Author : Badiat Ibrahim Mrs Bukhari Category : Read Hausa Novels
ya ji ya
d'auki zafi rau.
"Ya salam haba Badiyya. yanzu abunda za ki yi mun kenan? kin sa k'afa kin shure alk'awarin da
ki ka d'aukar mun, kan Aure na bazai zama abun d'aga hankalinki ba. Gashi ba'aje ko'ina ba kin
yi ta kuka, har zazzab'i ya sauka miki." Hannu tasa ta k'ank'ameshi gam a jikinta, ahankali ta
soma sassauta kukan na ta, shi kuma ya na ta aikin rarrashinta, tare da shafa bayanta, cikin
shigar rarrashi, sai magana ya ke bata. Sai da ta tabbatar nutsuwarta ta dawo mata ta d'ago
kanta hawaye cab'e cab'e.
"Safwan rayuwata amana ta ke a hannunka, ka yi k'ok'arin zamewa namiji d'an goyo da zani.
Kar ka wulak'antani, kar ka ba da k'ofar da za'a wulakanta ni. Zuchiyata jaririyar zuchiyace,
tattali da lallab'a kawai ta sani. Na san kai mun halacci da ka zauna da ni fin shekaru goma
babu haihuwa, duk da irin gori da danginka su ke yi mun." Hannunshi ya sa ya rufe mata
bakinta da shi, cikin mutuwar jiki ya ce.
"Badiyya kishi ne ya saki subda hawaye ko? Iya k'ok'ari kin yi, kuma na yaba. Ki sani k'arin
auren da na yi ba ya nufin kin gaza ta ko ina. Wallahi na yi aure ne, dan buk'atar hakan ta taso
mun, amma ki sani ke macece tamkar da dubu. Baki rageni da komai ba. Ba na son uwar
gidana ta sake yin kuka, ki ta shi mu je asibiti." "A'a Safwan Na warke, dama fargaba ce kawai ta haifar da zazzab'in Amma yanzu ka k'arfafa
mun guiwata. Je kai kwamciyarka ka huta."
Cikin soyayya su kai sallama, kai tsaye d'akin zaure ya nufa. Mudi ne ya shiga da sallama,
hannunshi rik'e da ledar kaji da shayi mai kauri a cikin k'aramar robar fenti.
"Safwan ga shi a kai ma amarya da k'awayenta." Ya na dariya ya amsa. A kunyace yai sallama
b'arayin su Sadiya ya mik'a musu kajin. Hadiza ce ta amsa tace.
"Bari a kirawo ma Sadiyan."
Sadiya
Muna ta zabga hirar mu kamar ba dare ba, Hadiza ta shigo da ledar kaji da shayi. Da ta ajjiye
tace.
"Sadiya ki je Safwan na son ganinki."
Duban ta na yi na ce
Ni wallahi Hadiza kunyar su Goggo na ke ji, kawai sai in wuce su?
"Munafuka, duk sun yi bacci tuni, ki tsallake su ki fice kawai.
Ahankali cikin sand'a na fice a d'akin.
A jingine na same shi a garu, da ganina ya zuba mun idanunshi masu karya mun kuzarina.
Kallon da Safwan ya ke jifa na da shi na musamman ne, ni na fahimci in da kallon ya dosa."
Barka da dare angon Sadiya" Murmushi ya mun, yai k'asa da muryarshi kamar mai jin bacci
yace."
"Barka da shigowa rayuwata Sadiya, barka da sabunta mun jini da kike k'ok'arin yi gobe uwar
haka, ina miki barka da shigowa familyn Safwan Sales Gwarzo." murmushi kawai na bishi da
shi.
Matsowa ya yi daf da ni, take numfashina na ji ya na katsewa, soma jawo shi da kyar na yi
kamar wata mai ciwon asma. Hannayena ya kamo yana murzawa a hankali_ a hankali. D'umi
da taushin hannunshi su ka sanya ni bisa wani yanayi na daban.
"Sadiya ki shirya amsar Baby na gobe, ki shirya jiyar da ni dad'inki, ina mararinki Sadiya. ki je ki
kwanta, dan ki samu bacci har da na gobe."
Hannuna ya saki, ya soma ja da baya da baya. Ni kuma ina tsaye a wajan ya maishe ni tamkar
poster, har sai da na ga k'ulewarshi, na sauke numfashin da na ja. Idanu na lumshe tare da
shigewa ciki."
Washe gari aka shiga bud'ar kai. Eh lallai nasan na auri d'an dangi. Kuma abun sha'awar duk
k'anne da yayyun Safwan kamanninsu d'aya, har da wad'anda ba ciki d'aya su ka fito ba. Anty
Salaha ce ta shigo d'akina tare da Badiyya. Ina uwar d'aki da k'awayena su ka yo sallama.
"Anty Saliha kin dawo?" Murmushi ta yi mun
"Uwar gidan Safwan ce ta dawo da ni, ta na son ganinki tun jiya amma cunkoso ya hanata
ganin naki.
Da kallo na bita, iya mace Badiyya ta kai mace, tsaiwar diri da cikar k'irji kawai zan nuna
mata,farace sol. gata doguwa siririya. Ta sha kwalliya har da jan k'unshi ta yi shar tamkar
amarya. Yak'en dole na yi mata.
"Barka da isowa uwar gida."
"Ke zan yi ma barka da zuwa, da fatan ba ki yi fishi da ni ba ko?" Da sauri na girgixa kai na,
jikina ya mutu lakwas. dan ba haka na yi tsammanin ganin Badiyya ba. Katse mun tunani ta yi
da cewa.
"Ga wannan babu yawa, tawa gudunmawar kenan" Laida ta mik'o mun cike. Hadiza ce ta amsa
tare da yi mata godiya. Anty Saliha tace.
"Abincin k'awaye da aka aiko da shi, ita ta yi komai da komai." Godiya su Hadiza su ka shiga yi
mata. Har suka juya ni dai na kasa d'auke idanuna akan Badiyya. Fargabace ta tasan mun.
Gani nake Safwan ya Aure ni ne, kawai dan in haihu mishi, kuma sabida tausayin Haidar. Nan
take damuwa ta shigeni. Ina gani su Hadiza da su Goggo su ka had'a yana su yana su, Su ka wuce, Bayan sun zagaya
da ni wajan matan yayyen Safwan maza, da ma sauran dangin nashi, Anty Saliha ita ta dinga yi
mun bayanai dalla dalla. Ni ba gane komai da kowa na ke yi ba. Bayan tafiyar su Goggo. ina
k'unshe a d'aki. Yayyen Safwan suna falo dank'am Har dare. Da misalin k'arfe goman dare na jiyo Sallamar Safwan. Ajjiyar zuchiya na sauke. Amma abun
mamaki sai na ji na shak'i k'amshin turaren da ban san Safwan da shi ba." Badiyya ce ashe,
hannuna ta kamo, ni kuwa na biyota tamkar rak'umi da akala har zuwa falo.
Ita ce 'yar rakiyar Ango. Doguwar nasiha tai mana, tare da yi mana sallama.
Ta na fita Safwan ya matso jikina cikin zumud'i. Manna ni yayi a yalwataccen k'irjinshi. Idanu na
lumshe hawaye su ka kwaranyo mun, bansan na fashe da kuka ba sai da na ji, labb'an Safwan
a kan nawa, yana lallashina.
A daren babu wata hira data gudana a tsakanina da Safwan, bayan gabatar da nafila bisa
koyarwar addini, sai kaza da madara da Safwan ya baje mana, ni tsabar sanyi jiki, madarar
kawai na sha.
A cikin darennan Safwan ya raya sunna da ni, sai dai fa lallai na san na auri jarumi, awa guda
Safwan ya yi a kaina. Sannan da komai ya lafa ya murgina yai bacci. Sambatun kalmar da
Safwan ya dinga nanata mun ita ce ta sa ni na kwana cur ina kuka.
"Ki sama mun d'a Sadiya, zan baki Baby a cikin darennan, ki haifa mun kyawawan 'ya'ya." Sune
kalmar da Safwan yai ta nanata mun, sai hud'un asuba bacci ya fisgeni, idanuna duk a
kumbure. Sai ajjiyar zuchiya na ke saukewa a cikin baccin kamar k'aramar yarinyar da ta wuni
kukan rigima. "Sadiya Sadiya, uwar 'ya'yana, ki tashi ki yi sallah, shidda har da rabi."
A cikin mafarki nake jiyo sautin muryar Safwan ya na dukan dodon kunnena. A hankali na bud'e
idanuna, banko kalli in da ya ke ba, sauka na yi akan gadon, tare da fita zuwa kitchen. Risho na
kunna na d'aura ruwan zafi, wankan sallah na yi, tare da gargasa jikina.
Da sallama a bakina na shigo, ya na tsaye a gaban madubi, yana gyara tsaiwar hular shi."
"Kin fito uwar 'ya'yana?"
Eh. Kawai na iya ce mai.
"Bari in je in duba ya Badiyya ta kwana da jiki, ki jira ni kar ki yi kumallo, Innah zata aiko da shi."
Fuskata ya shafa, ya fice.
Yuuu na bishi da idanuna da suka cika tab da hawaye, ina zubar da hawaye na yi sallah, bayan
na idar zama na, na yi akan sallayar ina ta ragargazo adda'a tare da neman dacewar Aure.
Gidan na gyara ko ta ina, turaren wuta d'an tsinke 999 na kunna, ko ina ya d'auki k'amshi.
'yar kwalliya na yi a fuskata mara hayaniya. Shadda ce a jikina d'inkin doguwar riga ruwan goro.
Mayafi na yafa, na fice zuwa cikin gidan."
d'akin Innah kawai na shiga, su Anty Saliha, da su Anty Murja duk su na nan, amma da halama
shirin tafiya ma su ke yi. Farin cikinsu ya kasa b'oyuwa har akan fuskarsu, musamman Innah
wacce ta rasa inda za ta tsoma ni. A kunyace na gaishe su dukka, kaina a k'asa. Cikin fara'a da
zaulaya su ka amsa mun, Innah ta ce. " 'Yannan na ji dad'in ganinki sosai, inai miki maraba da zuwa gidannan, dama yanzu mu ke
shirin zuwa wajan na ki da su Murja da su ke shirin tafiya. Tunda kin shigo mu yi komai a nan,
Bilkisu ga Sadiya, a yi mata nasiha, sannan ki fayyace mata waye mijinta a sauk'ak'e dan ta ji
dad'in zama da shi cikin sauk'i, da ma abokiyar zaman na ta"
mrs Bukhari ce.
*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. ♀️*
1, *MU GANI A ƘASA...*
_Ummu Affan_
2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*
_Ummu Maher_
3, *GUNTUN GORO..*
_Mom Islam_
4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*
Badi'at Ibrahim
_Mrs Bukhari_
5, *AUREN WATA TARA*❤️
_Miss Hajo_
Guda biyar 1k
Guda huɗu N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda ɗaya N300
*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*
0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.
Domin tura shaidar biya
0810 433 5144
Masu tura katin MTN
0814 179 9224
Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.
0817 952 3215
Guda biyar 1000f
Guda huɗu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ɗaya 300f
*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* ❤️
Instagram links
https://www.instagram.com/p/CgPTv1-oML6/?igshid=MDJmNzVkMjY=
Facbook group
https://facebook.com/groups/463653111781414/
Telegram links
https://t.me/+xYZCR9JY-aMzNDFk
*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*
Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -
*Enter your name:* (Cikakken sunanki)
*Enter your mail:* (Email ɗinki)
*Enter an username* (Sunanki)
*Enter your password:* ( misali 12341234)
*Confirm password:* (misali 12341234)
Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks.
*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google
za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.
*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.
Masu iPhone
Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com
MRS BUKHARI
67-68
Anty Bilkisu ta ce.
"Safwan ya na da sauk'i, ga shi da d'aukar shawara. kuma ya na da kafiya da taurin kai a bisa
abun da ya sanya a gaba dan gudanarwa. Ya na da hak'uri, amma kuma akwai zafi musamman
in ki ka tab'a dangin shi, Akwai biyayya da jin maganar na gaba. Ya na wani irin murd'add'en
hali wanda in ya birkice babu mai iya gano kanshi. Abincin da ya fi so shine. Tuwon shinkafa
miyar kub'ewa d'anya da bushasshen kifi da man shanu, Baya shan shayi sai kunu, kuma ya fi
son mai tsami. Ya na da tsabta wanda a lokacin da yake yaro mu kai tunanin ko aljanune su ka
shafe shi. Matar shi Badiyya kuma ni bansan wani halinta ba. Gare ki Anty Saliha an zo wajan
ku. Dariya Anty Saliha ta yi ta ce.
"Badiyya dai ta na kirki da kawaici sosai dan ta shanye abubbuwa da yawa a cikin dangin mu,
kuma ta ba Safwan goyon baya d'ari bisa d'ari a rayuwar shi ma ba ki d'aya. Ba mu santa da
mummunan hali ba. Mu na fatan ke ma ki zama kamarta ko fin ta ma. Allah ya baku zaman
hak'uri ya kawo 'yan biyu sau hudu." Dariya mu ka yi dukka. Ina zaune a falon Innah surukan gidan su ka rik'a shigowa gaisheta d'aya bayan d'aya. Sai a
yanzu ne na ke kallonsu da kyau tare da k'ok'arin rik'e sunayensu.
Na jima a d'akin Innah ina jiran Safwan ganin bai shirya dawowa yanxu ba, na mik'e tare da yi
musu sallama.
Tare da Madina muka fito, yarinyar wajan Anty Saliha ce, tana rik'e da kwanukan abincinmu har
zuwa b'arayinmu.
Ina zaune kwalam tamkar wata mara gata, agogon dake kafe a bangon d'akin na ke ta kallo, sai
sha d'ayan rana Safwan ya shigo d'akin."
"Amarya bakya laifi, aimun afuwa Yayarki ce ta d'auke mun hankali. amma a yi hak'uri dan
Allah."
Zama ya yi a kusa da ni, tare da hamo hannaye na dukka biyun ya na murzasu. Lumshe
idanuna kawai na yi amma na kasa cewa da shi komai.
"Kin ta shi lafiya?" Sai lokacin na dube shi, fuskarshi da bakinshi duk janbaki yayi jawur. Ajjiyar
zuchiya na sauke, ahankali na zame hannayena.
Ina kwana, ya gajiyar hanya?"
Jawo ni ya yi na fad'a jikin shi a hankali, k'amshin turaren shi da k'amshin turaren Badiyya ya
cakud'e a jikinshi ya ba da wani kalar k'amshi na da ban."
"Sadiya kamar fishi ki ke yi da Angon na ki ko, ko akwai wani abun da na aikata wanda bai miki
ba? Ki sanar da ni in baki hak'uri, yanayin tamkar horo kike mun." Cikin cijewa na aro dauriya da
juriya na dangana ma kaina. Da murmushi na d'ago fuskata na dube shi. murmushi mu ka sakar
ma juna, Hannu nasa na goge mishi bakin shi da fuskar shi. Babu laifin da kai mun, sam gajiyar biki ce ba ta sake ni ba. Kuma ka sake d'aura mun wata
gajiyar....
Ban rufe baki ba, Safwan ya rufe mun da na shi, kusan minti 30 ya na muzata yanda ya ga
dama, ga ciki na babu komai.
A cikin satikan amarcin mu na murzu a hannun Safwan. ga tsaiwar dare da ya ke yi kullum kan
Allah ya dube shi ya ba shi magaji.
Ranar da na cika sati guda a gidan Safwan, har da kwana ukun da Badiyya ta k'aramun a kai.
Ranar Badiyya ta tare a d'akinta. Na ga zumud'i da rawar kai sosai a wajan Safwan, dan tun
magriba ban kuma sa shi a idanuna ba."
A shashen Innah na ke kusan rabin wuni na, kullum inai mata wanki, shara, gyaran d'aki, har
kitso da tsifa duk ni na ke yi mata. Hakanne ya d'aga darajata a idanun Yayyen Safwan maza
da mata da ma shi kan shi Safwan d'in."
Yau dai na ta shi jikina babu wani ishasshen k'arfi, ga amai da duk ya addabe ni sai ta so mun
ya ke yi, Safwan a d'akina ya ke. bayan na sallameshi ya ta fi wajan aikin da Mudi ya ne ma mai
a kamfanin shinkafar da ya ke aiki. Safwan ya na 'daya daga cikin masu d'ura shinkafa a buhu
su sa a inji ya rufe bakinta, sannan in za'a sa a mota a tafi da shinkafar zuwa store d'insu a
Bauchi. su za su yi dakon shinkafar. Lallab'awa na yi na shiga d'akin Badiyya dan muna zaune lafiya kan mu a had'e ya ke sosai,
dan duk zuk'e jikina da na ke yi, Badiyya tak'i yarda fur, a jiki ta dinga jana, kuma na ga Safwan
na k'aunar hakan dole na saki jiki da Badiyya.
"Ah Sadiya ya dai yau na ganki haka lafiya dai ko?" Sai da na zauna tukunna na ce."
Ke dai bari Badiyya rai dangin goro, yau jikin dai sai lallab'awa kawai na ke yi. Amma ya
maganar mu, dan Allah kin yi mai maganar kuwa? Na ga ya shigo nan kafin ya fita."
Dariya ta sakar mun
"Wallahi Sadiya na yi mishi magana, kuma cikin yardar ubangiji ya amince da hakan, ya ce mun
zai karb'i takaddun naki, zai je asibitin da kan shi zuwa gobe akwai abokinshi likita zai kai mishi,
ya ne ma miki gurbi, dama mu na da k'arancin mata a harkar kiwon lafiya, ni kaina sai na ji
dama na yi boko, ko dan in ba da tawa gudunmawar ga d'umbun lada da zan samu." Ajjiyar
zuchiya na sauke na dinga yi mata godiya, ita dai sai dariya ta ke yi mun.
"Amma fa ya kwab'eni kan cewar kar in fad'a miki. Sai ki ja bakin ki ki yi shiru." Magana na
bud'e bakina zan yi, wani tari me had'e da amai ya tunk'uro mun. A guje na isa madugana na
dinga shek'a amai Badiyya na kaina ta na mun sannu, na yi amai sosai a wajan. Da taimakon
Badiyya na gyara bakina da jikina da na soma b'atawa. Ita ta kaini har kan gado na. "Alhamdulullahi abun naima fa ya samu, yau zan mallaki k'aton goron albishir kenan."
Hannunta na rik'e ina haki na ce.
Badiyya dan Allah kar ki sanar da shi komai, ki bari takaddar samun aikina ta zo hannuna, na
baki dama ya ji a bakin ki."
"Toh babu damuwa, amma na yi farin ciki matuk'a. tsawon shekaru sama da goma sha muna
neman d'a amma sai yanxu Allah ya amshi rok'onmu. Sadiya ko akwai wani abun da ki ke
sha'awar ci?" Kai na girgiza mata na ce.
"Zan lallab'a in je wajan Innah akwai kunun tsamiya shi kad'ai na ke sha'awar sha." Ta ce
"Amma za ki iya zuwan? Ki huta mana" Dariya na yi mata.
Ai ba na jin ciwon komai, dama amanne ya dame ni, kuma da na yi sai na samu sauk'i, zan
lallab'a"
B'arayin Innah na wuce, a can na wuni cur, har abincin dare a can na ci, kasancewar Safwan a
d'akin Badiyya ya ke yau.
Ina zaune ina matsa ma Innah k'afa, mu ka jiyo sallamar Safwan, hannunshi rik'e da jaka, ga
Haidar na biye da shi a baya."
Na yi farin cikin ganin Haidar sosai, shima yaron ya yi farin cikin ganina, sai tumurmusata ya ke