Gishirin Zaman Duniya Book 1 Mrs Bukhari

Author :  Badiat Ibrahim Mrs Bukhari Category :  Read Hausa Novels

Chapter   23 / 33

66K to 69K   out of 98.4K words


"Ga zam zam da dabino ma, daya farka a tauna a cusa mai a baki, kuma a bashi zamzam ya
sha." Na sa hannu na amshi butar a hannun Goggo.H, ina jin dad'in yanda Iya ta nuna
kulawarta akan Hassan, Ni sai lokacin na tuna cewar ban yi musu adda'a ba. Lallai na tabka
kuskure babb." Dr ne ya isa wajan gadon da Sallama, Allura yai ma jaririn, sannan ya ba da sallahun magani
na.
Dana fito ne Iya ke mik'a mun, karb'a na yi na sha, sai na ci tuwon da Iya ta kawo, amma ba
dan inaso ba, so nake Hassan in ya farka ya samu abinda zai sha. Ina kwanciya Sai baccin
gajiyar nak'uda ya kwashe ni. Su Iya sun tausaya mun a halin da na ke ciki.
Ina bacci su Anas su ka zo, Anas ne yai ma jaririn hud'uba da Sunan Aliyu.
"Iya sunan shi Aliyu Allah ya raya."
Iya ta sa hannu ta amshe shi ta na kuka.
Bani na farka ba sai jefin taran dare, rabona da irin baccinnan tun Aliyu na da ran shi"

mrs Bukari ce
*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. ‍♀️*




1, *MU GANI A ƘASA...*
_Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*
_Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*
_Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*
Badi'at Ibrahim

_Mrs Bukhari_

5, *AUREN WATA TARA*‍❤️‍
_Miss Hajo_


Guda biyar 1k
Guda huɗu N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda ɗaya N300

*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*

0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.

Domin tura shaidar biya

0810 433 5144

Masu tura katin MTN

0814 179 9224

Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.

0817 952 3215

Guda biyar 1000f
Guda huɗu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ɗaya 300f

*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* ‍❤️‍


Instagram links

https://www.instagram.com/p/CgPTv1-oML6/?igshid=MDJmNzVkMjY=

Facbook group

https://facebook.com/groups/463653111781414/


Telegram links

https://t.me/+xYZCR9JY-aMzNDFk


*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*

Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -

*Enter your name:* (Cikakken sunanki)

*Enter your mail:* (Email ɗinki)

*Enter an username* (Sunanki)

*Enter your password:* ( misali 12341234)

*Confirm password:* (misali 12341234)

Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks.

*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google
za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.

*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.

Masu iPhone

Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com
G Z D
MRS BUKHARI
53~54



"Sadiya bashi nono bawan Allah tun d'azu ya tashi, ya d'an yi kuka kad'an" Kab'ar shi na yi a

hannun Goggo.
man zaitun da muka tawo da shi na bud'e. na goggoga a kayikan nonon nawa. Sannan na zura
mishi.
Addu'ar da d'axu ban samu nutsuwar yi musu ba, yanxu na yi mishi nashi. Goggo ta sanar dani
Aliyu aka mayar mishi.
Goggo a rink'a kiran shi Haidar. Goggo Hansatu tace.
"Babu laifi Sadiya. ni ina zuwa. Fita ta yi ta barni da kallon Haidar, fari k'al da shi, gashin kan shi
ja, haka bakinshi jawur da shi, a raina nace.
Ina ma zai tsaya a haka ba tare da yayi wannan kurajen da dabbara dabbaran ciwo a jikin shi
ba, da zan yi farin ciki. Murmushi na yi na shafi fuskar Haidar bawan Allah kenan, sai mama ya
ke sha, ni kuma zafin shan maman har can cikin raina na ke ji.
Washe gari da safe akai mana transpar zuwa asibitin cikin gari.
Dr ne ya amshi Haidar ya shiga da shi zuwa ciki.
waje mu ka samu ni da Goggo Hansatu mu ka zauna. Mu na wajan Sai ga Kawu ya tawo, shi
da Yaya Kabiru. Babu yabo babu fallasa su ka amsa gaisuwata, kawar da kaina na yi daga gare
su, dan k'iyayyar da su ke nuna mun ta yi mun yawa, kuma lokaci ma ya cika da zan bar musu
gidansu, Ina ji Kawu na fad'an garin yaya na haifi 'ya'yan k'azanta, yaran da ake samun su ta
hanyar, in mace na jinin al'ada aka sadu da ita shine ake haifar zabiya. Wannan a canfin da
hausawa su kai ma zabiya kenan, hakanne yasa suke ganin kamar k'abilar kirista sun fi
musulmai yawan haifar zabiya, musamman ma Inyamurai." Dr ne ya ne mi ganina, ina hawaye
na wuce su, sai zabga fad'a kawu ya ke yi, Yaya Kabiru na ta ya shi.
"Zauna madam"
Waje na samu na zauna, cikin k'arfafa guiwa da ya zama halayyar likitocin kwarai yace.
"Haidar kyakkyawa ne sosai, zan so ki kula da shi, da fatar shi, ta yanda ba zai samu kuraje da
k'onewar fata dama, dabbara dabbaran bak'i ba. Ko dan ma guje ma Sankarar fata da ke
addabar zabiya.
Duban shi nayi
"Dr in sha Allah in dai ina numfashi, kuma in dai akwai magangunam da zan yi ma Haidar
amfani da shi ba tare da fatar shi ta k'one ba. Toh ni kuwa ko nawa ne zan jure siya mai. Amma
Dr meye sababin da ke sa a haifi zabiya?
yace
"Good Albinism cuta ce da ake iya kamuwa da ita daga Iyaye, wanda abun ya shafi wasu
kwayoyin halittar da ke d'auke da rashin daidaituwa ta hanyar samar da melaninn. za a iya
yad'a shi ga yaro." Cikin fahimta nace
"Dr yaya zan yi in kare yarona daga kamuwa da sankarar fata?"
"Binciken ido da dermatological yana da mahimmanci, dan gyara lahani na gani da ke da alak'a
da cutar zabiya.
mutanen da ke da albinism, riga kafin rana yana da mahimmanci don guje ma had'arin ciwon
daji, sabida fatar su mai rauni ce sosai, kuma ta na kula da hasken UV. don haka kariya ga fata
da idanu na da mahimmanci. ya kasance ko da yaushe ya na cikin inuwa, tare da sanya tufafi
mai rufe jiki kirib. Sa tabarau dan kare ido daga hasken rana, sai shafa 50+index cream dan
yana taka muhimmiyar rawa. Akwai mayuka da sabulan da zan rubuta miki. Da su za'a mishi
amfani ko da yaushe.

B'angaren matsalar idanun shi kuwa, ku je zuwa nan da wata d'aya sai ku dawo dan a sake
dubawa, xuwa kafin lokacin idanun zai iya bud'ewa ya soma gani ba tare da mun yi mishi komai
ba." Godiya na yi mishi sosai. sannan na fito, Haidar na je na d'akko na fito.
Gida mu ka koma, abun mamaki sokotawa Allah ya yisu da canfi, nan fa labari ya karad'e
k'auyan na haifi yaran k'azanta, babu wanda ya xo mun barka, har matan gida, Goggo Asabe
da su Goggo Safiya ma, babu wanda ya zo. ranar suna daga ni Sai Goggo Hansatu sai matan
Kamilu ne kad'ai. Kamilu ya yanka ma Haidar k'aton rago, haka mu ka yi sunan mu, daga mu
sai mu. Bayan kwana biyu muka tattara ya namu ya namu, motar kayan da zata bi yanke cikin
jeji, ita mu ka bi, babu wanda yai mun batun gadon Haidar, haka na yi musu sallama ina kukan
tuno da Aliyu.

Kano state
Mama na zaune a tsakar gida, tana shirin had'ama Malam Kaka sob'o, mu ka shigo. Baki ta
rik'e.
"Hansatu kaddai har ta sauka?" Dariya Goggo Hansatu tayi.
"Tun yaushe har an yi suna ma, an samu Aliyu Haidar. Hamdala Mama ta yi, a baya na ta sunto
Haidar, wanda na rufe kirib, hular zata janye na yi maza na rik'e hannunta.
"Mama mu shiga daga ciki, Haidar ba ya son rana. Bata ce komai ba, mu ka shiga ciki. Goggo
Hansatu ta labarta mata komai, sai da ta yi hawaye.
"Ki yi hak'uri Sadiya komai mai wuce wa ne, yau ina Aliyu, baya kwanta dama ba? Toh haka za
a k'are a duniyar ma. ki kula da yaronki, ki samu nutsuwar shayarwa Babu komai. Hansatu kin
yi zumunci Allah ya biya ki."
Cikin kwanciyar hankali na ke shayar da Haidar, ya yi b'ulb'ul abun shi, gwanin sha'awa da shi,
kullum a k'unshe a cikin suturar da zata rufe mai jiki yake. K'awayena da basu samu damar
zuwa mun ta'aziyya ba, sun zazzo, har da abokan aiki na duk sun zo. cikin shekara guda Haidar
ya zama kamar yaron turawa, babu ko sofane a jikin shi, kuma yana gani da idanunshi, sosai
Haidar ke samun kulawa, sai da ya cika shekara biyu cib na cire shi a mama, yana gudun shi ko
ina, baki kuwa rairai. tsawon wannan lokacin babu wanda ya tab'a zuwa duba Haidar daga cikin
dangin mahaifinshi. Na koma bakin aiki na, a nan ne fa manaima su ka soma yi mun yawa,
amma ni kula da Haidar da aiki na ya fi mun komai. Couse gwamnati ta d'auki nauyin tura mu
'kasar India, bayan 'yan setin farko sun dawo. Tare da Haidar na tafi, couse ne da zai d'auke
mu tsawon shekaru biyu. Da hakan na samu damar jefa Haidar makaranta, tunda shekarun shi
uku a lokacin, muna gama couse d'inmu mu ka dawo najeria, a lokacin Haidar na da shekara
biyar a duniya. Ya sake yin mugun kyau, duk in da na shiga da Haidar sai ya samu masoya,
fatar shi ta yi kyau, dan acan k'asar India na samu wasu mayuka ba irin namu na gida najaria
ba, kuma sun amshi fatar tashi sosai.
Na murje na sake yin wani irin kyau, fatata ta murje sosai, na k'aro ilimi na kuma sake wayewa
sosai. Mama ta ji dad'in ganinmu dukkan mu, bayan mun nutsa ne sai na jefa Haidar a
makarantar firamare, da kuma islamiyya.
"Sadiya na zuba miki idanu in ga gudun ruwan ki amma fur kin k'i yin batun aure, sai hidima da
Haidar kawai kike yi, kinga kar mu zama abun zagi a anguwa ke ba aure ni ba aure, kinsan
yanzu kiwon mutane ake yi ba dabba ba. Ajjiyar zuchiya na sauke
Mama ba aure na k'i yi ba, ina tunanin yanda Haidar zai soma agolanci ne, amma da na yi

auren, akwai wani Dr Saminu da ya jima ya na biyiyata, tare kuma mu ka tafi da shi wannan
couse d'in, bayan shi akwai su da dama, Mama ba kowa ke iya auran bazawara me d'a ba,
kuma ya iya rik'esu dukka, ba tare da ya nu na ma wannan agolan banbanci ba, ni kuma akan
Haidar zan iya hak'ura da auran." "Dallah rufa mun baki, shashasha, akan ki aka soma yin aure a tafi da agola ne,ko so ki ke yi
sai bakin jama'a yai ma rayuwarki illah? tun wuri ki fito da mijin aure. wata d'aya na baki, in ba
haka ba za ki ga hukuncin da zan d'auka akan ki, shekarunki sama da arba'in " A zaune mama
ta barni ina tunani, Haidar na tuno da lokacin tashin su a makaranta yayi, ai ba shiri na fita da
sauri zuwa makarantar.
Da gudu Haidar ya iso wajena na, rungumeshi, mu na dariya.
"umma zo ku gaisa da Abbana, kullum ya na gaisheki. Shafa kan shi na yi.
Haidar ka bari sai wani lokacin mana. Fur Haidar yak'i, hannuna ya rik'e har cikin ofishin
malaman makarantar. Da sallama mu ka shiga. D'ago kai yayi mu ka had'a idanu, saurin kawar
da kaina na yi, dan ban cika son had'a ido da maza ba.
"Angle ga umma na."
Murmushi malamin yayi.
"Sannu da zuwa umman mu." Dariya na yi kad'an nace.
"yauwa sannu malam da k'ak'arin aiki. Ina jin labarinka a bakin Haidar, kuma na yi farin ciki
sosai da kake kula dashi, ya fad'a mun baka barinshi wasa a cikin rana. Ina godiya sosai da
kulawarka ga Haidar."
Kallona ya ke yi. Ba yaro bane dan zai iya ba ni shekaru fin goma ma.
"Babu damuwa umman mu, ai d'a na kowa ne, kuma na yaba da k'ok'arin ki dan inganta
rayuwar Haidar, zan zo gidan in sha Allah." Godiya na yi mishi, na kama hannun Haidar mu ka
tafi.
wasa wasa malam Safwan kusan kullum sai ya zo wajan Haidar, tare da hidimomin da ya ke yi
ma Haidar, Ahmad ma ya dawo waje na, kamar zai mai da ni ciki tsabar so, amma na kasa ba
kowa Fuska, Kamilu ma yayi halacci, dan yana zuwa duba Haidar sannan ya na bashi kulawa
dai dai da yanda zai iya. Ya nuna ya na son aure na, amma na nuna mishi yayi hak'uri, kuma
na gode da kulawarshi gare mu.
Amina ce ta haihu yau suna, daga wajan aiki na wuce" K'awayenmu na makaranta duk sun
zazzo, mu na zaune ana hira kawai sai ga Fatima, da k'aton cikinta ta shigo, sai tsokanarta ake
yi, Fatima ta ji kunyar ganina dan tunda Ahmad ya aureta ba mu sake had'uwa ba."
"Sadiya ke ce kika zama haka? Hmmm manyan mata. zama ta yi, na ce.
"Fatima ai fishi na ke yi dake, ace duk a cikin k'awayenmu babu wacce bata zo mun ta'aziyya
ba, sai ke." kai ta sosa.
"Wallahi ni kunyar abunda na yi miki ne ya sa na kasa zuwa. Dariya na yi.
"Haba.Fatima ai matar mutum kabarinshi, yaranki fa hud'u ga na biyar a cikin ki, da ya za'ayi da
rabon yarannan? komai ki ka ga ya faru, ubangiji shi ya tsara faruwar shi. Dad'i Fatima ta ji, ta
sake mu kai ta hirar mu abun sha'awa. Da na tashi tafiya ma ita ta yi mun ta yin mu je Ahmad
ya rage mun hanya. "Ahmad ka ga fa mutuniyar mun shirya, kuma ta fahimce ni sosai, shi dai Ahmad ta mirror ya ke
kashe ni da mayyar soyayyar shi, dan shi d'in gwanine fagen iya soyayya. yace
"Na ji dad'in wannan had'in kan na ku sosai. Hira mu kai ta tab'awa, Fatima ya soma ajjiyewa

sannan ya kaini k'ofar gida.
"Sadiya so ki ke yi son ki yai mun illah ko me? Sai bani wahala sonki ya ke yi, ke kuwa sai k'ara
kyau ki ke yi abunki, ni ne fa Ahmad mai yawan sonki da k'aunarki, kuma na yi miki bayanin ba
laifi na bane fasa auranki da na yi ba. Hannu na d'aga mishi.
"Dakata Ahmad kar ma ka soma cewa haka, dan in ba da sanin ka hakan ta faru ba, ba zaka
auri Fatima a ranar da ka fasa aure na ba, wannan abun a shirye yake, kai da ita duk
munafurtata ku kayi, bazan iya baka wata dama ba." Fitowa na yi daga cikin motar. Da Safwan
mu ka had'a idanu, ashe ya na zaune a k'ofar gida yana jira na, kishi 'karara na gani a idanun
shi, har ruwa ruwa k'wayar idanun shi ta yi. Sai na ji jikina ya mutu, a hankali na iso in da yake,
zama na yi a dakalin da yake zaune. Ajjiyar zuchiya ya sauke, ya sanya idanun shi a cikin
nawa.
"Sadiya sannu da dawowa." Kasa amsawa na yi, shi kuma sai bina da kallo ya ke yi. Mik'ewa
yayi, tare da ajjiye mun ledar da ke hannunshi yace.
"Ki tashi ki shiga ciki, ni zan wuce gida, dama duba ki kawai na zo yi, ki gaishe da Haidar duk da
shi yai ta taya ni hira."
A wajen ya tafi ya barni. idanunnan nashi sun yi jawur da su, Nasan Safwan yana sona, amma
nauyi da kunya sun hana shi furta wa, gashi yau ya tafi cikin ciwon zuchiya. a sanyaye na shiga
cikin gida."

mrs Bukari ce

*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. ‍♀️*




1, *MU GANI A ƘASA...*
_Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*
_Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*
_Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*
Badi'at Ibrahim
_Mrs Bukhari_

5, *AUREN WATA TARA*‍❤️‍
_Miss Hajo_

Guda biyar 1k
Guda huɗu N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda ɗaya N300

*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*

0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.

Domin tura shaidar biya

0810 433 5144

Masu tura katin MTN

0814 179 9224

Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.

0817 952 3215

Guda biyar 1000f
Guda huɗu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ɗaya 300f

*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* ‍❤️‍


Instagram links

https://www.instagram.com/p/CgPTv1-oML6/?igshid=MDJmNzVkMjY=


Facbook group

https://facebook.com/groups/463653111781414/

Telegram links

https://t.me/+xYZCR9JY-aMzNDFk


*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*

Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -

*Enter your name:* (Cikakken sunanki)

*Enter your mail:* (Email ɗinki)

*Enter an username* (Sunanki)

*Enter your password:* ( misali 12341234)

*Confirm password:* (misali 12341234)

Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks.

*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google
za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.

*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.

Masu iPhone

Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com
G Z D
MRS BUKHARI
55~56


Mama da Haidar su na tsakar gida, shi yana aikin da aka basu na makaranta, ita kuma ta na
karanta mujalla. Haidar ya tawo da gudu, tsugunnawa na yi na rungumeshi ina dariya. Mama ta
zuba mun idanu.
"Sadiya zo ki zauna, Haidar k'arbi kayan hannunta ka shiga ciki.
Xama na yi kamar yanda mama ta

23 / 33