Author : Badiat Ibrahim Mrs Bukhari Category : Read Hausa Novels
ya iya samun magaji. raunin yayi
yawa, sab'ulewa fa, ga wasu wajan sunji raunin da yawa. Amma kar ka fad'ama mata. Allah ya
kare gaba, k'una babu kyau." Kawu ya yi shiru kai a k'asa ya na nazari akan maganganun
wanzan, can ya nisa ya ce.
"yanzu wanzan babu wani taimako kenan daya dace a bashi, yaronnan in haka ta faru,
rayuwarshi durk'ushewa za ta yi, yana matashi mai k'arancin shekaru ace gabanshi ya dena
aiki,ko bazai haihu ba. Ai za'a shiga mummunan tashin hankali da damuwa. wanzan duk wani
abunda ya dace na magani da kulawa a mai." Shiru wanzan yayi cikin tausayawa yace. "zuwa wayewar gari, zan lek'a jeji. zan harhad'o duk wani kauci da ya ke da nasaba da wannan
lalura, zan d'aura shi akan magungunan hausa. in Allah yasa da rabon farfad'owar abun, sai ka
ga ya farfad'o" Sallama wanzan ya yi ma kawu. shi kuwa kawu yafi sama da awa d'aya a inda
wanzan ya barshi, ya shiga rud'u da tashin hankali. ya na mamakin garin yaya su Aliyu su ka
k'one daga shi har matar tashi."
"Yaya, lafiya, mekakeyi anan?" Su Goggo Safiye da Goggo mariya, da Goggo Asabe ne suka
iso gabanshi.
Juyowa yayi ya kallesu, cikinshi a matuk'ar mace. Bayanin da wanzan yayi mishi yanzu, ya
zayyana musu suma.
Goggo Asabe babu abunda ta iya cewa sai kuka, tasan ta zalunci d'anta. Gashi ta jefa shi a
cikin mummunar lalura, mai cike da tashin hankali, yaya zata iya wanke laifinta? Ji tayi wutar
tsanar Sadiya na sake ruruwa a zuchiyarta, domun duk sabida k'iyayyar da take ma Sadiyanne
ya ja wannan abun. yanzu kam lokaci yayi da zata tasanma cin mutumcinta har sai ta yi zuchiya
ta bar auran. Allah Allah take yi gari ya waye ta je wajan mai dambu, su san nayi. Goggo mariya
tace.
"wannan tashin hankali da mai yayi kama, bama fatan haka ta faru, zan je k'auyan me gidana,
zan karb'o mishi magani, a wajan wani shahararren mai bada magani ko za'a dace.
Goggo Safiya tace.
"Amma Yaya kar'a sanar da kowa wannan lamarin. Ni ina zargin Sadiya da sa hannunta a cikin
wannan ciwon. Asiri k'ila ta yi, danta lalata musu rayuwa, uwarta ma fa haka take muguwa, in
ba asiriba me yasa ita hakan bai faru da ita ba, sai khadija?."
Kawu yace
"Asabe kiyi hak'uri, karki d'aga hankalinki. Ba na fad'a miki wannan abun bane, dan ki tayar da
hankalinki ba. na fad'a miki ne, a matsayinki na uwa dan ki san da zaman hakan." kiran sallar
asuba su ka soma jiyowa. Barin wajan su ka yi, kowa ba guiwa.
Anas ne ya ta fi b'arayin Sadiya dan sanar mata meke faruwa.
Sadiya
fitowa ta kenan daga ban'daki, sai naji ana doka mun sallama. Cikin fad'uwar gaba na so jin
waye.
"Anas ne, Aliyu ba lafiya yana d'akin zauran su Baba. Ki je ki zauna dashi, za mu ta fi masallaci.
Rass gabana ya fad'i. Rashin lafiya, mutumun da muka rabu da shi cikin farin ciki. Anas tuni har
ya yi gaba. A rud'e na koma ciki, hijab d'ina na d'auka na fita cikin sauri.
Da sallama na shiga d'akin, Aliyu ya farka ya na kici kicin mik'ewa amma ya kasa. Da sauri na
k'arasa nasa hannu dan in taimaka mishi ya tashi.
Kai ya girgiza mun halamar a'a. zamewa yayi da dabara ya koma. Dubana yayi idanunshi sun
kad'a sun yi jawur yace.
"k'addarace ta same ni Sadiya. Bansan dalilin faruwar hakanba. d'an tsumman da ya rufe
jikinshi da shi ya yaye mun. tocilar dake cikin d'akin na jawo, tare da haskawa." zare idanu na
na yi waje. take na soma zubar hawaye. cikin gijijicewa nace.
"Aliyu k'onewa kayi garin yaya?"
Labarin duk abunda ya faru da su ya bani turyan turyan.
"Ki yi hak'uri Sadiya mu d'auka wannan k'addararmuce, bana son ganinki a mawuyacin hali plz.
Shesshek'ar kuka na ke yi na ce.
Kayi hak'uri, amma bai dace ace irin wannan ciwon ana zaune a gida ba. Aliyu ka tashi mu je
Asibiti. plz" Hannuna ya rik'o yana d'an murzawa a hankali yace."
" ki kwantar da hankalinki Sadiya na. dama ina jira ki zo ne, sai mu tafi, ki kaini Asibiti, nasan
zako iya kulawa dani, amma nasan ba lallai bane su Baba su yarda da hakan." Matsawa nayi
kusa da shi dab, sumbatar leb'enshi na yi. A take ya lumshe idanunshi. murmushi mu ka
sakarma juna. Rarrashinshi na shiga yi, tare da bashi baki. Lamo yayi a jikina. Sai can ya ce. " Toh taimaka mun in tashi, In nayi sallah sai mu tafi kafin su sani ko?. mik'ewa na yi, na
kamashi. da taimakon Allah har zuwa b'arayinmu. Nina taimaka mishi ya d'auro alwala. a zaune
akan kujera yayi Salla. Ni kuma kaya na sake na d'auki jakata na fito.
"Akwai kud'i a k'aramar jakata Sadiya. Ki debo mu rik'e. Komawa ciki na yi na bi umarnin
abunda ya ce mun.
"Ki je ki kirawo khadija mu tafi, dan itama tana cikin mawuyacin Hali, sai Kamilu ya taimaka miki.
Toh. kawai na ce mishi na fice.
Kamilu na je na soma kirawowa. wuce ni ma yayi da sauri, ni kuma ta k'ofar gaba na biyo. da
sallama na shiga d'akin khadija. Bilkisu ta na zaune tare da ita.
"Ya mai jikin Bilkisu?" Babu yabo babu fallasa tace.
"Ga jikinnan tana jin jiki, wannan lamari duk mai hannu ya ciki Allah ya toni airinshi." kallon
khadijar na yi, tana kwance ido biyu, Bilkisu kuwa banza na ba ajiyarta. nace
"Sannu Allah ya baki lafiya. Zaki iya tashi muje Aliyu nasan ganinki?" Cikin yamutse fuska ta
soma yunk'urin mik'ewa. Amma sai ta kasa. Taimaka mata na yi, na mik'ar da'ita tsaye.
mayafinta dake kan gadon na yafa mata. Tana rik'e a hannuna har zuwa b'arayina. Ba tare da
b'ata lokaciba mu ka fice ta k'ofar baya. Babur biyu mu ka samu, Kamilu yasa Aliyu a tsakiya, ni ma nasa khadija a tsakiya.
Sun sha wahala sosai, kafin mu isa bostop. kasancewar yau talata, ranar kasuwar mafara ke ci.
Mota ba wuya, kuma nan da nan take cika. Muna isa mu ka samu mota mu ka shiga. Kan Aliyu
ya na kafad'ata. Hannunshi kuma yana ta bayana ya rik'emun kuguna yana d'an matsamun a
hankali. Amma da ganin yanayin shi, jiki ya ke ji. Dauriyace irinta jaruman maza. Amma khadija
kuka take yi ita sosai."
Goggo Asabe, tana yin sallah ta fice a gidan, sai wajan mai dambu.
"Lafiya Asabe irin wannan fitowar duku dukun?
"Ga yaranmu can rai a hannun Allah mai dambu, boka ya cuceni, ya mayar mun da yaro ba
namiji ba. Gabaki d'aya yaran, gabansu ya lalace."
K'irji mai dambu ta dafe, tace.
"Nashiga uku har da khadijar abun ya shafa. ya boka zai mun haka?" Sororo Goggo tabi mai
dambu da kallo, ita kuwa mai dambu bata san ma ta furta wannan furucin ba.
"Ohh mai dambu, kinso komai ya k'are akan shi Aliyun ne? baki da laifi ni ce na zama lusarar
uwa mai yima d'an cikinta asiri. In da iyaye za su ji kuskuren dana aikata, nasan za su
tambayeni, ina wannan son na uwa da d'a na jefar dashi. kaicona, mai dambu.
mai dambu ta zulle tace.
"Ba abunda ki ke nufi bane Asabe. wato yaronnan dan rashin Adalci sai da yayi tarayya da
Sadiya, bacin a d'akin khadija yake? Asabe aiki ne ja a gabanki, ina yaronnan ba haka aka bar
miki shi ba.
"me dambu, abunda yake gabana yanxu shine, mu tafi wajan boka ya warware wannan asirin
da yai ma yarannan.
mayafi kawai mai dambu ta yafa su ka fice a gidan, sai gidan boka."
Mrs Bukhari
*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. ♀️*
1, *MU GANI A ƘASA...*
_Ummu Affan_
2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*
_Ummu Maher_
3, *GUNTUN GORO..*
_Mom Islam_
4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*
Badi'at Ibrahim
_Mrs Bukhari_
5, *AUREN WATA TARA*❤️
_Miss Hajo_
Guda biyar 1k
Guda huɗu N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda ɗaya N300
*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*
0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.
Domin tura shaidar biya
0810 433 5144
Masu tura katin MTN
0814 179 9224
Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.
0817 952 3215
Guda biyar 1000f
Guda huɗu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ɗaya 300f
*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* ❤️
Instagram links
https://www.instagram.com/p/CgPTv1-oML6/?igshid=MDJmNzVkMjY=
Facbook group
https://facebook.com/groups/463653111781414/
Telegram links
https://t.me/+xYZCR9JY-aMzNDFk
*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*
Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -
*Enter your name:* (Cikakken sunanki)
*Enter your mail:* (Email ɗinki)
*Enter an username* (Sunanki)
*Enter your password:* ( misali 12341234)
*Confirm password:* (misali 12341234)
Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks.
*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google
za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.
*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.
Masu iPhone
Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com
G Z D
MRS BUKHARI
33~34
"Boka ta fa b'aci, yaronnan sai da ya sadu da d'ayar matar tashi, sannan ya je ga d'ayar. Yanzu
haka dukkansu suna kwance, jinya su ke yi, sosai ga zubar jini, muna cikin tashin hanali mara
misaltuwa."
Dariya boka ya saki, yace.
"Dama ni nasan da wuya su tsallake, laulayine da asirin sosai. gashi da wuyar karyuwa. Aikine
a gabanku ja. Domun har sai furen da shine mahad'in makarin, asirin ya fito. Kuma sai shekara
ta zago, da damina yake fitowa."
Goggo Asabe wacce ta kasa magana tun zuwansu tace.
"shi yaron fa, wanne taimako za'a bashi?"
"Ai tashi ta k'are, shi da kwanciyar Aure kuma, sai a mafarki. maganin kashe namiji mus yake
yi, sai dai ha'kuri." wasu hawayene suka shiga sunturi a kumatun Goggo, tana mai nadamar
kuskuren data tabka. Mai dambu duk da dai ba ta so, abun yai tsanani haka ba. amma taji fari a
ranta sosai, kuma kad'anma Asabe ta gani indai itace. A nata wautar tana ganin kamar Sadiya
bazata amince ta zauna ba.
magani ya mik'o musu.
"Ga wannan, a samu bado a dafa musu da shi, sai su cinye badon, su kuma shanye romon. Za
su samu sassaucin d'aukewar zafi."
Jiki a mace su ka fito
"Mai dambu ki kaini wajan wani bokan ko za a dace ya warware wannan asirin yaronnan ya
samu zuriya. Na cuci kaina dana biye miki, mu ka zo wajan boka. na gwammaci da dole na yi
mishi ya saki Sadiya, ko na fatattaketa da kaina, ai ina da wannan k'arfin.
"Haba Asabe, taya zan cutar da mijin 'diyata da gangan? Ni kaina bansan hakan bane zai faru.
Kina ji fa, itama kanta a cikin hatsarin take, tunda shekara guda za ta yi a cikin ciwo."
"Shifa da rayuwar duniyarshi na lalata mishi fa? mai dambu na yi nadamar saninki ma a
rayuwata, Allah ya tsine miki, ke da halinki, da masu irin muguwar nifak'a irin taki, tsinanna
matsiyaciya"
A wajan Goggo Asabe ta tafi ta bar mai dambu. Mai dambu kuwa sai kiran sunanta take yi.
"Haba Asabe, fishi ba naki bane a cikin wannan halin. ki biyo ni mu je wajan fa'da da cikawa."
Goggo Asabe, ba ta da mafita. Haka su kai ta zagaye bokaye da 'yan tsibbu, har wajan 'yan bori
sai da su ka je. Nasarar samo makarin Asirin khadija kawai aka samo. Amma Aliyu magana
d'aya ake yi, cewar gabanshi har abada bazai sake aiki ba. Iya tashin hankali Goggo tana
cikinshi. cirko cirko su ka samu mata da mazan gidan. Gabanta ne yai mummunan fad'uwa.
"Sun mutu ko? Allah sarki Aliyu ka yafe mun. mai dambu cikin kuka tace.
"Shikenan khadija ashe hanyar Ajalinki kenan.
"Ba fa mutuwa su ka yi ba" Kawu ne ya katse musu, sambatun da su ka shiga yi. tsit su ka yi.
"Ba mu gansu bane, daga Aliyun har khadija, Sadiya ma ba ta nan.
Abokin su Aliyu ne Bilya ya shigo, cirko cirko ya samu jama'ar gidan. Bayan ya gaishesu ne
yace.
"Kamilu ne ya bani sak'o in sanar da ku, sun wuce babban Asibitin cikin gari, domun ciwon bana
gida bane." Godiya kawu yai ma Bilya.
"Ni nasan wannan matar tashi uwar kilbibi ita ce zata kawo wannan gurguwar shawarar,
wannan ciwon ai ba na asibiti bane." Kawu ya ce.
"Ba komai, kai Anas sai ka zo mu tafi, zamu dawo da su gida, ga wanzan ya kawo magunguna.
Sadiya kuma sai na ci mutumcinta baza ta zo mana da iyayin zuwa wani asibiti ba. Gargajiyar
mu ta ishe mu. mutane nawa ne su ka kasa warkewa a asibiti, kuma su ka
warke a gargajiya."
SOKOTO GENERAL HOSPITAL
ba mu sha wata wahala ba, aka ba su Aliyu gado. shi ya na b'angaren maza, ita kuma tana
b'angaren mata. Likocine a kansu duka, ana kan binciken gano kan matsalar dan maganceta.
Ni kuma na kasa zaune na kasa tsaye. Ni ce a b'angaren mata, ni ce a b'angaren maza. Haka
nai ta zurga zurga. likitan dake duba khadija ne ya soma fitowa. Binshi nayi, nace da Kamilu.
"Ka tsaya a k'ofar d'akin da Aliyu ya ke ciki, ko likitan zai buk'aci ganinka kafin in dawo.
A office na samu Dr yana rubuta wasu allurai da magunguna.
mik'o mun takaddar yayi.
"A gurguje, ga Allurai da magani ki je kantin maganin dake cikin asibitinnan sai ki siyo. ana
buk'atarsu da gaggawa." Amsa nayi na fita. Ban samu magungunan a cikin asibitin ba, sai da
nai doguwar tafiya. bayan na kawo ma Dr magungunan, da alluran, sai kuma na je na bud'e ma
su fail a asibitin." Dawowata kenan. Dr ya fito daga d'akin da aka shiga da Aliyu. yace. "D'aya ya biyo ni, d'aya ya zauna da shi.
Ni na bi Dr dan inaso sanin meke damun Aliyu.
"Madam da me k'aninki ya k'one, ruwan zafi ko mai? shiru na yi na wasu mintuna. Bayani na yi
mishi Dalla dalla kan abinda ya haddasa wannan ciwon. Kai ya girgiza yace.
"Wala Allah ta yi cushe cushen magungunan da mata su ka saba yi da sunan maganin mata ne,
shine ya haifar musu da wannan matsalar. Ya samu rauni da kyailewar fatar wajan, fatar da take
ba abun kariya ta sab'ule, abune mai wahala ace, ko zai iya gamsar da mace, ko da zai yi d'in,
zai zama very wick. But za mu d'aurashi akan magunguna na sha da shafawa. Sannan
kuskurene, wannan garin maganin da aka barbad'a mishi, domun da ba dan kunyi sauri ba.
infection zai iya shiga ciwon, ya iya haifar mai da daji. Zan baki ki je phamacy a siyo Allurai da
magunguna, ki same ni a d'akin." Jikina a mace na fita, na sake shiga cikin gari na siyo
magungunan da alluran na dawo.
Aliyu ya na kwance, amma idanunshi biyu. d'akine da ba'a cika barin mace ta shigo ba. domun
maza ne a d'akin, yawanci masu d'auke da lalurar ciwon gaba ne, da masu infection, wasu ma
harda robar fitsari a jikinsu. Naga Aliyu ma an sa mishi robar fitsari. Dr na kanshi.
ledar hannuna na mik'ama Dr.
gefen Aliyu na dawo. Hannuna ya rik'e dam a cikin nashi, bai ce komai ba sai ido da ya
kafamun.
"Sannu da d'awainiya Sadiya, Allah ya saka miki da aikhairi." Kamilu ke magana. da ameen
kawai na bishi.
Allurai aka ma Aliyu, sai magani da aka bashi na had'iya, kana Dr ya shafa mishi tobe.
"A lemo mishi Abinci, domun zuwa nan da wasu mintuna zai samu bacci." Kamilu ne ya mik'e
ya ce.
"Bari in nemo maka abunda zaka ci ko" Na yi saurin cewa.
Bari in nemo mishi, zan dubo Khadija daga nan." Fita na yi daga d'akin na lek'a dakin da
khadija take, a zaune na tarad da ita. Nose na d'aura mata ruwa na biyu.
"Sannu yaya jikin? Kau da kai ta yi tace.
"likitoci tun d'azu su ka ce a nemo mun abinda zan ci, sannan likita yace ya na son ganinku.
juyawa na yi na fita. tea da biredi kawai na iya samo musu. Akwai jerin masu sai da abinci ta
waje, amma ban gamsu da tsabtar abuncin ba. Aliyu na soma kaima, na tsuguno daidai
kunnenshi nace
"Zan je in zauna da khadija, ba daidai bane a barta ita d'aya, kuma likitanta ya na jirana.
Sannan inaso in ta samu bacci zan d'an shiga cikin gari dan Allah." Hanuna ya rik'e gam yana
girgiza mun kai.
"No Sadiya kasancewarki na k'aramun lafiya, ki je dai ki ga Dr ki dawo. Baxan jure rashin naki
ba.
kan shi na shafa cikin sigar lallashi.
Toh na ji, bari in je in ga Dr din zan dawo.
Ahankali nake tafiya, harna fice a d'akin, dan na gaji sosai. wajan Dr'n khadija na isa.
"Dr gani, na shiga d'azu take fad'amun sak'onka. d'agowa yayi ya kalleni.
"Eh hakane, inaso in san meye abunda ya faru da ita? dan nasha samun ire iren casses
d'innan. Yanzu haka a d'akin da take, akwai mata fin goma, masu d'auke da lalurarta.
Sakamakon wata masifa da ta b'ullo na magungunan mata da ake ba ku ku dinga cusawa a
gabanku, kuna kashe kanku da mazajen ku da magungunan da dayawa ba'asanma dame ake
had'asu ba. wata baiwar Allah na ta ke d'akin jinyar take sanar dani, wai kashin raqumi ne ta
cusa a al'aurarta ya haifar mata da mummunan matsala kwananta talatin a cikin asibitinnan
tana jinye. Shima kuma mijin nata,