sorry fa,na tsorata ka ko?
Nannauyar ajiyar zuciya haroon ya saki tare da cewa"Yanzu me kike so ayi ne,just command me zanyi maki koma menene,"!
"So nake ka kashe JUNAID!saboda shikaɗai ne hanyar da zanbi wurin ƙuntata masu,banaso junaid ya rayu,muddin yana araye toh farin cikin gidan zai cigaba da wanzuwa ne,ni kuma abunda bana so kenan!,"
girgiza kai haroon yashiga yi tare da cewa"Kiyi haƙuri wannan ne karo na farko da kika ban umarni na musa maki tunda na fara maki aiki!junaid is innocent I can't kill him,zan iya kawar maki da duk wanda kikeso acikin gidan nan,Amma banda junaid!banda Abbana,Rafayet kuma yafi ƙarfina banda wata hanyar da zan iya cutar dashi,sai ma in jefa kaina cikin matsala!"
fashewa da dariya tayi tamkar zata fasa screen ɗin wayar,bayan ta tsagaita da yin dariyar taci gaba da magana"kasan koni wacece,kasan kuma abunda zan iya!idan har bazaka iya kawar mun dasu ba,to ni zan iya kawar dasu ta cikin ruwan sanyi,Haroon u must do what i command you!if not i wll expose ur secrets,kai kasan me zai biyo baya,ko ka kashe junaid ko kuma ni in kashe maka rayuwa gaba ɗaya...!!!!
Waro ido waje Haroon yayi yana sauraronta,
Cigaba da magana tayi"Maganar videon su Twins daka ɗauka,nasan ka goge na wurinka,amma akwai wani a hannuna,zanyi amfani dashi wurin tarwatsa zuciyar mahaifin nan nasu,da kuma masoyina Rafayet!inason ganin tashin hankalin shi sosai...."
A tsorace haroon yace"Kada ki kuskura ki saki bidiyon nan!in ba haka ba asirina zai tonu ne!kuma kina sane da cewa,muddin asirina ya tonu to ke ma kin gama yawo!!atare zamu fuskanci sakamakon mu,zasu kamo ki ne aduk inda kika 6uya!!"
ya ƙarasa maganar yana faman sakin huci yayin da idanun shi sukayi jawur saboda tsananin 6acin rai,
fashewa ta kuma yi da wata irin mahaukaciyar dariya kafin ta tsagaita da yin dariyar tace"Haroon!Iska bata ruƙuwa!domin ni tamkar iskar nake,kada kamanta ina amfani da baƙaƙen aljanu wurin gudanar da aiki na,kuma zanyi amfani dasu ne wurin ganin na tarwatsa dukkan zuri'ar Salahuddeen Hussein!wannan alwashi ne na ɗauka,rai uku masu mahimmanci suka kashe mun,ni kuma rayuka zan ɗauka!don bana yafiya arayuwata!"
Shiru yayi bai ce komai ba kusan minti biyar, sam baison wani abu ya samu abbanshi shi kaɗae yafi ji sannan yace"Maganar yaran nan fa?su kuma ya zakiyi dasu?
"Inaso saina fara sanya soyayyarsu acikin zukatan ƴan uwansu sosai,saboda inaso inyi amfani da wannan damar ne wurin ƙuntatawa dukkan wani jin daɗi na zuri'arsu,kamar yarda suka ƙuntata ma tawa zuri'ar,"
Jinjina kai haroon yayi kafin ya kuma cewa"Yanzu menene plan ɗinki"?
Wannan karan anatse ta soma magana"plan ɗina shine kawar da junaid,dalilin dayasa nakeson kawar da junaid shine!sihirina bazai ta6a tasiri akan Rafayet ba har sai an samu lagwanshi,kuma ba kowa bane lagwanshi ba fa ce Junaid,da zarar ya rasa junaid zaiyi sakaci da ibadarshi hakan zai bani damar yin aiki akanshi,kuma shi ya kasance Bugun zuciyar family ɗinsu inaso na ɗanɗana masu raɗaɗin rasa mutumin daka kwallafa rai akansa!sannan maganar bidiyon nan zan sake shi a social media kowa ya gani,daga zarar hakan ta faru nasan cewa Martabar family ɗinsu da kuma ƙimar da suke dashi a duniya gaba ɗaya zasu zube,kowa zai tsani zuriyarsu duk wata daraja da suke dashi a idon duniya zata tashi abanza ne!ni kuma hakan nakeso,kafin na saki bidiyon inaso kayi amfani da kuɗin da suka baka wurin barin ƙasar,ka koma malaysia da zama,na shirya maka komai najin daɗin rayuwa acan,giya da mata har saika gaji dasu,"
shu'umin murmushin nan nashi ya saki aranshi yana ayyana irin rayuwar da zaiyi acan cikin daular da aka shirya mashi,nan take yaji cewa zai iya aikata komai takeso,
Sam yama manta da waya yake yi saboda tsabar farincikin da ya ziyarce shi,mayar da bayanshi yayi a jikin seat na motar yana cigaba da sakin murmushi,
"Kana jina kuwa,"muryarta ce ta ratsa kunnan shi,hakan yasa ya dawo daga dogon tunanin daya tafi,
Sai da ya samu natsuwa sannan yace"Naji duk abunda kika ce,hakan yayi mun sosai,musamman da kika ambaci giya da mata,sai naji wani nishaɗi araina dama irin rayuwar da nakeson yi kenan,amma akwai wata shawara da nakeson baki,in ba damuwa,"
Tace"ina sauraronka haroon,"
"Ga me da bidiyon tsaraicinsu twins,kada ki sake shi a social media pls,sun riga sun biyani kuɗi kamar yarda na buƙata,shiyasa nakeso ayi masu sassauci,mutun biyu kawai nakeson suga bidiyon nan Abban su da kuma wannan ifiritun sarkin jin kan nan,sannan maganar kashe junaid nasan ban isa na hanaki aikata abunda kika yi niyya ba,amma abunda nakeso ki bar komai a hannuna,ni ko ke babu wanda zai kawar dashi!kiyi amfani da sihirin ki kawai ta cikin ruwan sanyi yarda babu wanda zai zarge ni!!"
Dariya sosai tayi da alama shawarar Haroon tayi mata,
Sannan tace"daga yau komai zai fara"!!!
murmushi haroon ya saki tare da cewa"Allah yaba mai rabo sa'a"
daga haka su kayi sallama ya kashe kiran,kasa fitowa daga cikin motar yayi ba don komai ba sai don kasalar da yaji ta baibaye shi,fuskar junaid kawai yake gani acikin idanun shi,😢
******************
Lokacin da Hayaam ta shiga cikin gidan da sallama abakinta tashiga main palour ɗin,tsayawa tayi da tafiya ganin babu kowa acikin babban falon,takun tafiyar da taji ne yasa ta juyawa ta gefen hagunta tana kallon mai tafiyar,bakowa bace face Sehrish sai faman sauri take yi don ta shiga kitchen,har yanzu shigar ɗazu ce a jikinta,amma ta yafa mayafi ajikinta tayi rolling ɗinshi,
ta wutsiyar idonta ta hangi mutum hakan yasa ta dakata da yin tafiyar ta ɗan juya don taga wanene,karaf idonta suka haɗu akan na Hayaam,cike da mamaki take kallonta,batasan ko wacece ita ba,amma ganin hasken fatarta yasa tayi tunanin ko ƴar uwarsu Junaid ce,
tunkararta sehrish tayi fuskarta ɗauke da murmushi ta ƙarasa inda hayaam take,tunkan sehrish ta ƙaraso zuciyar Hayaam ta shiga bugu,don ta gane cewa itace Ƴar aikin da Aunty laila take bata labarin cewa tana rayuwa acikin gidan,yarinyar da Abbansu ya mayar da ita ɗiyar shi,
fuska ɗauke da murmushi sehrish tace"Sannu da zuwa,"
hayaam tace"yawwa,ina mutanen gidan nan?naji shiru ko ba kowa ne"?
sehrish tace"duk sun fita,amma junaid da Fawan suna acikin bedroom ɗinsu,sai Aunty azmee tana acan cikin kitchen,
Jinjina kai Hayaam tayi har ta buɗe baki zata kuma cewa wani abu,sai ga Azmee ta fito daga cikin kitchen ɗin,ganin Hayaam yasa ta soma Sakin fara'a kamar gonar auduga,cikin sauri ta tunkaro wurinsu tana cewa"Wata sabon gani!Anya ba idona ne ke nuna min badaidai ba?
dariya hayaam tayi tare da wuce sehrish ta tunkari wurin Azmeen suka rungume juna,
ɗago da ita azmee tayi daga jikinta tana cewa"Oh ni Hayaam!ashe dama zan sake ganinki a duniyar nan?gaskiya kun yada zumunci!ina ji tun bikin Amani yaushe rabon ki da gidan nan!
Sai faman washe baki Hayaam takeyi ba don komai ba sai don sanin cewa Azmee zata kar6eta hannu bibbiyu kuma zata goya mata bayan zama acikin gidan,
"Kai Aunty azmee,nafa zo bayan bikin Amani kin dai manta ne,gaskiya nayi missing ɗinku sosai,shiyasa ma nace dole nazo naganku,"
Magana takeyi amma hankalinta na akan Sehrish dake tsaye tana sauraronsu,
Azmee tace"mu ma munyi kewarki sosai,amma dai bada wuri zaki koma ba ko?don bazan bari ki tafi batare da kin zauna mana ba,".
Anzo wajen da tafiso nan fa tashiga washe baki tana cewa"ae Aunty azmee har sai kun gaji dani,in dae ba ku kuka kore ni ba,amma ni ina nan ba inda zanje,"
murmushi Azmee tayi tare da cewa"Ae bama wanda zai kore ki hayaam,".
taƙarasa maganar tare da mayar da idonta kan sehrish tace"wannan Hayam kenan!ƙanwar matar yayansu ishaq,da kuma Amani wadda tazo ran nan harna gabatar maki da ita"?
wani irin bugu taji zuciyarta tayi mata ba don komai ba,sai don tuna kalaman Amani da tayi in har wannan takasance ƙanwarta ce,lallaikam akwai matsala,
da ƙyar sehrish ta ƙaƙalo murmushin yaƙe sannan tace"Allah sarki,ashe kanwarsu ce,naga suna yanayi da Aunty amanin,"
ta6e baki hayaam tayi jin abunda sehrish tace,
ruƙo hannunta Azmee tayi tare da cewa"Kada na cika ki da surutu,mu shiga ciki ki huta don nasan ba ƙaramar gajiya kika kwaso ba,"
atare suka wuce ciki da Azmeee,zuru sehrish tayi ita dai tun da tayi arba da Hayaam taji sam bata kwanta mata arai ba,kama hanyar shiga kitchen ɗin tayi tana cikin tafiya taji muryar junaid ya ambaci sunanta,
dakatawa tayi da tafiyar sannan ta ɗan juya tana kallon shi,fuskar nan tashi a yamutse alamar daga bacci ya tashi,sai faman sakar mata wannan kyakkyawan murmushin nashi yake,
acikin ranta tace"Shagwa6a66e halan yunwa yake ji ne,"
ƙarasa saukowa yayi daga saman stairs ɗin kai tsaye wurinta ya nufa,
Lokacin da ya ƙaraso inda take tsaye muryar shi cike da kasala yace"Reesh har yanzu Abbanmu bai dawo ba"?
ɗaga mashi kai tayi alamar eh,tamkar zaiyi kuka yace"dama nasani,tunda wannan abokin nashi yazo mai farin gemu,nasan cewa ba zai barshi ya shigo ciki ba,yana can yaja shi sun tafi yawo gidan abokanansu,"
maganar shi ba ƙaramin dariya taba Sehrish ba,
"Amma dae baka da mutunci junaid,abokin abban naku ne kake ce ma mai farin gemu"?
turo baki yayi cike da shagwa6a yace"eh mana,farin gemu gare shi,ae ba ƙarya nayi ba,
Ya ƙarasa maganar da cewa"nidai yanzu ki taimakamin bana jin daɗin bakina farfesu nakeson sha,"
bin lips dinshi tayi da kallo yarda yake magana ashagwa6e,sunyi dark red dasu kamar wanda yashafa jan baki,
Tunanowa tayi da maganar shi ta ɗazu da ya furta mata kalmar so,acikin ranta tace"yanzu ace dagaske junaid sona yake yi,tabbas zan iya haƙura da wanda nakeso don na aure shi,saboda ba ƙaramin tausayi yake bani ba,komai nashi kuma yana burgeni,sai dai bansan ya rayuwar auren mu zata kasance ba,yarda yake shagwa6a66en nan ba ƙaramar wahalar shi mace zata ci ba,wannan rainon shi ma zanyi kenan?kullum sai ya tashi tsakar dare da kukan rigima,don haka sai in tanadi feeder da zan rinƙa haɗa mashi madara yana sha.......'
Kasa ƙarasa zancen zucin nata tayi saboda dariyar data zo mata,tafin hannunta tasa tare da rufe bakinta,ta ƙumshe dariyar don karta fito da ita,junaid ya gani ranshi ba ƙaramin 6aci zaiyi ba,
Harara ya watsa mata tare da cewa"meyasa kike kallona ne?kuma kinsa hannu kin rufe mouth ɗinki da alama baki da gaskiya sehrish,"
kafin tace wani abu,sai ga haroon ya faɗo cikin main palour ɗin,jin takon tafiyar shine,yasa gaba daya suka juya suna kallon shi,adaidai lokacin shima ya ɗago da idanunshi kai tsaye suka sauka akansu,
Nan take sehrish taji gabanta ya faɗi rass,saboda ta tsani ganin shi acikin idanunta,
da alama wurinsu yake tunkarowa,murmushi junaid ya shiga sakar mashi yana cewa"Ya haroon sannu da dawowa,"
"Yawwa baby junaid,me kuke yi anan ne"?
. yayi maganar yayin da yake ƙarasawa wurinsu,
sunnar dakai sehrish tayi batare da ta ɗago sun haɗa ido dashi ba,
Junaid yace"muna magana ne da sehrish,"
ɗan ta6e bakin shi yayi kafin yace"okey,ka wuce ciki inason magana da ita,"
batare da musu ba junaid ya wuce cikin palourn tare da samun wuri saman 3 seater ya zauna,
ja da baya sehrish tayi aɗan tsorace tana jiran jin mai zai ce,
"Kinyi kyau sosai,shigar jikin ki tayi mun,"ya fadi yana faman bin wandon jikinta da kallo,
Shiru tayi mashi batace komai ba,jira kawai take yayi ƙoƙarin ƙure mata ta watsa a guje,
"dama nasan ba zaki ce komai ba,hakan yayi mun sosai,bakomai ne yasa nace inason magana dake ba face don in baki wata shawara mai kyau,sai dai bansan ko zaki ɗauka ba
Sai lokacin ta ɗago da idanunta tare da kallon shi tace"wata irin shawara kenan?kada kayi tunanin cewa zan ɗauki shawarar ka,saboda kai ba abun yarda bane!nagama yarda da duk wani abu da zai fito daga wurinka,burinka kawai ka cutar dani!"
hannunshi ya zura acikin aljihun shi tare da ƙara matsawa dab da ita yace"shawarar ba akanki bane!akan junaid ce!
daram!!taji gabanta ya faɗi a ɗan rikice take kallon shi,
"Nasan tunda na ambaci sunan junaid,yanzu zaki so ki saurari me zance,don na lura ba ƙaramin jinshi kike yi ba,"
Murya na rawa sehrish tace"me...me..kake son cewa ne agame da junaid?me junaid yayi ne?
Maimakon ya bata amsar tambayarta sai cewa yayi"ran nan nayi maki ƙarya na cewa ni shaiɗanin aljani ne,wannan maganar ba gaskiya bace,abunda ya faru shine akan idona Omar yashigo cikin falon nan kai tsaye naga ya wuce upstairs sai raina ya bani cewa dole zai ji sautin kukan ki,kasancewar part ɗinshi dana sgr basu da tazara sosai a tsakaninsu,maganar cewa ni na shaƙe maki maƙoshinki alokacin da kika zo ambaton sunana agaban Marshal Omar shima duk ƙaryace,bani nayi maki hakan ba,kawai nayi guessing ne kuma da alama na canka dai dai,nasan kin tsorata alokacin kuma kinyi tunanin cewa ni ba Mutum bane,don haka inaso kisa aranki cewa Ni haroon cikakken mutum ne kamar kowa,"yana ƙarasa maganar tashi yasa ƙafa zai wuce part ɗinsu,
..cikin sauri sehrish tace"ka manta baka ban shawarar da kace zaka bani ba,"
dakatawa yayi da tafiyar batare da ya juyo ba yace"ku dage da addu'a," yana fadin hakan yasa kai ya wuce ciki,
Tsayawa tayi cike da zullumin maganar haroon nacewa su dage da addu'a,tana cikin wannan yanayin muryar Azmee ta katse ta da cewa"Sehrish!tsayuwar me kikeyi anan ne?nayi tunanin zan zo na same ki a cikin kitchen,'
cikin sauri sehrish ta nufe ta,tana cewa"yanzu nake ƙoƙarin shiga kitchen ɗin,wani abune ya ɗauke mun hankalina,"
Atare suka shiga kitchen ɗin,batare da 6ata lokaci ba suka soma aikace aikacen girke girken nasu kamar yarda suka saba,
94.
Tun bayan da azmee takai hayaam ɗaya daga cikin bedroom ɗin da suka saba ajiye baƙi insun zo,zame hijab ɗin jikinta tayi,wata ƴar short gown ce ajikinta daidai guiwarta,kai tsaye toilet ta faɗa,bayan wasu ƴan mintina sai gata ta fito waist ɗinta ɗaure da towel,sai lokacin ta tuna cewa ashe tabar trolley ɗin kayanta acikin boot ɗin motar Sofwan,yanzu dole ta neme shi ko don ya kawo mata abunta,
ƙarasawa tayi tare da hayewa saman gadon ta zauna,sannan takai hannu tare da ɗauko purse ɗinta da ta ajiye asaman gadon tun shigowarta tare da Hand bag ɗinta,
wayarta ta ciro anan taga missed calls na Aunty babba har kusan uku,
Murmushi ta saki tare da bin kiran nata,wayar na fara ringing Aunty babba ta ɗaga,.
kara wayar a kunnanta tayi tare da cewa"Auntyna takaina!yanzun nan naga missed calls ɗinki,banji ma da fitowa daga toilet ba,
on the other hand aunty babba tace"kin isa gidan ne!"?
Hayaam tace"eh,yanzu hakama gani asaman gadona inaso nayi bacci don na rage gajiyar dake ajikina,amma fa aunty nasha wahala kafin nasamu shiga cikin gidan nan!"
Aunty babba tace"wahala?kamarya kenan?
Nan hayaam ta kwashe duk abunda ya faru a wurin shigowarsu cikin gidan ta sanar mata,
uban tsoki aunty babba ta saki tare da cewa"Ke kika ban haushe wlh!taya zaki tsaya yi masu kwatance cewa ke ƙanwa tace?to menene alaƙar dake tsakani na dasu ne da har zasu shaidaki!tun a lokacin yakamata ki kirani awaya sai inyi ma wani magana daga cikin gidan akan yayi masu magana su barki ki shiga,amma don kince hayaam ƙanwar matar yayansu,to koni nan da kike gani Sgr baisan sunana ba,bare har yasan naki sunan hayaam,wannan mutumin ma bana tunanin yasan kamannin fuska ta nikaina,"
yatsina fuska hayaam tayi tare da cewa"aunty inaso in kwanta bacci nake ji,"
. Aunty babba tace"to shikenan!kardae ki manta da abunda yakai ki cikin gidan,so nake kafin sati mai zuwa naji ana zancen bikinki da Sgr,kafin shekara mai zuwa kuma inji kukan jariri,"
Fashewa da dariya hayaam tayi jin abunda Aunty babba ke cewa,
Sun jima suna waya kafin daga bisani sukayi sallama,wurgi da wayar tayi gefe guda sannan ta kwanta asaman lallausan bedmattress ɗin,nan take bacci yayi awon gaba da ita,
**********************
Abun da ya faru bayan barin Amal gidan,wuraren bayan sallar la'asar mammy da Abra suka shigo cikin gidan,jikinta na sanye da hijabi abra kuwa atampa ce ajikinta ta aza mayafin asaman kafaɗarta,sai faman fira suke yi atsakaninsu,
"Mammy yanzu me zakiyi da kuɗin nan da sofwan ya baki?naga kamar suna da yawa,dama akwai ankon bikin wata ƙawata da nakeson yi,kinga sai ki aramun dubu takwas aciki inyi amfani dasu,"
. tsuke fuska mammyn tayi tare da cewa"matsalarki kenan!daga kinga wani ya bani kuɗi sai ki bijiro da maganar anko,tun wuri ma ki fidda rai don ko sisi bazan baki acikinsu ba,malam zan kaima cikon kuɗin shi sannan sauran ni zanyi amfani dasu,ko ɗan farfesu naman nan an samu ayi,dama na kwana biyu ban sha ba,
ta ƙarasa maganar a lokacin da suka ƙarasa tsakiyar filin gidan,.
Rai a6ace abra tace"mammy kalli kiga fa har yanzu yarinyar nan bata fito daga ɗakin ba,ko ubanwa takeso ya ɗaura mana girki?gidan ma ko share shi ba tayi ba!
cike da masifa mammy ta shiga kwaɗa mata kira"Amal!!Amall!!don ubanki kina ina ne?bazaki fito kiyi mana aikin cikin gida ba!