Gishirin Zaman Duniya Book 1 Mrs Bukhari

Author :  Badiat Ibrahim Mrs Bukhari Category :  Read Hausa Novels

Chapter   9 / 33

24K to 27K   out of 98.4K words

gama gulmar. Da sauri ta saki labulen nata. Tare da sauke
kanta.
"Dama nasan ko me ake ciki kece mara gaskiya. munafuka mai ta da husuma. Amma Abokiyar
husumarki ta nanan zuwa, 'yar sarkin magulmata." Wucewa ya yi ya barta a wajan tare da
ficewa a gidan. Ita kuma ya barta da cizon yatsa.

Sadiya
Ahankali muke ta fe. Aliyu ya jera mun sannu ya fi sau a k'irga. akan doguwar kujerar falona ya
sauke ni. Hawaye kuwa bai bar.zuba a idanuna ba. tsugunnawa yayi a gurwarsa ya ce.
"Anty ki yi hak'uri dan Allah da dukkan abubbuwan da suka Faru. Goggo ba ta tsaya ta yi
bincike bane, kuma zan d'auki tsattsaran mataki akan Yaya Dauda, bazan bari ya bige ki a
banza ba.Amma me ya had'aki da Yaya Dauda?.
A cikin kuka na bashi labarin kab habaice habaicen da Hasiya ta sani a gaba da shi. Har zuwa
wanda tai mun yau. Shiru yayi ya na kallona k'ur, kallon da duk shekaruna na kasa fassarashi.
na ce.
"Yanxu sakin nawa zaka yi ko?"
Bansan sanda bakina ya furta hakanba. Domun duk abunnan da ake ciki maganar sakin ya
girgizani. Ban sani ba ko dan ban jima da yin auran bane. Bana son duniya ta kafa hujja a kaina
wajan zagin 'yan boko. Na dai tsinci kaina cikin tsoron SAKI. tunda nai wannan maganar ya ke
bina da kallo kawai. Ni kuma kunya duk ta kama ni. "Bari in hura kara in d'aura miki ruwan zafi ki gaza jikinki. zanje Lamba in siyo miki magani a
kemis. Da sauri na ce. Akwai kalanzir a risho. Magani kuma i na da shi a box d'ina."
bai ce komai ba ya fita. hawayen fuskata na share. zuchiyata a cikin zugi da tashin hankali ta
ke. Haka

Aliyu
Aliyu ma. Tunda ya d'aura ruwan wankan a kan risho. ya ke tsaye a kitchin din. sai tunanin
mafita kawai yake yi. shi bai ji cewar zai iya sakin Sadiya ba. baisan alkhairin dake cikin auran
shi da ita ba. Kuma a zahiri Sadiya ta kai macen da ko wanne namiji ya sota, ya kuma ji yana
son kasancewa da ita. bugu da k'ari gata 'yar uwa ta jini, wacce bai kamata a yasar da'ita
ba.Amm ya na auna kalaman da Goggo ta jefe shi da shi. cewar indai nononta ya sha ya rayu
toh dole ya saki Sadiya. Ajjiyar zuchiya ya sauke, ya rasa tudun dafawa, balle makamar da zai
kama. Ruwan ya juye mata ya sirka. har ban d'akin ya kai ruwan.

Sadiya
ya shigowa yayi ya sameni da box d'ina da mirro ina dressing bakina da Goggo ta fasa mini.
Zama ya yi yana kallona k'uri yace."
"Ashe da likita na ke tare ban sani ba. Kai masha Allah. Murmushinshi ya fad'ad'a.
Bance dashi komai ba. sai da na gama tas nace.
" 'yar koyo dai waneni da likita. murmushi yai mun.
"Ki je ki yi wankan. zan je in dawo yanzu, ina mai baki hak'uri a karo na barkatai, kuma ki sani
ina tare da ke." fita ya yi. ni kuma na shiga toilet na dinga gasa jikina dan ko ina ciwo ya ke yi

mun, juyayin maganganun Goggo kawai nake yi, cike nake da mamaki. Wai dama ashe haka
lalurar jahilci take? Wallahi gara mahaukaci sau dubu akan jahili.

Aliyu
Fitarshi ke da wuya ya zarce gidansu kamilu.
Kamilu ya fito k'ofar gida, Sai kawai ya ga abokinshi a cikin yanayin tashin hankali mara
musaltuwa. Dafa kafad'arshi yayi dan bai ma san Kamilu ya fito ba.
"Aliyu lafiya kake kuwa na ganka a cikin irin wannan yanayin, Meke faruwa? Aliyu ya juyo ya
kalli kamilu, idanunshi sunyi jawur, ga wani ciwon kai dake addabarshi, hatta d'and'anon
yawunshi ya gurb'ace tsabar tashin hankali.
"Kamilu Baba ce ke son birkita mun fissafi na. Waifa magana take yi akan sai na saki Sadiya,
kuma ni bazan iyaba wallahi." Hannunshi Kamilu ya rik'o zuwa cikin gidan na shi. Kai tsaye su
ka shiga d'akin da anan ya ke. Kasancewar matanshi biyu ne. Sai da su ka zauna Kamilu yace.
"Saki kuma daga dawowarka. wani abun Sadiyar ta yi ko me?" Labarin komai da komai Aliyu ya
ba Kamilu ciki harda abunda ya faru yau."
"Tabb aiki ja kenan. Amma tunda Sadiya ta amince ta zauna da kai a wannan k'auyan namu da
mu kanmu muke gudunshi. Ai kuwa ta cancanci a yabeta. Ni nasan duk akan khadija Baba ta
ke yin wannan abun. Ita bata san khadija ta canja ba shiyasa." Aliyu ya gyara zama ya ce.
"kamar ya Kamilu wanne irin canjawa ta yi?"
" Aliyu nasan k'ila abun bazai xo maka da sauk'i ba ko. Amma sau uku ina had'uwa da khadija
da mahaifiyarta a wajan rabe. Amma su ba su ganni ba. Duk fad'in k'auyannan waye bai san
Rabe ba?. Bazan bari ka cutu ba, dama naso sai ka huta sannan zan sanar maka, yanayin da
ake cikine yass dole na sanar maka yanzu. Aliyu ya girgiza da jin wannan labari. take har
idanunshi ya sake kad'awa yayi jawur, har wata jijiyace ta faso a goshinshi. yace.
"Indai har na yi bincike na gano abunda ke kai khadija da mahaifiyarta wajan Rabe. Toh Aure ni
da khadija babu shi. Yanxu mu kawar da wannan matsalar Kamilu Baba na can tana jiran in
kawo mata takaddar sakinne fa. Kamilu yace.
" Ni ina ganin muje mafara wajan Iya mai Tubani. A ganina ita ce kawai za ta iya dakatar da
Baba akan abunda tai k'udiri."
"Kamilu Baba mahaifiyata ce na santa fiye da tunanin mai tunani. Iya mai Tubani kuma k'anwa
ce ga gyatumarsu Baba. Baba babu wanda ya isa ya sa ta yi hakuri akan wannan sakin, kasan
muguwar tsanar mahaifiyar Sadiya dake zuchiyar Baba kuwa? ina tunanin ubangiji ya bani
Sadiya ne dan mu zama silar kawar da duk wani gaba. Ni tunani nake yi ko in mai da Sadiya
gidane zuwa komai in ya lafa sai ta dawo, wallahi Kamilu ina son Sadiya. Amma me ka ce?
Kamilu yace.
"zuwa gidanne bazai mata kyau ba Aliyu. Sati guda da.Aure a ganta a gida, Hakan zai iya b'ata
mata suna. Sannan mahaifiyarta abun zai mata ciwo. Kaga da haka sai zumunci yai ta
lalacewa. Mu jarraba zuwa wajan Iya. In yaso mu tafi da Sadiya. Ko a can ne sai ta zauna xuwa
wani lokacin." A hakan su ka samu matsaya. Mik'ewa Aliyu yayi yace. "Ka shirya bari in sanar da ita ta shirya sai mu tafi kawai." Kamilu ya dafa kafad'ar shi yace.
"Kar kayi sake lu'u lu'un da rabbi ya baka ya subce a hannunka. Ka yi iya yinka, Saki dai a
hannunka yake. Kuma ka k'arfafi guiwarka karka basu damar karaya. Sadiya alkhairice.
Ficewa yayi a gidan Kamilu. Gida ya wuce da Sauri, kuma cikin k'arfin guiwar da Kamilu ya aro

ya yafa mishi.

Sadiya
Ina zaune a saman kujera. ina karanta wasik'ar jaki. tare da yin lissafin dokin rano. Sallamar
Aliyu ce ta katsemun tunanin da na ke yi. Idanamu muka zuba ma juna, murmushi ya sakar
mun.
"Anty ki shirya za mu d'an fita yanzu. Bari na sake kaya."
uwar d'aki ya shiga. Take zuchiyata ta shiga bugawa da k'arfi. Harya fito ina zaune a wajan cikin
muryar kuka nace.
"Aliyu ka sake ni ko. Amma me nayi maka toh?" lumshe idanu yayi yace da ni.
"Ban sake ki ba Anty, babu wanda zai iya kwace mun ke. gidan Iya mai Tubani zan kai ki ki d'an
zauna acan zuwa wani lokacin. ki yi hak'uri da yanayin da muka riski kan mu a ciki. amma ki
sani Ni bazan iya sakin ki ba." jikina a mace na shiga cikin d'aki tare da tattare 'yan suturu na
nasa a k'aramar jaka. mayafi na yafa na fito. kallona yayi da kyau yace. "Baki da hijab ne?" Da mamaki nadubeshi sannan nace.
Ina da na yin Sallah."
" Ki je ki saka shi. Daga yau karna kuma ganin kinsa mayafi. Ni namiji ne mai tsananin kishi
sosai." mamaki Aliyu ya bani. Yanda ya b'ata rai bai ko ji nauyi na ba. Yake bani umarni. Bani da
yanda zanyi haka na koma na zumbulo hijab har kusan k'asa.
Bai ce komai ba. Jakar hannuna ya karb'a ya shige gaba. ni kuma ina biye dashi a baya
Ta k'ofar baya mu ka fita. Kamilu ya na tsaye a gindin bishiya yana jiranmu. Da isowarmu muka
wuce. Babur muka hau har zuwa bustop. Daga nan kuma mu ka hau motar da zata kaimu
Mafara k'aramar hukuma.
Ina zaune a kusa da Aliyu jikina yana gugan nashi. musamman in an shiga kwazazzabo. wani
irin yanayi nake shiga in jikina ya manne da nashi. Duk da suna d'an jefa hira shi da kamilu
Amma kuma hankalinshi yana kaina. Ina kallon irin satar kallona da ya ke yi. Ni kuma tunane
tunane duk ya cika mun kaina. A haka har muka iso mafara. Babur muka sake hawa har zuwa cikin anguwar su Iya. Sukam naga suna da makarantun
gwamnati da ma babban Asibitin gwamnati, ga wutar lantarki.
sai kalle kalle na ke yi. Ina ganin mata da k'ananun yara. ga 'yan makaranta an tasosu su na
tafe suna wasanninsu. wasu ko takalmi babu, wasu kuma kayan makarantar duk datti. wasu
nasu a yage, Abun gwanin tausayi. Ta ya ma yaro zai yi karatu mai kyau. Jikinshi duk tsami da
datti, makarantar duk a rub'e ajujuwan ko bencin zama babu dana hango,ga wani zarni dake
tashi na bayan gidan makarantar, wanda kab rabin anguwar zarnin ya damesu, ina ga malamai
da d'aliban cikin makarantar? Shi yasa manyan masu muk'amin k'asar suke sanya yaransu a
makarantun kud'i,domun sunfi kowa sanin me suka shuga a makarantun gwamnatin nasu. Ya
ilayi ka tab'a zukata shuwagabanninmu su dube mu. a kofar wani gida muka sauka. ni dai ina
biye da su har cikin gidan, sai kalle kalle nake yi. Kai kallo na k'auye."


mrs Bukhari

ANAN NA KAWO K'ARSHEN FREE PAGE. KI BIYA KUD'INKI DANJIN YADDA ZATA

KASANCE. WANNAN TAFIYAR TA
*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. ‍♀️*


1, *MU GANI A ƘASA...*
_Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*
_Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*
_Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*
Badi'at Ibrahim
_Mrs Bukhari_

5, *AUREN WATA TARA*‍❤️‍
_Miss Hajo_


Guda biyar 1k
Guda huɗu N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda ɗaya N300

*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*

0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.

Domin tura shaidar biya

0810 433 5144

Masu tura katin MTN

0814 179 9224

Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.

0817 952 3215

Guda biyar 1000f
Guda huɗu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ɗaya 300f

*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* ‍❤️‍


*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*

Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -

*Enter your name:* (Cikakken sunanki)

*Enter your mail:* (Email ɗinki)

*Enter an username* (Sunanki)

*Enter your password:* ( misali 12341234)

*Confirm password:* (misali 12341234)

Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks.

*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google
za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.

*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.

Masu iPhone

Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com
G Z D
MRS BUKHARI
21~22


Da sallama a bakinmu dukkanmu mu ka shiga.
Iya ta tsakar gida ta na k'wad'a zogale da rama. sai da yawuna ya tsinke da ganin wannan

k'wad'on.
" A ahhhh Aure yau igiya goma sha biyu. Yaushe a gari inji mak'i bak'o. masu kwalli a ido Ai sun
san da dawowarka, amma ni da yake ba'a auran dani ai saida ka yi kwantai." Dariya Aliyu yayi
ya ce.
"Da surutu dama nasan zaki tarbeni ke irin auran naki kenan. Kinga kishiyarki magana bata fiye
damunta ba, amma ke magana ta yi miki yawa." Dariya Iya ta yi. Tabarma ta nuna mana.
" Ku zauna. Kamilu baka da mutumci Ace rabon da in sanya ka a ido. shekara sama da hud'u.
Tunda mai gidan ya tafi madina karatu ka d'auke k'afarka a gidannan sabida Allah dai_dai
kenan?. Dubana ta yi tace.
" uhmm baiwar Allah sannu da zuwa. ganin mazajennan nawa ne yaimun dad'i sosai. Kamilu
wannan itace Amaryar da aka ce ka yi? Sai yau Allah yayi n ganta. Kai amma kuwa ka mori
mace, ji mace a dire. Kamilu yace.
"Ki bari mu gaisa tukunna. Nina soma gaisheta dubana take yi da kod'addun idanunta da baza
kai zaton tana gani ba ma, gasu fici_fici kamar k'wark'wata.
"Ai wannan kamar Sadiya ta wajan Adamu ko? Nayi matu'kar mamaki data kama sunana. Aliyu
ya ce itace.
Kuka Iya ta fashe da shi, tana yi tana sharce majina, ta ce.
"Allah ya jik'an Adamu d'an boko mai mata 'yar boko. yaro mai hakuri da yakana. kai Adamu ya
sha wahala a Hannun dangi da suka sashi a gaba. Dan kawai ya auri 'yar boko, musamman
Asabe. Ni banga laifin Aisha ba. Tunda mahaifinta shi ya d'aga darajar Adamu har ya shiga
gwamnati, Amma dangi sun d'aura ma Aisha wata iriyar jahilar tsana. Ke Sadiya taho in ji
d'umin Adamu a jikin ki, ko na ji sanyi, haihuwa mai rana kenan.
Hawaye ne su ka soma xubo mun. A karon farko da na ji yabo daga dangin Babana kenan akan
mahaifiyata, Aliyu ne ya girgizamun kanshi cikin sigar lallashi. Idanuna na lumshe. Ina isa inda
take na rungumeta mu ka ci gaba da kuka.Kuka nake rerawa mai tab'a zuchiyar mai sauraro.
Iya kuwa har da fyace majina. Mun jima a haka sannan ta d'agoni tace. "Yaushe ki ka zo Sadiya? rabona da ke tun kina 'yar shekara goma, nayi mamaki dana ganeki
ma. Ni kin sanni?" kai na girgiza mata. Wannan shine karo na farko da na soma ganinta a
rayuwata.
"Assha wannan illar ta rashin zumunci ce. zumuncinnan inma ba'ayi anan gidan duniya ba, ayi a
k'iyamar Allah. An hura wata iriyar muguwar gabar da tasa 'yan uwa suka mance da Adamu,
balle su waiwayi abunda ya bari. Yaron.arxiki mai kunya. Adamu shine mutum na farko da yayi
karatun boko a Raquma, dama na addinin mai zurfi. k'arfi da ya ji Sulaiman ya hana kowa
zumunci da iyalan Adamu. Shi na d'aurama laifin tunda shine babban banza. Asabe ita ba kai
bane da ita. shegen taurin kai da kafiya shiya sa ta auri ubanka ta k'are a wahale a gidan haya.
Sai da ubanta mai hula ya mutu ta samu matsuguni na kai."
Aliyu yace.
"yanzu ma fa Iya sabida ita mu ka zo wajanki. Wani al'amarine ya faru ina madina lokacin." Nan
ya kwashe komai da komai ya sanar mata.
Kuka ta kuma fashewa da shi har ta na bubbuga k'afa. cikin kuka tace.
"Amma Sulaimanu da Asabe sun yi Asara, sunyi fad'uwar bak'ar tasa, zan kuma b'ata musu
tura takai bango zan nuna musu ni uwarsu ce. Dan k'asa ta rufe idan Adamu iyalanshi har sun
kai ai musu wannan wulak'ancin saki fa? da data amince fa. akan bare Asabe zata sa a saki

d'iyar k'aninta? Jahilci masu gari, yau saina sa Asabe ta shiga hankalinta. Aliyu yace.
"yanzu haka Yaya Fatima ta na gida. Wai dole sai mijinta ya sake ta. Yau za su je gaban me
gari ma.
Nan ta mik'e tsaye tace.
"Haka asabe ta sake lalacewa? ta zama me kashe kashen Aure kenan, ko hauka tayi ne?. Ku
barni da su wallahi sai sun yi dana sanin zuwana gidan dan yau wallahi sai kowa ya zubar da
hawaye. Kai bacci ma sai naga dama za'ayi a gidan. Dauda da matarshi kuwa duka zansa
jama'ar gari su yi musu, Bansan yaushe Dauds ya zama sallamamme ba. Me gari ko ya baka
Dijangala ko kar ya baka duk d'aya. ga mata dirarriya mai k'ira mai kyau ka samu. Ni bazan so a
had'ata zama da kishiya bak'auya ba ma. Bazan yadda da wani k'arin Aure nan kusa ba.
Ta inda Iya ta ke shiga ba ta nan ta ke fita ba. Iya irin mafad'atan jinin sakkwatawannan ne. Har
wani hunguna hancinta ya ke yi tsabar fad'a. Aliyu da Kamilu sai farin ciki su ke yi da goyon
bayan da su ka samu a wajan Iya. Ni kaina banso maganar Saki ba har ga Allah. Ashe furucim
saki masiface ga duk macen da tasan darajar kanta ? Sai yanxu ne na soma shak'ar iskar
duniya. Kwad'on zogalennan Iya ta sa jikarta ta zuzzuba mana tare da kawo mana Dawo bako
sukari dan su a haka su ke sha, kuma sun saba.
" ku ci abinci sai mu hanzarta tafiya. Jikina bazai daina rawa ba har sai na ga Asabe a cikin
damuwar da ta fi damuwar da ta sanya ku a ciki, domun walahi sai hawayen Asabe ya k'afe
yau. Ba wanda ya ce mata wani abun. Ni dai zogalen na ci. na kasa sabawa da dawonnan na
sokotawa. Ba mu b'ata lokaciba muka kammala. Iya ta kwad'ama jikarta Hafsatu kira ta yi. da
sauri ta fito tare da tsugunnawa. cikin ladabi ta gaida mu. Iya tace.
" ki ciro mun kaya kala biyu a akwati ki sa a leda maza. Idan Ramatu ta dawo daga asibiti ki ce
mata na tafi RAQUMA ta kula da ku sosai. ko da Jikar Iya ta shiga ciki bata jima ba ta dawo da
leda a hannunta. Ni na amshi ledar. mu ka fita.
"iya Yaya Ramatu

9 / 33