Gishirin Zaman Duniya Book 1 Mrs Bukhari

Author :  Badiat Ibrahim Mrs Bukhari Category :  Read Hausa Novels

Chapter   5 / 33

12K to 15K   out of 98.4K words

ina biye da ita a baya
har zuwa falon Goggo Asabe. wasu mata na gani da gani K'awayen Goggo ne. sune su ka
rakani d'akina. a falo su ka zazzauna. nasiha su ka shiga yi mun. sannan su ka yi sallama su ka
fice. da sauri na bud'e mayafina. ina hawaye Goggo Hansatu ce ta matso kusa da ni. da sauri na
fad'a kirjinta nai lamo. kau ta ji jikina da zafi rau. nan hankalinta ya tashi.
"Sadiya kin kuwa sha maganinki kuwa, kin ma ci abinci kuwa?
kai kawai na iya girgiza mata dan a mugun galabaice nake. Amina ce ta shiga kitchen ta kunna
risho. ruwan zafi ta d'aura mun da zan yi wanka. ina zaune kusa da Goggo. kaina na d'aga na
kalli rufin d'akina. lantarki mai yin chaji da hasken rana na gani a manne. kamar kwan wuta ya
ke, ya na da haske sosai. kuma ya na rik'e chaji. ajjiyar zuchiya na sauke dan na d'anji sanyi a
raina. rufin d'akin na sake kallo inaso in tantance da me aka rufe saman d'akin. naga dai abu
bak'i zare zare a jere ras. da kyar na gane igiyar dake cikin video kaset ne wannan bak'in mai

d'an fad'i na ciki. Goggo Hansatu ce ta katse mun tunani na da cewar.
"Sadiya mu je in nuna miki toilet ki yi wanka. ga shayi ki sha sai in baki magani."
mik'ewa na yi. na bita a baya. langa langa ta nuna mun ta ce.
"ga toilet d'innan ki shiga ruwan na ciki."
to.
kawai na iya ce mata.
na shige toiket d'innan ya sha plasta ya yi kyau. ga shadda irinta gargajiya mai k'aramin baki.
cikin nutsuwa na yo wankan tare da d'auro alwala na fito.
bedroom na shiga dukkansu su na ciki. wadrope d'ina wacce ta cika bango guda na bud'e. kaya
na su na jere reras. doguwar rigar bacci mai sauk'i na sanya. turare na fesa a jikin rigar. sannan
na yi sallah. Hadiza ta mik'amun tea a kofi mai kauri, dan har kayan tea duk sun siyo mun
manyan gwangwamaye. ahankali na ke sha har na shanye. sannan na sha magani. ina jin su suna ta tab'a hirarsu da
ban dariyar jama'ar k'auyannan, yanda su kaita tururuwar zuwa ganin d'akina. ganin hakanne
yasa har na d'an sake. a lokacinne na samu damar karema d'akin kallo. iya ha'duwa ya tsaru ko
a birni d'aki ne na azo a gani. tabkeken gadone 6 by 7 fararene kayan katakon sai ratsin gold da ke jiki. wadrope dina
babbace mai kofa shida, sannan ga dresing mirror na a gefe harda kujerar zaman kwalliya.
labulayen d'akin kuma gold colour ne. haka ma kafet din dake malale a cikin uwar d'akin shima
kalar gold ne. falona kuma kujerune kirar Royal masu kalar gold da ja. manya manya ne sosai daga gefe
kuma show glass ce me biyu da abun 'daura tv a tsakiya. show glass dinnan ta sha roses da
kiristal masu kyau sai tv na a tsakiya aka ajjiyeshi da video a k'asan shi. kafet ne ja malala a
kasan falon haka labulayen falon jajayene masu kyau. falon ba tarkace sam abun sha'awa. Goggo Hansatu tace.
"Sadiya hauro ki kwanta kinji. kuma ya kamata mu bar hirar nan haka nan gobe za'a d'auki
hanyar gida kuma.
koda na kwanta na kasa bacci sam. sai tunane tunane na ke yi. babu abunda ya fi tsaya mun
sai zancan Auran Aliyu bayan dawowarshi da wata guda. idanu na lumshe a raina nace.
"yau ni ce a tsakankanin masoya biyu na shigo rayuwarsu ba tare da sun shirya ba. na rusa
musu duk abunda su ka jima su na tsarawa. Haka nima duk wani tanadi da tsara yanda zan
gudanar da rayuwar aurena, da yanda zan gigita mijina da soyayyar da saina juya mishi
k'wak'walwa, yanxu duk ya kau. Na auri d'an k'auye yaro k'arami.Da wanne idanunma zan iya
mishi kallon miji. Shin yama rayuwar k'auyan zata kasancemun?
haka nai ta tunani. sai jefin asuba bacci yai awon gaba da ni.

WASHE GARI
tun sassafe na yi wanka. sanye nake da shadda mai ruwan k'asa. dinkin riga da siket yasha
surrani da milk colour d'in zare. d'inkin ya zauna a jikina sosai. kwalliya na yi mai tsari, jikina
kuma sai tashin kamshi ya ke yi. takalmi ne mai tsini a kafata milk colour, haka ma mayafin
jikina ya kasance milk. Goggo Hansatu tace. " su Hadiza su raka ki ku gaisa da ayagin surukarki da matan gida. kafin su d'au haramar tafiya
kuma. dubanta na yi nace.

Goggo kema yau za ki tafi?
"A'a Sadiya. zan zauna sai nan da kwana hud'u ranar da Aliyu zai dawo sai in tafi. a k'alla zan
d'ebe miki kewa.
da'di naji sosai da jin bayanin Goggo.
fita mu ka yi da su Hadiza. mu na tafe ne nace.
Hadiza lallai Bashir yayi kok'ari daya barki ki ka zo bikina tun daga katsina. gaki har kauyenmu.
dariya Hadiza ta yi tace.
"Haba Sadiya ai muna tare. abinda na ke so dake shine. karki sake kallon rayuwar da ki ka
gudanar ta baya. Sadiya abu guda mace take buk'ata a rayuwarta shine ta samu kulawa da
tausayi a gidan mijinta. in gidan aure ya samu wannan toh magana ta k'are. ni shawarar da zan
baki shine. ki kawo walwala da farin ciki gidan auranki. ki gaiyato haske da raha a zamanki
da.Aliyu. ke wayayyace kinsan meye makamar d'a namiji. idan ki ka yi hakan zaki samu
nutsuwar da sai kauyannan ya zame miki tamkar America.
kai na kad'a. maganarta gaskiya ne.
Hakane Hadiza zanyi kokarin hakan. amma wannan sai mun samu fahimtar juna tare da shi.
kinsan yaro ne, dole al'amuran ba za su zo mun da sauk'i ba. ni wallahi kunya ma nake ji.
Amina tace
"shi namiji ba ya kad'an. ni mijina sai da na shekara d'aya a hannunshi ba mu'amalar Aure. sai
dai mu yi wasa da juna kawai. gaban na shi ashe ya na da matsala. sai da ga baya ne ya samu
lafiya. amma ba wanda yasan wannan labarin sai ku da na sanar ma yau. shi namiji ba'a
shekaru bane. kar ki yi girman kai ki je ki shiga wuta a banza." hirar ta mu ta tsaya ne, a sakamakon isowa b'arayin su Goggo Asabe. da sallama mu ka shiga
falon Goggo Asabe. duk yayyan Babana su na ciki, da alama tattaunawa su ke yi. gurfana mu
ka yi a gabansu mu ka gaishesu da girmamawa. sun amsa a sake babu laifi. kawu Sulaiman
yace. "Sadiya. sai ki sake hakuri nan da kwana hudu mu ke sa ran Aliyu zai dawo. ki kula dan baza
mu yadda da fitsara irin taku ta 'yan boko ba ma su ido a tsakar ka. Aliyu kuma dole ki mai
biyayya domun duk shekarunki da matsayinki kin dawo karkashin ikon shi ne. kar kuma ki ji
wani iri. bayan wata guda da dawowarshi za'a d'aura Auranshi. gyatumarki ma ta san da hakan.
akwai dokoki da k'a'idoji akan ko wacce surukar gidannan. dan haka za ki iya samun Bilkisu.
matar wan Aliyu ta yi miki bayanan daya dace.
A sanyaye na ce.
Toh kawu zan yi hakan in sha Allah.
Su Goggo Asabe a cikinsu ba wacce ta ce da mu uffan. sai daga baya Goggo Asabe tace.
"Toh ki koma d'akin ki. magana mu ke yi.
dole na kalato murmushi na d'aura ma fuskata nace.
Toh Goggo.
jiki a mace mu ka fito. mun d'an zazzaga cikin gidan Bilkisu ce tai mana jagora. tare da gabatar
mun da surukan gidan. gaggaisawa mu ka yi da kowa. sai dai da dukkan alama ban samu
karb'uwa ba sam a wajansu. Dan sai wani hararata suke yi, su nai mun kallon banza haka.
komawa mu ka yi b'angare na. Sallama muka soma jiyowa ta namiji a k'ofar b'arayina. Hadiza
ce ta fita.
"Sannu baiwar Allah, kune k'awayen Amaryar tamu ko? Hadiza da dariya a fuskarta tace.

"Eh mune"
Murmushi yayi yace.
"Sunana Kamilu, nine aminin Aliyu, tun jiya naso in zo dan mu gana da ku, toh sauran abokan
namu suna waje, dama a game da sallamar k'ayawyene, bisa ga al'ada."
Hadiza tace.
"Hakane, sai ku bayar da duk abunda ya sauwak'a, jiya ma baku kawo mana abinci ba" kai
Kamilu ya sosa.
"Eh ayi mana afuwa, sai yau na gama harhad'o kan abokan, Amma ga abun kari." Hannu tasa
ta amsa, leda ce mai d'auke da gasassun zabi, sai robar fenti cike da tea, wanda sai da Kamilu
ya fita zuwa cikin zamfara ya siyo kayan tean. nera dubu biyar ya mik'ama Hadiza"
"Ga wannan ayi hak'uri, abun yazo mana babu shiri."
"Ah babu komai mun gode" ciki Hadiza ta dawo ta kawo mana kayan kari, tare da yi mana
bayanin yanda su ka yi da Kamilu. bayan sun gama karyawa, sun yi wanka. sai kuma su ka fito
dan tafiya.
ina kuka mu ka rabu da su. tare da mun al'kawarin za su kewayo ni.
Goggo ce ta ri'ke hannuna mu ka koma ciki. kan gado na fad'a ina ta kuka amma mara sauti.
wai wanne irin matsalolin zan fuskanta ne a wannan zaman Auran?



mrs Bukhari ce

*INA MAI SANAR DA MASOYA CEWAR, LITTAFIN GISHIRIN ZAMAN DUNIYA, YA K'UNSHI
ABUBBUWA DA DAMA WANDA YA SHAFI MATSALOLIN DA MATA KE FUSKANTA A
GIDAJEN AURE TA FUSKA DA DAMA. DAN HAKANE ZAN BUGASHI A TAKADDA, DOMUN
KO WACCE MACE TA MALLAKESHI. KUMA A WAJENA KAWAI ZA'A IYA SAMU, INA KAN
HAD'A LIST NA JAMA'AR DAKE SON LITTAFIN, KAFIN IN BAYAR DA AIKIN BUGAWAR, IN
KINASON MALLAKAR NAKI A TAKADDA BA TARE DA KINSHA WUYAR BINSHI SHAFI
SHAFI BA, KI YI MUN MAGANA IN SAKA SUNANKI DOMUN A BUGO HARDA NAKI, INA
MARABA DA KU MASOYANA. SAI NA JIKU.*

*GAWURTATTU BIYAR,5TAFIYAR TA MUSAMANCE*



1, *MU GANI A ƘASA..*
_Ummu Affan_

2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*
_Ummu Maher_

3, *GUNTUN GORO..*
_Mom Islam_

4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*
_Mrs Bukhari_

5_ *AUREN WATA TARA‍❤️‍*
_Miss Hajo_


Guda ɗaya N300
Guda biyu N500
Guda uku N600
Guda huɗu N700
Guda biyar 1k

*ZAKU TURA KUƊINKU TA WANNAN HANYAR*


Fatima Rabiu Sunusi
0037219728
StanbicIBTC Bank.


Shaidar biya tanan
0810 433 5144


Masu tura katin MTN
0814 179 9224

...........‍❤️‍....

*ƳAN NIGER GA HANYOYIN BIYAN KUƊINKU

Guda biyar 1000f
Guda huɗu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ɗaya 300f
Kai tsaye ku tura da katin Airtel ta wannan number 08141799224



*MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU TAKUN FARKO*

*INA MATAN MASU AMSA SUNANSU NA MA, INA UWAR GIDA, INA AMARYA, INA 'YAN
MATA 'YAN KWALISA?* *HAK'IKA DUK MACEN DATA ISA, SAI DA K'AMSHI DA GYARAN JIKI
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI. 'YAR MUTAN KATSINAWA NAZO MIKI DA SIHIRTACCEN
K'AMSHIN DA ZAI JIJJIGA MIKI OGA, TA YANDA OGA ZAI LIK'E MIKI.* *SUNAN WANNAN
K'AMSHIN MANNE MATA, MAK'ALE MATA* * *WASU KUMA SUKAN KIRASHI DA D'AYE
MANNA* 'YAN MATA AKWAI NAKU HAD'IN NA DABAN.

*AKWAI KULACCA TA SUDAN*
MAI SIRRIN K'AMSHI DA GYARA FATA, GA UWA UBA SA LAUSHIN JIKI, DA KUMA
DAWWAMAR DA K'AMSHI A JIKIN FATA.

*AKWAI SIHIRTACCIYAR HUMRA, 'YAR SUDAN*
WACCE AKAI MA LAK'ABI DA 'YAR BAIWA MAI ABUN MAMAKI.
ITA KUMA TADA SHA'AWAR ME GIDA TAKE YI, TARE DA K'ARA DANK'ON SOYAYYA, DA
KUMA DAWO MA DA MATA MARTABARSU. UWA UBA AN HAD'ATA NE DA ITATUWAN
GYARAN JIKI, DA KUMA SIRRIN K'AMSHI MAI MOTSO SHA'AWAR DUK WANDA YA
SHAK'ETA.
BAN TSAYA IYA NAN BA.
AKWAI TURAREN KWANCIYA, WANDA AKE SHAFAWA A MATSE MATSI, DA SAMAN CIKI.

KE DAGA JI KINSAN AKWAI AIKI, DAN MAI GIDANKI SAI K'ARA SONKI DA KUMA MAK'ALE
MIKI.

INA DA TURARE D'AN GASKE NA TSUGUNNO, MAI FARFAD'O DA MARTABA DA KIMAR
GABAN MACE, K'AMSHI YA DAWWAMA A WAJAN, YANA SAUKAR DA NI'IMA, YANA KASHE
INFECTION, YANA MACE MACE TA HAD'E TSAM. YANA K'ARA D'AND'ANO.

INA HAD'A TURAREN FANT 'YAR UWA, WANNAN MA WANI SIRRINE NA MUSAMMAN

TA B'ANGAREN KAYAN MATA KAMA DAGA NA NI'IMA, NA INFECTION,DAMA NA MATSI IRI
IRI. DA DUK WANI MAGUNGUNAN MATA A KWAI SU, 'YAN GASKE, MRS BUKHARI 'YAR
MUTAN KATSINAWA TA ZO MUKU A SHIRYE TSAB.

AKWAI SETI NA MAI JEGO, WANDA YA K'UNSHI KOMAI DA KOMAI A CIKI.

KANA AKWAI SETI NA AMARYA, ITAMA NA MUSAMMAN NE, YANA D'AUKE DA
INGANTATTUN MAGUNGUNAN JIJITA ANKO.
'YAN MATA WANDA SUKE SHIRIN SHIGA DAGA CIKI KUMA AKWAI NAKU SETI NA
MUSAMMAN.

AKWAI MAN DILKAR GYARAN JIKI NA AMARYA, DA SABULUN AMARE NA MUSAMMAN

*BANGAREN TURARUKAN WUTA NA INA NAN*
*TURARUKAN D'AKI, DANA KAYA, DA TURAREN GASHI, DA TURAREN WANKA, TURAREN
MOPPING, TURAREN WADROPE, TURAREN BAYAN GIDA. KUJERAR TSUGUNNO,
KABBASA, DUK INA SIYARWA. DOMUN NEMAN K'ARIN BAYANI TU TUNTUB'I MRS
BUKHARI 'YAR MUTAN KATSINAWA. 08179523215
saina ji ku
*GISHIRIN*
*ZAMAN*
*DUNIYA*
_Daga Al'kalamin_
_Badi'at Ibrahim_
( Mrs Bukhari Ibrahim B4B)
GAWURTATTU BIYAR



Labari wanda yai duba kan gwagwarmayar mata a duniya. Da irin gudummawar da ilimin mace
ya ke bayarwa ga al'umma. Da kuma rawar da ilimin mata ke takawa a cikin gidajen Aure.

ina mik'a sak'on gaisuwar ban girma ga masoyan littafinnan, kuma aminaina na arxiki.


Maman Yaseer Kina k'arfafamin guiwata Hajiyata.

Anty Yabi yunusa Kin bani gudunmawa ta musamman ina jinjinar ban girma.

oum shuraim 1 Dear ke tawace har abada

oum shuraim 2 Godiya ta musamman gareki

ummu safais ina jin dad'in comments

Aisha Auwal godiya nake yi

Ban mance da 'yan amanata ba
kabo dota.
khadija Beebee
Ta marad'i
Atitin mama
Anty faty Rayyana
Mrs Abdul
Anty Baraka

Mmn Nour
ummi Barwa
Soopy ta yanzu
Da duk masoyan wannan littafin da basu ji sunayensu ba, kuyi hakuri abunne da yawa.

Bazan manta da iyayen gidana ba

ANTY HADIZA BARA'U GIDAN IKO.

FAUZIYYA D SULAIMAN

SUMAYYA ABDULK'ADIR TAKORI

ina mik'a gaisuwata gareku

Kashi na 1
Babi na 11~12

Goggo Hansatu ce ta dafa baya na. ta ce da ni.
"Haba Sadiya. kar ki bari shaid'an ya yi miki wasa da zuchiya. ki dena kuka, kar ki ji kinyi dana
sani akan kasancewarki a wannan k'auyan. iliminki zai fi amfani a wannan k'auyan. ba mu san
mai Allah ya ke nufi da had'a wannan Auran ba. k'ila ta dalilinki Gishirin zaman duniya ya
yawaitu a wannan karkarar. Aliyu kuma kisan yanda za ki yi, ki ja hankalinshi gareki. nasan kinyi
girman da kin riga da kin san ta kan duniya. ki yi amfani da iliminki. ki dena duban shi a
matsayin k'aninki, tunda k'addarar Aure ta maida ki k'asanshi. dole shine jagoranki, kuma
shugaba a gareki, kiyi k'ok'arin k'irk'irarma kanki farin ciki da kwanciyar hankali, Aliyu masanin
addinine bazai salwantar da hakkin daya rataya a kanshi ba. ki gode ma Allah mijinki zai dawo a
matsayin malamin Addinine. Ba jahili kamar Asabe uwarshi ba."
baki Goggo Hansatu ta dinga ba ni. tare da yi mun musalan matan da su ka sha gwagwarmaya
kuma daga baya su ka samu nasara. Allah ya d'aukaka su, har tauraruwarsu ta haska duniya ta
san da zamansu. da misalan matsalolin da mata su ke fuskanta a gidajen Aure. har da ma
gararin da yaran jahilar uwa su ke fa'dawa, da kuma shafarsu da jahilcin uwar ta su ya ke yi.
tad'aura da cewa.
"Shi rayuwar Aure. Sanyi da taushi ce. Ba zafi da Haushi ba. shi zaman Aure hak'uri da juriya
ne. Ba rashin ha'kuri da mita bane. Miji d'an lallashine, ba abun tsokanar fad'a bane. Sadiya in
ki ka bi da Aliyu ta hanyar daya dace. sai ya zame mijin alkhairin da ba lallai samarin ki na
maraya su zame miki ba. sha'anin zamatakewar Aure ya tab'arb'are ba irin na mu na da bane.
amma da yawan tashin hankula da fitintunun da su ke tashi a gidan Aure. kaso mafi tsoka
matsalar daga matan mu na hausawa ne. Bance mazan basu da laifi ba, dan sun d'auki kaso
mafi rinjaye, tunda sun fimu kaifi hankali da tunani. ke kam kina da ilimin da ni kaina ina alfahari
da kasantuwarki d'iyata. Sadiya kar ki yi saken da Aliyu zai soma amsar Budurcin waccan
yarinyar da zai Aura. domun shi daren Farko na musamman ne, a rayuwa. duk sanda zai tuno
da macen daya soma jin d'uminta a rayuwarshi. toh ke zai tuno. kuma za ki samu Babban

matsayi na musamman a matsayinki na uwar gidan Aliyu. Ban sanki da taurin kai da raini ba."
wunin ranar kab Goggo Hansatu ta na yi mun jawabai ne na yanda zan gyara rayuwar Aure na.
kuma na ji dadin hakan matuk'a. Hakan ya wawuce mun kaso mafi tsoka na damuwar dake
addabata.
washe gari da safe.
bayan na yi wanka. ina sanye cikin atampar soso. jikin atamfar bak'ine, sai manyan fulawa
jajaye da aka k'awata atampar da shi. kwalliya na yi me kyau. Goggo Hansatu tace.
"Sadiya na ji dad'in yanda jawabai na su ka shige ki. shine gudummawata ta bikin ki da ban
bayar ba. kuma na ji dad'in yanda naga annuri a fuskarki, kuma kin saki jikinki sosai, tare da
rungume k'addararki hannu bibbiyu, ina fata da rok'on Allah yasa hakan ya zame miki alkhairin
duniya da lahira, ki samo tikitin shiga aljannah a hannun Aliyu." murmushi kawai na yi mata. tabbas na d'auki dakon duk shawarwarinta domun babu na
yadawa. amma a xuchiyata akwai wani miki da bansan yaushe zai warke ba na soyayyar
Ahmad da yai ma rayuwata raunin da bana jin akwai namijin da zai iya warkar mun da wannan
raunin. k'addarata kam na amsheta. domun bazanyi jayayya da buwayar Allah ba. Goggo hakane. in

5 / 33