ABBAN SOJOJI TAKUN TSAKIYA 2 BY BOSS BATURE.txt

Author :  Boss Bature Category :  Arewa Pen

Chapter   30 / 80

87K to 90K   out of 238K words

tun ɗazu,
  Junaid kuwa lokacin da Abban su yashigo dashi ɗakin shi ya wuce dashi tare da kwantar dashi ya farfaɗo daga suman da yayi amma ya dasa da bacci,

  Yanzu wanda suka rage a cikin gidan daga su matasan gidan sai abokin su sgr Shattima sun hallara a garden din gidan suna tattaunawa tare da marshal Omar dashi babban yayan,
   Cg Abbas ya jima da tafiya amma yabar Amani a gidan saboda yace zai dawo da daddare ya ɗauke ta, duk ita ta taya azmee rarraba ma masu zuwa dubiya lemun a cups har suka lafa,

   shigowa ɗakin Abbansu yayi yana kallon junaid dake baje asaman bed dinsa yana ta sharar bacci, ƙarasawa yayi wurin shi tare da zama daga gefen gadon nashi, sannan yaɗan sa hannun shi tare da bubbuga ƙafar junaid kamar mai jira aikuwa a firgice ya tashi zaune yana faman zazzare kyawawan idanun shi da suka canza launi saboda bacci, yana jin muryar abbansu ya kira sunan shi nan take ya fashe da wani sabon kukan yana cewa "Abba yaya fawan ! Yana ina ! meya faru dashi.....'
   Cikin natsuwa abban nasu ya soma cewa "Calm down ur mind junaid,ɗan uwanka yana cikin ƙoshin lpy yanzu haka yana can medical room dinmu mun kwantar dashi, shima sai kiran sunanka yake yi yana cewa Abba ina junaid akawo mun shi in ganshi, inaso in ganshi,"
   jin wannan maganar ta abban nasu yasa junaid dakatawa da yin kukan nashi ya zuro da ƙafarsa zai sauko daga saman gadon, abbansu ya ruko hannun shi tare da cewa "pls junaid kada kaje mashi kana wannan kukan saika tayar mashi da hankali yaga kamar mutuwa zaiyi,
  Cikin sauri junaid yasanya tafin hannayenshi tare da share hawayen dake zubo masa sannan abban nasu ya saki hannun shi, jikin shi har rawa yake yi wurin saukowa daga gadon, bin shi da kallo abban yayi har cikin ranshi yana mamakin yarda junaid ke tsananin son ƴan uwanshi don ji yake yi da wani abu ya same su kwara shi ya same shi koda mutuwa ce,akwai wani lokaci da abbansu bazai ta6a mantawa ba in ya tuna abunda ya faru har dariya yake yi wani sa'in kuma yaji saukar hawaye, wannan ba kowane lokaci bane face lokacin da junaid yana da kananun shekaru, idan suka je masallaci tare dashi suke zuwa saiya bari an kammala salla an natsu liman na kora addu'a, sai shi kuma ya ɗaga hannayen shi sama ya ɗaga murya yana cewa "Ya Allah ya Allah kasa na riga Abbana mutuwa da ƴan uwana,ya Allah kafara ɗaukar raina kafin nasu," a lokacin kowa mamaki ya kama shi jin abunda ƙaramin yaron kecewa, har wasu ke tambayarshi dalilin dayasa yake son ya riga abban nasu mutuwa da yan uwan shi sai cewa yayi "Saboda idan na riga su mutuwa bazan ga tasu mutuwar ba in tazo,zuciyata zata samu salama akan na rasa su da raina," gaba daya mutanen dake a masallacin abun ya basu mamaki sosai, kuma ka'ida ne duk in suka je masallaci tare dashi dole liman ya jira shi ya kammala addu'o'in shi mutane na amsa mashi da ameen, kafin shi liman yayi tashi addu'ar saboda rigimarshi,
  Murmushi abbansu ya saki lokacin daya kammala tunanin nashi aranshi yace "Allah yabar mana kai junaid,ni kuma banaso naga mutuwarka nafiso nariga kowannan ku mutuwa don bazan juri ganin gawar ɗaya daga cikinku ba a kan idona," jikin shi a kasalance yake wannan zancen zucin,

  Wayarsa ce ta soma ringing daga cikin aljihun rigarsa ta yadi, cikin sauri ya zura hannu ya ɗauko ta tare da duba sunan mai kiran nasa sunan AMMI ne ya bayyana akan screen din wayar hakan na nufin mahaifiyarshi ce Ammi ke kiransa

   Nan da nan ya shiga natsuwarshi tare da ɗaga kiran ya kara a kunnan shi ya zabga sallama,
  daga can bangaren Ammi ta amsa mashi sallamar sannan tace"yaro na ya kake ya kuma jikokin nawa? Naji abunda ya faru da fawan shiyasa ma na kira don na tambayi ya jikin nashi,
   Tamkar yana agabanta cikin biyayya ya soma magana "lpy lou ammi suna cikin ƙoshin lpy,amma ba zaki zo gida ki duba jikin nashi ba?
  "Hmmmm ni me zanzo inyi agidanka? Ae yafi ƙarfi na, daga nan ma zan iya yi masa ya jiki ba sai na kwaso jiki nazo ba balle inga abun tashin hankali abun kunya,'
   nan da nan fuskar Abban nasu ta canza jin abunda tace,
   "Ammi dan Allah kidaina faɗin hakan bana jin daɗi saboda me zaki ce gidana yafi ƙarfinki bayan nikaina a ƙarƙashin ikonki nake ke fa kika haife ni, kuma wane irin abun tashin hankali da abun kunya kike magana akai"? yayi maganar fuskarshi a yamutse,
  tsoki taja tamkar zata fasa screen din wayar sannan tace "babu wani iko da nake dashi akanka hussein! Tunda har ban isa nasaka abuba kayi, wato son ƴa'ƴa ya rufe maka ido ko? ka daina ganin kowa da gashi? ba yarda banyi dakai ba akan ka tattara ƴa'ƴan nan duka ka haɗasu ka aurar kaƙi jin maganata, ka tara ƙattan maza,garada acikin gida sai sinturi suke yi acikin gidan ka,kaine jagoransu kai Gwauro su kuma tazurai gasu nan jibga jigba dasu kaƙi aurar dasu, daga anyi magana sai kace baka son ka takura masu ko kace ba su isa suyi aure ba don ka rainawa mutane hankali, dukansu kaf babu wanda in aka aura masa mace bazai iya yi mata ciki ba hatta wancan shagwa6a66en daka sangarta.......'

  runtse ido abbansu yayi tare da saurin cewa "Ammi dan Allah kidaina fadin hakan, aure fa lokaci ne kuma in yayi duk zan aurar dasu ne.....'
   wani tsokin ta sake buga mashi kafin ta kuma cewa "haka kullum kake faɗamin, narasa meyasa ƴa'ƴana duk basu jin maganata,daga kai har azeeman da wancan fitsararren da yayi hijra yabar ƙasar batare da sani na ba, ban ta6a tunain hussein zaka yi mun haka ba saboda duk kafi yi mun biyayya acikinsu amma yanxunn. .....' kukan da ta fashe dashi ne ya yasa ta kasa ƙarasa maganar nan take hankalin abbansu ya tashi, muryarsa har rawa take yi wurin cewa"Ammi dan Allah kidainamun kuka, ke fa mahaifiyata ce saboda me zakiyi mun kuka, hakan zai iya jefa rayuwata cikin matsala,dan Allah kidaina na roƙe ki mommyna indai akan wannan maganar ne yasa kike mun kuka wlh ashirye nake da nayi maki biyayya koba da son ransu ba, zan aurar dasu ne kawai saboda farin cikin ki !!!!!

79.
  jin abunda yace ne yasa ta sassauta kukan nata tace "yaushe kenan zaka aiwatar da hakan? kasan natsufa sosai kada na mutu ba'ayi auran nan ba, dan Allah hussein ka tattarasu duka ka aurar a lokaci ɗaya in har kayi mun hakan zan shaida cewa kai hussein ɗinane dana haifa,'
   Ajiyar zuciya abban nasu ya sauke yana kara gyara wayar a kunnan shi yace "Insha Allah ammi nan bada jimawa ba,amma ki ban time saboda yanzu muna cikin fargaba game da waɗanda suka kaima su fawan hari,kin san sunce fansa suke ɗauka,kuma babban tashin hankalin ma maca ce AVENGER ɗin,'
  shiru ammi ta ɗanyi kafin tace "Shikenan hussein,nima na shiga damuwa dana ji hakan,dama nasan dole hakan ya faru saboda mahaifinku kafin yabar duniya ya tara maƙiya sosai kasancewarshi kwararren jami'en Soja sun halaka dubban masu tada ƙayar baya a ƙasar nan, shiyasa nake tunanin ko daga 6angarensa ne maƙiyan suke son ɗaukar fansa,duk da nasan cewa wannan mai shuɗin idon baya rasa maƙiya don mutun ne mai haɗarin gaske shima baya gajiya da kame ƴa'ƴan mutane yana kaisu lahira, kaga kuwa dole su ɗauki fansa suma,yakamata kasanya tsaro sosai agidanka, kuma akwai shawarwarin da nakeso na baka,"
   Abba yace "Ammi dan Allah kixo gida mana,ina ga zaifi in kika zo sai mu zauna mu tattauna akan matsalar tunda wannan abun ya shafi zuri'armu, kuma nama fi jin cewa akaina abin zai ƙare tunda ni ne na tara ƴa'ƴa,"
   Ammi tace "shikenan zan fidda lokaci nazo insha Allah, amma inaso ka sani in zanzo saina tattara ƴan matan family ɗinmu gaba ɗaya na kwaso su don suzo ayiwa ƴa'ƴanka baiko dasu,"
  dariya kawai abba yayi yana sauraronta sun jima suna fira kafin daga bisani su kayi Sallama 😊
  ya ajiye wayar gefen shi yana ɗan murmushi,
   A can kuwa junaid na isa ɗakin da fawan yake kwance yana bacci, cike da tausayi yake kallon shi yadda yake jan numfashi da ƙarfi da ƙarfi,
  ƙarasawa yayi tare da hayewa saman gadon yayi zaman cin tuwo tare da zabga uban tagumi yana kallon shi hawaye na zuba a fuskarshi,
  Jin shessheƙar kukan junaid a kunnan shi yasa shi farkawa daga baccin da yake yi, ya buɗe idon shi a hankali yana kallon shi, yarda ya tallabe fuskarshi hannu bibbiyu ya tasa shi gaba yana sharar kwalla,a hankali fawan ya furta "junaid "
  Kallon shi kawai junaid yake yana cigaba da matsar kwallo,hankalinsa ba ƙaramin tashi yayi ba ganin yarda jikin fawan yayi ruɗu ruɗu da bulali wurin yayi jawur ya faffashe duk da anyi masa dressing na wurin an shafa masa magunguna,ga kuma ɗinkin da akayi masa a chest ɗinshi,
  dakyar ya daddage ya tashi daga zaune yana fuskantar junaid ɗin daya tasa shi gaba,
    "Junaid," fawan ya sake ambaton sunan shi a karo na biyu ganin yarda ya zabga tagumi yana kallon shi hawaye na zubowa gefe da gefen fuskarshi, zama su kayi suna fuskantar juna, kallon shi kawai junaid keyi batare da yace uffan ba,
  daƙyar fawan ya ƙaƙaro murmushi yana kallon shi, hannun shi yakai tare da shafa gefen fuskar junaid yace "bari nabaka wani labari ƙanina,"
junaid ya zuba mashi ido yana sauraron shi,
  fawan yace "lokacin da waɗannan miyagun suka ɗauke ni ko, suka shiga dani wani ƙogon dutse mai rikitarwa, suka ban za6i biyu, su kashe ni ko su azabtar dani wanne nakeso, kasan me nace masu? ya fadi yana kallon shi, girgiza kai junaid yayi alamar a'a,
  Fawan yaci gaba da cewa "a lokacin kai kawai ka faɗo mun araina, aranar da zamu tafi kai ta zabga kuka kana cewa babu inda zamuje ƙafarka ƙafarmu dakyar abba ya shawo kanka, ka tuna abunda ka faɗamun lokacin?
  shiru junaid yayi yana tuna lokacin daya cakumi rigar fawan yana ce "ya fawan kayimun alƙawarin cewa zaka dawo araye inaso na sake ganin ka,' a lokacin fawan yace mashi "junaid ae tafiya ba mutuwa bace, insha Allah zan dawo araye in Allah ya yarda," murmushi junaid yayi tuna wannan
  shima fawan murmushin yayi sannan yaci gaba da cewa "saina ce masu ni bana tsoran mutuwa, ban isa na hana kaina mutuwa ba in lokacina yayi, kamar yarda kuma baku isa ku hana kan ku mutuwa ba idan tazo maku, sai ɗaya daga cikin su yace mun "Ka za6i ka mutu kenan? mu kashe ka kawai? Saina girgiza kai nace "a'a ku azabtar dani kuyi mun duk irin hukuncin da zakuyi mun amma kubar ni da raina saboda akwai ƙaramin ƙanina da nayi ma alƙawarin cewa zandawo da raina, inaso na cika mashi wannan alƙawarin nasa na gani na araye, bana so na karya mashi zuciya nafiso ko mutuwarce ma to na mutu agabanshi yadai ganni da raina...............' dakatawa fawan yayi da maganar saboda hawayen da suka zuzzubo mashi, junaid kuwa tuni ya fashe da wani irin matsanancin kuka mai cin rai,
haɗe kansu su kayi wuri ɗaya suna faman shessheƙar kuka atare,
  dakyar fawan yaci gaba da cewa "Shine suka bankamun kayan maye sannan suka ɗaure ni tamkar dabba, su ka dunga zuba mun bulali da kaca a jikina har saida suka ga jini na zuzzuba ajikina amma hakan bai ishe su ba, ba don su babban yayan mu sun zo ba to da tabbas kashe ni sukayi niyyar yi a lokacin, Amma alhamdlh naji daɗi sosai da Allah yacika mun burina na ganin na rayu don na cika maka alƙawarinka......
.. murmushi junaid ya saki tuni ya ji sanyi ya ratsa mashi zuciyarsa,
  janye kansa yayi daga na fawan sannan yace "kana jin yunwa in kawo maka abinci"?
   girgiza kai fawan yayi tare da cewa "junaid a ƙoshe nake,ɗazu azmee ta haɗamun kakkauran tea tare da fruits na sha,naji daɗin su sosai,"
   "Bari nabarka ka huta sosai, na katse maka baccinka, amma ka sani zan dawo don atare zamu kwana," yayi maganar yana ƙara jaddada masa ayayin da yake sauka daga saman gadon,
  Murmushi kawai fawan ke bin shi dashi harya fice daga ɗakin,komawa yayi a hankali ya kwantar da bayansa saman filonsa tare da lumshe idon shi,
   Cikin sauri junaid ya fito tare da tunkarar hanyar fita saboda tunawa da sehrish wadda ke a school, lokacin tashin su yayi gashi time na salla na kokarin wuce shi, yana dab da fita daga ƙopar Amani ta kwada masa kira, dakatawa yayi tare da juyawa yana kallon ta da murmushi a fuskarsa, cikin sauri ta ƙaraso gab dashi tana cewa "ina zaka je ne? Junaid yace "inaso zance masallaci ne nayi sallah, daganan zan wuce na dauko sehrish daga school,"
  ɗan jinjina kai tayi kafin tace "wannan yarinyar da muka gani ɗazu itace sehrish"? Ta tambaya tana kallon shi duk da tasan akanta yake magana
  "Yeah itace," ya bata amsa atakaice tare da fucewa yana cewa "Sauri nake aunty amani time ɗin sallah zai wuce ni,"
   Juyawa amani tayi tana jinjina kai, a ƙagare take da junaid ya dauko yarinyar daga school saboda tana son ta sake ganinta har ma ta yi magana da ita,
*wannan kenan*😍👍


**************************

Har suka koma Class jikin sehrish a sanyaye ita kuma amrish fuskarta ta nuna alamun damuwa sosai game da abun da zeenat tace mata, gaba ɗayansu dae babu daɗi har suka taso daga school ɗin,tsayawa su kayi daga wajen school din sai ga drivern Amrish ya ƙaraso, juyawa tayi ta kalli sehrish tace"Ni zan wuce,sai mun haɗu gobe in Allah yakaimu,"
  Jinjina kai sehrish tayi tare da cewa"Allah yakaimu lpy,"
  "Ameen" ta amsa mata sannan ta wuce cikin motar,
  ta jima a tsaye tana jiran ƙarasowar motar junaid dalilin dayasa bata hau bus ba kenan saboda tasan dole yazo ɗaukarta,masu motoci saiyi mata tayi suke don tazo su rage mata hanya amma taƙi yarda tahau motar kowa saboda tasan cewa ba kowa bane zai ɗauke ta don Allah ba,
tana cikin wannan tsayuwar ta hango motar junaid ya shawo kwana,murmushi ta soma saki tamkar tayi tsalle don murna, tunkan ya ƙaraso ta tunkari motar da sauri,
  yana tsayar da motar ta sanya hannu ta buɗe motar sannan tashiga ciki tare da rufe motar,
  juyawa tayi ta kalle shi tare da cewa "ka manta dani ko"? Ina ta faman jiranka,"
   ɗan murmushi yayi yace "am sorry ba da son raina ba reesh, kina araina ynx ma daga mosque na wuto nan,' ya ƙarasa maganar yana kallonta, bin fuskarshi tayi da kallo alamun damuwa ta gani sosai atattare dashi,tuni itama taji zuciyarta babu daɗi, cikin sanyin murya tace "junaid kayi kuka yau ko? kuma kana cikin damuwa"?
   jinjina mata kai yayi alamar eh,
  ɗan 6ata fuska tayi tare da cewa "dan Allah junaid kadaina sa damuwa aranka wlh bana so, natsani naga mutun mai cike da farin ciki irinka a Yanayi na damuwa,'
   A kasalance yace "don't worry ur self,zan daina ne reesh da zarar nasamu abunda nakeso, ki sani acikin addu'arki da kuma sauran ƴan uwana,'
  "Insha Allah junaid bana mantawa da kowannan ku acikin addu'a ta," ta fadi tana jaddada masa maganarta,
   "Yanzu kayi mun dariya in gani kona samu kwanciyar hankali,"
  tunkan takarasa maganarta, ya wage bakinsa yana dariya,bin fararen haƙoransa tayi da kallo a jere tsaf suke tamkar mai tallar maclean saboda kyal ɗinsu, ga 2 dimples dinsa da suka lotsa sosai,
  Yatsanta takai acikin dimple ɗinsa ta zura shi saboda burgetan da yayi, sun jima suna shiririta acikin motar kafin ya tayar da motar suka miƙi hanya, cike da nishaɗi suke sauraron waƙar da junaid ya kunna masu ta lilin baba,natsuwa yayi a hankali yake driving yana sauraron muryar rishi dinsa dake bin waƙar
  "Kaine zuciya take ta yabo🎶kaine nawa in da rai da rabo, amanar zuciya ka damkeee, da kaine zanyi Wuff, zanyi wuff zanyi wuff🎶🎶
  Fashewa da dariya junaid yayi saboda daɗin waƙar da yaji, sai yaji tamkar dashi take, musamman da tadinga nuna shi da hannu tana cewa(dakaine zanyi wuff)
   Tana kai baitin ƙarshe shima ya ɗauka,
   "Ke ce zuciya take ta yabo kece tawa inda rai da rabo,amanar zuciya ki damkeee, da kece zanyi wuffff !🎶
   Zuba mashi ido sehrish tayi tana kallon shi, yana driving yana raira wakar kuma yana ɗan waiwayon ta,
  gaba ɗaya sun shagala basuyi aune ba, suka ji wata mota a bayanzu ta bugi motarsu da karfin gaske,ƙarar da sehrish ta saki ne yasa junaid sakin sitiyarin motar gaba ɗaya, aikuwa nan take motar ta karkace ta nufi wata tamkekiyar bishiya da gudun gaske,
  Waro ido sehrish tayi tare da cewa "Junaiiiid !! Innalallahi wa'inna ilaigirraji'un,
  Ƙanƙame shi tayi ajikinta saboda gaba ɗaya yagama rikice wa, gaba ɗaya sun ƙanƙame juna, maimakon Sehrish ta taimaka mashi ya rike sitiyarin motar yayi control dinta, Amma saita janyoshi jikinta ta kankame suka bar motar Tana control din kanta,
   Cikin ikon Allah motar ta kashe kanta adai dai bakin bishiyar ƙiris ya rage su gabje ta da ba ƙaramin buguwa zasu yi ba,
   Ajiyar zuciya suka shiga sauke wa tare da dagowa atare suna kallon bishiyar, Allah ya takaita wahala da motar ta kashe,
   Sai faman zazzare Ido suke Yi su duka biyun, sun ji kamshin mutuwa, juyawa Sehrish yayi tare dasa hannu ta zuge glass din motar Don taga wanene ya bugi motarsu,
  wata bakar motace Mai black tunted kirar range Rover, Kamar jiranta suke ta leƙo,suma na cikin motar suka zuge nasu glass din motar,
  Gabanta ne yayi mugun bugawa daraaam !! Ganin mutanen dake cikin motar, giggan Yan iska ba Imani a fuskarsu bakeke ne wulik, kana ganinsu kasancewa turo su akayi, da gangan suka bugi motar Junaid din,"
  duk Tasha jinin jikinta, ɗaya daga cikinsu ne ya ɗago mata hannu tare da cewa"hi We're sorry guys mun bugi motarku batare

30 / 80