Gishirin Zaman Duniya Book 1 Mrs Bukhari

Author :  Badiat Ibrahim Mrs Bukhari Category :  Read Hausa Novels

Chapter   22 / 33

63K to 66K   out of 98.4K words

turnik'eni,tuni hawaye ya
gama wanke mun fuskata, ni daman nasan akwai wani abu a cikin dawon da.Aliyu ya sha, da
nasan da wani abun a ciki da ni na sha na mutu Goggo ta huta ai. Muryar Iya ce ta dawo dani
daga nisan da xuchiyata ta yi.
"Asabe akwai wani abunda kika aikata kenan akan mutuwar Aliyu ko? cikin nishi Goggo tace.
"Iya na cuci kaina, Tabawa ta kashe ni, mai dambu ta cuceni. ita ta kaini wajan bokan da zai
zubar mun da cikin Sadiya, na zuba a cikin dawo, ashe Aliyu ne zai sha. mai dambu kuma ta
kaini wajan 'yan bori aka bani maganin da zai kassara rayuwar Sadiya. Iya Aliyu ne ya fad'a
halin jinyar da bai ma warke ba ya rasu." Kuka ne ya ci 'karfinta, nima fashewa da kuka nayi, da
gudu na bar d'akin ina haki.
"Lallai Asabe kin cika jahilar uwa, mara tsoron Allah, kin kasa d'aukar wannan auren a matsayin
k'addara, kina wasa da auran da akwai rabo a cikin shi, Asabe har rashin imanin naki yakai ki
iya aikata wad'annan abubbuwan da kika aikata? Toh Aliyu ya bar doron duniyar, sai ki zuba
ruwa a k'asa kisha ya rabu da Sadiya, rabuwa irinta har abada. kuka ta fashe dashi, tace. "Amma Allah wadaranki Asabe, Allah ya tsine masu hali irin naki, ni kinga tafiyata" Iya ta suri
jakar ledar ta ta fice, batai ma kowa sallama ba a gidan." Fatima da take zaune a wajan, a
gabanta aka tattauna komai tace.
"Baaba amma baki kyauta ma Aliyu ba, yaron da yake yi miki biyayya sosai, gashi kin kasheshi,
nima kin zugani inai ma mijina rashin kunya, kin kashe mun aure na, kin raba ni da yarana,
Aliyu kuma kin rabashi da duniya da, d'iyarshi ko 'danshi da za'a haifo a matsayin maraya."
kuka ta fashe da shi, me ciwo. Goggo kuwa hawaye ya gama jik'e pillown da take kwance a
kai.

Sadiya
jikin Goggo Hansatu na fad'a tare da rikice mata da kuka, ina fad'in nidai tazo mu bar gidannan.
Da kyar Goggo Hansatu ta rarrasheni na dawo Hayyacina, fayyace mata duk abunda Goggo
tace na yi, ta tsorata sosai, kuma ta sake ganin amfanin ilimin mace, dan wannan aikin jahilci
ne.

kwanci tashi asarar kwana
yau cikina yana da wata takwas, yayin da Aliyu ke da wata bakwai a kwance, ga laulayin ciki, ga
rashin miji duk sai na had'e na lalace sosai, nayi wata muguwar rama, ga b'aki da na kuma yi,
babu a duniya abunda ke mun dad'i. duk kwanan duniya mutuwar Aliyu sabunta kanta take yi.
Dan dare da rana a cikin rok'a mishi rahamar ubangiji nake. Goggo kuma tasha jinya mai tsayi
har da kwanciya gadon asibiti, amma yanzu ta warke sumul, saidai ta dawo shiru shiru abun
tausayi, tayi rama sosai sai dai ta bi jama'a da ido kawai. khadija kuma ta na gidansu har ta
mance da Aliyu a rayuwarta, ta sake ta na harkokinta na yau da kullum.
Rayuwa kenan. matar Yaya kabiru, da matar Anas sun samu juna biyu, yayin da Hasiya ita
kuma kullum jaraba ita da abokiyar zaman nata, sun haddasama Dauda deeprecion, domun
kullum a cikin tashin hankali da tunani yake, ko wacce yai mata saki guda guda, ya korasu
gidan tsofaffinsu. cikina na kwata takwas da kwana goma sha biyu, na tashi da safe, sai na soma jin halamun
nak'uda na ke yi, da kad'an kad'an, ni anguwar zoma ce, na tabbatar wannan haihuwace,
Goggo Hansatu wacce yau kwananta uku da zuwa na sanar ma, babu shiri ta had'a kayan
Babyn da na bata kud'i ta shiga kasuwar Zamfara ta harhad'o mana. Ina rik'e a hannun Goggo
Hansatu ina d'an cijawa, Goggo Asabe tace."
"Hansatu Lafiya kuwa, ina zaku je da kaya a cikin riyo da jaka?" Goggo Hansatu tace."
"Nak'uda ta soma ji, shine za mu yi hanzarin zuwa asibiti, dan a can zata haihu." Nan fa Goggo
Asabe ta dirar mata.
"Ai mu a gidannan bama xuwa asibiti, canjan yara su ke yi, ko kuma su kashe muku d'a, tun
daga kan margayiya Zainab matar wannan yaron aka dena zuwa Asibiti a gidannan, kasheta su
ka yi, abunda ta haifa ma su ka kashe, ranar munga tashin hankali." Goggo Hansatu tace.
"Hak'uri za ki yi Asabe, akwai had'ari babba a ce mace zata haihu an barta a gida, musamman
haihuwar fari,yanda akeso ma, ko a gidan ka haihu sai ka tafi asibiti, dan a duba lafiyarki data
jaririnki, ki yi hak'uri, a samu wacce zata raka mu kawai." Fur Goggo Asabe ta k'i, da k'arfin tsiya
Goggo Hansatu ta fige ni a hannun Goggo, kamar za su yi dambe, ta tasa k'eyata muka fice. Ni
dai ba bakin ma magana. kafin mu isa asibiti, nak'uda zanga zanga, dan da k'yar na iya
k'arasawa cikin harabar Asibitin, a harabar na kakare. wai ashe haka haihuwar take?

Goggo
sai raraka fad'a ta ke yi, har zuwa shashen Goggo Safiya tace.
"Safiya ki xo mu je, mu gani da idanunmu dan kar su yi mun canjan jika, Hansatu ta figi hannun
Sadiya zuwa Asibiti, ki fito muje." Goggo Safiya tace
"Ba mu ci ta zama ba, muje kinji" mik'ewa ta yi, ta sa mayafi su ka fice. A wajan hawa babur ne
suka had'u da Kamilu yace.
"Baaba gari zaku shiga? Goggo Safiya tace.
"Matar aminin naka ne haihuwar taxo. Cikin gigicewa yace.
"Yaushe? ko d'azu naje na duba lafiyarta fa. Goggo tace
"Ai kasan nak'uda, yanzu haka suna asibitin birni. kamilu yanke uxirin da ke gabanshi yayi, ya
ma manta matarshi ce kwance ba lafiya, daga lamba yake, ya siyo mata kwayar bature. Tare da
shi su ka wuce zuwa asibitin.

Sadiya
Ina cikin labour room na had'a mugun zufa, idanuna duk sun firfito waje, sai cije baki da rik'e
baya na ke yi. Adda'a kam duk wacce tazo yin ta kawai nake, Nafi awa biyu ina abu d'aya. tun
ina iya nishin har ma na dena, marata kuwa ta d'auki d'umi tamkar zata tarwatse. ruwa da allurai
sunyi mun babu adadi, a hankali nace da wata anguwar zoma. "Ku yi mun tiyata k'arfina ya k'are bazan iya haihuwa ba." tace
"Gaskiya ne madam, bari in samu mijinki yasa hannu sai ayi miki tiyatar kema ki huta, ga matan
da su ka zo su ka same ki a d'akin duk sun haihu, har sun tafi 'dakin hutu."
Tana fita su Goggo na isowa.
"waye mijin Sadiya, ya biyo ni." Kamilu bai tsaya kwana kwana ba ya bita. Goggo Asabe ta
harari Goggo Hansatu tace
"Bata haihu ba har yanzu?
"Eh wallahi tukunna dai, amma in sha Allah ta kusa. Goggo Asabe tace.
"Allah yasa yarinyarnan ta haifi abunda ke cikinta lafiya, yaronnan yazo duniya ko zanji sanyi, in
ina kallon Aliyu a fuskar jaririn."
"Malam Hannu zaka saka mana, dan baza ta iya haihuwa da kanta ba, bayan dubawa da mu ka
yi, sai mu ka gano kamar 'yan biyu ne a cikin nata, zuwa wani d'an lokaci in bata haihu ba,
zamu shiga da ita tiyata" inda zai sa hannun aka nuna mishi ya saka, cikin tashin hankali ya
dawo wajan su Goggo"
Sadiya
wani nishi ne naji yanayin kan shi da kanshi, k'arfen gadon da nake na rik'e, kamar yanda muke
ce ma mata su yi, jaririne ya sunb'ulo, amma kafin in kai dubana ga abunda na haifa, sai na ji
sabuwar nak'uda zanga zanga, amma ba tai tsawo ba, na sunkuto yarinyata. Numfashi na shiga
saukewa a hankali, hawaye sai zubo mun suke yi, ana yanke musu cibi aka manna mun su a
jikina. Sai lokacin na bud'e idanuna na dubesu.
Kau idanuna ya d'auka, gabana yai mummunar Fad'uwa da ganin irin abun dana haifa. Runtse
idanu na yi na sake bud'ewa. Tabbas zahiri idanuna suka nuna mun, rungumesu na yi sai na
fashe da kuka, aduk yanda suke sai naji son su na bubbud'e mun k'ofofin jinina. ina son su,
kamar yanda ko wacce uwa take son abunda ta haifa. Amma ina mai cike da tausaya musu, a
yanda na haifesu, ga kuma maraici, ko ya za'a amshesu a matsayin 'ya'ya oho, dan al'umma
mugun kyamarsu da tsangwamarsu suke yi, ni kuma bazan iya juran ganin marayun yarana a
irin wannan halin ba. Nose ce ta zare su a jikina, ta fita da su, ina kwance ana kwashe mun jini,
mutuwar Aliyu ta dawo mun d'anya, yaranshi sun fama mun mikin dake zuchiyata. Kuka na ke yi
sosai.

mrs Bukhari ce

*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. ‍♀️*

1, *MU GANI A ƘASA...*
_Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*
_Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*
_Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*
Badi'at Ibrahim
_Mrs Bukhari_

5, *AUREN WATA TARA*‍❤️‍
_Miss Hajo_


Guda biyar 1k
Guda huɗu N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda ɗaya N300

*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*

0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.

Domin tura shaidar biya

0810 433 5144

Masu tura katin MTN

0814 179 9224

Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.

0817 952 3215

Guda biyar 1000f

Guda huɗu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ɗaya 300f

*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* ‍❤️‍


Instagram links

https://www.instagram.com/p/CgPTv1-oML6/?igshid=MDJmNzVkMjY=


Facbook group

https://facebook.com/groups/463653111781414/


Telegram links

https://t.me/+xYZCR9JY-aMzNDFk


*YADDA AKE BUƊE ACCOUNT A AREWABOOKS*

Bayan kaje play store ka ɗakko ya sauka a kan wayarka. Za'a cike Form ɗin kamar haka: -

*Enter your name:* (Cikakken sunanki)

*Enter your mail:* (Email ɗinki)

*Enter an username* (Sunanki)

*Enter your password:* ( misali 12341234)

*Confirm password:* (misali 12341234)

Sai a taɓa *Sign Up* shikenan an buɗe account a ArewaBooks.

*Continue with Google* - Idan kana da gmail/email akan wayarka kawai Continue with Google
za'a taɓa zata buɗe maka account a ArewaBooks kaitsaye.

*Register* - Shine cike form domin buɗe account a ArewaBooks.

Masu iPhone

Zaku iya bibiyar shafinmu
https://arewabooks.com
G Z D
MRS BUKHARI
51~52




"Baiwar Allah ki dena kuka akan abunda kika haifa su ma fa mutanene kamar kowa, kuma suna
rayuwa mai tsayi kamar kowa, ki taso in raka ki d'akin hutu." Bance da ita komai ba, ni ba kukan
kyautar da Allah yayi mun nake yi ba, in na yi hakan ai tamkar na butulcema kyautar da Allah ya
bani kenan, ga mata da yawa na neman haihuwa Allah bai basu ba. Aliyu ne ya dawo mun
d'anye. Gado ta nuna mun, da dabara nahau kan gadon, ina ta kallon matan da muka haihu a
d'aki 'daya da su, ko wacce ga mijinta a kusa da ita, ana basu kula amma banda ni. Allah ya
jik'an ka Aliyu, Allah ya isar da haske kabarinka. Ga yaranka nan Aliyu, in sha Allah duniyar
musulunci za su yi alfahari da su, ba zan bari su yi maraici ba. Hawaye na na share, dan na
hango tahowar Su Goggo.
Sannu su ka shiga yi mun, na kasa amsa kowa, sai kuka na nake had'iyewa, amma ina. da
kuka na fashe mai tsanani, kowa na wajan sai da ya tausaya, domun sun fahimci halin rashin
Aliyu nake, dan an riga an sanar musu na sauka lafiya, Allah ya azurta ni da mace da namiji.
"Ki yi shiru Sadiya, tsakanin ki da Aliyu sai adda'a, dan ma Allah ya nufi zamu ga jininshi."
Goggo Safiya ke rarrashina. kamilu yayi shiru daga gefe sai bina da idanu ya ke yi. wasu
ma'aikatan kiwon lafiya ne, su ka shigo da yaran a hannunsu, daya an sa mai saiti fari, dayar
kuma ovaroll mai kauri da hula aka saka mata, a cikin bargo d'aya aka nannad'esu, kasancewar
kayan mutum d'aya mu ka tawo da shi. Goggo Asabe da murna ta amshi yaran a hannun
wannan Nose d'in, dayar kuma ta nufo ni dan ta duba lafiyata."
"Wayyo Allah mutane ko aljanu? Goggo hannunta na rawa ta saki yaran a k'asa, su ka fad'i
tum. Idanu na rintse, dan wani irin abu na ji a zuchiyata mara misaltuwa. Kuka na fashe da shi,
da Sauri Goggo Safiya da Goggo H su ka nufi jariran da kukansu ya cika ward d'in da muke.
Amma ganin yaran yasa Goggo Safiya ja da baya, Goggo Hansatu ce, ta yi k'arfin d'aukar yaran
ta rungume a jikinta tare da aikin jijjigasu.
Suna kafad'ar Goggo H, Kamilu ya je ya lek'a fuskar yaran.
"Allahu akbar" shine kalmar da ta fito a bakin shi, mutanen d'akin sai bin mu da kallo su ke yi.
"Ke Hansatu, wad'annan yaran aljanu Sadiya ta haifa? Ji yara kamar yasan sarkin aljanu, tsabar
fari" cikin zafin xuchiya Goggo.H tace.
"zabiya ne Allah ya bata, amma ai ko ba ku tab'a ganin zabiya ba, ai bai dace ki yar da jarirai
haka a k'asa ba.
Goggo Asabe da muryarta har rawa take tace.
"Wallahi Allah ban tab'a ganin zabiya ido da ido ba, nasan dai 'ya'yan k'azanta ne, wanda aka

haifa a k'azance." Kai Goggo H ta girgiza kawai, za ta yi magana, wata nose ta k'araso tace.
"Dan Allah a ara mana jariran za mu d'an k'arashe gwaje gwaje a kan su." Goggo H tace.
"Akwai wani damuwa ne a tattare da yaran?
"A'a Baaba, kinsan su irin wannan bayin Allah yawanci masu lalurar ido ce, ba su cika gani
sosai ba, idanun nasu za'a duba dan a san a wanne matsayi suke." Goggo ta mik'asu, ni dai na
yi shiru na zuba ma sarautar Allah idanu.
Bayan kamar awa guda da fita da jariran da aka yi, ina zaune ina shan tea da kamilu ya sawo
mun a waje, Dr ya shigo, a gabana ya tsaya ya dube ni.
"Maman biyu ya jikin na ki?"
Da sauk'i. kawai na ce mishi, ruwan da ke d'aure a hannuna ya cire mun sannan yace.
"ke kam mun sallame ki, Amma twins mun basu gado a b'angaren yara, zuwa gobe zamu tura
ku zuwa asibitin sokoto, dan acan za su fi samun kulawa." kwarewa da tea d'in nayi nan na
shiga tari, aka shiga yi mun sannu.
Sai tsiyayar hawayen tausayin marayun zabiyan yarana nake yi, nan nace.
Allah ya jik'an ka Aliyu, da rabon ba zaka gana da kyawawan yaranka ba." Dr ya zuba mun
idanu. su Goggo dukka kowa ya dubi Likita. Kamilu yace
"Dr me ya same su? bayan ya gama cire mun ruwan yace.
"Basa gani sam, kasan zabiya da ma da matsalar idanu, toh wad'annan ganin ma basa yi,
amma zan tura ku zuwa babban asibiti, dan a yi musu bincike da kyau, tunda sunfi nan kayan
aiki, nima ina aiki a can d'in." Kuka na fashe da shi sosai. Nan jikin kowa yayi sanyi kowa ya
tausaya halin damuwar da nake ciki. D'unguma mu ka yi d'akin da 'yan biyu su ke kwance.
D'akin yarana, ga sunan lalurori iri iri, jarirai da na'urar numfashi, wasu da roba ta hancinsu, ga
wata yarinya itama a kusa damu abun tausayi, uwar sai kuka take yi. Dr na ke kallo yanda naga
yana juya Husaina abun ya tsorata ni, bayan ya gama aune aunen shi. sai kawai ya juyo ya
dube ni tamkar mai jin tsorona yace.
"Allah ya amshi rayuwarta ita kam." Sumewa ne kawai ban yi ba, amma duk mai tausayi saiya
zubar mun da hawayen tausayi. inaji ina gani, Su Goggo Asabe, da Goggo Safiya su ka tafi da
gawar Husaina, da k'yar su ka iya rik'eta.
Jikin Goggo H na fad'a na kuma sau kuka.
Goggo yanzu shikenan itama yarinyar mahaifinta ta bi kenan, itama rasata na yi? Allah na gode
maka, ubangiji ka bani ikon cinye wannan jarabawar, shi kuma wannan bawa naka ka raya mun
shi da imani." Hawaye na na share, na saki Goggo H wacce itama kukan ta ke yi, take wani
dangana gami da juriya su ka saukar mun, ban sake yin kuka ba. Da yamma Dr ya sake shigowa duba mu, duba na yayi.
"Yaron ya farka kuwa?"
A'a bai farka ba tukunna, kuma k'alau ya ke? murmushi ya yi mun.
"k'alau ya ke ba ya d'auke da wani ciwo in ba ciwon idanunnan ba. ki same ni a office zan
rubuta miki allura a je a siyo." Juyawa yayi ya fice. Goggo H tace.
"Toh maza jeki, ko ni zani, sabida yanayin jego ga ba ruwan zafi. Murmushi na yi mata nace.
"Babu damuwa bari in je, zan iya.
Wuce wa na yi zuwa waje, dai dai ya b'ille wata kwana, ahankali na ke jan jikina, dan har jiri
nake ji, babu abunda nake buk'ata face ruwan zafi. Ko da na b'uulla inda naga yabi, ban ganshi
ba, gashi ni bansan sunan shi ba. haka na gama bukayi na, harna juya zan koma sai na ji yace.

"Gani nan Halima" Da sauri na juyo, yana tsaye a baya na, yace.
"Jikin ki baya miki dad'i ko? Nace
"Babu damuwa, akwai magungunan da zan siya dan kare lafiyar jikina, in sha. Da mamaki yace.
"Kina da ilimin hakan kenan? Bance mishi komai ba, takaddar allurar ya nuna mun, amma bai
ba ni ba, yace
"Ki koma, zan kawo miki, shima wanda zaki sha d'in zan kawo miki, kije"
Wuce wa na yi, ina shiga na tadda Iya da Anty Ramatu sun iso, da ruwan zafi a flaks da
abincinsu. Hassan yana hannun iya tana tofe shi da adda'a.
"Sadiya sannu da jiki, ayi hak'uri da yanda aka tsinci kai." murmushi kawai na yi, na gaishesu da
ladabi, buta Goggo.H ta mik'a mun.
"Ungo je ki kama ruwa ki ji dadi, ga abinci mai nauyi kici, kafin yaronnan ya tashi, dan nono zai
naima afujajan." Iya tacs.

22 / 33