Author : Badiat Ibrahim Mrs Bukhari Category : Read Hausa Novels
umarce ni, Haidar kuma ya shiga ciki.
"Sadiya yaronnan Safwan meye matsayar maganar ku? Na ga ya na hidima da yawa a kan ki
da Haidar, me yasa ba zaki bashi dama ba? Bana son in yi aure in barki a gidannan, domun
hakan ba mutuncin bane. Ko ba kya son Safwan d'in shima? Ajjiyar zuchiya na sauke nace.
"Mama bawai bai yi mun bane, ni halin da Haidar zai shiga ne damuwata. Duk da dai Safwan ya
na son Haidar, amma mama bai tab'a mun maganar soyayya ba gaskiya, iyakata da shi
mutunci."
"Sadiya ho, duk wannan jewar da Safwan ya ke yi, kin fi so sai ya furta miki yana sonki? Toh ki
mai maganar turo magabatanshi, sai su je can Raquma a d'aura auran ke ma ki huta.
Toh mama in yazo zan sanar mishi."
D'aki na shiga, bayan na rage kayan jikina, wanka na yo, nazo na samu Haidar ya barbaje
kayan da Safwan ya kawo mana.
mayukan Haidar ne, da sabulan wankan shi, lallai Safwan ya cancanci in bashi dukkan wata
dama. Amma ta ina zan soma rarrashin shi ma? dan da fishi ya tafi.
Tun daga wannan lokacin Safwan bai sake zuwa gidanmu ba, sai dai ya aiko mun da sak'on
gaisuwa. Da dai naga tafiyar ta mik'e har wata guda, ranar na taso aiki da safe, kai tsaye
makarantar su Haidar na wuce. Aike nayi a kira mun Safwan.
Yana sanye cikin wani yadi da ya sake fito da kamalar shi. Shima sai kallona ya ke yi da
mamaki, take kunya ta lullub'eni. Nama rasa in ya k'araso me zan ce mishi.
"Malama Sadiya barka da wannan yanayin, idanki kenan?" Tausayi ya ba ni sosai
Safwan kwana biyu me ya faru ka dena.zuwa zance gida? Hannayenshi ya zura a aljihun shi
yace.
"Sadiya na lura kamar takura miki hakan ya ke, kuma bana son Bazawarin ki me mota da yake
yawan suntiri a k'ofar gidan ku yayi tunanin ko akwai wani a tsakaninmu, kuma ni wajan Haidar
Aliyu mai hula na ke zuwa. Gabana ya fad'i sosai, bansan son Safwan ya shige ni har haka ba.
Jiki a sanyaye mu ka yi sallama da Safwan. ko da na koma gida kasa nutsuwa na yi. da yamma lis yaro ya turo kira na. Da zumud'i na fita a
tunanina Safwan ne, ina fita na ci karo da Ahmad. yana jingine a bakin motar tashi, raina bai so
zuwa ba, dan dai na riga na fito ne. Ina zuwa in da ya ke, Safwan ya na shawo kwana Idanu
muka had'a, a mugun zuciye ya koma. Ni kuwa sai lek'e na ke yi, ji na ke tamkar in bishi da
gudu.
"Sadiya lafiya kuwa, naga hankalin ki baya tare da ni?" Harara na zabga mishi tare da jan tsaki
na koma cikin gida na barshi a nan a tsaye."
Safwan yana tafe yana tunanin me yasa ma ya damu da Sadiya alhalin ita bata ma san yana yi
ba? da tunane tunanen daya isa gida kenan.
Badiya ya samu ta na wanke wanke a tsakar gida, murmushi su ka sakarma juna, kujera ya
jawo ya zauna a gaban wanke wanken, ya shiga d'auraye mata.
"Sannu da zuwa, yau baka je wajan su Haidar bane, naga ka dawo da wuri, kuma ranka a b'ace
?"
"Badiyya ni na hak'ura da Sadiya kawai, kamar ba sona ta ke yi ba Allah." murmushin danne
kishinta ta yi tace."
"Gobe zan je ni da kaina dan yi ma yak'in nemo soyayyarta,burina shine inga ka samu magaji,
ko ni ma na huta da gorin da 'yan uwanka su ke yi mun.
Inna ce ta bankad'o gidan ta shigo, salati ta shiga jerawa.
"Safwan bawan Badiyya ka zama? ka fita ka nemo abinci, aikin gidanma sai ka taya ta? Dama
ta cika mun gidannan da jikoki ai duk da sauk'i, yarinya ta hana ka sak'at da makirci irin namu
na mata." Da Sauri Badiyya ta mik'e, tare da rik'e jakar ledar Innah.
"Sannu da xuwa Innanmu.kawo jakar in shigar miki da'ita." Fisge jakarta Inna ta yi tace.
"Ke zan ma sannu da xuwa dan ke ce bak'uwa, nan gidan d'anane." Tana kaiwa nan ta shige
ciki ta barsu a wajan, Safwan ya kalli Badiyya wacce take ta faman aikin tsilalar da hawaye.
Rungumeta yayi yana shafan bayanta cikin sigar rarrashi. Hannunta ya kamo su ka shiga
matsakaicin falon na su, da hanzari Badiyya ta zame hannunta a na shi, ita ta soma isa wajan
Innah.
"Ina wuni Inna ya hanya, ya aka baro mutanen Azare?" Babu yabo Babu fallasa Inna ta amsa
mata. Mik'ewa ta yi dan kawo ruwa da abinci. Safwan kuma yana gefen Inna a zaune, yana
gaisheta ta yashe baki da fara'a ta amsa.
"Baffan ka yana godiya da irin hidima da kake yi da su, Safwan ni dai kwanciyar hankalina shine
ka komo gida, sannan ka yi aure, anan d'in koyarwa kake yi, a can ma akwai koyarwar, ni
nafison ina ganinku a kusa dani. Ya batun bazawarar da kai mun maganar ta, kwanaki dana zo?
na tafi cike da murna wallahi." Kai ya sosa yace. "Yanxu maganar da mu ke yi da Badiyya kenan, akan gobe zata je da kanta da shawo mun kan
Sadiyan." Had'e fuska Innah ta yi tace.
"Ni na shiga uku na da zancen Badiyya, dama fa kakarta ance mayya ce, yarinyar nan dai ni na
ja ma kaina, tunda ni na had'a wannan aure na jaraba. Ni da kaina zanje gidan su Sadiyar mu yi
magana da gyatumarta, ayi komai a gama, amma fa a Azare zaku zauna, in ba haka ba,
Badiyya ba zata barka ka yi adalci ba, da shanyayyen jiki zaka tashi gaban ubangiji, ni kuma
bazan so hakan ba, zai fi mun sauk'i ka dawo gida."
"Toh Inna sai yanda kika ce ai, sai in koma d'in ai Innah" Badiyya ce ta kawo ma Inna tuwon
shinkafa da miyar taushe, taji tantakwashi da man shanu, da ruwan sha da na wanke hannu.
Safwan ne ya zuba abincin suna ci tare da Innah ya na bata labarin Sadiya da d'an yaronta."
Badiyya kuma tana uwar d'akinta ta yi rub da ciki, sai kuka ta ke yi mara sauti."
Bayan sun kammala cin abincin, sun tab'a hira,sai Innah tace.
"Bari in shiga daga ciki in d'an huce gajiya, in Badiyya ta gama mulkinta. Kace ta kai mun ruwa
ban d'aki."
Da "Toh" Kawai ya bi Innah.
Da sallama ya shiga cikin d'akin, sautin shesshek'ar kukan Badiyya ya doki dodon kunnenshi.
Da sassarfa ya isa gareta, tare da jawota ta fad'a kirjinshi. Tsintar kanta ta yi da sake rushe
mishi da sabon kuka. Cikin nuna kulawa ya shiga rarrashinta.
"Haba Badiyya ta. Ki yi hak'uri da mahaifiyata, ita ta haifeni, kuma in kina sona, so na gaskiya.
Dole ki yi mata biyayya. Ni ne mijinki, rashin haihuwarki ba ya damuna sam, shekaru goma sha
biyu mu ka yi tare, ki ka yi rayuwa da ni ke kad'ai. Ta b'angarena baki tab'a fuskantar wani
k'alubale ba. Inna fa ta yi hak'uri maganar gaskiya, kinsan iyayenmu da maganar jikoki. Yin
Aure na, shine zai kawo kwanciyar hankalinmu baki d'aya. Kuma ina son Sadiya, da Haidar. Ki
share hawayenki, ki kaima Inna ruwan wanka band'aki."
Hawayenta ta share tace.
"Amman Safwan bai kamata ace Inna...."
"Dakata Badiyya! Bazan lamunci ki fad'i ko wacce irin kalma bace akan mahaifiyata, dole ki bi
abunda tace, in dai ni ki ke Aure. Son da na ke miki bazai hana in sa sab'a miki akan
mahaifiyata ba. Kin ko san irin fad'i tashin da ta yi dan ganin na tsaya da k'afafuna?" Ficewa
Badiyya ta yi ranta na tafasa, ta ma rasa da me za ta ji, ga zancen Sadiya kullum da Safwan ya
ke cika ta da shi, da irin k'aunar Haidar da ya ke yi. Ga cusgunawar da danginshi, da
mahaifiyarshi su ke yi mata, da me za ta ji, sai a dake ka a hana ka kuka?"
Ruwan zafin dake wuta akan (Itace), ta juye ma Innah, sai da ta kai ban d'aki tukunna, ta je ta
sanar ma Innah ta kai ruwan" Amma ko kallon banzan da Inna ta saba yi mata ba ta yi mata ba,
dan ko bud'e idanunta ba ta yi ba, balle ta san ta ji ko ba ta ji ba. Haka ta k'araci tsugunno, ala
tilas ta mik'e ta fita. Da harara Inna ta bi bayanta." Safwan ya na kwance a kan katifa, ya yi zurfi cikin tunanin Sadiya, tare da fargabar wanne irin
sakamako Inna za ta dawo da shi in ta je gidan su Sadiya? Tsoron shi Allah, tsoronshi kar ace
Sadiya na da wanda za ta aura."
Badiyya ta zauna a bakin katifar ta su, idanu ta xuba ma Safwan. Ta na jin tsantsar kishin shi na
nuk'urk'ushe mata zuchiya."
Yanzu nan da wani d'an lokaci Safwan zai zama mallakin su, su biyu?" Duk wannan batu a cikin
zuchiyarta ta ke yi"
Mrs Bukhari ce
*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. ♀️*
1, *MU GANI A ƘASA...*
_Ummu Affan_
2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*
_Ummu Maher_
3, *GUNTUN GORO..*
_Mom Islam_
4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*
Badi'at Ibrahim
_Mrs Bukhari_
5, *AUREN WATA TARA*❤️
_Miss Hajo_
Guda biyar 1k
Guda huɗu N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda ɗaya N300
*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*
0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.
Domin tura shaidar biya
0810 433 5144
Masu tura katin MTN
0814 179 9224
Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.
0817 952 3215
Guda biyar 1000f
Guda huɗu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ɗaya 300f
*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* ❤️
Instagram links
https://www.instagram.com/p/CgPTv1-oML6/?igshid=MDJmNzVkMjY=
Facbook group
https://facebook.com/groups/463653111781414/
Telegram links
https://t.me/+xYZCR9JY-aMzNDFk
*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*
Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -
*Enter your name:* (Cikakken sunanki)
*Enter your mail:* (Email ɗinki)
*Enter an username* (Sunanki)
*Enter your password:* ( misali 12341234)
*Confirm password:* (misali 12341234)
Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks.
*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google
za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.
*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.
Masu iPhone
Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com
MRS BUKHARI
57-58
Sadiya
Ko da na shiga gida kasa sukuni na yi, ina jin babu dad'i sam, a bisa halin da Safwan ya tafi a
ciki. Tsaki na ja mai tsayi. Haidar ne ya shigo da gudu Mama na biye da shi da bulala. Jikina ya
haye sai faman sukuwa ya ke yi. Na kasa ce musu komai, da idanu kawai na ke binsu.
"Umma kinga Mama zata dake ni ko? Ki yi mata Bulala ke ma." Mama tace.
"In ita uwarka ce, ni kuma uwarta ce, ba za ta iya duka na ba. Amma ni dukkan ku zan iya
duka." Haidar ya juyo mun da fuskata yace."
"Umma hakane?" Kai kawai na gyad'a mai, ba tare da na ce komai ba. Mama ce ta ce.
"Maza je ka gaisa da Baba kace ina zuwa yanxu." Aguje Haidar ya fita zuwa zaure dan sanarma
Malam Kaka sak'on Mama.
Ita kuma zama ta yi a gefe na."
"Sadiya, na lura tunda ki ka dawo daga wajan kiran da Safwan yai miki, sai walwalarki ta
d'auke." Ajjiyar zuchiya na sauke.
Mama ba ma Safwan d'in bane, Ahmad ne. Mu na tsaye da shi, sai ga Safwan d'in ya zo. Amma
ganin Ahmad yasa bai 'karaso wajen ba. A cikin fishi ya tafi, sai banji dad'i ba. Ko dan hidimar
da ya ke yi da Haidar Mama." Kaina na sauke k'asa ina jiran me Mama za ta ce.
"Sadiya kenan. Ki rabu da shi, zai zo da k'afarshi. Da ya zo ki sanar mishi ina neman shi. Ga shi
mun tsaida lokacin Aure da Kaka, sai dai hakan bazai yuwu ba, har sai na kawar da ke a
gabana. Ni ma sai in koma gidan mijina. Yanzu dai bari in je in same shi." Fita Mama ta yi a
d'akin. Ni kuma ina jin kunyar zance da Mama su ke yawan yi da Malam Kaka, kuma ni ma ana
zuwa waje na."
......
washe gari.
Ina tsakar gida na fito da wankin Mama da na Haidar, kasancewar yau ba ni da aiki sam.
Mama ta na kan tabarma, ita da Haidar, suna karatun makaranta.
Sallamar mace mu ka jiyo daga zaure.
"Ameen wa'alaikis salam, shigo baiwar Allah" Mama ce ta yi magana. Dattijuwar matar ta shigo
cikin gidan. Da fara'a Mama ta tarbeta, tare da nuna mata wajan zama.
Ni kuma na shiga kitchen na kawo mata ruwan sha, sannan mu ka gaisa."
"Ko ke ce Sadiya Maman Haidar?" Da mamaki na ce mata.
Eh ni ce" Baki ta yashe"
"Tubarkallah Safwan ya iya zab'in mace. Ji yarinya kub'ul_kub'ul da ita, dirarriyar mace ma
malam." Murmushi kawai na yi mata, a raina ita tunanin To ita kuma wacece?. Kamar ta ji me na
ce, sai tace ma Mama."
"Mahaifiyar Safwan ce, daga Azare. Wannan baturen shine Haidar?" Mama da fara'arta ta k'aru
tace."
"Maraba lale da zuwa. Eh Haidar kenan. Haidar ga Kaka, ka yi gaisuwa" Ni kuma kunya duk ta
lullub'eni, a tsaneke na shige 'daki, ina jiyo ta, ta na hira da Haidar. A bayan labule na lab'e dan
zumud'in son jin me za su tattauna."
"Dama shi Safwan d'in ne ya turo ni, tunda na zo, akan ita Sadiya ne, ya na naiman Auranta, in
har babu wanda ya riga shi, mu dai mu na so. In kuma za mu samu, ba ma so ya wuce wata
biyu, tunda su ba yara bane k'anana. Ya na da mata Badiyya sunanta. Amma Allah bai azurtasu
da samun rabo da'ita ba." Mama tace. "In ma dai akwai wani, toh ni dai na ba yarona Safwan. Sai dai dangin mahaifinta suna Zamfara
cikin k'auyan rak'uma. A can zai je ya biya sadakin na ta, sai kuma Ayi bikin anan. An baku ita
dai a ta'kaice."
"Kai amma na yi farin ciki ainun. Allah yasa ayi damu, Babu damuwa, in aka ba mu adirishin can
Raquman, sai Baffan shi ya je, a kai sadakin ai. Wani hanzari ba gudu ba. A garin Azare za su
zauna in an yi bikin, dan zai tattara duka ya koma Azaren, da fatan babu matsala?" Mama ta yi
murmushi, ta ce." "Babu damuwa, ai aure babu inda baya kai mace, shi Aure haka yake, sai ya cillaka k'asar da
ba kai zato ba."
Ina daga bayan labule. murmushin farin ciki na sauke, ashe dai dama Safwan na sona? Allah
sarki bawan Allah, yayi wuff ya riga Ahmad turowa, gudun kar garin kallon ruwa kwad'o yai
mishi k'afa. Barin wajan na yi na zauna, ina tunanin Azare kuma Aure zai d'ebe ni ya kai. Ahh
iko sai Allah." Mama ce ta katsemun tunanin da na yi zurfi a cikin shi."
Mama har ta tafi ne?"
"Ta tafi, na san kinji komai, ni dai na basu dama. Ke ma kuma nasan hakan take a wajanki.
Sadiya sai ki bi mijinki sau da k'afa. Danginshi, iyayenshi. Kuma zan yi magana da shi, ko Allah
zai sa ya amince miki, ki ci gaba da aikin na ki, bayan kun yi aure. Kuma zan baki shawarar ki
bud'e shagon sai da magani a can. Allah yasa albarka.Zan sa ai mun bincike kamar yadda
sharia ta tanadar"
Ameen Mama" Kawai na iya cewa. Amma kuma inajin wani karsashi na sabuwar soyayya na
fisgata. Kai soyayya me dad'i"
Safwan
Kasancewar yau Asabar ce, ya na gida, ya ba matar shi dukka lokacinshi. Ita kuma ta saki jiki
da shi tamkar ba su samu d'an sab'ani jiya ba.
"Ka ga har yanzu Inna ba ta dawo ba. Allah ya sa a dace dai"
"Toh ameen Badiyya gimbiya, gabana tun fitar ta ya ke fad'uwa wallahi." Danne kukan da ya ke
shirin tsinka ta a idon Safwan ta yi, cikin dakewar zuchiya, tare da nuna jarumta ta ce.
"Ni kuwa zan so ganin wannan Sadiya da ta rud'amun mai gida, kai da kallon mata bai dame ka
ba. Ba ka damu da kula su ba ma"
Jawo Badiyya ya yi kusa da shi, dan ya fahimci a cikin maganarta akwai kishi. Kunyarta ma ya
ji, yanda ta saki jiki su na hirar Sadiya."
"Za ki ganta ne, macece kamarki, amma ita bak'a ce, ba kamarki fara ba, kin fi Sadiya kyau ne
sa ba kusa ba. Amma yanayin ku ne ba d'aya ba. Akwai abubbuwa da yawa tattare da'ita.
Badiyya" Fasali ya ja tare da k'ura mata idanunshi, wanda ya riga da ya san sune logonta.
"Ke ta musamman ce a rayuwata. Babu macen da za ta shigo gidana, ta taka mun ke, ki na da
mahimmanci a cikin rayuwata. Kuma ina girmamaki as uwar gidan gidana. Dole ko wacce mace
da za ta shigo rayuwarmu, ta girmamaki. wallahi a kan ki zan iya sakin Sadiya kinji na rantse
miki, kuma kinsan bazan yi miki rantsuwa dan ki ji dad'i ba. Muddin Sadiya tak'i girmamaki, ta
kuma k'i yadda da zaman lafiya. Toh sallamarta zan yi."
Wani dad'ine ya lullub'e zuchiyar Badiyya. Jinta ta ke yi tamkar wata sarauniyar matan duniya.
Murmushi ta yi, tare da cewar.
"Ni kuma zan baka goyon baya d'ari bisa d'ari, kuma zan ta ya ka mu so Sadiya. Na yi maka
alk'awarin