Gishirin Zaman Duniya Book 1 Mrs Bukhari

Author :  Badiat Ibrahim Mrs Bukhari Category :  Read Hausa Novels

Chapter   8 / 33

21K to 24K   out of 98.4K words

ma. harna soma fargabar ta yanda jaririyar xuchiyata zata rayu ba mai rainonta."
gyara zama yayi ya fuskanceta da kyau.
"Dije na. Babu wani namiji da zai so ki irin rabin son da na ke yi miki. Bazan bari ki subce mun
ba. ai bazan iya gudanar da rayuwa mai dad'i ba. ko kin manta da sonki na ke rayuwa.? Nan su
ka shagala a soyayya. Suna yi ya na cin abincin da khadija ta kawo mishi. Har sha biyu na dare
bai sani ba." Da kyar su ka yi sallama da juna. dan ji ya ke yi kamar ya rungumeta su kwana a
waje d'aya. ya kasa d'auke idanunshi akan khadijar. domun ta kara mishi wani kyau ne na
musamman.
Da sallama ya shiga cikin b'arayin na shi, wanda khadija ce ta nuna mishi ma wajan.
Babu motsin kowa.
tura k'ofar d'akin yayi gabanshi na dokawa."



mrs Bukhari ce

*GAWURTATTU BIYAR,5TAFIYAR TA MUSAMANCE*



1, *MU GANI A ƘASA..*
_Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*
_Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*
_Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*
_Mrs Bukhari_

5_ *AUREN WATA TARA‍❤️‍*
_Miss Hajo_

Guda ɗaya N300
Guda biyu N500
Guda uku N600
Guda huɗu N700
Guda biyar 1k

*ZAKU TURA KUƊINKU TA WANNAN HANYAR*


Fatima Rabiu Sunusi
0037219728
StanbicIBTC Bank.


Shaidar biya tanan
0810 433 5144


Masu tura katin MTN
0814 179 9224

...........‍❤️‍....

*ƳAN NIGER GA HANYOYIN BIYAN KUƊINKU

Guda biyar 1000f
Guda huɗu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ɗaya 300f
Kai tsaye ku tura da katin Airtel ta wannan number 08141799224



*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU TAKUN FARKO*
*GISHIRIN*
*ZAMAN*
*DUNIYA*
_Daga Al'kalamin_
_Badi'at Ibrahim_
( Mrs Bukhari Ibrahim B4B)

Labari wanda yai duba kan gwagwarmayar mata a duniya. Da irin gudummawar da ilimin mace
ya ke bayarwa ga al'umma. Da kuma rawar da ilimin mata ke takawa a cikin gidajen Aure.

Kashi na 1
Babi na 17~18

Falon ya turo ya shiga. k'arema falon kallo yake ta yi. komai tsab ga k'amshin sabunta da falon
ya ke yi, ga kuma k'amshin turaren wuta na hulut sai tashi yake yi a d'akin. Mamaki ya ke ji. Yau
shine ya Auri Sadiya yayarshi, kuma duk kyan d'akinnan nashi ne. k'ofar d'akin da Sadiya ta ke
ciki ya tura, cikin fad'uwar gaba. Yana son shiga Amma yana jin nauyinta sosai.
Sadiya
Da sauri na share hawayena, nai saurin kulle idanuna. Kunya na ke ji in sake ma ganin Aliyu."
Da sallama a bakinshi ya shigo. A cikin zuchiyata na amsa mishi sallamar tashi. gabana sai
sake tsananta bugu ya ke yi. Tamkar wacce aka kama ta yi k'arya. Ajjiyar zuchiya na ji ya sauke
da bansan ta meye ba. shiru ya na tsaye a inda ya ke. Amma ina jin tsinin idanunshi a jikina. Da
dukkan alama k'arema surata kallo ya ke yi." k'ut ya had'iye tsinkakken yawunshi da ganin
surata ya tsinka shi. tudun kirjina kawai ya ke bi da kallo ba ko k'ibtawa. ina kallonshi ta k'asan
idona. sai ajjiyar zuchiya ya ke saukewa a jere a jere.
Aliyu kuwa tunda yai arba da Sadiya a kwance cikin goduwar rigar bacci, a take ta kwance shi.
surarta wacce ta tsaru ya ke kallo. bai tab'a ganin cikakkiyar mace mai cikakkiyar sura irin
Sadiya ba. kirjinta yafi komai jan hankalinshi. yana hangosu ta cikin riga suna k'ara burgeshi.
lumshe idanu yayi. Sadiya.
Ni kuwa duk halin da ya ke ciki ina gani. kallo na kai kan wandonshi daya cika yai fam. har wani
danshi na gani a jiki. Da sauri Aliyu ya juya ya fice a d'akin. akan kujera ya zauna tare da dafe
kan shi. mararshi na wani juya mishi.
Ajjiyar xuchiya na sauke. Kwanciyata na gyara tare da juya ma k'ofar shigowa d'akin baya.
amma abun takaici da haushin na kasa samun bacci sam. damuwowin da su ke damuna yawa
garesu sosai.

Aliyu
kwanciya Aliyu yayi a saman kujera. ya na rik'e da mararshi. Bai tab'a jin wani abu mai zurfi
haka game da mace ba sai akan Sadiya. lumshe idanu yayi. hoton kirjinta suna sake haska
kansu a cikin duniyar tunaninshi. mararshi ya kuma rik'ewa sosai tare da sakin nishi a hankali. A
cikin daren dai daga Sadiya har Aliyu Babu wanda ya runtsa. Hakanne yasa su ka wayi gari da
matsanancin ciwon kai mai zafi. Sadiya har bata iya bud'e idanunta da kyau.

Sadiya
kiraye kirayen Sallar Asuba ne ya mik'ar dani daga kan gadona. fitowa na yi falon. Aliyu na gani
a kwance a kujera Bacci ya fisgeshi. wandonshi na bi da idanu. sai da gabana ya buga. A take
tsoro da fargaba ya kamani. Maganar Amina ce ta fad'omun da tace NAMIJI BAYA KAD'AN

naga halama. bud'e idanu Aliyu ya yi fes a kaina. Akan kirjina idanunshi ya sauka. Ni kuma duk
na dibibice dan kunya. cikin in ina nace.
Dama dama naji za'a shiga Sallah ne. shi ne ka je masallaci."
" Toh" kawai ya iya ce mun. Da sauri na wuce band'aki na d'auro Alwala na fito. ina shiga Falon
Aliyu ya mik'e ya fita."
Sallah na soma yi. Ina jiyo fitar shi daga gidan.

Aliyu
yana tafe ya na tunanin taya zaije d'akin Goggo ya ce ta bashi kaya zai sake da asubar nan?
Gashi bazai iya zuwa wajan kamilu ya ce ya bashi kaya ba. Dan hakan tamkar tona asirin auren
su ne. Duk da dai Kamilu ya zarce aboki a wajanshi. Amma wannan wani sirrine da yake a
b'oye. hakan cikin taraddadin abunda zai faru yai k'undunbalar shiga b'arayin su Goggo. tura
k'ofar d'akin Goggo ya yi a hankali tamkar b'arawo. A falo ya samu Goggo idar da sallarta
kenan. da sauri ya tsugunna dan karta kama danshin dake jikin wandonshi, wanda ya fito ta
cikin jallabiyar jikinshi, ga Jallabiyyar ta kunbura. kai ya sauke kunya ta lullub'eshi ya ce.
"Barka da Asuba Baba Ina kwana?" Harara ta zabga mishi tana bin yanayin da ya zo mata da
kallo. cikin zargi tace."
"Ka aikata abunda na haneka da aikatawa ko k'usar yak'i?" Kuka ta fashe mai da shi tace.
"wallahi tsinema zan yi insan na sallamama duniya kai. Da kuma Sadiya. Sai ka koma.Aisha ta
zama uwarka." bakinshi na rawa ya ce.
" Babu abunda na aikata. wallahi a falo ma na kwana." Ajjiyar zuchiya ta sauke. dan tasan Aliyu
ba ya k'arya. Balle kuma ya rantse ma. Tace.
"Akwatin kayan na ka ya na can an kaima ita Sadiyar."
"Toh" kawai ya ce.
"Aliyu" ta kira sunanshi da manyan bak'i. Harya kai bakin k'ofa ya tsaya.
"Kar ka manta gobe da safe ka tawo mun da takaddar sakin Sadiya. karka shigo sai da
takaddar."
Bai ce komai ba ya fita. Da sauri ya wuce b'arayinsu. Hasiya ce ta bishi da harara.

Sadiya
ina zaune ina karatun Qur'ani cikin suratul maryam. ya shigo da Sallamar shi. A hankali na
Amsa. Kaina na k'asa na ce.
"Barka da asuba an tashi lafiya?. Jin dad'in shi har ya kasa b'oyuwa a fuskarshi. cikin kulawa ya
ce.
"Lafiya lau Anty. Amma bari na yi sallah sai in zo mu gaisa a tsanake." Wajan Akwatinshi da ya
gani a gefen sip ya wuce.
Jallabiya ya zaro da wandonta. Sannan ya koma falo ya wuce band'aki yayo wanka. Sallah ya
yi. Mik'ewa yayi. ya soma nad'e kayan na shi. Daidai fitowata. Ahankali na ce.
Dama ka barshi." Da murmushi ya ce.
"Babu damuwa Anty. Zo ki zauna mu gaisa." dukkan mu a kunyace muke magana. Amma
kasancewar shi namiji ne harya soma sakewa.
Zama na yi a saman kujera. Na yi shiru ina sauraronshi. Shima shirun ya yi. Sallamar da aka
doko a bakin k'ofar d'akin ce ta katse shirun.

Anas ne. Da dauri Aliyu ya fita.
"Yaya Anas? Rungume juna su ka yi cikin tsananin murna. Anas ya d'agoshi daga jikinshi ya ce.
"Aliyu kaine ka zama babban mutum haka? kai kawai ya sosa yana dariya.
"Yaya naga kowa amma banda kai da yaya Dauda."
"Kaidai ka bari. masu sayan hatsine daga Zamfara su ka shigo. Shine mu ka tsaya a kansu sai
da aka gama komai. Ni da Dauda mu ka lissafi. Kusan buhu talatinne ba mu samu ba. Ana
yawan yi mana satar da ba mu da masaniyar ko waye a cikin gidannan. Ni da Dauda ne ke rike
da makullin rumbun." "Aliyu ya ce idanu za'asa sosai Yaya. Tunda dai a cikin gidane. Kai amma ko waye ke yin
wannan b'arna bai kyauta ma kanshi ba. mu shiga daga ciki mana Yaya."
"Wanne ciki kuma? tsarabata kawai za ka bani malam." Dariya Aliyu yayi. Tare da zura takalma
yace.
"muje tsaraba na d'akin Baba ai. Su murtala suna almajirci har yanzu basu gama ba ko? Ficewa
su ka yi a gidan nawa. sai da na dena jin muryarsu sannan na mike.
Kitchen na nufa. Na yi tsaye ina tunanin shin mai zan girka a matsayin abincin safe?" shiru na yi
can sai na tuno bari kawai in dafa kuskus tunda bani da d'anyen kayan miya a hannuna. cikin
k'ank'anin lokaci na dafa kuskus dina. Ta yi warawara sosai abun sha'awa. kula na sake
farkewa na zuba ma.Aliyu. ruwan wanka na d'aura minti goma yayi akan wuta na juye. Rishon
na rage tare da d'aura dumamen miya.
Cikin minti Talatin na gama kintsawa. ina sanye cikin wata jar atamfa hightaget. Dinkin diga da
siket. Atampar ta amsheni sosai ta kuma dace da kalar skin dina. Dan jan abu na haska bak'i
sosai. Kitchin na koma na kashe miyar. zubawa na yi a cikin kular Aliyu ta miya. Sannan na
zubama Goggo Asabe nata. a basket na jera komai. takalmi flat shoe ne ja a k'afata. bak'in
mayafi na yafa. Sabida atamfar da bak'in kala akai mata ado.
fitowa na yi babban tsakar gidan. Da Hasiya na ci karo ta na k'arema takuna kallo. Shewa na ji
ta yi tace.
"Allah ya wadaran naka ya lalace. An salwantar da budurci dole a fito babu d'ingishin komai. Mu
kuwa a ranar da komai ya faru munfi sati muna jinya." Da sauri na dubi Hasiya. Tana rik'e da
k'ugunta da ganin fuskarta a cike take da ni. Karasawa nayi har inna take nace.
Wannan jahilcin naki ya soma isata. Ya kamata kisan ni ba sa'arki bane, sannan ni ba kishiyarki
bace balle in zama abar tsokanarki. Ya isheki na Fad'a miki kenan.
Tafi Hasiya tayi tace.
"ke ce dai jahila wacce ba ta san me ke yi mata ciwo ba. wacce ta kasa auruwa a maraya
kawai. Kuma ki sani duk wani wanda ya ci ciwo da ni miya yasha."
"miyar ma bazai gane ya sha ba. "Wato ke Sadiya rashin kunyar taki har takai ki zagarmun
mata a matsayinta na matar.wanki? Dauda ke magana daga bakin k'ofarshi.
"Toh ki sani mu a gidannan baza mu d'auki raini da iskancinnan naki ba. Maras kunyar kawai. Ai
dama barewa baza ta yi gudu d'anta yai rarrafe..... Kafin ya idasa na daka mishi tsawa.
"Dakata cin kashin ya tsaya iyakar kaina. Kar ka kuskura iyayena su shigo. Dan zamu yi uwar
watsi. iyayena sunfi mun kowa da komai a daniya." Da sauri Dauda ya nufoni Banyi Aune ba na
ji saukar hannunshi akan fuskata ya zabgamun marin da saida idona ya makance na wucin
gadi. ya sake d'aga hannu zai sake sauke mun . Da sauri na tare fuskata Ina jiran inji a inda
hannun nashi zai sauka. sai na ji shiru. Ahankali na bud'e idona. Aliyu ne a tsaye ya had'e

ranshi hannun da Dauda ya d'aga zai mare ni Aliyu na rik'e da shi. Rannan nashi a murtuke.
"Ba daidai bane dukan mata. Balle macen da take matar Aure. Danme za dukar mun mata?
Bakasan darajarta bane ko me? Ina daraja matata bazan ba da wata k'ofa da za'aci kashi a
kanta ba, domun a k'ark'ashin kulawata take, kuma hakkinane kula da mutumcinta. Kai wane
girmanka ya dace ka rik'e. Dauda ya fisge hannunshi ya na nuna Aliyu da yatsa jikinshi har
rawa ya ke cikin d'aga murya ya ce.
"Akan wannan karuwar 'yar bokon ka rik'emun hannu a matsayina na Yayanka. Kuma ba tare
da ka yi tambaya akan wanne irin rashin kunya ta yi ba?" Bilkisu ce ta fito dan taji ana hayaniya
har da ihu. Ganin abunda ke faruwa ne ta zame jikinta.zuwa b'arayin Goggo Asabe ta sanar
mata. Ta wuce wajan kawu ta sanar mishi. Aliyu ya rintse ido, dan kalmar karuwa ta gigita tunaninshi ya ce.
" Babu buk'atar sai na ji me ta yi maka. Amma ai kasan ba matarka bace. Matata ce kuma
inasonta duk karuwancinta. Domun y'ar uwata ce ita, Anty bakiji ciwo ba ko?."
"Ai kuwa wallahi baka isa ka ci gaba da zama da ita ba yau ba sai goben ba Auranka da Sadiya
ya k'are." cewar Goggo Asabe wacce ta iso ita da kawu da matanshi. Gabana ya yanke ya fad'i
take na soma zubda hawaye. Isowa ta yi gabana tace.
"Makirar 'yar duniyar mace. Harkin juya mishi kai kenan yau k'usar yaki ne ke yin fad'a.
Fad'anma da wanshi. yaron da ya samu shaidar jama'a a gari bai tab'a fad'aba. Shine da
zuwanki kin soma haddasa husuma ko. Kinaso ki raba shi da danginshi kamar yanda uwarki ta
raba mu da d'an uwanmu. wallahi Allah ba ki isa ba." Nidai ina tsaye jikina har rawa ya ke yi.
Aliyu yace.
"Baba zuwa na yi na tadda ya mareta fa. me yasa zai d'aura hannu a jikinta matar Aure ce fa."
"Auran wa? kama daina kallonta a matsayin matar Aure dan indai nonona kasha toh sai ka saki
Sadiya yau d'innan ta koma wajan muguwar uwarta." Kawu yace.
"Ke Sadiya ba su fad'a miki doka da tsarin gidannan bane akan girmama kowa ba? kuka na ke
yi sosai kukan da ba na ma iya ganin kowa. cikin shesshek'a kuka na ce.
An fad'amun. Amm"
"Dakata Sadiya iyakar abunda na tambaya kenan. Dauda ya ce.
"kuma fa fitowa na yi sai na ji ta na zage Hasiya. Har da ma Goggo Asabe. Shine daga magana
ta hau zagina. kuma ita ta soma marina." cikin kururuwa Goggo da Fatima su ka rufu a kaina da
duka kakaf kakaf. ina tsugunne ina kuka. ko yunk'urin guduwa na kasa yi. Aliyu duk ya bi ya
rud'e Goggo ya ke ta ba hak'uri. Amma ta k'i fur. Sai da tai mun lis bakina da hancina duk sai
yayyon jini ya ke yi sannan ta na huci tace.
"Shegiya maras kunya fitsararriya. kai kuma ka kawo takaddarta yanzu ina jiranka ko kaga mai
zai biyo baya. Shashasha mai fad'a akan macen da bata cancanta ba." Fuuu ta fice a gidan.
Kawu kuma ya ce.
"Kai Dauda kar ka sake dukanta. Kome ya faru ka kawo gaban manya. Kai kuma Aliyu ka bi
umarnin mahaifiyarka kar tai ma baki."
watsewa kowa ya yi ya barmu. Zuchiyar Hasiya da Bilkisu fes dan murna. Aliyu ya zuba mun
idanunshi da suka kad'a su ka zama jawur, tausayina tsantsa na gani a idanun Aliyu, kuma ko
ba komai ya daraja auranmu, ya kuma kira ni matarshi. Wani sanyi naji a zuchiyata.

mrs Bukhari ce
*GAWURTATTU BIYAR,5TAFIYAR TA MUSAMANCE*



1, *MU GANI A ƘASA..*
_Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*
_Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*
_Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*
_Mrs Bukhari_

5_ *AUREN WATA TARA‍❤️‍*
_Miss Hajo_


Guda ɗaya N300
Guda biyu N500
Guda uku N600
Guda huɗu N700
Guda biyar 1k

*ZAKU TURA KUƊINKU TA WANNAN HANYAR*


Fatima Rabiu Sunusi
0037219728
StanbicIBTC Bank.


Shaidar biya tanan
0810 433 5144


Masu tura katin MTN
0814 179 9224

...........‍❤️‍....

*ƳAN NIGER GA HANYOYIN BIYAN KUƊINKU

Guda biyar 1000f
Guda huɗu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ɗaya 300f
Kai tsaye ku tura da katin Airtel ta wannan number 08141799224



*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU TAKUN FARKO*
*GISHIRIN*
*ZAMAN*
*DUNIYA*
_Daga Al'kalamin_
_Badi'at Ibrahim_
( Mrs Bukhari Ibrahim B4B)
GAWURTATTU BIYAR




Labari wanda yai duba kan gwagwarmayar mata a duniya. Da irin gudummawar da ilimin mace
ya ke bayarwa ga al'umma. Da kuma rawar da ilimin mata ke takawa a cikin gidajen Aure.


*INA MIK'A SAK'ON GAISUWA GA DUKKAN MASOYAN LITTAFIN GISHIRIN ZAMAN DUNIYA,
HAK'IK'A NAJI DAD'IN ADDU'ARKU GARENI. GISHIRIN ZAMAN DUNIYA YA D'AUKAKA FIYE
DA TUNANINA, YA TSALLAKA INDA MA BANYI TUNANIBA. TUN JIYA NAKE TA SAMUN
SAK'ONNI DA KIRAYE KIRAYEN MASOYANA. INA GODIYA SOSAI, ALLAH YA BAR K'AUNA.*

Kashi na 1
Babi na 19~20

Kallona ya sake yi cikin tausayi da tausayawa. Hannunshi ya saka ya d'agoni tsaye. Tare da
jinginani da jikinshi. wani irin shocking mu ka ji a jikin juna. wata wawuyar ajjiyar zuchiya na
sauke, tare da haki, ga bakina a fashe sai jini yake zubarwa Hannu yasa rik'e mun k'uguna,
ahankali ya soma tafiya. Har d'ingishi nake yi tsabar azaba." Hasiya ta na lab'e ta na cizar
yatsa. Domun ko a mafarki Dauda bai tab'a mata hakanba. ko a Zamanin amarcinta Sanda
gishiri ya ke kan kaza kenan. Ko yau ta ji mamaki da ya shigar mata fad'a. Dauda ne dake

bayanta, inda take a lab'e ya ce.
"malama matsa zan wuce in kin

8 / 33