Gishirin Zaman Duniya Book 1 Mrs Bukhari

Author :  Badiat Ibrahim Mrs Bukhari Category :  Read Hausa Novels

Chapter   29 / 33

84K to 87K   out of 98.4K words

amma sai na ga wayam. Muryar Safwan na ji yo.
"Sannu Sadiya kin farka?" Murmushi na yi mishi na ce
Na farka." Ina son in tambaye shi yarona amma kunyar su Anty Zulai da su ke ta yi mun sannu
ya hana ni tambaya. Maman ummi ce ta k'araso hannunta rik'e da katon flacks na ruwan zafi,
da kuma k'aramar kular abinci."
"Me jego sannu, Angon k'arni ina ta ya ku farin cikin samun k'aruwa Allah ya raya shi da imani,
ai ta gida na biya na ga yaron a hannun Badiyya wallahi tubarkallah masha Allah." Da mamaki a
fuskata na juyo na dubi Safwan, yayin da maganar maman ummi ta shiga yi mun amsa kuuwa.
Safwan kuwa dakewa na ga ya yi, ya wani kawar da kan shi daga kallona. Anty Zulai na kalla,
amma ban fahimci komai a fuskarta ba, na dai ga ta girgiza kai irinna wanda takaici ya isheshi,
sai na ji ta ce."
"Maman Ummi tunda ga ki kin zo, mu za mu je gida, mu rarrage aikace aikace, Sadiya sai kun
dawo, Allah ya ba da lafiya."
Ameen" kawai na iya ce wa da su, kamar wawuya na bisu da ido, Safwan ne ya mara musu
baya, k'asa_k'asa ya ce.
"Bari in raka su waje" Ya ma kasa had'a idanu da ni sam, sai wani sun sun da kai ya ke yi.
Kamar mahaukaciya haka na d'amk'i hannun Maman Ummi nace."
Ki ka ce kin ga jaririna a gida, a hannun Badiyya?" Da mamaki Maman Ummi ta kalle ni, d'an
nazarina ta yi na wasu dak'ik'u, sannan ta ja nunfashi tace."
"Safwan bai sanar da ke komai ba ne Sadiya?" Haushi tambayar da ta je fo mun ma ta bani, ba
abunda na shirya ji kenan a matsayin amsa ba. Wato nose ce ta iso hannunta rik'e da takadda,
Maman ummi ta mik'ama."
"Gashi in ya shigo a bashi, an yi sallama, Tana cikin k'oshin lafiya haka ma abunda ta haifa.
Malama sai ki kula da jikin ki, da ma jaririnki, Allah ya ba da lafiyar shayarwa." Ko kallo ba ta
isheni ba, Maman ummi ce ta had'a mun ruwan tea.
"Ungo Sadiya ki sha, ki samu hanjinki ya warware, ki kwantar da hankalinki, ni shawarar da zan
baki shine ki bi komai a sannu, kuma da za ki iya zuba ma Safwan idanu kiga iyakar in da zai
k'are gudun na shi ruwan da zai fi. In kin lura kunyarki ce cike a guraben idanunshi. Kar kuma ki
tambayeni komai, domun babu abunda za ki iya ji daga gare ni, kar kuma ki tambayi Safwan
jaririnki. Ungo sha." Hannuna na rawa na karb'a, dan dama wata iriyar muguwar yunwar
haihuwace na ji tana kad'a hanjina. Da zafi zafi na kukkurb'i tean har na shanye. Farfesun
d'anyen kifi ta zuba mun, shima na cinye, amma banji na k'oshi ba sam, nan ta ke cikina ya
soma murd'amun, marata na wani irin karta, ji nake tamkar mutuwa zan yi, dan abunda na ke ji
a k'asan marata ya fi k'arfin abunda na ji a cikin labour room. A guje Maman Ummi ta fita, tare
da noses ta dawo. Nan su ka rufu a kaina, sai zufa ke keto mun, idanuna na neman kakkafewa.
Daga nan ban sake sanin in da kaina ya ke ba, Allura na ga anyi mun, nan na soma ganin kowa
dishi dishi, harda Safwan da shigowarshi kenan."


mrs Bukhari ce

*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. ‍♀️*




1, *MU GANI A ƘASA...*
_Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*
_Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*
_Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*
Badi'at Ibrahim
_Mrs Bukhari_

5, *AUREN WATA TARA*‍❤️‍
_Miss Hajo_


Guda biyar 1k
Guda huɗu N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda ɗaya N300

*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*

0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.

Domin tura shaidar biya

0810 433 5144

Masu tura katin MTN

0814 179 9224

Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.

0817 952 3215

Guda biyar 1000f
Guda huɗu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ɗaya 300f

*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* ‍❤️‍


Instagram links

https://www.instagram.com/p/CgPTv1-oML6/?igshid=MDJmNzVkMjY=


Facbook group

https://facebook.com/groups/463653111781414/


Telegram links

https://t.me/+xYZCR9JY-aMzNDFk


*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*

Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -

*Enter your name:* (Cikakken sunanki)

*Enter your mail:* (Email ɗinki)

*Enter an username* (Sunanki)

*Enter your password:* ( misali 12341234)

*Confirm password:* (misali 12341234)

Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks.

*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google
za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.

*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.

Masu iPhone

Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com
MRS BUKHARI
73/74



SAFWAN
"Maman Ummi lafiya me ke damunta kuma, da ta farka sumul?"
Nose ce ta ce.
"Ba wata matsala bane babba, ku kwantar da hankalinku, wannan yana faruwa da mata a
bayan haihuwarsu, amma ba wani damuwa, da zaran ta farka ma za ku iya tafiya." Ajjiyar
zuchiya ya sauke.
"Mun gode sosai."
Maman Ummi ta mik'a mishi takaddar sallama.
"Ga takaddar sallama sun rubuto, amma kafin ka je biya ina so in yi wata muhimmiyar magana
da kai."
Sallamar shigowar su Innah da Matar Baffa Goggo Hadiza ne ya katse Maman ummi."
Wani mugun kallo Innah ta ke watsa ma Safwan, gabaki d'aya jikinshi yai wani irin mugun sanyi.
Flacks d'in da ke hannun su yai maza zai amsa, Innah tai saurin kaucewa, sai na hannun
Goggo Hadiza ya amsa ya ajjiye a saman durowar gefen gadon.
Waje Maman ummi ta ba Innah, Safwan ya fita da hanzari ya kawo ma Goggo Hadiza wata
kujerar.
"Barka da Goggo, Barka da zuwa Innah." Da fara'a Goggo Hadiza ta amsa mishi, ta na
zaulayarshi.
"Ahh kaga Angon k'arni kana asibiti ashe har yanzu? Toh Allah ya raya wannan yaro da imani,
Allah ya yi albarka. Na yi murna na yi murna." Innah ta ce ma Maman Ummi wacce su ka gama
gaisawa.
"Bata farka ba har yanzu baiwar Allah?"
"Toh farka har ma ta sha tea da farfesu, sai kuma ciwon ciki ya murd'eta, shine su kai mata
allura. amma har an ba da sallama ma." Innah tace.
"Sannu Maman Ummi da k'ok'ari mun gode Allah ya bar 'kauna." Innah sam ta k'i yarda su
had'a idanu da Safwan, shi kuma sai sosa kai ya ke yi. Goggo Hadiza tace.
"Safwan sak'on ka ya isa, kamar yanda ka wakilta Jamila. Toh ta isar maka da sak'onka. Amma
ka sani ka d'auko hanyar rushe duk wani gini na zaman lafiya da kwanciyar hankali a gidanka,
in ban da wauta irin ta ku ta yaran zamani, ina kai ina yin kyautar d'an mutum guda ba b'ari ba.

Wannan ai ganganci ne, kuma ba son yarinyar nan Sadiya ka ke yi ba. Yarinya mai hankali da
yakana irin haka iyi."
Tsugunnawa Safwan ya yi a gaban Goggo Hadiza ya ce."
"Kui mun afuwa a bisa hukuncin da na zartar a kan iyalina. Ni na yi hakanne dan a sake samun
had'in kai a tsakani, Badiyya ba ta tab'a haihuwa ba, ni na yi zaton kowa zaiyi farin ciki ne da
abunda na aikata, amma sai na ga sab'anin haka. Ku yi hak'uri, Allah zai ba ita Sadiyan wani."
Innah da ba ta so yin magana amma jin abunda Safwan ya ce, ya hasala zuchiyarta, cikin b'acin
rai ta ce."
"Ubangiji ne bai ba Badiyya haihuwa ba, shi kuma ya ba Sadiya. Kai baka isa kai ma Badiyya
d'a da d'an da ta rayu wata tara a cikin mahaifiyarshi ba, kuma tana rayuwa a doron k'asa, ba
nakasa ba ciwo. Amma da ya ke ku maza haka kuke baku da burin da ya wuce ku d'and'ana ma
mace mad'aci a cikin rayuwarta, ga ku da son kan tsiya. Safwan za ka yi nadamar abunda ka
aikata gaba. Za ka sha ruwan mamaki, ka ci nadama akan irin hukuncin da zan yanke ma. Ka
sanar ma duniya ba son Sadiya ka ke yi ba." Maman ummi tace."
"Innah ni ina ganin maganar nan ko a barta ba yanzu ba, in an je gida a tattauna komai, Ni
fargabata ma shine ya Sadiya zata d'auki wannan lamarin?"
" 'Yannan ai kinga daga nan ? Toh maganar nan ta k'are, bana so a sake tayo mun da ita, zai ga
kafiya nima a waje na, kuma jariri ko ya maido ma Sadiya ba za ta k'arb'a ba, ya je ya kaima
mowa."

Sadiya
Farkawa na yi, na samu a na wasu irin maganganu da na kasa fahimtarsu, Innah ce ta iso
bakin gadon da na ke."
"Sadiya kin farka, sannu, akwai in da ya ke yi miki ciwo ne?" A jere tai mun tambayar. na ce
mata
A'a ba na jin ciwon komai Innah."
"Toh tawo mu tafi gida kinji, Sadiya na."
Hannuna ta kama na sakko a kan gadon, Safwan ya na gefe ya jingina da bango, da gani kasan
a cikin rud'u yake.
Innah Jaririn fa?" Kasa hak'uri na yi, shi yasa na tambayi Innah, in ji daga bakinta cewar Jaririna
na hannun Badiyya."
"Mu je Sadiya, Jaririnki na gida." Safwan na kafe da idanuwana wanda su ka sauya launi, wasu
zafafan hawayene su ka surnano daga guraben idanuna zuwa kan kumatukana, ni kaina
bansan ko kukan me na ke yi ba, ko dan an ce Jaririna na hannun Badiyya ne oho, amma kuma
bakina cike ya ke fal da tarin tambayoyin da kowa ya kasa bani dama balle in amayar da su,
abunda na ke ta juyawa a xuchiyata shine, meye dalilin da za'a tafi mun da Jaririna gida, alhalin
ni ina asibiti? Gashi kallo d'aya na yi mishi, idanuwana a cike suke fal da son sake yin tozali da
kyakkyawan jaririna, wanda k'aunarshi na baibaye jini da tsokar jikina, a matsayina na uwa.
Safwan binmu ya yi da idanu har mu ka bar cikin d'akin.
mamaki ya ke yi da aka kasa fahimtar manufarshi na alkhairi da ya sa ya mallakawa Badiyya
Jaririnnan, A d'aya b'anrayin na xuchiyarshi kuma, sai juyayin maganganun Innah ya ke yi, a
k'ok'arinshi na son ganin lallai ya fahimci in da furucinta ya dosa, amma ina tunanin na shi ma
k'arewa ya yi kab. Idanu ya lumshe ya ce.

"Ya Allah"
Ya rada ina tudu balle ya dafa, jiki a mace ya fice a ofishin kwakwalwarshi na hasko mai videon
kallon tuhumar da Sadiya ta bi shi da shi, tare da tausayin hawayen da ya ga suna zuba a
fuskarta.
Wajan biyan kud'i ya nufa, duk abunda ya dace yayi sai da ya yi, kafin ya baro asibitin."

Sadiya
Abun hawan da mu ke ciki gudu ya ke yi, amma ni ga ni nake yi tamkar ma baya wata tafiyar
arziki, zuchiyata sai tunzura ta ke yi ita kad'ai, har wani amai ke taso mun.
Har k'ofar gida motar ta kaimu, mak'ota ne su ka soma fitowa, ganinmu da basket da flacks, ya
tabbatar musu jikina da sauk'i. Tun daga waje aka so ma yi mun barka barka, da saukar Jaririn
da kallo d'aya kawai na yi mishi.
Shiga mu ka yi cikin gidan Innah na rik'e da ni. Yayin da ni kuma sai ware ido na ke yi ko zan ga
Jaririna. Amma ina babu kowa ma a tsakar gidan.
Kwanar b'arayin Innah na ga mun sha, ni dai ina biye da ita na zuba ma sarautar Allah idanu. A
falonta mu ka ya da zango"
"Ungo Maman Ummi da kin sha 'yar kwana bayan d'akina, za ki ga wani d'aki ta damanki. Ki
bud'e ki share, a b'allo gadon Sadiya da sib d'in kayanta a mayar mata cikin d'akin maza. Bari in
Kira Zulai ta taimaka miki." Key d'in d'akin Innah ta ke mik'ama Maman Ummi, jiki a sab'ule ta
amsa ta fice. Innah ta dawo da dubanta ga Goggo Hadiza. "Hadiza had'a mata tea d'in ta sha, kafin a kawo kunun kanwa da tuwo, kafin fitarmu na sa
Jamila ta yi, ina zuwa ni kuma." Fice wa Innah ta yi a d'akin, ni dai a cikin duhu na ke sosai.
B'arayin Zulai Innah ta soma zuwa, ta sanar da ita, ta je ta ta ya Maman Ummi aiki. Daga nan ta
wuce b'angaren Anty Jamila.
Badiyya ta na d'akin, Anty Jamila ta na kwatanta mata yanda zata shayar da Jaririn. domun har
ruwan nono ya zo mata. Ana cikin haka Innah ta d'aga labule, Kawar da kai ta yi dan gudun
ganin abun takaici.
"Jamila, yarinyar nan mun dawo, ki had'a wuta a d'aura kwatanniya, sannan a kai mata kunun
tsamiya da tuwon, ki bad'e shi da ya jin daddawa, da man shanu.
In kuma Safwan ya shigo, ki ba shi sak'o cewar ya kawo naman gashi, da kaza da za'ayi mata
farfesu, ki lillisa mun farin kwalli."
juyawa ta yi abunta, Anty Jamila ta yi tsaye jiki a mace, dama irin abunda ta gudanma Safwan
kenan tun farko, ita kanta tasan hukuncin da ya yanke, yayi tsauri, ba daidai bane abunda ya
aikata.
Duban Badiyya ta yi wacce ta ke zubar da hawaye, tace.
"Ki dena Kuka Badiyya da sakel bari Safwan d'in ya shigo, ki dank'a mishi d'an shi, ni dama na
fad'a miki ma da baki sha wani gadali ba, domun wannan kyauta bazata kyautu ba. I na dai
zuwa bari in aiwatar da abunda Innah ta sa ka ni."
MRS BUKHARI
75/76


Sadiya

Ni dai ina zaune kamar wata gunki, tea na ke kurb'a amma ruhina baya tare da gangar jikina
sam. Al'amuran sai d'aure mun kai su ke yi, zarge_zarge iri_ iri ne su ke bijirowa a zuchiyata.
Anty Jamila ce ta kawo mun tuwo da kunun kanwa, Goggo Hadiza ta tusa ni gaba, kan lallai sai
na ci a gabanta."
Bayan awa guda, su Maman Ummi su ka kammala gyaran d'akin da Innah ta sa musu hannu
aka yi tare da ita. Dukkan su ukun su ka shigo nan in da muke.
"Sadiya ta so kinji, ki ta fi d'aki ki kwanta, kafin ruwan wankan ya tafasa. A d'akin da na sa aka
gyara miki za ki zauna zuwa wasu lokacin. Ki yi hak'uri da duk abunda zan zo in sanar miki."
Inna ce ke magana da ni, Anty Zulai ta ce.
"Innah ba'ayi haka ba, ni bari Safwan d'in ya zo da kaina zan sa ya karb'o jaririn a hannun
Badiyya ya dank'a ma uwarshi kayanta, bai yi tunani ba ne shi yasa ya yanke wannan
hukuncin."
" Zulai ba na so a sake ta yar da wannan maganar, iyalanshi ne, shima jaririn ai na shi ne. Ki je
d'akin ki kawai maganar ta k'are daga nan."
Ni dai jikina har rawa ya ke yi haka na fita ina gauraye hanya, Maman ummi ce ta rik'e ni har
zuwa cikin d'akin da su ka gyara yai tsab. A kan gado ta zaunar da ni. Dubanta na yi ina
murmushi na ce.
Badiyya ya ba kyautar Jaririna in dai na fahimci zancan. Lallai kuwa zamana da Safwan ya
k'are, tun a daren farko da na yi a gidan na fahimci dan in haihu mishi ya auro ni, tsantsar so
kuma matarshi kad'ai ya ke yi ma. Kaico na. Kukan da na ke dannewa ne ya kwace mun, na
jima ina kuka mai cike da tuk'uk'in bak'in cikin da duk wanda ke saurarom sautin kukan zai ga
ne. Maman Ummi ta san abunda a kai mun mai girma ne irin wanda harshe baya iya bayyana
zafi da radad'in shi, shi yasa sam ba ta yi yunk'urin hanani kukan ba. Har sai da na yi ma'ishina
tukunna, na yi shiru a karan kan kin kaina. Sannan ta dafa ni.
"Sadiya kar ki ce za ki yi wani abu da za ki zo kina cizan yatsanki, ki bi komai sannu kan hankali
ke fa ba yarinya bace, kuma kin d'and'ani zafi da gararin zawarci."
Ban d'and'ani komai ba, ilimina ya d'ebe mun kewar da ko lokacin kaina aiki baya ba ni balle har
tunane tunane su addabi rayuwata. Ke ba ki ga k'ask'antar da ni da.Safwan ya yi ba? Jaririna ya
na tsumman haihuwa ya raba ni da shi, sabida ya fi kyaunar ganin Badiyya ta na dariya. Maman
Ummi da wanne idon ma Safwan zai dube ni yai mun bayani?" "Ni Sadiya abunda na ke nufi shine, ki nunar mishi kuskuren shi ko dan ya gyara gaba. Sannan
lallai a baki d'anki ya kasance dake, in kuwa ya ci nasarar raba ki da wannan Jaririn, kuma ya
hana ki shayar da shi, toh wallahi ko me yaron zai zama a gaba, bazai dube ki ba, Badiyya zai
bud'e idanu ya gani a matsayin uwarshi. Shi goyo yana da mugun tasiri, bawai dan kin yi
nak'udar silar zuwan shi duniya bane kad'ai zai sa ya soki har ya dinga jin motsin sonki da
shak'uwa a ranshi ba. goyo da cin kashin yaro da fitsarinshi, da shayarwa, da kula da
rayuwarshi, shi ke haddasa wannan soyayyar a tsakanin D'a da uwa. Ko gidan marayu ki ka je
ki ka d'akko d'a sabowar haihuwa, ki ka rene shi, ki kai wahala da shi, toh fa ko da bayan ya
girma za ki nunar mishi ke fa ba ke ki ka haifeshi ba. Shi kuma a wajan shi babu wata uwa
bayan ke. Har abada kuma ke ce uwarshi...
Ya isa Maman Ummi kar ki sa zuchiyata ta fashe. Saurin dakatar da'ita na

29 / 33